← Book details Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 58

Sashe 39

Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Munanan kalaman da Umma ta yaɓa mini kenan da ya tursasa Yaya Alhassan tsaya cak ya kasa gaba ya kasa baya, ya runtse idanunsa cike naman leɓensa alamar ya ji zafi da ɗacin kalaman Umma matuƙa. Ina iya jiyo ajiyar zuciyar da ya saka daidai sa'ilin da yake buɗe idanunsa ya fita na yi wuf na bi bayansa ina ƙiran sunansa cikin kuka da tsananin damuwar da ya sanya ƙirjina yi mini wani irin nauyin gaske.
Bai amsa mini ba kamar haka nan bai waigo ba ya ci gaba da tafiyarsa har sai da muka zo zaure kana na yi nasarar shan gabansa. Na haɗe dukkan hannayena waje guda alamar roƙo ina wani irin kuka mai matuƙar ciwo da cin rai, duk yadda na so ce da shi wani abu na gaza samun wannan damar saboda galabaitar da ni da kukan ya yi jikina har rawa yake yi tamkar ana jona mini lantarki.

Babu shiri na durƙushe akan gwiwoyina sakamakon gazawar ƙafafuna ban gushe ba ina yin kukan don a halin da nake ciki shi kaɗai ne abun da nake yi na ji sanyi a raina, bayan ambaton Ubangijina.
Na ja dogon numfashi na fesar kafin na sama zarafin faÉ—in"don Allah kar ka tafi".

Ya tsuguna akan ƙafafunsa a gabana kansa a ƙasa gabaɗaya shi ma jikinsa ya mutu murus. Zan yi magana ya ɗaka mini hannu.
"Ba sai kin ce komai ba Amatullah ba ki da laifi kuma ba ki yi mana komai ba. Anty uwa ce a gare mu baki ɗaya dama su iyaye wani lokacin sai ana haɗawa da haƙuri, ko kaɗan ban ji ciwon abin da Anty ta yi ba kuma ke ma ina so ki cire damuwar hakan daga cikin ranki, ki daina wannan kukan laifinmu ne don mun zo ba tare da mun sanar ba".

Na jijjiga kaina alamar ban gamsu da kalamansa ba"ina mai ba ku haƙuri a madadin Ummata. Don Allah ki yi mata uzuri...". Kafin na gama maganar ya ɗaura yatsansa a saman leɓena alamar na yi shuru.
"Normal ne fa don haka kar ma ki damu. Yanzu dai alfarman da za ki yi min shi ne ki goge fuskarki ki daina wannan kukan har tsakiyan kaina nake jin sa".

Ya ƙarƙare zancen yana zaro handkerchief ɗaga aljihun farin jamfan da yake jikinsa ya soma goge mini fuskana da shi, na koma sauƙe ajiyar zuciya wani na bin wani tamkar wacce ta yi aikin fasa dutse.
Tamkar daga sama muka ji an sheƙa mana ruwan sanyi duk muka yi mutuwar zaune na wucen gadin, sanyin ruwan na ji ya ratsa har jini da jijiyoyin jikina na daskare a wajen na kasa motsa gaɓoɓin jikina illa idanuna da nake sarrafa su daga wannan gefen zuwa wani.
Ummi da mahaifiyarta ce tsaye a kanta sun riƙe ƙugu suna jefanmu da wani irin kallo da na gaza gano manufarsa.

"Bayin Allah lafiya? Za ku yi mana wannan aika-aikan?".

Yaya Alhassan ya jefa musu tambayar yayin da yake miƙewa tsaye yana kakkaɓe jikinsa da ruwan ya yi masa lajab.
"Ahayye! Yau ina ganin iskanci da wasalinsa. Ai kamata ma ya yi idan ka dawo cikin hankalinka ka yi mana godiya".

Cikin rashin fahimta ya ce"godiya kuma? Na meye kenan?".

