← Book details Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 58

Sashe 14

Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Sai yau na tabbatar har yanzu ba ki da hankali Amatullah girman jiki ne kawai da ke amma hankali kam sam babu shi a tattare da ke. Don ya wulaƙanta ni sai da ya ƙira yo ki sannan ya yi wannan ikirarin, ko rantsuwa na yi ba zan yi kaffara ba wannan duk shiri da tuggun Maman Umar ne kuma sai na nuna mata ina daidai da zamaninta. Manniru kai da ka bar gidan nan wallahi sai dai a cikin makara amma zaman daram yanzu ma aka fara sai mun ga abin da ya turewa buzu naɗi".
"Umma ki tuna fa komai ya yi zafi maganinsa Allah shi ne ya ke juya dare zuwa rana. Ya yaye ƙunci ya wanzar da farin cikin a zuciyar da cikinta babu kusuni. Me zai hana ki yi alwala ki yi salla raka'a biyu ki ba shi zaɓi ya zaɓa mana mafi alkhairi". Ba ta ce da ni komai ba illa bangaje ni da ta yi gefe guda ta shiga ɗaki ta ɗauko hijabinta ta fita, zubewa na yi a wajen na kwanta na yi luf ina sakin wani maraya kuka marar sauti.

Jikina gabaɗaya ya yi sanyi ƙalau ji nake yi kamar na tashi na ruga da gudu na je na dakatar da Umma daga abin da yake shirin aikatawa, sai dai gangar jikina ya ƙi ba ni haɗi kai wajen motsa ɗaya daga cikin gaɓoɓina. Har na ci gaba da kwanciya har izuwa lokacin da Amira ta shigo ta iske ni cikin mayuwayacin hali. Cikin tashin hankali ta iso inda nake zube ta ɗago ni sai dai na kasa tashi dole na koma na zauna na kifa kaina akan gwiyoyina ina ci gaba da kukan.

"Amatullah me ye ya faru?". Ta jefa min tambayar muryarta tana rawa, rashin samun daga gare ni bai hana ta ci gaba da tambayar duk abin da take tunanin shi ne sanadi da musabbabin kukan nawan ba.
"Ko dai mutuwa aka yi muku ne?". Na jijjiga mata kaina alamar a'a kafin na yi nasarar cira kaina ina duban ta da kumburarrun idanuna da suka rikiÉ—e suka sauya kala zuwa launin ja.
"Da abin da yake shirin faruwa ai gwara mutuwar ma Amira. Tun da dai shi wanda ya mutu ya huta daga rikici da fituttunun duniya sai dai ya je ya tarar da abin da ya shuka".

Ta waro idanunta tar a kaina"ke kin san zafin mutuwa kuwa? Ko don har yanzu kina ganin iyayenki biyu kuna rayuwa tare? Billahillazi mutuwa ta fi komai ciwo da raÉ—aÉ—i don har yanzu zuciyata cike take da gurbin rashin mahaifina duk da ya rasu tun kafin na mallakin hankalin kaina. Kuma alhamdulillah Baba Habu mijin Umma bai bar ni na yi kukan maraicin uba ba".

"Wani babban lamari ne yake dab da faruwa ko ina ce warhaka kam komai ya faru".

"Ki sanar da ni me ye yake faruwa don Allah, kar ki bar ni cikin duhu Amatullah".

Dogon numfashi na ja na fesar kafin na zayyana mata duk abin da ya wakana ban ɓoye mata komai haka nan ban tsallake ko da layi guda ba. Ta yi shuru kamar mai tunanin wani abu kafin can ta yi magana.
"To amma ke me ye kike tunanin ya sanya Abba yanke wannan hukuncin lokaci guda haka?".
"Ban san dalilinsa na yanke wannan hukuncin ba kuma cikinmu babu wanda ya tambaye sa".

Ta gyara zamanta kafin ta soma cewa" Samu gidan hayan a ƙurarran lokaci fa abu ne mai matuƙar wuya gwara ma ina kana da kuɗinka a hannu. Kuma ko da kuɗinka ma ba za ka sama yadda kake so ba, shi yasa gaskiya ni ban ga laifin Umma ba. Me ye amfanin a yi abun da daga baya za a zo ana dana sani?". Mamaki kwance a fuskana nake bin ta da kallo saboda dukan da zantukanta suka yi wa kwanyata.
"Kina nufin ba ki ga ma rashin dacewar abin da Umma za ta yi a addinance ba kenan?".
Ta riƙo hannuna"har ga Allah ban ga ni ba, don a tunanina haƙƙin kowacce uwa ne samar da daidaito a rayuwar gidan aurenta. Kuma Umma ta fi mu tunani ba za ta taɓa yanke hukuncin da zai cutar da ɗaya daga cikinku ba don haka kawai ki goya mata baya". Na fizge hannuna"kin manta wajen wanda na ce miki za ta je ne Amira? Wannan Malamin ba da yake fakewa da addini yana aikata alfasha. Ta inda mutum kamar ta mai ƙafafu biyu zai taimaka maka bayan shi ma mabuƙaci ne a wajen Allah?".

Taƙaitaccen murmushi ta yi tana kallona da wutsiyar idonta ta furta"amma kin san aikinsa yana tasiri akan ko waye kuma an yi ittifa'i ba a taɓa zuwa masa da kukan da ya kasa gogewa mai shi hawaye ba. Bari na sanar da ke wani sirri ko Ummata da shi ta dogara wajen kankaro mutunci, daraja har da kima a idanun Baba Habu".
"Kina nufin Ummanki tana zuwa wajensa? Tirƙashi!". Na yi mata tambayar a rikice.
Ta gyaɗa mini kanta"ƙwarai kuwa har ma tana aike na na karɓo mata saƙo daga wajensa".
"Innalillahi wa inna ilaihir raji'u! Shikenan mun shiga uku!".

