Sashe 8
Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ni kuwa nake da abubuwa da yawa tun da na rayu da imani da kuma ƙaunar ma'aikinmu. Ina da lafiyar da zan fita na nema halal ɗina ban taɓa aika wani abun alfasha ba. Ba na so muna musayan yawo da ke a gaban Amatullah don haka wani mataki ne na lalata mata tarbiyanta". Tsaki ta buga ta koma ɗaki ta bar shi tsaye a wajen.
Hularsa Abba ya ɗauka zai fita na yi saurin cewa"Abba abincin fa?". Ba tare da ya kalle ni ba ya furta"lokaci ya riga ya ƙure zan tafi kar na yi latti". Yana dure zancen ya fice ya bar ni zaune cikin tarin damuwar da ya yi wa zuciyata katutu.
"To ke kuma munafuka sai ki tashi ki tattare É—akin kafin na gama dama kunnun nan ki fita da shi. Yarinya kamar Æ´ar gaba da fatiha tun da na haife ki ban huta ba har yanzu, oh! Ni kam ina ganin takaicin haihuwa". Ta yi maganar tana ficewa daga É—akin. Dole na tashi na tattare falon kana na koma na gyara É—aki cikin tashin kuzari, wanka kawai na yi na kora kokon da na damawa Abba wanda bai sha ba ya fita. Na fito waje na tarar da Umma zaune ta kammala komai na kunun.
"Umma na fito".
Ta ɗago kai ta ƙare mini kallo kafin ta miƙe ta ja hannuna muka koma falo ta shige ɗaki ta fito. Ta miƙa mini kwalli.
"Ga shi kar ɓi ki saka sa a idanunki. Sannan ga can garwashi wuta ki ɗauko ki turare da shi".
[7/12, 1:06 PM] Maimunatu Iyam: *DAFIN HARSHE*
Â©ï¸ Maimuna Tijjani Iyam
_________________________________________
Page 0ï¸âƒ£7ï¸âƒ£
Ban san lokacin da ƙwalla suka wadaci koramar idanuna ba sai jin ɗuminsu na yi suna shawagi a bisa kuncina. Ban share su ba kamar yadda ban yi wani yunƙurin hana su kwaranya ba. Na haɗe hannayena wajen guda alamar roƙo kafin na sa magana cikin rawar murya da sarƙafewar harshe.
"Umma don girman ki rufa mana asiri kar mu garin neman gira mu rasa ido, garin neman duniya mu faɗa cikin fushin Ubangiji, wannan abun fa kamar shirka ne. Don yana nuni da cewar ba mu yarda cewar Allah ne mai yi ba, ba mu yarda shi yake kawo kasuwa kuma ya buɗe wa bawa ƙofofin samunsa a duk lokacin da ya so kuma ya ga dama ba. Umma na yi miki alƙawarin ko zan wuni ba zan dawo ba sai na sayar da wannan kunun".
Tun da na fara maganar ta kafe ni da idanu tana bi na da irin kallon da mai hankali yake yi wa zautacce, ta taɓe baki kafin ta soma faɗa a fusace.
"Lalle wuyanki ya yi kauri ya isa yanka Amatullah, har ni za ki kalla tsabar idona ki ce zan jefa mu cikin fushin Ubangiji?. In don islamiyyar da kike zuwa ne ko kuma kina ganin kina dab da haddace alƙur'ani ya saki faɗa min waɗannan kalaman, to sai na hana ki zuwa ko'ina. Ko Allah ma ai ya ce tashi na taimake ka ba zai taɓa yiyuwa kana daga kwance ka ga kuɗi suna zubowa daga rufin ɗakinka ba dole sai ka tashi ka neme su. Da ke gwara ƴar zina sam ba kya tausayina balle mu haɗa kai mu samarwa kanmu mafita. Ni kam ina ganin takaicin haihuwa".
Haƙiƙa kauraran kalamanta sun yi nasarar narkar mini da zuciya har su yi sanyaya mini dukkan gaɓoɓin jikina. Kaina ya ɗauki zafi kamar garwashin dake ƙasan tukuban tsire. Kafin na yi magana na tsinkayo amon muryar Anty Sawwama babbar ƴar Abba da take kusa da mu. Na waiga ina kallonta daga yanayin fuskarta na fahimci ta ji abin da Umma take faɗi.
"Yau ina ganin ikon Allah wai na zaune ya faɗi. Yanzu Hafsatu haka abin nakin ya girmama har ta kai ta kawo ki titsiye ƴar cikinki kina jifan ta da irin waɗannan mummunan kalaman? Kar ki manta ke ba uwa ce DAFIN HARSHEnki yana da matuƙar tasiri akan ta kamar yadda duk addu'ar da kika yi mata Allah zai amsa ta don babu hijabi tsakanin addu'ar uwa da Ubangiji". Ta gyara ɗaurin zaninta kafin ta ci gaba da faɗin"tabbas sai yau na ƙara yarda da cewar babu butulu kamar ɗan Adam shi ne mai manta alkhairi cikin ƙiftawan ido. Ashe Hafsatu kin manta tsawon shekarun da kuka shafe da Manniru a matsayin ma'aurata kafin Allah ya azurta ku da samun Amatullah?. Kin manta wahalhalun da kika sha a yayin goyon cikinta har zuwa lokacin haihuwarta wanda dalilin hakan aka cire miki mahaifa gabaɗaya?. Waɗannan dalilai guda biyu ba su isa su sanya zuciyarki karaya ba ba su isa su dasa so da ƙaunar Amatullah a cikin ƙirjinki ba tun da kin sani na sani daga ita ba za ki ƙara haihuwa ba a duniya, amma don kin cika cikakkiyar butulu mai mance ni'imar da Ubangiji ya lulluɓe ta da shi har kike buɗe baki ki ƙira da ita gwara ƴar zina. Hafsatu ina guje miki ranar ƙin dillanci ranar da ido za ta raina fata. Wannan harshen da muke rainawa wallahi yana da tasiri akan ƴaƴanmu".
