Sashe 1
Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
[6/9, 6:34 PM] iyammaimuna: Bismillah rahmanir rahim. Da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai wanda cikin ikonsa, yardarsa, amincewarsa tare da tagomashin aron rai da numfashi da ya ba ni na rubuta wannan littafin mai suna DAFIN HARSHE bayan kammala littafin KE CE MADADI, wanda har yanzu ana dillancinsa a kasuwar online. Ina rokon Allah da ya tsare mini hannayena daga rubuta abin da zai zama ɓarna ko cutarwa ga al'ummar musulmai tare da tarbiyyansu da kuma al'ada.
Ga mai buƙatar litattafaina
*MATAN AREWA
*SALON ƘADDARATA
*UWATA CE SANADI
*ÆOYAYYAR MANUFA
*KE CE MADADI
Zai iya samun su kai tsaye a wajena ko kuma ya tuntunɓi wannan layin 07038908713, ba kya bi na ba shi rantsuwa duk wanda ya karanta tabbas ba zai yi dana sanin sayan guda daga cikin su ba.
Page 0ï¸âƒ£1ï¸âƒ£
Kamar ko wacce safiya yau ma ba ta sauya zanin ba, kururuwa da ihun ƙiran da Ummata take doka mini shi ya farkar da ni daga baccin da ya sace ni, bayan iddar da sallan asubahi. A firgice na tashi Ina rarumar kallabina na saka na bayyano waje. Inda da yawa daga cikin mutanen gidan sun tashi sun fara aikace-aikacen gabansu a ƙofar ɗakunansu. Kasancewar gidan haya ne da ba mu da wadataccen fili sai yawan ɗakun da take ɗauke da su guda goma reras, hakan ya sa mutanen unguwar suke yi masa laƙani da gidan yawa wasu kuma su ce gida goma.
"Za ki iso ki ɗauka tallan kunun nan ko kuma sai na zo na saɓa miki? Oh! Hafsatu ina ganin takaicin rayuwa. Ya tabbata in ban kai zuciya nisa ba baƙin cikinki ke da ubanki sai ya kai ni ƙasa".
Zantukan Umma kenan da suka yi nasarar dawo da ni duniyar zahiri daga kogin tunanin da na dulmiya, na yi ƙasa da kaina ina sauraron zancen da ta ɗaura da shi. Wanda tun suna yi mini ciwo har sun zame mini jiki duk nusar da ita da Abba yake kamar yana zuba ruwa ne a bayan ƙwarya.
"Umma yanzu fa garin ya waye. Kuma ba sayan kunun nan suke yi ba da safe". Ta yi hanzari katse ni tana nuni da Æ´ar manuniyar Æ´atsarta.
"Kunun ne aka daina shan sa ko kuma mene ne? Ai kuwa da safe ake cinikin kunu tun da ga masu fita aiki nan suna shiri".
Ta ƙare zancen tana yi mini nuni da ido zuwa ga Baban Adnan da yake saka takalmarsa sau ciki cikin shigar jami'an ƴan sanda. Matarsa da take tsaye kusa da shi ta bankowa Umma harara babu wata-wata ita ma ta rama kafin ta juyo kaina a zafafe.
"Za ki zo ki ɗauka ko sai ya huce? Ƴar iska mai baƙin hali irin na Ubanta". Tana kai wa aya Abba yana sako kan sa cikin gidan muka yi ido huɗu da shi kafin ya sadda kaina ƙasa.
"Mu je ciki mu yi magana Hafsa". Abba ya furta cikin sanyin amon, don mutum ne marar son hayaniya, uwa uba yana son sirri duk dambarwar da za a yi zai yi wuya ya tattauna da Umma akan abin da ya shafe mu a filin gidan.
"Daga zuwanka ba za ka kafa min ƙahon zuƙa ba. In naje cikin uwar me ye zan yi maka? Kai ba yaro na goye ba balle ka ce ina mun shiga shayar da kai zan yi".
Da hanzari na ɗauko kaina na kafe Umma da idanuna da suka kawo ruwan ƙwalla. Shewar da Maman Adnan ta saka game da tafa hannu ya yi daidai lokacin da hawayen da suka wadaci kurmin idanuna kwaranya a bisa dandamalin fuskana. Takaici ya zo mini a wuya wanda ina da tabbacin shi ne ya tunzura zuciyar Abba har ya soma cewa.
"Wani irin magana ne wannan haka Hafsa? Ko za ki furta min wannan furucin zai ki yi a nan".
"Mtschew! Ka ji da shi yanzu kam kanka ake ji, wai mahaukaci ya faÉ—a rijiya ya ce ni wanka na nake yi. Ki zo ki É—auka kunun nan shegiya mai zubin munafukai".
"Babu inda za je shin sau nawa zan ce da ke ba na son wannan tallan da kike ɗaura wa Amatullah?". Ba ta amsa masa da baki ba illa tsakin da ta buga tana wurga masa harara tare da yatsina fuska tamkar ta yi tozali da ɗanyen kashi sakin yanzu. Na jayo ƙafafuna da ƙyar na zo na ɗauki gammo na naɗa na ɗaura a kaina ina kici-kicin ɗaura bokatin kunun a kaina. Baban Adnan ya zo wuce wa har ƙasa Umma ta durƙasa tana gaishe shi tare da yi masa addu'ar a dawo lafiya, kalamanta na ƙarshe su suka fi komai shayar da ni ruwan mamaki.
