← Book details Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 58

Sashe 20

Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daga haka na daina fahimtar abin da take faɗa sai dai na ƙura mata idanu ina ganin leɓanta yana motsawa da hakan ya tabbatar mini da har yanzu ba ta daina maganar ba. Sai da ta taɓo ni kana na dawo daga karatun wasiƙan jakin da na afka na figigi na ɗaga kai ina kallonta.
"Tunanin me ye kike yi ne haka Amatullah? Tun da safe na fahimci akwai abin da yake damunki, amma kika ce min babu komai. Me ye amfanin muna ƙiran kan mu aminai kuma ƴan uwa amma ba ma iya sanarwa junanmu abin da yake damun mu?".

Na ja dogon numfashi na fesar kafin na sama lasisin faÉ—in"Amira babu abin da yake damuna akwai dai matsaloli ne na yau da kullum, kuma kin san ba'a raba bawa da tunani komai daular da yake cikinta".
"Ko kin ɓoye min abin da yake damun ki fuskarki ba zai ƙi bayyanar da labarin zuciyarki ba. Tabbas akwai abin da yake damun ki".

"Babu komai na ce miki babu komai. Ki yarda da ni mana Amira". Ina ƙare zancen na miƙe tsaye na ɗaura daga inda na tsaya"kin ga ni bari na je na duba ko Umma ta dawo". Ban jira abin da za ta ce ba na yi wuf na fice.
Kai tsaye É—akinmu na nufa sai dai kafin na kai ga shiga muryar Baban Adnan ya tursasa mini dakatawa.

"Amatullah ƴan mata, kwana biyu kamar ba kya cikin gidan nan". Maimaikon na ba shi amsa sai na rusuna na gaishe shi na yi wucewa ta cikin ɗaki da mamakina na tarar da har yanzu Umma ba ta dawo ba. Na fito na yi alwalan sallan magrib na zo na yi ina raka'ar ƙarshe Umma ta shigo cikin ɗakin ta zauna tana huce gajiyar da ta kwaso.
Sai da na iddar na shafa addu'ar da na yi kafin na yi mata sannu da zuwa ta amsa mini fuskarta babu yabo babu fallasa, so nake yi na tambaye ta inda ta je amma sam tsoro ya yi mini katutu na kasa cewa komai.

"Umma me ye za a dafa ne?"

"Ki tafasa doya".

"To".

Na amsa da shi a taƙaice ina tashi na fita na haɗa wuta na ɗaura ruwa. Yayin da na ɗauko doyar ina ferewa na zuba a cikin tukunyar. Na ɗaukar jakar islamiyyata ina duba litattafaina. Ban tashi daga wajen ba sai da doyar ta dahu ba soya manja kana na shiga ciki na zuba nawa na ci na yi sallan isha'i na fito zaure wajen yaran da suke jirana. Sosai na zage damtse na yi musu karantu duk wani ƙoƙarin manta abin da yake ta'azzaran raina na yi shi. Muna tsaka da karatun Ummi ta fito daga cikin gida ta tsaye mini a kai kamar mai karɓan bashi.

"Ummi lafiya?".

Ta riƙe ƙugunta tana yi mini kallon hadirin kaji ta ce"ku tashi ku nema wani wajen, zan shigo da Auwal".
Na cira kai ina duban ta da mamakin rainin wayon da yake tafe da ita.
"Ban gane mu nema wani wajen ba? Sanin kanki ne a ko wani daren duniya a cikin zauren nan muke yi karatu a daidai irin wannan lokacin. Sai yau kawai za ki ce mu nema wani wajen don za ki yi zancen, ai kuwa sai dai ke da shi Auwal É—in ku nema wani wajen".
Ta yi poster tana ganina da nake da tabbacin mamakin furucina ne ya hana ta motsawa.

"Lalle Amatullah wuyanki ya yi kauri ya isa yanka. Yau zan bar ki ne kawai amma wallahi gobe ba za ku yi karatu a nan ba".

"Ba gobe ba har jibi da gata ma a nan za mu yi, ki sa hakan a cikin ranki". Ba ta tanka mini ba illa dogon tsakin da ta ja ta fice daga ciki zauren tana shuri da takalmar yaran, na raka ta da kallo har ta fice kafin na ɗauke kaina. Babu jimawa Abba ya dawo na tashi na yi masa sannu da zuwa kana ya shige cikin gida. Ƙarfe tara muka yi addu'a kowa ya watse na naɗe tabarmar na shigo cikin gidan, muka yi kiciɓus da Amira za ta fita daga ni har ita dariya muka sakarwa juna. Na matsa na ba ta waje ta wuce ina faɗin"Allah ya shirya ki ke kam".

Ta bangaje ni"ki sa munjaye Allah dai ya shirya mu". Daga haka ta fice ni ma na ƙarisa ɗakinmu.
Cak! Na tsaya na ɗaga ƙafarta ɗaya amma na gaza sauƙe ta sakamakon zancen da suka sauƙa a ƙofifin kunnuwa tamkar sauƙar aradu, take jikina ya soma rawa kamar ana jona mini wutar lantarki. Zuffa ya soma tsatstsafo wa daga dukkan mafitan gashin jikina, tsoro da firgici ya bayyana ƙarara a fuskata. In dai ba matsalar ji na samu ba tabbas muryar Abba na ji yana cewa"Hafsatu na gama ki da girman Allah kar ki yi fushi da ni zuciyata ba za ta iya jura ba, na yarda ki hukunta da ko wani irin nau'in hukunci amma ban da wannan. Na biya ta wajen Maman Umar ne shi yasa ban dawo da wuri ba ban san hakan zai ɓata miki ba da ban tun magriban fari na dawo cikin gidan nan".

