← Book details Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 58

Sashe 53

Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Allah na tuba ka yafe mini. Allah ya kawo mini ɗauki da mafita. Ya Allah na yarda babu kuskure a cikin hukuncinka kuma ba ka ɗaurawa Bawa abin da ba zai iya ba, Ya Ubangijin sammai da ƙassai bakwai ya Ubangijin talikai da dukkan wasu halittu ina roƙon da ka tashi kafaɗun Abbana ka ba shi lafiya, kar ka bari baƙin ciki ya yi silar faɗawarsa cikin wani irin yanayi".

A raunane na ƙare zancen cikin dushashewar murya, da ƙyar na miƙe akan ƙafafuna saboda rawar da suke yi na yi wanka na fito sai da na yi alwala kana na shiga cikin ɗakin. Anty Zulaihatu ta ba ni zani da riga t-shirt na saka kasancewar gidan babu ɗiya mace wannan ma a cikin kayan Anty Sawwama ta binciko mini. A zaune na yi sallan saboda ba zan iya tsayiwa ba, na daɗe a sujjadata ta ƙarshe ina kuka kafin na ɗago na ɗaga hannayena dukka biyu sama sai dai na kasa cewa ko kanzil.
Ko buɗe abincin da Anty Zulaihatu ta kawo mini ban iya ba na kifa kaina da gwiwa ina ta sauƙe ajiyan numfashi.

Haka na wuni cikin wani irin mungun yanayin da ban taɓa tsintar kaina a cikinsa ba tun da na zo duniya sai bayan sallan la'asar Anty Sawwama ta farka. Anty Zulaihatu ta kai mata ruwa ta yi wanka ta zo ta gabatar da salla ita ma ta kasa cin abincin sai cewa ta yi a ƙira mata Alhassan, Anty Zulaihatu ta ƙira shi ta miƙa mata wayar bayan ta sanya ta a amsa-kuwwa.

"Alhassan ya mai jikin?".

"Da sauƙi dai kawai za a ce Umma, amma tabbas Kawu yana jin jiki wallahi. Bayan tafiyarku ma sun mayar da shi emergency sannan sun hana kowa ya shiga ya gan sa, sun ce zuwa safiya idan babu wani ci gaba dole za su tura mu asibitin dake maƙwabciyar jihar nan, wanda su daman masu irin laluransa kawai suke dubawa".

"Innalillahi wa inna ilahirin raji'un! Wai me ye suka ce yana damunsa ne haka?". Ya yi ɗan jim kafin can ya ce"Umma gefensa ɗaya ne ya shanye sannan zuciyarsa ta kumbura. Dole akwai buƙatar a yi masa gashin ƙashi da aiki a zuciya". Tun kafin ya ƙarisa zancen muka saka salati wani kuka marar control ya ƙwace mini na so ma yin sa da dukkan ƙarfina.
Anty Zulaihatu ta karɓa wayan" in mun zo za mu sama ganin sa ne?".

"Babu wanda ake bari ya gansa likitotin ne kawai suke shiga, kuma sun dawowa za mu yi don sun ce su a tsarin su ba a kwana a tare da majinyancin da aka kai emergency. Suna da ƙwararrun ma'aikata da kuma masu kula da majinyanta".
A rikice Anty Sawwama ta furta"ku kuka shi da waye za a bar shi?".

"Umma ki kwantar da hankalinki fa babu wani abun da zai same shi. Idan na dawo sai mu gama maganan". Da aka suka yi sallama duk muka zauna jimgum-jimgum kamar masu karɓan gaisuwar mutuwa.
Sai bayan sallan isha'i Yaya Alhassan da Amir suka dawo suka ƙara yi mana bayanin halin da Abba yake ciki, ni dai ina rakuɓe a gefe guda ina jin na wanin zazzaɓi mai zafi yana ƙoƙarin rufe ni.

Anty Sawwama ta umarce mu da mu tashi mu je mu alwala kowa ya karanta alƙur'ani iya yadda ya sawwaƙa mu yi tawassali da hakan wajen nemawa Abba lafiya a wajen wanda babu abin da ya gagari ƙarfin ikonsa. Hakan muka yi ba mu kwanta ba sai ƙarfe ɗayan dare, daga Yaya Alhassan har Amir tun da suka shigo cikin su wanda ya ce mini ko kanzil haka nan ba su buƙacin jin dalilin kasancewata a gidan ba.
Yadda nake jin jikina a wannan daren ban taɓa zaton za a wayi gari da ni cikin rayayyu ba, gaba ɗaya na cire tsammani da rayuwa na saddaƙar da komai na miƙa wuya ina jiran yadda Ubangiji zai yi da ni. Don na yadda duk abin da ya zartar hakan shi ne daidai kuma babu kuskure a cikin sa. Yadda na ga rana haka na ga ban runtsa ko na sakon guda ba. Daga masallacin sallan asubahi Yaya Alhassan da Amir suka wuce asibiti wajen Abba.

Wajajen ƙarfe goma Anty Sawwama da Umar suka shirya za su tafi asibitin na dage akan zan biso na je na ga Abba amma ta hana ni babu yadda na iya dole na haƙura muka zauna da Anty Zulaihatu zaman jiran tsammani.
Ba su daɗe da tafiya ba Amira ta zo ta ina jin sallamarta na zabura da sauri na fito filin tsakar gidan, muka rumgume juna muna wani irin kuka mai ban tausayi da ƙyar Anty Zulaihatu ta lallashe mu muka tashi muka cikin ɗakin.

