Sashe 42
Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ban É—au lokaci ba na isa wajen aikin Yaya Alhassan na gyaran shinkafa, na tsaya a waje ina ta hange-hange kafin can na hango wani saurayi yana fitowa daga cikin wajen na yi hanzari na isa gare sa bakina É—auke da sallama. Ya amsa yana kafe ni da idanuna.
"Don Allah wani taimako nake nema".
"Ina jinki".
"Ina so ayi mini magana da wani ne a ciki, sunansa Alhassan". Ya yi ƙuri yana kallona kafin can ya furta"a wani sashi yake aiki? Kin san akwai ɓangaren masu zuba ita shimkafan a buhu akwai masu ɗinke bugun sannan akwai masu lissafi". Na yi shuru ina cizon ɗan ƴatsa, kafin na kai ga furta wani abun ya katse mini hanzari.
"Mu je ciki sai na saka a duba miki shi. Amma me ye haÉ—in ki da shi Alhassan É—in?".
"Yayana ne". Ya jinjina kansa yayin da ya yi gaba ina bin sa a baya muka bi ta wani ƙaramin ƙofa mun ɗan yi tafiya mai nisa kafin na tsaya saboda ganin wajen shuru babu gilmawar mutane.
"Malam wai ina za mu je ne?".
"Ina kike tunani?". Na yi zancen yana riƙo gefen hijabina na fizge ina nuna sa da ƴar manuniyar ƴatsata.
"Kar ka sake ka yi kuskuren taɓa jikina, don ina mai tabbatar maka da cewar hakan da za ka yi shi ne kuskure mafi girma da za ka yi a rayuwarka".
Da mamakina sai na ga ya fashe da dariya yana ƙara matso ni. Na sa dukkan ƙarfina na hankaɗe sa ya faɗi sai dai kafin na yi wani yunƙuri tunin ya tashi ya finciko ni ya ɗaga hannu da nufin zabga mini mari. Na yi saurin runtse idanuna cike da tsoro ina jira na ji ta wani ɓangare zai sauƙe mini marin, jin shurun da na yi na sanya ni buɗe idona a hankali.
Tagwayen ajiyar zuciya na sauƙe bisa ganin Yaya Alhassan da na yi tsaye a wajen ya riƙe hannun mutumin da ya ɗaga da nufin zuba mini mari.
"Halilu ashe har yanzu ba ka sauya wannan halin nakan ba?. Ina maka nasiha da ka tun kafin lokaci ya ƙure mata ka sauya zuwa mutumin kirki wanda iyaye da al'umma za su yi alfahari da shi".
Yana gama faɗin hakan ya sakar masa hannunsa, cikin rawar jikin da borin kunya mutumin ya bar wajen tana ta muzurai tamkar wanda ya yi wa sarki ƙarya.
"Amatullah me ye ya kawo ki wajen nan?".
"Wajen ka na zo Yaya Alhassan".
Ya murtuƙe fuskarsa tamkar bai taɓa yin dariya ba"me ye kawo ki? Me ye da ba za ki iya zuwa gida ki same ni ba. Yanzu da ya yi galaba akan ki fa, ki wuce ki tafi islamiyyarki in kun tashi zan zo na same ki a can".
"Don Allah Yaya Alhassan ko minti biyu ne ka ba ni, ka saurari abin da na zo da shi".
"Ki wuce ki tafi". Cikin tsare gida ya yi zancen da hakan ya hana ni cewa komai haka na wuce na tafi har na isa islamiyyar ina ji na wani iri, ina shiga aji na kifa kaina akan benci ina kuka marar sauti ban gushe ina yi ba har sai da Malam Suleiman ya shigo ajinmu kana na ɗago kaina fuskana ya kumbura ya ya tsimtim yayin da idanuna suka yi ƙulu-ƙulu tamkar za su faɗo ƙasa.
Har aka fito salla jikina gabaɗaya babu ƙwari tamkar kazar da ƙwai ya fashe mata a ciki. Ko tambayoyin da Rauda da Ammi suke haɗe suna yi mini ban amsa musu ko guda ba ko da suka matsa mini cewa na yi da su ba ni da lafiya ba, dole suka rabu da ni bayan sun yi mini addu'ar samun sauƙi.
Tun kafin mu fito daga cikin aji na hango Al'amin da alama ni yake jira haka kawai na ji raina yana ɓaci ba tare da wani dalili ba.
Ko da aka shafa fatiha mun tattaunawa sosai akan walimar sauƙarmu da yanzu ya rage saura kwanaki ashirin cif, an tsara komai yadda zai gudana domin abubuwa su tafi yadda ake so a kuma fita kunyar baƙin da aka gayyata.
Muna fitowa daga ajin na yi wa su Rauda sallama na ɗauki hanyar har na yi nisa na ji ana ƙiran sunana. Ya tsaya ina dafe goshina don muryar Aliyu ce, ban motsa ba har iso gabana.
"Saurin me ye kike yi haka? Tun da kuka fito nake ƙiran sunanki amma ba ki waigo ba".
"Aliyu yau ba na jin daÉ—i ne so nake yi na tafi gida da wuri". Cike da kulawa ya furta"Ayya! Sannu ai ban sani ba da ban tsayar da ke ba. To amma don Allah ina neman alfarma ina son gobe idan kin shigo akwai maganan da za mu yi da ke".
"To ba matsala sai goben". Na furta ina barin wajen ba tare da na jira abin da zai ce ba. Ina shawo kwanan layinmu na hango Yaya Alhassan akan mashin É—insa yana zaune yana latsa wayar hannunsa.