Na furta cikin maɗaukakin tashin hankalin gami da firgicin da yake ƙoƙarin tarwatsa zuciyar da take dashe a cikin ƙirjina. Da mamaki babu ko ɗigo mamaki balle kiɗima a tattare da Amira.
"Me ye abun cewa mun shiga uku Amatullah? Ni da wannan kalmar tsinka min zuciya take yi, zamanin ne ya lalace an daina kiwon dabba an koma na mutum. Ba ka damu da mutum ba amma shi yana can yana hana idonsa runtsawa a ƙoƙarin ganin ya ga bayanka kin ga kuwa ai dole ka tashi ka kare kanka, tun da ko Allah ma cewa ya yi sai ka tashi sannan zai taimake ka".
Takaici ya zo mini har wuya wani ɗaci ya gauraye da yawun bakina ya jirkita shi gabaɗaya ta yadda sai da na ji kamar na yi amai. Da ƙyar na haɗiye sa ta hanyar wuyana ya wuce kamar na haɗiye ƙarangiya.

"Ai ba irin wannan lamarin ake nufi ba. Ta yaya za ka je wajen wanin Allah kana neman taimakon da shi kasan in ya tsinci kansa a cikin irin halin da kake ciki ba zai iya samarwa kansa mafita ba, kina ganin akwai basira a cikin aikata hakan?". Ta taɓe baki tana jefa da wani irin kallo alamar ta soma gajiya da fahimtar da ni abin da kaina ya gaza ɗauka balle ƙwaƙwalwata ta amshe shi.
"Ni kam ban wani irin taurin kai Allah ya zuba miki ba. In da kin fito a cikin mutanen farko irin riƙaƙƙun kafiran nan zai yi wuya ki karɓi musulmci, ga zahiri nan ki na kallo amma kuma runtse ido . Amatullah ya zama dole fa mu amshi abin da zamani ya zo mana da shi, mazan ne yanzu sai da haka sai ana danganawa ga Malamai kafin a shawo kansu. Na rantse miki ba don irin wannan taimakon daga malamai ba da yanzu wani maganar ake yi ta daban mussamman Baba Habu da Allah ya yi wani irin murɗaɗɗan mutum mai wuyar sha'ani, a hakan ma yaya balle kuma an zauna haka nan".

Ni kam shuru na yi don gabaÉ—aya na rasa me ye zan ce da ido kawai nake bin ta har ta kai aya. Na ja wani gauron ajiyar zuciya na fesar kafin na gyara zamana, na soma ambaton Allah a cikin zuciyata.
Ina da tabbacin shurun da na yi ne ya sanya ta ta ture komai ta koma kwantar mini da hankali da kalamai masu taushi da sanyi. Har sau da na ji raina ya sanyaya, na ƙara yarda a duniya bayan iyaye da dangina ba ni da wacce take yi mini irin ƙaunar da Amira take gwada mini wanda babu sirki a cikinsa.

"Yanzu dai ki tashi mu gyara É—akin nan. Sannan na ba ki wani daddaÉ—an labari".
"Fara ba ni labarin tukunnan". Na yi zancen cikin dauriya ina ƙoƙarin dasa murmushi a fuskana.
"Mansur yanzu haka yana hanya. Saura kuma in munje ki ɗaure fuska ki yi ta shan magani". Ta ƙarishe zancen tana galla mini harara.

"Allah ya kawo shi lafiya".
"Amin ta hannun dama.Don Allah ki saki ranki ke ba wani shegen kyau kike da shi ba kuma ki zo kina wani ƙara haɗe hanci da gira duk sai ki ƙara muni". Ta ƙarishe zancen tana galla mini harara.

"Ai kuwa a hakan kin san na fi ki kyau sau dubu ɗari". Ta fashe da dariya tana faɗin"kin dai fi mi auki shi ma kuma girman buredi ina gaya miki, amma ni ba ta yau ba ce". Daga haka duk muka saka dariya kamar babu wani abun da ya faru, wannan dalilin yana daga cikin muhimman dalilin da yasa nake jin Amira har ƙasan raina. Don ba ta jure ganina cikin ƙunci duk yanda zai ta yi sai ta yi ta fitar da ni daga halin da nake ciki. Tare da ita muka yi komai har na ɗumama mana ragowar abincin jiya muka ci ita ma ta amso mana waina a wajen Ummanta muka ci muka yi hani'ƙan, sai na ji duk damuwar da na tashi da shi na neme shi na rasa sa. Muna gamawa wayarta ta soma ruri ta hasko mini fuskar wayar tana faɗin"kin ga Mansur ne".
Ta ɗaga ya sanar da ita ya zo muka tashi muka fito har mun zo zaure kafin ta soma ba ta labarin yadda muka yi da Abba daren jiya. Ta ja ta tsaya riƙe da kunkuminta tana kallona.

"Kina nufin Abba ya gane gaskiyar komai? Mun shige su". Na gyaÉ—a mata kaina alamar e.
"Wallahi ya gane komai amma na ba shi haƙuri ya ce komai ya wuce sai dai na kiyaye gaba".
Ta murmusa kafin ta ce"Allah sarki! Abba wallahi sauƙi halinsa da yanda yake kulawa da tarbiyyanki wani lokacin yana sani kewar mahaifina sai na ji duk duniyar na yi mini zafi".
Chapter 14 · 0% Book details