← Book details Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 58

Sashe 58

Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Na sadda kaina ƙasa"kuɗin motan ne ya faɗi a hanya ta ta zuwa nan".
"Ba komai kar ki ji kin damu mu shiga ba zai gagara ba". Ban kuma cewa komai ya yi gaba ina bin sa a gaba kamar raƙumi da akala har cikin motar babu jima aka sama ciko mutum ɗaya motar ta cika. Karan motan ya zo ya karɓan kuɗi riƙe da wani takarda a hannunsa in ba ka da kuɗin sai ya ce ka sanya lambar wayan wani nata ta yadda ko da na Allah ya kasance ba fata ake yi ba za a tuntunɓe sa.
Ko da aka zo kaina na rasa lambar wayan wanda zan saka ƙarshe da tunanina ya ƙore na saka lambar wayar Abbana ina rubutawa hawaye suna jiƙa littafin haka har na gama, na yi saurin goge su don na ga yadda mutumin ya kafe ni da ido kamar majigi.

Tun da motar ta ɗau hanya na ji gabaɗaya hankalina ya tashi nutsuwata ta yi nisa da gangar jikina. Tun da nake a rayuwata ban taɓa jin sunan garin jafari ba balle har na yi tunanin zuwa cikinta, ban san kowa ba amma yau ƙaddarata ta ja ni zuwa gare ta. Tafiya ce mai nisan gaske don a hanya muka sallan zuhur da kuma Asr dab ƙiran sallan magriba muka iso kowa ya fiffito, nan fa idona ya raina fata don ban san inda zan nufa ba. Tsoro da firgicin da nake ciki ya ƙara hauhawa tashin hankalina ya ninƙu.

"Baiwar Allah ke kuma haka ake yi za ki fito ba tare da kin jira ni ba".
Na yi ƙoƙarin ɓoye firgicin da nake cikin kafin na furta"a'a ba haka ba ne ina sauri ne shi yasa". Ya ƙare mini kallon tsaf kafin ya ce"ina kika nufa daga nan? Kuma ke da za ki yi wannan doguwar tafiyar nan na gan ki ko jakan kaya babu". Na daburce na kasa cewa komai ina ta inda-inda da na kamo bakin zaren maganan sai ya zille.
Ya ƙara taku uku ya matso kusa da ni"tun kallon farko da na yi miki na ga ne akwai damuwa da firgici a tattare da ke amma kika nuna min ba komai. Tun da na gan ki babu ko jaka na dasa alamar tambaya akan ki don na san nisan tafiyar jafari da irin lalacewar hanyarta da wuya mutum ya ce a wuni guda ya dawo a ranar. Kin gan ni nan da kike ji da gani na ga abubuwa da yawa a cikin wannan duniyar, na ga ƴan mata kala daban-daban na yi mu'amala da mutane iri-iri. Tun daga yanayinki na yi zargi biyu wanda ciki dole ɗaya ya tabbata ko dai cikin shege kika yi kika gudu daga gida kike neman mafaka ko kuma iyaye ne suka wofartar da rayuwarki".

Kalamansa suka sanya hawaye suko mini kurmin idaniya da hakan ya ba shi daman ci gaba da maganan.
"Wannan hawayen da kike yi ya ƙara tabbatar min da abin da nake zargi akan ki".
Na haÉ—e hannayena waje guda"don Allah ka taimaka mini da inda zan zauna. Da zaran na sama inda zan zauna zan kama sana'a ko na aikatau ne na biya ka kuÉ—inki gidan hatta kuÉ—in motan da ka biya mini". Da mamakina sai na ga ya bushe da dariya.

"Kowacce yarinya da irin kalaman nan take fatawa Æ´an mata. Indai wajen zama ne to kin sama akwai inda zan kai ki ki zauna kuma cikin mata Æ´an uwanki".

"Na gode Allah ya saka da alkhairi".

Bai amsa mini ba ya zari jakarsa ya rataya ya kafaɗa ya tari adaidaita muka shiga ba a yi wani tafiya mai nisa ba muka tsaya a ƙofar wani gida ya fito ni ma na fito ya sallami mai adaidaitan. Kana ya yi gaba ina bin sa a baya har cikin gidan.
Tun daga shigar mu na sha jinin jikina, don wasu garke ƴan mata da samari muka iske manne da juna suna ta busa hayaƙin sigari gefe guda kuwa mata ne sun tsuke cikin shigar da bai taimaka da komai wajen rufe tsiraicinsu ba sun zage sai buga caca suke yi. Ya shiga wani ɗaki ya je na jira shi a waje.

