← Book details Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 58

Sashe 4

Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta ɗage mini ido guda"tunanin me ye kike yi haka? Ina ta magana kin yi shuru". Na sauƙe ƙaƙƙarfan ajiyar zuciya mai sauti kafin na sama zarafin cewa" ba zan miki ƙarya ba Rauda rayuwar gidanku yana burge ni, yadda muke mu'amala da iyayenku abin sha'awa. Babu tsangwama balle hantara uwa uba kullum cikin sa muku albarka suke yi da yi muku addu'ar shiriya. Ku kam kun dace".
Sai da ta murmusa kafin ta ce da ni"haka kowa yake cewa amma ke ma ai kin dacen mahaifi Amatullah, kowa ya shaida cewar mutumin kirki ne mai ƙoƙarin kiyaye halak da haram. Sannan duk layinku da ke ake kwatance wajen kyawawan ɗabi'u da halayen ƙwarai, ga nutsuwa ga ƙur'ani". Duk mu biyun muka fashe da dariya haka muka ci gaba da tattauna har na iso gida kana muka yi sallama na shiga gida ita kuma ta wuce, layin gabanmu inda za ta iske gidansu.

"Mun rantse da girman zafin Allah ba za ta taɓa saɓuwa ba wai bingida a ruwa. Dole mu ƙwatawa ƴar uwarmu haƙƙinta. Don ba daga sama ta faɗo ba ita ma ƴa ce kamar kowa mai gata da galihu yau sai mun ga abin da ya turewa buzu naɗi".

Kalaman da suka fara sauƙa a ƙofofin kunnuwana kenan yayin da na kutsa kai cikin gidan. Maman Adnan ce tsaye ta sha ɗamara ga kuma wasu jibga-jibgan mata uku masu ƙiran samudawa tsaye a kutsa da ita wanda suka kasance ƴan uwanta ne na jini. Da ƙyar na jan ƙafafuna na ƙariso ƙofar ɗakinmu na rakuɓe jikin Ummata da take zaune tana sauraran rediyo ta yi bakam kamar ba ta san wainar da ake toyawa ba.
Na durƙusa kusa da ita ina cewa"Umma wai me yake faruwa ne?".

"Safina ce ta É—ebo Æ´an tashan Æ´an uwantan suka zo cikin nan suke yin tijara. Wai don mijinta ya lakaÉ—a mata É—an banzan duka, yo daman wacce ta mai da kanta jaka kam ai dole ta zama abin jibga a wajen miji a ko yaushe".

Ɗaya daga cikin matan ta yi kukan kura ta yo kan Umma, kallo kawai Umma ta yi mata ta tsaya cak ta kasa gaba balle baya. Na sha jin ana cewa Umma tana kwarjini da cika ido wannan dalilin ya sanya kowa a gidan yake matuƙar shakka da tsoron shiga gonarta ban gama gaskata hakan ba sai yau ɗin nan.
Ƙafarta ta ɗaura ɗaya bisa ɗaya tana ƙare musu kallon ɗaɗɗaya"ai ko giwa ta faɗi ta fi ƙarfin kare ya ja ta. Idan ki na ji da rashin kunya da tashanci ne to gidansa kika zo. Da kin ƙariso ai da na nuna miki yadda ake yin wasan".

Maman Adnan ta ɗaura hannu a ka ta fasa ihu tana durƙushewa akan gwiwoyinta"shikenan na shiga uku na lalace wannan matar so take yi ta guntile min igiyoyin aurena. Anti ku taimake so take ta ƙwace min miji, jama'ar gidan nan muna gani kun kasa cewa komai".
U
Ɗaya daga cikin mata ta ɗago ta tana faɗin"ta yi tsararo ta raba ki da mijinki Safina. Idan taƙamarta sammako da to mu a hanya muka kwana idan ta san wata ai ba ta san wata, sai mun nuna mata faɗa da aljani sai an shirya wallahi kin taɓo tsuliyar dodo". Tana ada aya ta figi hannun Maman Adnan suka wuce ɗakinta raguwar mata biyun suka rufa musu baya. Shewa Umma ta saka har da tafa hannu tana faɗi"ai ni wargi ce daidai ƙugun ko wani ɗan iska, mu zuba mu gani ɗan halak ka fasa".

"Umma don girman Allah ki fita daga harkan mutanen nan ki bar su su zauna lafiya da mijinta..".

Kafin na ƙarisa ta sauƙe mini ƴatsunta biyar a fuskana, a kufule take cewa"ke har me ye kika sani da za ki zaunar da ni kina faɗa min abin da ya dace na yi ko kar na yi. Amatullah ki fita daga idona na rufe daman ina cike da ke ƴar iska mai kunnen ƙashi, ban ce da ke ki dawo da wuri ki fita min da farar ayan nan ƙofar gida ba?".
Kaina a sunkuye na ce"mun tsaya tsara yadda walimar sauƙar mu za ta kasance ne". Ba ta ce da ni komai ba kamar yadda ba ta ba ni umarnin tashi ba, haka na ci gaba da tsugunawa akan ƙafafuna don na san idan na tashi ni na san abin da na taro. Sai da aka yi ƙiran sallan magrib kafin na tashi daga wajen na je na yi alwala na shiga ɗaki na yi salla na fito na soma ciki-cikin haɗa wutan dare.
Sai da na sha baƙar wahala kafin wutan ya kama na aza sanwa na ɗauko kayan miya na soma yankawa. Ganin mutum tsaye a kaina ya sani hanzari ɗaga kaina ina dafe ƙirjina ganin Ummi ce ya tursasa mini sauƙe ɓoyayyar ajiyar zuciya.

"Ummi lafiya? Kika zo kika yi mini tsaye a tsakiyar kaina?".