"Allah ya yi wa Adnan albarka, ya raya shi bisa turban addini. Al'umma su yi alfahari da shi". Daɗin addu'ar ya sanya Baban Adnan washe baki yana amsa da amin wani na bin wata. Sai da Maman Adnan ta fizgi hannun rigarsa ta ja shi waje kana ya rufe bakinsa. Babu kunya Umma ta miƙe ta kakkaɓe jikinta ta yi ciki Abba ya ce na dakata daga fita tallan ya rufa mata baya ina daga tsaye ina jiyo abin da suke tattaunawa.
"Hafsatu ki ba ni hankalinki mu yi magana na fahimta ba na jin daÉ—in abin da kike yi min a cikin gidan nan, musamman wannan tallan da kike É—aura wa Amatullah. Ba mu rasa abin sawa a bakin salati to mene ne na tada hankali?".
Ta ya wata doguwar tsaki kafin ta zarce da cewa"Cimar gidanka da kullum babu canji, buhun masara ce in ka jingine ta sai kuma ta ƙare a kawo wata ina shi ne alfaharinka?. Da an yi magana ka ce ba mu rasa ci ba ba mu rasa sha ba. Dole na nema kuɗi kuma wajibi ne na ɗaura wa Amatullah talla".
"Yanzu abin da kika yi kin kyauta kenan? Kin kasa sawa Æ´arki ta cikinki albarka balle ki yi mata fatan gama wa da duniya lafiya amma ki na yi wa É—an wasu. Kullum cikin jifan ta kike yi da munanan furuci, Hafsatu ke uwa ce bakinki yana da tasiri akan Amatullah shi yasa nake tsoron ranar da DAFIN HARSHEnki zai kama ta". Cikin É—aga sauti na ji ta mayar masa da martani kamar za ts rufe sa da duka.
"Dole kuma aka ce idan zan sa mata albarka sai na yi a fili kowa ya gani? Ka san adadin abubuwan da nake roƙa mata a cikin sujjadana?". Daga nan ban ƙara jin muryar Abba ba sai ganin Umma na yi ta fito daga ɗakin kamar an jefo ta na zabura na matsa gefe.
"Don ɗiban albarka har yanzu kina tsaye ba ki tafi ba? Allah na gode maka ni kam. Kowa yana haihuwa don ya huta amma ni kam ko kusa ko alama, tsinanniya mai baƙin hali". Ta ƙare zancen tana suran murfin tukunya da nufin wurga mini, babu shiri na fice ƙafafuna suna harɗewa cikin ɗaurin zanina. A ƙofar gidan na iske raguwar mazajen gidan zaune akan taburma suna zaman sa ido, kaina a ƙasa na wuce ta gabansu sai dai hakan bai hana jikina ba ni tabbacin cewa idanunsu yana kaina ba har na fice daga layin. Na nema wani waje na zauna tare da zabga tagumi na faɗa cikin duniyar tunani na yi nutso sosai da har ya hana ni jin sallamar da matashin saurayin da yake bisa kekensa yake yi, sai da ya tafa hannayensa kana na dawo daga karatun wasiƙan jakin da na faɗa.
"Na nawa kake so?".
Na jefa masa tambayar ina ciki-cikin É—auro robar da zan zuba masa. Amsar da ya ba ni ya dakatar da ni daga abin da nake yi, na cira kai ina bin sa da wani irin kallo.
"Mai kunun nake so".
Kallon da na tsare shi da shi ya sanya sa É—age mini ido guda yana ci gaba da cewa.
"Ayi min farashi ko nawa ne zan biya. Don kyawunki ya kai a kashe ko nawa ne".
"Dalla! Malam ba na son maganar banza, idan za ka saye ka faɗin na nawa kake buƙata. In kuma ba saya zaka yi ba ka ba wa masu saya waje". Kallon da yake bina da shi yana lashe baki kamar tsohun maye ya ƙara ƙular da ni na doka tsaki ina ci gaba da zancen.
"Malam ka matsa mini daga ka, kana wani lashe baki kamar maye".
"Ke kar ki yi min rashin kunya don kawai na yaba ki".
Na taɓe baki kafin na ce"idan sarki bai ji kunyar hawa jaki ba ai kuwa jaki ba zai ji kunyar jefar da shi ba". Ya sauƙo daga kan keke ya nufo ni gadan-gadan yana zazzare idanu, nima na miƙe tsam na kamfato kunun na watsa masa a fuska. Kafin ya yi wani yunƙuri na tattari kayana na saɓa hanya.
Sai da na yi nisa na fice daga layi gabaɗaya kana na waiwaya na sauƙe ajiyar zuciya. Ganin ba ya bibiyata gida cikin faɗuwar gaba izuwa yanzu mazan da suke zama a ƙofar gidan duk sun watse kowa ya tafi harkokinsa. Kamar ƙadangaruwar bayan murhu kana na shigo ciki ina raɓe-raɓe iwa munafuka. Na yi kiciɓus da Ummi a zaure tana zance da wani mayatatcen saurayinta da inda ya zo tun safe har yammaci bai kula ta na sa kai na yi wucewa ta.
Na dire bokitin a ƙofar ɗakinmu yayin da duk ragowar matan da suke waje suka kafe ni da na mujiya. Na tsinkayo amon Umma daga bayana na waiga tana riƙe da buta ta fito daga banɗaki ta washe baki kamar gonar auduga.
"Ba shakka! Tsuntsu daga sama gashashshe. Amatullah har kin sayar da kunun kenan?".
Ba ta jira amsar da zan ba ta ba ta ajiye butar da ke hannunta ta nufo inda na ajiye bokiti, turus ta tsaya ganin kunun shaƙe taf a cikin bokitin.
"Me nake gani haka?Wani irin ɗanyen aiki haka kika jiƙa min Amatullah? Don tsabar mugunta da baƙin hali yanda na ɗaura miki haka kika dawo min da shi, shegiya ƴar iska wacce ba ta gaji abin azurki ba".