Sashe 28
Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ya gyara tsayinsa yana kallona tun daga ƙasa har sama kafin ya ce"ga ta kuwa ƴar ɗas da ita komai na ta cif-cif. Cikakken ƙirji ga kuma faffaɗan ƙugu". Take na ji wani jarumta ya zo mini ruɗewan da na yi lokaci guda na neme shi sama ko ƙasa na rasa shi, na nuna shi da ƴar manuniyar ƴatsata idonuna har sun soma ƙanƙancewa don masifa.
"Ahir É—inka ko kai maye ne sai dai ka ci kanka". Ina ada aya anan na figi hannun Amira kamar zan raba shi da gangar jikinta muka bar wajen, ba mu tsaya ko'ina ba sai wajen kayanmu na zauna a mazaunina ina jin zuciyata tana tafasa tamkar talgen da aka É—aura a bisa wuta.
"Har kun dawo kenan?". Bashir ya tambaya.
Na yi buga masa wani mungun kallon da bai ƙara yin gigin kallon inda nake ba balle ya yi nuni wata magana. Sai Amira ce ta ba shi haƙuri ta ce gobe ya dawo, muna gama sayar da kayanmu muka haɗa su almajiran da suke kwasar mana suka ɗeba suka yi gaba muna biye da su.
"Don Allah ki dunga É—aukar abubuwa a hankali Amatullah. Rayuwar nan fa sai ana kai zuciya nisa". Na galla mata hararar"babu wanda ya isa ya yi nuni maganar banza ba tare da na mayar masa da martani ba".
Ta sheƙe da dariya mai isarta kafin ta ce"ai kuwa duk mazan yanzu haka suke, maganar batsa ya zama ruwan dare a wannan zamani tsakanin samari da ƴan mata. Sai dai in ba za ki yi soyayya ba balle aure don duk maza halinsu ɗaya ne. Musamman ke da Allah ya bai rage ki da komai ba kina da kyawun sura da diri ina yaƙinin babu namijin da zai ganki bai yabi surarki ba, Amatullah surarki jikinki kawai ya isa namiji ya so ki. Shi yasa kowa ya ganki sai ya yabe ki".
Na ja dogon numfashi na fesar"Amira akwai na tabbatar akwai. Akwai namijin da muka rabu da shi bai yi mini magana akan kyawun sura na ba. Shi ne mutum na farko da na taɓa haɗuwa da shi har muka rabu bai yi mini maganar banza ba".
"Amatullah ƙarya kike yi in akwai kuma ki faɗa min wanene wannan? Ni kuma zan tabbatar miki da a cikin biyu dole akwai ɗaya, ko dai ba shi da cikakken lafiya ko kuma idanunsa ba sa aikin su yadda ya kamata".
Na tsaya cak a inda nake ina kallonta cike da yaƙini na ce da ita"ki yarda da duk abin da zai fito daga bakina, tabbas akwai".
[9/28, 9:31 AM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE*
Â©ï¸ Maimuna Tijjani Iyam
_____________________________________
Page 2ï¸âƒ£2ï¸âƒ£
Tsare ni ta yi da ido tana bi na da irin kallon da mai hankali yake yi wa zautacce, ta jijjiga kanta alamar duk abin da na furta bai sama matsuguni a cikin kwanyata ba. Balle har zuciyarta ta aminta da shi.
"Kin ga Amatullah ki zo mu tafi mu bar wannan maganar". Ban ce da ita komai ba ta yi gaba na bi ta a baya babu abin da nake yi illa saƙe-saƙe a cikin raina, kalamanta suna yi mini yawo a cikin ƙwaƙwalwata. Har muka kai gida cikinmu babu wanda ya ce ko kanzil muka shigo da kayayyakinmu ciki.
Har na nufi hanyar ɗakinmu ta dakatar da ni ta hanyar faɗin"kar ki manta yau Mansur zai dawo kuma komai dare a nan zai fara tsayawa. Don haka akwai shirye-shiryen da zan yi wanda ina buƙatar taimakonki".
Sai da na sauƙe numfashi mai nauyi kafin na iya raba tsakanin haƙwarana da suka manne da juna na ce da ita" zan je islamiyya fa amma....".
Ta katse ni"idan ba dole ba ne ki haƙura mana da zuwa na yau ne fa kawai".
"Ki yi haƙuri Amira ya zama dole ne, kin ga sauƙarmu fa wasa gaske sai ƙara matsowa yake yi. Amma na yi miki alƙawarin zan dawo da wuri".
Ta faɗaɗa annurin fuskarta"yauwa to jiran ki". Muka sakarwa juna murmushi kafin kowa ya shige ɗakinsu, Umma na iske a falo ta ɗaura ƙafa ɗaya bisa ɗaya tana sauraron rediyo, na yi sallama ta amsa mini kamar wacce aka yi wa dole na durƙusa na yi mata sannu ba ta kula ni ba, na ajiye mata kuɗin cinikin da na yi.
"Umma ga kuÉ—in na sayar da shi tas ban dawo da ragowa ba".
Ba tare da ta kalle ni ba ta ce"kin kyautawa kanki". Daga haka shuru ya cika ɗakin na wani lokaci kafin na gusar da shi ta hanyar faɗin"Umma daman ina ta so na yi miki magana akan bikin sauƙarmu da yake ta matsowa, akwai ankon atamfa da hijabi da zamu yi shi ne nake son idan Allah ya hore miki ki yi mini ko da hijabin ne kaɗai". Sai a sa'ilin ta cira kai ta kalle ni.
"Saura kwana nawa ne yanzu sauƙar nakun?".
Cike da farin ciki na gyara zama na soma zubo mata bayani daki-daki wani na bin wani.