Na ƙara sautin da nake yi na isa gare shi bakina ɗauke da sallama sai dai duk jikina ya bi ya yi sanyi ganin yanayin da ya amsa mini sallamar fuskarsa babu walwala balle annuri.
"Sai yanzu aka tashe ku?". Na yi ƙasa da kaina"mun tsaya mun tattaunawa akan walimarmu ne shi yasa na ɗau lokaci". Ya jinjina kansa yana kallo ya furta"gani kin ce za mu yi magana".
Kunya gabaɗaya ta yi mini dabaibayi na yi ƙasa da kaina"daman na je na ba ka haƙuri ne akan abin da ya faru". Ya ɗaga mini hannu alamar na dakata. Ya cira kai yana kallo na tare da faɗin"ba ki yi min komai abin da ya faru kuma ai ƙaddara ce wacce ba ta wuce rana da sa'ilin ta. Don haka ki ma manta da abin da ya riga ya faru, damuwata ma shi ne kar hakan ya sa Abba ya yi fushi da mu".
"Abba bai yi fushi ba. Don ya fahimci mu sosai kuma ya yi imanin cewar ba za mu aikata abin da suke zarginmu da shi ba". Ya yi ɗan jim kafin can ya ce"amma gaskiya mutanen nan sun ba ni matuƙar tsoro. Na sha jin ana cewa ka guji sharrin mace ai ranar na ga zahirinta".
"Yaya Alhassan sharri ai dodo ne mai shi ya kan ci". Ya jinjina kansa cike da gamsuwa"haka ne kam. Yanzu dai ya batun sauƙan nakun me da me ake buƙata".
Na lissafa masa komai da komai da za mu yi. Bai ce komai har sai da na gama lissafin ya É—ago ido ya kalle ni"shikenan ko akwai sauran wasu abubuwan?".
Na waro idanuna"kai! Yaya Alhassan to waÉ—annan É—in ma da na lissafo ba dole sai na yi su dukka ba. Hijabi daman Umma ta ce za ta yi mini ko atamfar ma ka yi mini wallahi ta isa".
"Ko atamfar ma ka yi mini wallahi ta isa". Ya kwaikwayi muryata da hakan ya sani murmusawa ina rufe fuskana.
"Duk abin da kika lissafa da ma wanda ba ki saka su cikin lissafin duk sai na yi miki su Amatullah. Gobe idan kin taso daga islamiyyar ki bi ta wajen Anty Zulaihatu zan ajiye miki a can sai ki karɓa".
Na turo baki ina furta"kar ka É—aurawa kanka nauyi da yawa fa".
"Ke ɗin ce za ki zama min nauyi? To ashe in haka ne ni ma wataran zan gaji da ɗaukar nauyin kaina da kaina. Amatullah ke ƴar uwata ce kuma ba zan gaji da yi miki ɗawainiyya ba har abada, yanzu dai ki wuce gida magriba ta kusa". Godiya na gabatar masa sosai kana muka yi sallama ya wuce yayin da ni kuma na ƙariso gida, ina shigowa ana ƙiran sallan magriba don haka sai da na yi alwala kana na shiga ciki na yi salla, na sauya kaya na fito na haɗa wuta na ɗaura girki. Ina girkin ina biya karatun da aka yi mana haka Amira ta zo ta iske ni har sai na kai ayan da na ɗauko kana na kallo ta tare da cewa"yau ba za ki ke tallan taren ba ne?".
Ta dafe ƙirji"ni jikar mutum huɗu rufa min asiri. Ai wataƙila in dai ba wani ikon Allahn ba kuma na daina tuya awarar dare".
"Me yasa?".
"Mansur ya ce ba ya so iya na safen da nake zuwa na ya isa. Ya ce na yi masa lissafin abin da nake samu a toyar awarar a kullum zai na ba ni, kin ga kuwa ai kakata ta yanke saƙa".
Na tallafe kuncina ina kallon ta"to Allah ya saka masa. Amma ni kam da wannan kashe miki kuÉ—in da yake yi É—in nan ai gwara ya fito ayi maganar aurenku. Tun da dai alhamdulillah yana da rufin aisirinsa daidai gwargwado".
"Yana so sai ya gama gininsa ne kana ya zo gida. Yau ma zai zo mu haɗe a gidan Tasallah za mu fi sakewa a can, kin san gidan nan da tsegumi da sa ido shi yasa duk nacin son zuwa hirar dare irin na Mansur na shata masa layi, ban isa ayi min sakiyar da babu ruwa ba, yadda ƴan matan gidan nan suka ƙware wajen ƙwacen saurayi ban isa ba. Don tabbas idan Mansur ya juya min baya ko ban bar duniya ba sai na zama marar amfani ta yadda ba zan iya amfanin kaina ba balle wani".
"To ya dai kamata iyaye su shiga cikin zancen gaskiya".
"Kar ki damu in Sha Allah ban da wani na mijin da ya wuce Mansur a duniya da lahira". Na bushe da dariya kafin na yi magana Abba ya shigo muka haÉ—e baki wajen amsa sallamar da ya shigo da ita, muka yi masa sannu da zuwa ya amsa ba tare da ko kalle inda muke ba.
"Wai har an yi isha'i?".
Amira ta tambaya, na gyaÉ—a kaina"ga shi kuwa tun da kika ga Abba ya shigo".
"Bari na yi je na yi salla kafin kin gama girki sai mu tafi".
"Wallahi Amirka yanzu kuma sai na ji gabaɗaya hankalina bai kwanta da zuwa gidan Tasallan nan ba, ina jin kamar ƙaddarar faruwar wani mummunan abu ne zai kai ni".