Ina tsaye na yi an kwanto a gadon bayana na yi saurin zamewa cike da tsoro.
"Ke Lawisa wai me yasa kike yi min haka ne?". Ya yi zancen cikin maye yana ƙara nufo ni, duk tarin jama'ar da suke zaune a yalwataccen filin tsakar gidan babu wanda ya kawo mini ɗauki. Na kurma ihu yayin da na ga yana ƙoƙarin kai hannunsa saman ƙirjina. Lamarin da ya jawo hankalunsu zuwa gare ni sai dai babu wanda ya taso, mutumin da ya kawo ni ya fito daga cikin ɗakin yana tambayar abin da ya faru na irge masa komai. Bai ce komai ba ya ce mu shiga cikin ɗakin ya yi gaba na bi shi a baya.

Wata dattijuwar mace muka iske a ciki tana zaune da ɗaurin ƙirji a jikinta, duk da ban san giya ba amma ba ni da inkari akan cewa kwalban da take kwankwaɗa giya ne. Na tsuguna har ƙasa na gaishe ta amsa tana kallona kafin ta mayar da idanunta kansa.
"Aminu wanna ita ce baƙuwar takan?".

"Ƙwarai kuwa Hajiya Babban ita ce, to ya ya kika gan ta?".

"Ba laifi komai ya yi akwai kuma yiyuwan da za sama riba akan ta".

Na gaza gane abin da suke faɗa illa rarraba idanun da nake yi, ta ƙira wata ta zo ta ce da ita ta kai ni wannan ɗakin da babu koma a cikin sa, na tashi na bi bayanta. Ta kai ta cikin ɗakin babu komai a ciki face tabarma. Za ta fice na yi saurin cewa"don Allah ko zan sama rufa na yi alwala na yi salla?".
Ta yi sakeke tana kallona kafin ta ce"ruwa? Ai sai dai ki cire kuÉ—inki ki saya don duk abin da idanunki ya gane miki a cikin gidan nan na sayarwa ne". Tana gama faÉ—in haka ta fice ta bar ni tsaye cikin matsanancin mamaki na daÉ—e a tsaye kafin na ja kafafuna na zauna akan tabarma na kifa kaina da gwiwa ina tunanin makomar rayuwata.

Sallamar da na ji an yi ya sanya ni É—aga kaina, na ga Aminu ne ya shigo da wasu ledodi guda biyu a hannunsa ya ajiye su a gabana ya zauna.
"Ga abinci da wasu kayan amfani na kawo miki, don na san za ki buƙace su".

"Don Allah nan ina ne ka kawo ni?".

Ba tare da shakkan komai ba ya ce"nan da kike ganin gidan masu zaman kansu ne". Babu shiri na miƙe tsaye"gidan ba masu zaman kansu kuma? gaskiya Allah ya sani ba zan iya zama a cikin wannan gidan ba, gwara na fita a cikin daren nan na nema inda zan kwana".

"A cikin garin nan dai ina da tabbacin babu inda za ki samu mafaka da ya wuce gidan nan. Amma idan ki na ganin za ki iya samu ba zan hana ki ga ƙofa nan sai ki bi ta inda muka shigo ki bita. Na san ba ki da ko sisi balle ki je ki kama wani wajen, kuma ma inda za ki kama ma ɗin ki na tabbacin za ki sama tsaro a can? Ki na tabbacin in kin je can ɗin kin tsira?".

Ya miƙe tsaye yana ci gaba da maganar"nan ne ya fi dacewa da ke don haka ki na mai ba ki shawarar za ki guje masa. Ga abinci da sauran kayan amfani in ki na buƙata za ki iya ci. Sauran bayanin kuma sai gobe kafin kin yanke shawarar zama ko tafiya". Yana dasa aya a nan ya fice ya bar ni tsaye kamar gumki.
Shirif! Na zube akan taburman ina kuka na ciro ɗan kwalina na cusa a cikin bakina a ƙoƙarin hana sautin fita. Rayuwa juyi-juyi wai kwaɗo ya faɗa a cikin ruwan zafi, ban da ƙaddara me ye zai kawo ni gidan masu zaman kansu balle har na yi rayuwa a ciki su?.

Alhamdulillah! Alhamdulillah! Alhamdulillah!

A nan na kawo ƙarshe littafin DAFIN HARSHE littafi na ɗaya. Shin ya ya rayuwar Amatullah za ta kasance a cikin wannan gidan? Shin za ta tsira da mutumci da tarbiyyan da ta zo da shi? Wani irin rayuwa za ta faɗa? Wani irin tashin hankali Anty Sawwama da iyalanta za su shiga idan aka wayi gari ba su ga Amatullah ba? Ta ina za su fara neman ta? Sannan daga ƙarshe wani irin gwarama za a yi tsakanin Anty Sawwama da Hafsatu idan ta ji labarin ɓacewar ɗiyarta?. Duk amshoshin waɗannan tambayoyin suna cikin littafi na biyu wanda za a posting ɗin sa daga ranar 10 November 2025 in Sha Allah, akan kuɗi naira N500 kacal babu ragi babu ƙari. Ga mai buƙata ƙarin yana iya tuntuɓata ta wannan lambar kamar haka 07038908713
Abin lura: ba complete document ba ne posting za a dinga a paid group daily har mu gama.
Chapter 58 · 0% Book details