"Yanzu dai saura kwana ashirin da biyar cif sati uku kenan Æ´an kai".
"Allah ya kaimu lokacin".
"Amin ya Allah, me ye za a É—aura?".
"Ki dafa iya abin da za ki ci".
"To". Na amsa mata da shi ina jin raina ya yi mini ƙal zuciya ta washe ta yi tas. Taliyar murji na tafasa na ci da manja da yaji. Wanka na shiga tun ina banɗakin nake jiyo hayaniya har ana dukan ƙofar banɗakin hakan ya sani saurin zura zumbuleliyar hijabinta da na shigo da ita, ina gama sawa ana bankaɗo ƙofar tamkar za a karya ta.
"Na rantse da Allah sai kin fito don ba za ta saɓu ba bindiga a ruwa".
Furucin Ummi kenan da suka sauƙo a ƙofofin kunnuwana tamkar sauƙar aradu ta finciko hannuna ta yi waje da ni.
Tsabar ɓacin rai da baƙin ciki da takaicin da suka yi wa raina rakon dangi ban san lokacin da idona ya makance ba na sauƙewa Ummi mari a kuncinta. Marin da ya jawo hankulan sauran mutanen zuwa gare mu.
"Ubara uban can! Ni za ki mara Amatullah? Ai kuwa kin taro balbalin bala'in da babu ranar mutuwarsa. Daga nan har yanzu lokacin da mahadi zai bayyana".
"Na mare ki ɗin na ce na mare ki Ummi ki yi duk abin da za ki yi. Wani irin wulaƙanci ne wannan ina banɗaki ina wanka za ki buɗe mini ƙofa, shin ba ki yi tunanin a wani irin halin za ki riske ni ba?".
Ta yi hanzarin katse mini numfashi"babu ruwa da ko wani irin hayaniya zan same ki, ai kina ganin ruwana a ƙofar banɗakin kika shiga don haka ban ga dalilin da zai hana ni fiddo da ke waje ba ko da kuwa tsirara kike". Baƙin cikin kalamanta ya tursasa mini runtse idanuna ina jin rai da zuciyata yana wani irin tafasa kafin na yi magana Amira ta iso wajen ta nema jin ba'asin me ke faruwa Ummi ta yi caraf ta amshi zancen tamkar jira take yi.
"Ruwa na ajiye zan shiga banÉ—aki tana gani amma don tsaurin ido ta riga ni shiga shi ne ni kuma na shiga na fiddo da ita".
Tsabar mamaki Amira ta riƙe ƙungunta"kanbu! Kika shiga kika fito da ita? Ke kuma Amatullah kina tsaye duk aka yi wannan abun?".
"Ai in gaya miki Amatullah ba ta yi ƙasa a gwiwa ba, sai da ta ɗauke Ummi da mari in ni ma kaina sai da na ji raɗadinsa balle ita kuma da aka sauƙe shi akan kuncinta". Furucin Maman Vector kenan cikin gurɓatacciyar hausarta da har yanzu ba ta hau hanya ba.
"Tabbas kin cika cikakkiyar ƴar halak, Wallahi da ba ki ɗauki wannan hukuncin ba Amatullah takaici da baƙin ciki sai ya hana ni motsawa daga nan wajen".
"Na rantse da Sarkin dake dake busa min numfashi ban zan yarda ba. Ko sama da ƙasa za su haɗe sai na rama marin da kika yi min, tun da ni ba jakar uwarki ko ubanki ba ne kuma ba cin azurki na zo yi cikin gidan nan ba. Yadda kuke biyan kuɗin haya haka mu ma muke biya". Ummi ta yi ikirarin tana tankaɓar da ruwan da yake cikin bokatin ƙarfe da za ta shiga wanka da shi ta sure shi ta nufo ni gadan-gadan da nufi rotse mini goshi.
Ƙam na tsaya a inda take tsaye kusa da Amira na riga da na ƙudurce a raina cewar duk abin da zai faru sai da ya afku. Ba zan matsa ba balle na yi ƙoƙarin guduwa in ta fasa yin abin da ta yi niyya ma ta raina iyayen da suka yi silar kawo ta duniya. Kafin ta iso gare ni muka ji tas sautin sauƙar mari duk muka jiyo da hakan ya yi daidai sake wani gigitaccen ihun da Ummi ta saka tare da zube a ƙasa tana yin burburku.
Duk muka tsayar da idanunmu akan Baban Adnan da yake tsaye a wajen cikin tsananin fusata ya yi cilli da bukatin da ya amshe daga hannun Ummi.
"Wannan wani irin fitina ce haka? Babu dama mutum ya yi aikin kwana ya dawo gida ya kwantar da haƙarƙarinsa ya huta sai kun ɗaga sa. Kar ku sake ku kai ni bango a cikin gidan nan don idan har hakan ya faru to kowa ba zai ji daɗi ba daga babba har yaro, ko wani bala'i daga gare ki yake fara ɓullowa Ummi". Ya ƙare zancen tamkar zai kai wa Ummi da take yashe a ƙasa duka.
"To wallahil azim yau kam ba zan yarda da wannan cin kashin da ake mana, babu dama abu ya haÉ—u yaran nan sai ka yi wankan tsarki ka tsunguma ciki ka yi kane-kane ka juya zancen ka ba wa Amatullah gaskiya, don ita ce ta gaban goshi".
Furucin Maman Ummi kenan yayin da take ɗaura ɗamara tamkar mai shirin tafiya filin yaƙin duniya na biyu.
"Idan ba ki rufe min baki ba yau sai na nuna miki iyakarki a cikin gidan nan, yanzu waya kawai zan ɗaga kawai na ƙira azo a kwashe ku a kai ku bayan kanta".