← Book details Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 58

Sashe 34

Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tambayar da Baban Adnan ya yi kenan da ya sani kai dubana gefen da na ka an fi cika, idanuna suka sauƙa akan Asabe da take yashe a ƙasa tana fitar da numfashi a wahale, cikinta ya yi jajir tun daga wuyanta har zuwa gadon bayanta ruwan ya ƙona ta, rigar dake jikinta ya manne a fatarta tamkar tare suka zo. Babu shiri na runtse idanuna sakamakon rawar da jikina ya soma yi tsikar jikina yana tashi.
"Duk taron yawan nakun nan a rasa wanda zai iya kai ta asibiti tun lokacin da abin ya afku, sai dai ku cika gidan ku yi cirko-cirko akan ta".
Furucin Baban Adnan kenan cikin zallar takaicin da ya cika masa birnin zuciyarsa, kafin kowa ya yi magana Maman Adnan ta yi caraf ta amshe zancen tamkar wacce take jira ya ce kulle ta ce cas.

"To kai ina ruwanka? Waye ya aike ka balle ya ga daÉ—ewanka?. Kai ka san abin da ita Asaben ta yi ta yi mata haka?".

Ba ta ƙarisa ba sakamakon marin da Baban Adnan ya sharara mata, daman an yi masa shaida a kaf cikin unguwan nan da kewayenta babu wanda ba ya shakkan dukan matarsa fiye da shi. Ko a gaban waye ba ya shakkan kai mara bugu ko da dalili ko akasin hakan.
"Ki bar ni na yi aikina yadda ya dace wannan ba abin da ya shafe ki ba ne". Furucinsa ya sanya kowa shiga tarairayinsa, tunin ya ba da umarnin a wuce da Asabe da take kwance magashiyan rai a hannu Allah zuwa asibiti.
Ita kuwa Maman Vector da na ji an ce ita ta yi aika-aikan aka maka mata ankwa suka tisa ƙeyarta. Mutuwar tsaye na yi don har aka fice da ita na gaza motsawa daga inda nake tsaye balle na yi wani yunƙurin barin wajen ban dawo daidai ba har sai da Amira ta dafo kafaɗuna.

"Ki je ki huta. Don matsalar gidan nan ba mai ƙarewa ba ne". Kaina kawai na iya ƙarfin halin jijjiga mata kafin na soma jan ƙafafuna da nake jin su tamkar ba sa cikin sassan jikina haka na isa ɗakinmu ba tare da na san inda nake cilla ƙafata ba, na iske Umma ba ta nan ko wanka ban yi ba na sauya kayan jikina zuwa na Islamiyya don lokaci ma ya riga da ya ƙure na fito na yi wa Amira sallama na tafi, sauri nake yi tamkar zan kife akan karan hancinsa ina isa cikin islamiyyan ana fara tarar masu zuwa latti ko aji ban wuce ba na nufi wajen Malam Suleiman a makare.
Tun kafin na iso na hango Aliyu Shehu ya fito daga cikin staff room ɗin malaman muna haɗa ido da shi ya ƙara murtuƙe fuskarsa daman can ba shi da annuri ko kaɗan kullum fuskarsa a haɗe take tamkar magribar ɗinya. An yi ittifa'i a duk cikin islamiyyan babu wanda yake ji da kansa da tunƙaho da fariya da ilminsa kamar sa.

"Dalla malama ki ɗago ƙafa, kin san ai ke kaɗai ake jira amma kike wani tafiya a hankali kamar ba ki san ana jiran ki ba".

Ya yi zancen cikin ɗaga murya ta yadda zan ji, na ƙara saurin da nake yi ina sowa wajen ya juya ya koma ciki na bi shi a baya har cikin staff room ɗin, da sallama na shiga wanda ta amsawar Malam Suleiman da na Malam Aminu sai kuma Al'amin Yakubu. Sai da na zauna kana na gaishe da su suka amsa.
"Amatullah ya ya aka yi kika makara haka?".
Tambayar da Malam Aminu ya jefo mini kenan da ya tursasa mini sadda kaina ƙasa saboda tuno munin abin da wakana, sai da na aro jarumta na yafawa kaina kafin na iya faɗin"Malam a yi haƙuri".

"Ba batun haƙuri ba ne Amatullah yanzu gabaɗaya kina ƙoƙarin komawa baya akan lamarin karatunki. Ga shi kuma aski ya zo gaban goshi". Jikina ya ƙara yin sanyi ƙalau na kasa cewa komai sai Al'amin ne ya kare ni da kalamansa.
"Malam in ba za ta faɗi gaskiyar abin da ya faru ba ni zan faɗa maka". Na yi hanzarin ɗago idona ina kallonsa sai dai ya ƙi yarda ya haɗa ido da ni, maimakon hakan ma sai ci gaba da ya yi da maganarsa.

"Malam na haÉ—u da ita a hanya kafin na iso, wata yarinya mai talla ce abin da take sayarwa ya zube shi ne ta tsaya ta taimaka maka. Kuma ta rakata har gida gudun kar a yi wa yarinyar faÉ—a".

Murmusawa kawai Malam Aminu ya yi tare da cewa"to Allah ya kyauta". Duk muka haÉ—e baki wajen amsawa da amin kafin Malam Suleiman ya soma jawabinsa.
"Mun tara ku anan ne saboda maganar zuwan baƙonku Sheikh Dawood bikin walimarku. Bayan shi akwai sarakuna da masu muƙamai a jihar nan da za su halacci wajen don aka mu na ku nutsu ku yi karatu mai kyau, domin tabbatar da ingancin karatun da kuka samu daga islamiyyar nan. Sannan kamar yadda muka sanar da ku a tsakaninku ne za a cire gwarzon shekara, ɗalibi mafi ƙwazo da kuma wanda ya zo na ɗaya".
Tun kafin ya gama maganar Aliyu Shehu ya soma murmushi tare da cewa"Malam ai ba za mu ba ku kunya ba, kuma in sha Allah wannan shekarar ma ni zsn cinye dukkan waÉ—annan kambun".