"Aw tambaya ma kake yi? To bari ka gani". Take Umman Ummi ta soma kurma shewa kan ka ce kwabo ta tara mana mutanen gidan manyansu da ƙanana suka cika akan mu suna rige-rigen kallon mu tamkar jinjirin watan Ramadana.

"Wai me ye yake faruwa ne?". Baba Habu ya tambaya, Ummi ta yi caraf ta ce"ga su nan kama su muka yi suna aikata baÉ—ala sun fita daga cikin hayyacinsu. Har sai da muka watsa musu ruwa kana suka dawo cikin hayyacinsu". Take wajen ya ruÉ—e da salati da sallallami kowa sai tofa albarkacin bakinsa yake yi ba tare da su ba mu damar cewa komai ba. Cikin tururuwan mutanen ban ga Ummana ba amma Abba kam tun da Ummi ta yi jawabin da ya hargitsa wajen bai ce komai ba, illa dafe kansa da ya yi cikin wani irin yanayin da kalmomin baki sun yi kaÉ—an wajen siffanta su.

"Me kuke jira? Ba za ku taru ku lakaÉ—a musu É—an banzan duka ba".

Na jiyo maganar ta gefen inda nake yashe sai dai na kasa tantance mai muryar, kafin na yi yunƙurin tashi na jiyo muryar Abba a karon farko.
"Ku yi haƙuri su ɗin dukkan su ƴaƴana, a ba ni damar ganawa da su kafin yanke ko wani irin hukunci". Aka wani ƙananun maganganu kafin a hankali-hankali aka fara watsewa daga wajen.

"Kawu wallahi wallahi sharri suke yi mana, ba mu aikata abin da suke zarginmu da shi ba. Amatullah Æ´arka ce ka fi kowa sanin irin tarbiyan da ka yi mata ni ma kuma ka san halina, ka san abin da za mu yi iya aikatawa da akasin hakan. Kawu ka yarda da ni sharri ne kawai.....".

Abba ya ɗaga masa hannu alamar ba ya ƙaunar jin komai daga gare sa.
"Alhassan ka wuce ka tafi, ina roƙanka da ka ɗauke ƙafarka daga zuwa gidan nan har sai wannan ƙurar ta lafa".

"Kawu don Allah ka saurare ni na yi maka bayani...".

"Alhassan ka wuce ka tafi ka tafi na ce, zan zo gidan na same ka". A tsawace Abba ya yi zancen har sai da zauren ya amsa. Cikin sanyin jiki da na murya Yaya Alhassan ya ce"shikenan Kawu na gode mu kwana lafiya".

"Amin".

Abba ya amsa da shi ciki-ciki bai ko kalle inda nake ba ya juya zai bar wajen, daidai sa'ilin da Amira ta iso tamkar an jefo ta sai da ta matsa kana Abba ya wuce. Ta iso inda nake yashe ta ɗago ni tsaye sai dai na kasa tsayiwa akan ƙafafuna.

"Wai me yake faruwa ne Amatullah? Tun ina wanka nake jiyo tashin hayaniya, na fito kuma na zo na tarar da taron mutane".
Na kasa cewa da ita komai illa kukan da nake yi tamkar raina zai fita, ƙafafuna suka fara rawa alamar sun gaji da ɗaukar nauyin sanƙararren gangar jiki da ba shi da maraba da bishiyar da ta baza jijiyoyinta a ƙarƙashin ƙasa. Na kwantar da kaina a saman kafaɗunta saboda jiri da hajijiyan da yake kwasa ta yana ƙoƙarin buga ni da ƙasa.
Haka har muka iso cikin ɗakinsu muka yada zango a falo har izuwa lokacin hawaye ba su bar kwaranya daga idanuna ba. Take jikina ya ɗauki zafi gau zazzaɓi mai ƙarfi ya rufe ni babu shiri na soma rawar ɗari tamkar jinjirin kazan da ruwa ya yi masa ɗan banzan duka.