"Amira kin ga yadda rayuwa ta yi da ni ko? Ni kuma tawa salon ƙaddarar kenan". Ta riƙo hannuna ta sanya cikin nata cike da tausayi ta soma cewa" komai yana da lokaci Amatullah komai watarana zai zo ƙarshe zai zama labari har ya shuɗe. Don Allah ki cire damuwar komai a ranki".
"Ta ya ya kike tunanin zan iya cire damuwa daga cikin raina? Ba ni da wannan ikon Amira, ba ni da wani buri yanzu da ya wuce na ga Abba ko da kuwa shi ne abu na ƙarshe da idanuna da su yi tozali da shi kafin rai ya yi bankwana da gangar jikina". Ta kai tafin hannunta ta rufe mini bakina ruf.

"In sha Allah ma babu wanda zai mutu. Kuma komai zai zo ƙarshe".

Na kasa cewa da ita komai illa kukan da na fashe da shi ina yi ita ma tana yi babu mai lallashin wani a tsakaninmu. Duk ƙarfin halin Anty Zulaihatu ma sai ta yi kukan haka muka sha kukan har muka gaji. Na ɗago idona ina kallon Amira da ita duk damuwa ya bayyana a fuskarta.

"Umma ba ta neme ni ba ko Amira?".
Ta É—an yi jim ba tare da ta ba ni amsa ba. Shurunta ya sani cewa"ba ta neme ni ba ko? Na kan ji ana cewa uwa ita ce majingina kuma mafaka a wajen Æ´aÆ´anta, na sha jin a cikin labarun hikayoyi cewar uwa ce kaÉ—ai ba ta juyawa Æ´aÆ´anta baya ita ce kaÉ—ai take rufawa Æ´aÆ´anta asira komai munin abin da suka aikata. Amma me yasa tawa uwar ta bambamta da sauran?".

"Umma ta na son ki Amatullah ke ma shaida don ta yi abubuwa da yawa da bayyanar da hakan. Ki yi mata uzuri akan abin da ta aikata ki ba ta lokaci ta huci sannan ku yi magana". Amira ta yi kalaman cikin sigar son kwantar mini da hankali. Haka muka zauna har sai bayan sallan asr Anty Sawwama da Umar suka dawo cikin wani irin yanayi na sanyin jiki. Nan suke shaida mana cewar an tafi da Abba asibitin ƙwararru dake maƙwabtaka da jiharmu ta kuma ƙara bayyana mana cewar yana buƙatar addu'armu, lamarin da ya ƙara gigita nutsuwar da ta yi saura akan jikina kuka nake yi tuburan jikina yana rawa tamkar mai shafan iskokai sai Anty Zulaihatu da Amira suka rirriƙe ni suna yi mini tofi kafin na lafa na kwanta na yi lamau. Sai dab da magrib Amira ta tafi mijin Anty Zulaihatu ma ya zo ya ɗauke akan gobe da safe za ta dawo ta ƙara duba jikin nawan. Haka na ƙara kwana cikin wannan yanayin kafin gari ya waye zazzaɓi ya rufe ni ko idona ba na iya buɗewa, na firgita na ruɗe bisa mummunan mafarkin da na yi da Abba, wai na je wajen sa a asibiti ya ce kar a bar ni na shiga wajensa ba ya son ganina.

Wajajen ƙarfe takwas Yaya Alhassan ya ƙira waya ya shaida mana cewar ga su a hanya suna dawowa. Tsam Anty Sawwama ta miƙe"alhamdulillah! Lafiya ta samu kenan? Ina shi Mannirun haɗa da shi".
"Umma ba zai iya magana ba, sai dai mun iso ɗin kawai". Yanayin da ya ƙare zancen da kashe wayar da ya yi ba tare da an gama maganar ba, ya samu ɗaura ayar tambaya akan sa. Haka muka dinga ƙiran wayar amma baya ɗauka daga ƙarshe ma ya kashe ta, daga shi har Amir muka daina samun wayoyinsu.
[10/27, 5:30 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE*

©️ Maimuna Tijjani Iyam

___________________________________________

Page 3️⃣8️⃣

Haka muka kasa tsaye balle zaune duk muka yi jigum-jigum da mu cikin mu babu mai walwala. A zaune na yi sallan zuhr saboda yadda ƙafafuna suke rawa ji nake yi tamkar ba sa cikin gangar jikina, ina zaune a wajen na zagba uban tagumi ina tunanin makomar rayuwata da yadda komai ya sauya mini cikin ɗan ƙanƙanin lokaci.
"Abba ka yafe mini Allah ya tashi kafaɗunta. Na san kai kaɗai ne za ka fahimce ni a kaf cikin faɗin duniyar nan. Abba kai ɗaya ne kake fahimtar shuru na kuma ina da yaƙinin kai kaɗai ne za ka yi mini uzuri akan abin da ya faru. Na yi kewarka ina son ganinka sai dai ba zan iya jure ganinka cikin yanayin da na yi silar jefa ka a ciki ba. Abba ka yafe mini ka yafe mini".

Na yi zancen cikin karyarwan zuciya wasu hawaye suna rige-rigen fitowa daga cikin rinannun idanuna. Na ji wani abu ya tokare mini ƙirjina numfashi ma da ƙyar nake fitarwa tamkar mai lalurar cutar numfashi. Kamar daga sama na tsinkayo sallamar su Yaya Alhassan take na ji fada na ya yanke ya faɗi zuciyata ta buga irin bugun da har sai da ya tilasta mini runtse idanuna. Anty Sawwama da Anty Zulaihatu suka miƙe a tare suka fita amma ni kam ko gizau na gaza motsawa daga inda nake zaune, sai dai ina zaune ina jiyo abin da suke tattaunawa.
"Alhassan ya ya na gan ku haka? Ina shi Mannirun? An sallama ku ne daga asibitin?". Duk jerin tambayoyin da Anty Sawwama ta jefa masa bai amsa ko guda ba.
Chapter 53 · 0% Book details