Kalaman Aliyu suka sani ɗago idona na saci kallonsa, mutum ne shi ma matuƙar son ganin ya kewa kowa akan komai. Shekara uku kenan a jere shi yake lashe kambun ɗalibi mafi ƙwazo a islamiyyar gabaɗaya, a bikin yaye wasu ɗaliɓan ma ya kan yi majinta balle kuma nasa, wannan dalilin ya sanya ni cire duk wani buri a raina.

"Amatullah kasancewar ki mace É—aya a tsakaninsu dole idanu za su dawo kanki don haka ina so ki yi karatu mai kyau kuma cikin nutsuwa".
"In Sha Allah Malam".

Dariya Aliyu ya fashe da shi da hakan ya ja hankalinmu zuwa gare shi, Malam Suleiman ya tsawatar masa.
"Dariyar me ye kake yi?".

Ya ladabtar da murya"tuba nake yi Malam, wani abun na tuna".

"Za ku iya tafiya mun sallame ku".

Godiya muka gabatar musu muka tashi za mu fita Malam Aminu ya ƙira suna na juyo ina sauraron abin da yake faɗa.
"Ki shiga aji huɗu ki karɓa haddansu. Yau Malama Khadija za ta sama zuwa ba".
Cikin girmamawa na ce"to Malam". Na juya na fita har na yi ɗan nisa na jiyo muryar Aliyu na tsaya har ya iso gabana ya tsaya har da naɗe dukkan hannayensa a ƙirjinsa.

Na bi sa da kallo tun daga ƙasa har sama, ƙal-ƙal uniform ɗinsa yake ya sha goga ga ƙamshin wani sanyayyan turare da yake tashi daga jikinsa, hularsa taɓa ni ka sha hadisi fara sol sai sheƙi take yi.

"Tunanin me ye kike yi?".

Na yi masa wani kallo guda na ɗauke kaina tare da cewa"tunanin me ye kuwa zan yi?". Ya murmusa kafin ya ce"tunanin yadda za mu fafata da ke mana, tun wuri ki sauƙaƙawa kanki yawan damuwa don ba za ki taɓa cin nasara akan Aliyu Haidar ba, tun shigowata islamiyyar ni nake yi na ɗaya kuma na lashe kambun ɗalibi mafi ƙwazo a duk shekara, na yi bajinta a shekarar wasu ma balle shekarar walimarmu. Har na bar Islamiyyar nan babu abin da zai sauya wannan tarihin don haka ma kar ki sa a ranki".

Taƙaitaccen murmushi na saka kafin na sama zarafin cewa"Aliyu kenan!. Ai kai ya fi dacewa na ba wa shawarar ka cire tunani daga cikin ranka don da dukkan alama kai hakan ya dama. Ina yi maka fatan nasara a ko yaushe ni ka ga tafiyata". Ina ƙare faɗin haka na bar wajen na nufi aji huɗu domin karɓan haddarsu kamar yadda Malam Aminu ya umarce ni, har na yi na gama raina a ƙutume na yi musu ƙari na fito lokacin har an tashi sallan asr don haka kai tsaye na wuce wajen alwala na zauna na zabga tagumi abin duniya duk ya fi ya ishe ni.
"Ke lafiyarki kuwa? Yau ki haÉ—uwa ba mu yi ba".

Na tsinkayo muryar Rauda a kusa da ni na zame hannayena daga tagumi da na rafza ina saki tagwayen ajiyar zuciya wani na bin wani.
"Wallahi na fara gajiya da abin da Aliyu yake yi mini a ciki islamiyyar nan".
Ta kafe ni da ido alamar son ƙarin bayani"wani Aliyu kenan?".

"Aliyu Shehu mana".

Ta taɓe baki kafin ta soma cewa"kin san Allah Amatullah wannan Aliyun sonki yake yi, matuƙar so ma kuwa. Ke in taƙaice miki bayani mazan ajinsu sun taɓa kama sa yana rubuta sunanki jikin ƙur'aninsa". Wani kallo na watsa mata da ya sanya ta haɗiye sauran zancen ba tare da furta su ba.
"Wani irin banzar magana ce haka Rauda? Sanin kanki ne babu wanda ba ya ƙaunar ci gaba na a cikin islamiyyar nan kamar Aliyu. Ko wani abun bajinta na yi sai ya ƙalubalence ni akan hakan ki na nufin wanda ma duk cikin so ne kamar yadda kika yi ikirari?".
"Ko waɗannan ba su kasance alamomin so ba to tabbas akwai soyayyarki mai ƙarfi a cikin zuciyar Aliyu. Shin ke ba ki lura da wani abu, duk yadda ƴan matan islamiyyar nan suke yi masa shishshigi baya kula su amma ke ko kina so ko ba kya so sai ya nema hanyar da zai yi magana da ke ko da kuwa baƙar magana zai faɗa miki".

Na miƙe kafin na furta"Rauda mu bar wannan maganar don hankali ba zai taɓa ɗaukarsa ba". Ban jira abin da za ta kuma cewa ba na tafi na soma yin alwala na zo na yi salla har iddar tana zaune a cewarta tana fashin salla a lokacin tare muka koma aji muka soma muraja'a cike da shauƙi da soyayyar abin da muke karantawa. Har sai da aka tashi ba mu sani ba sai da muka zo daidai inda muke son tsayawa kana muka yi addu'a kowa ya fito domin tafiya gida.
Chapter 34 · 0% Book details