"Don Allah ki yi haƙuri ki daina wannan kukan. Ki nutsu ki yi min bayanin abin da ya faru"

Amira ta yi zancen cikin damuwar da ya bayyana har a kalamanta. Na ja dogon numfashi na fesar daga bakina ina kafe ta da rinannun idanuna da suka sha kuka har suka saduda.
"Sharri suke yi mana, wallahi ba mu aikata ba".

"Sharrin kuma? Su waye suka yi muku sharrin kuma ke da waye?".

"Yaya Alhassan".

Ta maimaita sunan kafin ta zarce da faɗin"wani irin sharri? Kuma waye ya yi muku sharrin?". Sai da na cije leɓena saboda takaicin da ya cika mini raina kafin na sama zarafin cewa"Ummi da mahaifiyarta, su yi mana sharrin aikata baɗala ni da Yaya Alhassan. Lamarin da ya fusata Abba matuƙar har ya juya baya a Yaya Alhassan, Amira zuciyata bugawa take yi wallahi". Na ƙare zancen cikin rauni haɗe da ƙara fashewa da wani irin kuka mai cin rai da ruhi, na riƙo hannunta na ɗaura a saman ƙirjina da nufin ta ji yadda yake bugawa fiye da kima a kimiyance.
Duk ƙarfin hali irin na Amira sai gabaɗaya jikinta ya yi sanyi ƙalau ta kasa cewa da ni komai balle ta iya furta kalaman rarrashi a gare ni illa kallo na da ido tamkar majigi.

"Amira zan je na yi Abba bayanin duk abin da ya faruwa. Zan je na goge zargin da ya ɗarsu a cikin ransa". Na ƙare zancen tare da yin zumbur zan miƙe ta riƙo hannuna gam.
"Kar ki je kar ki je yanzu, ki bari sai ya huce tukunnan kafin ki je masa da kowani bayani". Na girgiza kaina"ba zan iya jira ba don hankalina ba zai taɓa kwanciya ba". Na yi kai aya ina ƙoƙarin fizge hannuna daga riƙon da ta yi mini sai dai ban yi nasarar yin hakan ba.

"Amatullah ki nutsu mana. Ba ki da kalmomin da za ki yi amfani da shi a yanzu wajen fahimtar da Abba ya fahimce ki saboda ransa ya riga da ya ɓaci. Ki yi haƙuri ko zuwa gobe da safe ne sai ki yi masa magana".

Na gaza cewa komai na faɗa jikinta ina ƙara sakin wani kukan mai matuƙar sauti, haka na ci gaba da yi duk lallashin da take yi mini bai yi amfani ba. Har sai da mahaifiyarta ta shigo ta sanya baki haka na lafa ta tashi ta shiga cikin uwar ɗaka ta bar mu.
"Yanzu za ki tashi ki je ki kwanta ne ko kuma? Don kin ga Baba Habu yana gari ni zan je gidan Ta salla ne na kwana....".

Na ji caraf na katse ta"daman kina zuwa wani wajen kwana ne?".
"Ban taɓa zuwa ko ina ba yau ne dai zan fara. Don ko Umma ba ta fito ta faɗa min ba na lura akwai takura a zaman, na yanke shawarar in dai Baba Habu yana gari zan dinga zuwa kwana sanda baya nan sai na kwana a gida".

"Waye ya ba ki wannan gurguwar shawarar Amira?. Duk wata Æ´a mace fa kwana a cikin gidan mahaifinta ko da kuma filin taku É—aya ne shi ne cikar darajarta".

"Ya kamata ki fahimce ni Amatullah don ke ma a cikin wannan yanayin kike. Ki na gaji dai gidan kowa É—aki ne da falo gare shi, in dan Baba Habu ya dawo shi da Umma suna cikin É—aki ni kuma ina kwanciya a falo amma hakan bai hana ni sauraron duk abin da suke yi kamar a gabana suke aiwatarwa ba, hatta idan suna raya sunna ina ji yi sumbatun da suke yi. To da hakan ya ci gaba da faruwa ai gwara na nemawa kaina mafita ko?".
Chapter 39 · 0% Book details