"Maman Umar ni fa ba ƙaramar yarinya ba ce da za ki wanko ƙafa ki zo har cikin gidana kina gaya min abin da ya dace na yi ko wanda zan bari ba. Ke fa bakinki kika furta na sha wahala a lokacin rainon cikinta har zuwa haihuwarta don haka kuwa kin ga duk wanda zai nuna mata wata soyayya a bayana yake".
"Hafsatu nusarwa ce na yi miki, ke É—in fa uwa ce duk abin da kika furta akan ta wallahil azim zai bibiyi rayuwarta ne. Kuma ko ba daÉ—e ko ba ji ma watarana sai abin da kika shuka ya yi tsuro kin girbe sa".
Kallon uku saura kwata Umma ta watsa mata kafin ta juyo kaina"fita ki je ki É—auki kunun nan ki wuce, idan Allah ya kaimu gobe za mu aiwatar da shirin mu".
Tana dure zancen ta shige ɗaki ta bar mu a wajen, na sauƙe tagwayen ajiyar zuciya kafin na tsugunawa har ƙasa ina gaishe da Anty Sawwama. Ta yalwata annuri fuskarta kafin ta amsa da faɗin"lafiya ƙalau uwarmu maganin kukanmu. Baya goya marayu Allah ya sa ki yi gadon halin mahaifiyarmu wanda tun yanzu ma alamomin hakan sun bayyana. Kina da haƙuri da ɓiyayya Allah ya yi miki albarka".
"Amin". Na amsa da shi ina sadda kaina ƙasa a ƙoƙarin tare hawayen idona kwaranya.
"Ki je ki É—auki kunun kar ta fito tun da kin fi kowa sanin halinta".
Duk yadda na so tare hawayen idona zuba lamarin ya faskara ba tare da na yi aune ba suka fara gudun famfalaƙi a tsakanin kuncina da saman haɓata.
"Anty zan dawo na same ki ko tafiya za ki yi?".
Ta matso kusa da ni ta riƙo hannuna da hannunta ɗaya, yayin da ɗayan kuma ta soma share mini hawayen fuskana da su.
"Za ki dawo ki same ni, don zan jira har mahaifinki sai ya dawo akwai maganar da za mu yi da shi". Kaina kawai na gyaÉ—a mata na zare hannuna na fita na É—auki bokitin kunun da ragowar robobin na fita.
Ina fitowa na tsaya a ƙofar gida ina kallon gabar da yamma kudu da kuma arewa. Na rasa wani hanya zan bi da sai sada ni nasara a safiyar yau. So nake yi na goge tunanin da yake cikin kan Umma na nuna mata cewar ko da laƙani ko babu idan Allah ya tsara zan sayar da kunun nan babu makawa sai na sayar ko da kuwa a ƙofar gida ne. Ganin tsayuwar da nake yi ba zai haifar mini da ɗa mai ido ba ya sani soma tafiya ƙirjina yana tsananta bugu. Sai da na fice daga unguwar gabaɗaya na fito bakin titin da ya rabu kashi biyu kudu da kuma arewa. Can na hango tawagar wasu masu talla sun haɗo kansu za su wuce na bi su a baya har muka isa wani babban fili da yake a bakin hanya kusa da wani sabon gidan mai. Suka zauna ni ma na nema waje na zauna bayan na ajiye tallana a gabana, duk suka zubo mini idanu kamar sun ga wata baƙuwar halittar da ta zo daga wata duniyar da ba namu ba.
Tabbas wajen fuskar jama'a ne don tun da muka zaune ake ta sayan kayan mussamman awara da wainar fulawa su suka fi ciniki. Raina ya yi fari ƙal nauyin da yake zuciya a hankali na ji ya fara sauƙa kamar an jefa dutsin a cikin ruwa. Farin ciki ya mamaye ni ganin a ƙasa da mintuna talatin na yi cinikin dubu da ɗari biyu. Farin cikin da yake fuskana ya soma dushashewa ganin sauran masu tallan sun yi cirko-cirko a gabana duk sun riƙe ƙugu fuskokinsu kamar a murtuƙe kamar hadarin da ya taso daga gabas.
"Bayin Allah lafiya?".
Na jefa musu tambayar bayan na haÉ—o jarumta na yafawa kaina, É—aya daga cikinsu ta wurga mini wani mungun kallo har da tsirta da miyau kamar ta yi tozali da kashi.
"Uban waye ya ba ki iznin kawo talla nan wajen?".
Na É—aya iso na yi mata kallo guda kafin na mayar mata da amsa"har sai an ba da
izni kafin a kawo tallan? Na yi zaton fili ne kawai dajin Allah kowa ya kawo tallansa in ya sayar ya koma gida....".
Kafin na rufe bakina ɗaya daga cikin da ta fi su fusata ta ɗauke da mari da ya sani jin hajijiya na ƙoƙarin buga ni da ƙasa duk da a zaune nake. Kafin igiyar firgicin marin ya gama sake ni sautinta ya dira a ƙofofin kunnuwana kamar sauƙar ungulu.
"Ke har kin isa Zaina tana magana kina mayar mata, wane ne ubanki a cikin garin nan? Kuma waye ya tsaya miki a nan wajen?".
Na dafe kuncina kafin na ce"laifina ne don ta tambaye ni na ba ta amsa?".
Ta ƙara fusata ta nufo ni wata ta dakatar da ita. Cikin isa take faɗin"ƙyale ta Zulfa'u akwai buƙatar sai mun yi mata komai a aikace".