← Book details Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 58

Sashe 17

Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tsorona guda kar ta cutar da shi don na tabbatar idan wani abun ya faru da shi ba zan taɓa rayuwa ba ni ma. Ko motsawa ban yi ba har aka yi ƙiran assalatul farko bayan mintuna ƙadan na ji ana bubbuga ƙofar ɗakin na tashi jikina gabaɗaya babu ƙwari ina dafe jiri yana ƙoƙarin buga ni da ƙasa na isa na buɗe ƙofar.
Ganin Abba tsaye yana ƙoƙarin saka hularsa ya sani yin mutuwar tsaye hasken tocilar wayarsa da ya kunna a falon shi ya ba ni damar ƙarewa fuskarsa kallo.
"Ku tashi asuba ta yi kar lokaci ya ƙure, ni ma masallaci zan tafi yanzu".

Kar ya juya ya fita na kasa cewa komai tsabar giyar mamakin da yake ɗawainiyya da ni. Na ja dogon numfashi na fesar da shi ta bakina ina jeranta hamdala da godiya ga Allah a cikin ruhina. Alwala na fito na yi kana na koma ciki na yi salla na zauna akan sallayan ta zabga tagumi duk damuwar da take kai kawo a cikin ruhina amma bakina ya kasa cewa komai sai dai ina da yaƙinin Ubangijina masanin abin da yake cikin zuƙatana ne kuma babu shakka yana sauraron yaren zuciyata.
Har gari ya fara haske Umma ba ta tashi ba balle ta yi sallan asubahi, kuma na yi mini kashedin kar na ƙara tashinta daga bacci kowa za ta kwana da wuni. Don na taɓa yi karon mu da ita a sa'ilin bai yi mini daɗi ba.

Yanayin da nake cikin bai hana ni tashi na haÉ—a wuta na É—aura mana É—umame ba, na zubowa Abba na shi na kawo masa na ajiye a gabansa ina gaishe shi, cike da kulawa ya amsa mini yana bi na da kallo. Zan tashi ya ce na koma na zauna.
"Kamar akwai abin da yake damunki ko?".

Na jijjiga kaina"babu komai".
"Amma kin san dai a duniya gabaÉ—aya babu wanda ya san halinki ya kuma karanci dukkan motsinki sama da ni ko?".
A sanyaye na furta"haka ne Abba".
"To sanar da ni me ye yake damunki Amatullah?".
Kafin na kai ga ba shi amsa Umma ta fito daga É—aki tsam na ga Abba ya tashi tsaye yana faÉ—in"kin tashi kenan? Ai daman yanzu nake son in mun magana da Amatullah na shiga na tashe ki sai kuma kika fito".
Ba ta amsa ba har sai ta zaune ta ɗaura ƙafa ɗaya bisa ɗaya tana jijjigawa ta ce"Allah ya yi na tashi ko ba ka ji daɗin hakan ba ne?".

"Ni na isa na faÉ—i haka Hafsatu ni waye? A'a wallahi kawai dai na ga shurun ya yi yawa ne".
Banza ta yi da shi hakan ya ba ni damar gaishe ta ta amsa mini a taƙaice ba tare da ta kalle inda nake ba.
"Kai kuma za ka zaune ne ko za ka ci gaba da yi min tsayeye a ka, kamar ka haɗiye taɓarya".

Da rawar jiki na ga Abba ya koma mazauninsa ya zauna ko abincin da yake gabansa ya kasa buɗe wa balle ya ci. Hakan ya sa Umma sakin wani ƙayataccen murmushin da har sai haƙwaranta suka bayyana.
"Amatullah tashi ki je É—aki ki fara haÉ—a mana kaya, tun da Ubanki ya dage akan sai mun tashi daga gidan nan gwara mu fara shirin tun yanzu".
Abba ya yi wuf ya karɓe zancen"ranki ya daɗe uwar gida ran gida ai tun lokacin da kika nuna ba kya so na janye maganar tashin. Babu inda za mu je tun da har kika nuna ba kya son hakan".
"Manniru ban isa ka watsa min tsaba kaji su bi ni ba, salon ƴan uwanka sun kwanko ƙafa su zo har cikin falon nan su yi min ɗiban albarka su ce na hana ka sauƙe aiwatar da abin da ka yi niyya. Ai tun da ka furta za mu tashi to babu makawa sai mun bar gidan nan".

"Wallahi babu wani daga cikin ƴan uwana da ya iso ya zo ya gaya miki magana ahalin ina ji ina gani. Babu inda za mu har sai lokacin da kika ji zuciyarki ta sama nutsuwa da lamarin". Abba ya ƙare zancen cikin tsatsar biyayya kamar zai yi mata sujjada.

Umma ta gyara zama tana duban sa da wutsiyar idonta"tashi ka zauna a kujerar mana. Ko ka manta ikararin da ka yi na cewar kai ne mai gidan". Da mamaki gami da al'ajabina sai na ga Abba ya tashi ya zauna akan kujerar, zuciyata ta harɓa da wani ƙarfin bala'i take na faɗa tunani. Kenan da Umma ba ta ce ya kau kujera ba a ƙasa zai ci gaba da zama?.
"Tashi ki ba mu waje za mu yi magana". Muryar Umma ta dawo ni duniyar zahiri daga tunanin da na yi nisan kiwo a cikinta, na tashi na fita waje ba na jin zan iya cin komai shi yasa ban zuba abincin ba na zauna na zuba tagumi yanayin da na sama Umma daren jiya da abun da ya faru yanzu ya dinga yi mini safa da marwa a cikin kwanyata. Tabbas akwai wani surkulle a cikin hayaƙin da Umma ta yi wa Abba jiya da ya juya masa kafatalin tunaninsa.