"Watau har kin manta abin da ya faru ko?". Ta yi ƙwafa kafin ta ɗaura da cewa"ai idan maye ya manta uwar ɗa ba za ta manta ba. Ke har kin mance rashin mutuncin da kika yi wa Auwal ɗazu watau a tunaninki kin ci banza ko?".

"Ni kin ga na har na kanta kimai. Kin ga Ummi ki tsaya mu yi magana ta fahimta wallahi Auwal ƙarya ya faɗa ba abin da ya faru ba kenan, shi ne fa ya tare ni da maganar banza".

Ta doka mini tsawa"dalla! Rufe min baki, ko da Auwal ya kasance É—an iska ai ba kuma kai matsayin da zai tunkare ki da maganar banza ba. Amatullah zan miki gargaÉ—in dab da mari ki fita daga harkan Auwal, don tun ba yau ba ina ankare da ke a duk lokacin da ya zo hira kin ginda shiga da fita kenan kina shawagi a gabansa kina juya manyan mazaunanki don kawai ki ja hankalinsa. To hawainiyarki ta kiyaye rama ta kuma wallahi Auwal dai nan gani nan bari É—umamen maya na gaba ya yi gaba".
Sake da baki da hanci nake kallon ta har ta kammala zancen tsabar mamakin da ta ba ni.

"Allah ya ba ku haƙuri ke da shi". Na furta a taƙaice ina mayar da hankalina ga aikin da ke gabana.
"Idan ya ba ni ki ƙwace banza shashasha, girman buredi kawai". Ban tanka mata ba har ta ƙarishe tsayiwarta ta gaji ta tafi, tana barin wajen Amira tana isowa ta ja kujera ta zauna.

"Wai me ye take faÉ—a miki ne?".

"GargaÉ—i ta zo ta yi mini akan saurayinta Auwal".

"Cab! Ke kuma kika ce mata me ye?".

"Me ye kuwa zancen da ya wuce na ce ta yi haƙuri".

Ta tafa hannu kafin ta ce"wallahi in ni ce ba ta isa na ba ta haƙuri ba, akan wani saurayinta mai zubin ƴan daudu ga shegen kallon matan tsiya". Ta ɗago kai na yi mata kallo guda kafin na furta"ki rufawa kanki asiri ki yi shuru kafin ta ji ki wani rigimar ya kaure. Kin san ita ba tsohon ta mutu take yi ba balle ta rayu".

Ta tsirtar da tsaki"to sai me ye in ta ji? Ke dai Amatullah Allah ya ƙara miki haƙuri kawai". Taƙaitaccen murmushin gefen baki na yi na amsa da cewa"Amin ya Allah". Mun ɗan taɓa hira kafin ta miƙe tsaye na bi ta da kallo kafin na yi magana ta riga ni.

"Bari na yi shiri fita tallan dare kafin lokaci ya ƙure".
"Da kin zauna mun yi hirar mu ke da in kika fita sai mutum ya yi bacci kafin ki dawo". Ta bushe da dariya kana ta ce"dududu ƙarfe nawa nake dawowa Amatullah? Karfe sha ɗaya ne fa zuwa da rabi. Ke dai bari na wuce na san yanzu an gama dafa min awarar a gidan Tasalla".
Kasa cewa da ita komai na yi har ta wuce saboda mamakinta da nake yi na rashin tsoro komai dare ba ya hana ta fita talla haka kuma za ta ratso ta dawo gida idan ta gama soya awarar.

Sai da na kammala girkin na kwashe na tattare wajen, na ɗeba nawa na ci a wajen na kai wa Umma na ta kana na ajiye na Abba. Wanka na yi na yo alwala na yi sallan isha'i na ɗauko littattafaina na fito zaure ina nake ƙara wa yara karatu bayan sallan isha'i.
[6/14, 11:31 AM] iyammaimuna: *DAFIN HARSHE*

©️ Maimuna Tijjani Iyam

______________________________________

Page 0️⃣4️⃣

Muna tsaka da karatun Abba ya shigo na miƙe zan karɓa ledar dake hannunsa bayan na yi masa sannu da zuwa.
"Zauna ku ci gaba da karatunku". Ya furta fuskarsa washe da annuri, hasken ƙwan fitillan aci bal-bal da na kunna a wajen shi yake ba ni damar kallon fuskarsa har na fahimci yanayin da yake ciki. Ƙarfe tara na sallami yaran kowa ya watse kafin na koma cikin gidan.
"Hafsatu na gargaɗe ki da ki fita daga harkan Ibrahim da kuma matarsa amma kin yi kunnen uwar shegu da zantukana. Ki sani kin fara kai ni bango fa, me ye haɗinki da mijin wata bayan kasancewarki matar aure? Da ilminki da komai amma kike takewa wane irin rayuwa ce wannan kika ɗaurawa kanki?. Saboda son zuciyarki da masifar son kuɗi ki ja wa baiwar Allah duka daga wajen mijinki kuma tsabar tsaurin ido irin na ki kika yaɓawa ƴan uwanta magana".

Zantukan Abba kenan da na fara cin karo da shi yayin da na kutsa kai cikin falon. Jikina ya yi sanyi ƙalau kamar kazar da aka jefa da ruwan gishiri, shirib na zauna akan ɗaya daga cikin kujerun da suke cikin ɗan madaidaicin falon na mu da hakan yake ba ni damar sauraron abin da suke tattaunawa daga cikin uwar ɗaka.

"Roƙansa kuɗi na yi ko kuma maula na yi? Da za ka ɗebo tsamin jikinka ka zo kana yi min hayagaga a kaina. Dare ma da ya kasance mahutan Bawa ba za ka taɓa barin mutum ya huta ba".

"Hafsatu ni kike cewa ina yi miki hayagaga?".
Chapter 4 · 0% Book details