"Manniru ni fa ba zan juri wannan cin mutuncin ba. Sati ba ta cika ba tare da matar nan ta wanko ƙafarta ta zo cikin gidan nan ba yanzu kuma kai da ka baro wajen aiki sai ka wuce wajenta kafin ka iso gida. In ce dai tun ƙarfe biyar kuke tashi daga makarantar amma don kuturun wulaƙanci sai ƙarfe taran dare za ka shigo min cikin gida".
Cikin wani irin yanayin na tsinkayo muryar Abba yana faɗin" ki yi haƙuri in Sha Allah hakan ba zai ƙara faruwa ba".

"Wai Maman Umar ɗin nan ita ta haife ka ne? Ko ita ta yi naƙudarka sai haka. Ni fa na gaji ba zan ɗauki wannan rainin hankalin ba".

Kamar an jawo ni haka na ji na faɗa cikin ɗakin sai dai na yi nadamar shiga ta saboda yanayin da na iske su a ciki. Umma tana tsaye yayin da Abba kuma yake durƙushe akan gwiyoyinsa ya riƙe ƙafarta.

Zuciyata ta yi wani irin harbawa sai da na ji duniyar gabaÉ—aya tana juya mini a lokacin. Da gudu na shige É—aki na zube akan gado, sai dai sam na gaza yin ko É—igon hawaye duk da suyan da zuciyata yake yi mini. Na sa hannuna na toshe dukkan kunnuwana saboda amsa-kuwwar da zancen da na ji suka yi mini a na'urar naÉ—ar sautina.
Har Umma ta shigo cikin É—akin ban motsa daga kwanciyar ruf da cikin da na yi ba, ba ta ce da ni ko kanzil ba ta É—auki abin da ya shigo da ita ta fita. Ba ta dawo ba sai da dare ta raba sosai ta shigo ta kwanta.

[7/25, 11:19 AM] Maimunatu Iyam: *DAFIN HARSHE*

©️ Maimuna Tijjani Iyam

___________________________________

Page1️⃣6️⃣

Har dare ta raba bacci ta ƙi kusanta na illa juyin da nake yi raina cike da wani irin zogin da raɗaɗin da yake tasowa tun daga ƙasan raina yana mamaye mini dukkan sashin da sassan ruhina. Sai da na tabbatar da Umma ta yi nisa a baccin da take har da munshari kafin na tashi na fito na yi alwala na zo na tada salla. Raka'a biyu na yi na sallame na ɗaga dukkan hannayena sama ina yi wa Allah kirari kafin na soma zayyana matsalolina na ƙarƙare da yin addu'ar da Malam Suleiman ya ba ni kafin na shafa addu'ar cikin sanyi da mutuwar jiki.
A zaune a wajen na ƙarisa daren yau sai can gabannin asubahi na runtsa ban yi nisa ba na ji an soma ƙiran sallan asubahi, na yi figigi na tashi ina murtsule idona tare da ƙara kasa kunna don tabbatar da abin da kunnuwana suke jiyo mini. Sai da na tabbatar da cewa lalle sallan ake ƙira kafin na tashi riƙe da kaina da yake matuƙar sarawa, na buɗe ƙofan ɗakin raina cike tal da mamakin abin da ya hana Abba tashi akan lokaci.

Turus na ja na tsaya bayan na kunna ƙwan wuta haske ya gauraye ɗakin. Na hangen Abba kwance a makwancinsa ko tashi bai yi ba, na je na tsuguna a gaban sa na ɗan buga matashin take ya buɗe idonsa ya tashi ya zauna.

"Subhanallahi! Kar dai har an yi ƙiran salla?".

"Tun ɗazu aka ƙira".

"Wallahi gabaÉ—aya na tara gajiya ne a jikina jiya. Shi yasa tun da na wanka ko juyi ban yi ba".
Na jinjina kaina"bari na je na sama maka ruwa a buta". Zan tashi ya dakatar da ni.
"Ki fara zuba wa Ummanki tukunnan. Bari na je na tashe ta". Na sakake ina kallonsa har ya tashi ya shiga cikin ɗakin na kasa tashi daga wajen. Sai da na sauƙe gwauron ajiyar zuciya kafin na tashi kamar kazar da ƙwai ya fashe mata a ciki na fita waje. A buta biyu na zuba ruwan kana ni ma na zuba nawa na yi na koma ciki na gabatar da sallan ko da na iddar ban tashi daga kan slalayan ba na ɗauko al'ƙur'ani na soma karantawa a ƙoƙarin dawo da nutsuwar zuciyata. Ban gushe ina yi ba har sai da na jin ɗan sanyi a cikin raina kana na rufe na ajiye na tashi na soma gyara ɗakin na gyara ko'ina kana na ɗaura mana abin kari.

Na kawo wa Umma da Abba na su, ko gama ajiye wa ban yi ba Umma ta soma faÉ—in"A'a ni kam ba zan ci ma wannan abincin ba É—auke shi kawai".
A hanzarce Abba ya ce"to me ye kike so ki ci?".
Ta yatsina fuska"ba na jin sha'awar cin komai".
"A'a haka kuma ai ba zai yiyu ba ace kin zauna ba tare da kin ci komai ba. Ki faɗi duk abin da kike son ci ni kuma na yi miki alƙawarin samo miki shi matuƙar dai akwai shi a cikin wannan duniyar da muke rayuwa".
Chapter 20 · 0% Book details