"Ke kuma lafiyarki da sanyin safiyar nan kika zagba tagumi?". Muryar Amatullah ya fizgo tunanina da ya yi nisa da gangar jikina, na saki ɓoyayyar ajiyar zuciya ina miƙa mata kujera ta zauna. Maimakon na amsa mata tambayar da ta yi mini sai na sako wani maganar na daban.

"Umma ta ce za mu na tafiya talla tare da ke, ban san ko kin san da maganar ba".

Ta É—an murmusa kafin ta ce"tun jiya Ummata ta sanar da ni. Kuma na ji daÉ—in haka sosai fiye da zatonki".
"Amma kin san ni fa ba zan na daÉ—ewa ba saboda zuwa islamiyya".
"To na ji ustaziya".

Tana rufe bakinta Abba tana fitowa ta gaishe shi ya amsa yana saka takalmarsa ya fita da sauri, sai da na bi shi da É—ayar takalminsa don haÉ—in gambiza ya yi ba tare da ya sani ba. Na tsaya a zaure na goge hawayen da ya zubo mini kafin na dawo wajen Amira, duk yadda ta so jan hankali da hira ta kasa samun kaina. Haka har Umma ta kammala kunun ta ce da ni na je na saka kwallin kafin ta shigo kasancewar kwallin yana wajena ina ajiye da shi.
Ban sa ka ba amma ko da ta shigo ta tambaye ni na ce da ita na saka. Don har cikin raina nake jin ba zan iya yin abin da take so na yi ba. Akan idona ta yi wa bokitin kunun turare har da gammo da zan naÉ—a bai
tsira ba, sai da ta gama komai ta ce na É—auka na fita na É—aura a kaina na fito na iske Amira har ta shirya tana jira na.

Ta ci ƙwaras cikin shigar doguwar rigar kamlafa da ya bi jikinta ya fito da surarta a bayyane. Ta yafa mayafi a kafaɗarta bayan ta buga ɗaurin da ake wa take da ture ka ga tsiya a kanta. Har muka fito ban yi mata magana haka nan ma ita ma ba ta ce da ni uffan ba illa latsa wayarta da take yi, kasancewar ita akwai almajirin da yake tura mata kayan tallanta a bairo ya kai mata har inda za ta.
Sai da muka yi nisa na ce"wai ina muka nufa ne?".

"Tasha mana".

"Tasha kuma? Haba Amira duk faɗin garin nan mu rasa inda za mu yada zango sai tasha?". Ta cira kai tana kallona"ke dai ba buƙatarki ki sayar da wannan kunun ba?". Na gyaɗa mata kaina da hakan ya ba ta damar zarce wa da faɗin"to ke dai kawai ki biyo ni". Daga haka ban ƙara cewa komai ba har muka isa tashan almajirin ya sauƙe mata kayan ta sallame sa ya juya ya tafi. Kan ka ce kwabo samari sun yi mana rumfa sayar masan suke yi ba ƙaƙƙaurawa.
Kafin awa guda ta rufa ta sayar da Masar tas har ana nema, sai dai ta ajiye take away guda biyar ta ƙi sayar wa kowa, ni ma ba laifi na dandani farin jininta na yi ciniki sosai.

Ganin ana ta zuwa neman masan tana cewa ya ƙare ya sani yi mata magana"ke kuwa ki sayar musu da wannan ɗin ma tun da ana ta zuwa nema".
"Wannan ba na sayar wa ba ne don a riga da an saye su tuntunin. Wannan da kike gani na Naziru ma Zamani ne kuma ko wani take away É—aya naira dubu biyar yake sayansa, sai dai shi yana da sharaÉ—i".
Na ware idona tar a kanta"wani irin sharaÉ—i kuma?".
"Har inda yake ake kai masa kuma a taya sa hira".
"To a ina za ki same shi?".
"A ɗakin mana". Na dafe ƙirji ina maimata abin da ta furta"a ɗakinsa kuma?".

"Ƙwarai kuwa. To me ye abu tada hankali dududu ba kya wuce awa guda ya ba ki kuɗinki ki dawo".

Shuru na yi na kasa motsin arzuki balle na yi furta wani kalma tsabar ruÉ—un da na shiga. Sai da na fizgo numfashina kafin na ce"yanzu kuma Amira sai ki je É—akin nasan?"

"To sau nawa kuwa. Wani lokacin ma da na fito a can nake tsaya wa ya yi min juye. Ke ma kwanan nan zan nema miki wani na jona ku". Na galla mata harara"Allah Ubangiji ya kiyayi gatari da saran shuka. Ke ma ki yi wa kanki faɗa don ke yanzu ba yarinyar ba ce ko a addini alƙalami ya hau kanki. Ya rage na ki ki yi daidai ko akasin hakan". Dariya kawai ta soma yi ta tashi ta ɗauki take away ɗin ta miƙe tsaye.

"Lokacin da za ki fara hakan Amatullah ke ma kanki ba za ki sani ba. Lokaci shi ne sauya komai, mu ma da ba mu tunanin za mu iya ba amma lokaci ya koyar da mu abun da ba mu taɓa tsammanin za mu iya aikata shi ba". Tana dasa aya ta juya ta tafi kai masa take away ɗin.
[7/21, 6:16 PM] Maimunatu Iyam: *DAFIN HARSHE*

©️ Maimuna Tijjani Iyam

____________________________________

Page 1️⃣4️⃣
Chapter 17 · 0% Book details