← Book details Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 58

Sashe 44

Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ba za ki mutu ba Amatullah, bari na je na sanar da Hajiya abin da ya faru". Amira ta yi zancen tana lulluɓa mini mayafi a jikina da ya taimaka wajen ɓoye tsiraicina da ya bayyana. Ta tashi ta fice daga cikin ɗakin cikin hanzari babu jimawa suka dawo tare da Hajiya Tasalla da ta na shigowa ta soma zagba salati da sallallami ganin mungun halin da nake cikinsa.
"Amatullah tashi ki yi min bayanin abin da ya faru? Waye ya yi miki haka? Waye ya shigo cikin É—akin nan ba tare da sanina ba? Alhalin tun É—azu ina zaune a filin tsakar gidan nan ban ga shigowar kowa ba balle fitar wani".

"Hajiya ku kai ni asibiti wallahi mutuwa zan yi". Na yi zancen cikin tsananin zafin ciwo da takaicin halin da na tsinci kaina, da kuma sauyawar da rayuwata za ta yi daga wannan lokacin.
Ta dafe ƙirji tare da waro idanunta waje"asibiti kuma Amatullah ai hakan daidai yake da tonuwar asirinki, na iyayenki da kuma ni da kaina. Bari na je na tafasa muka ganyan magarya da lalle ki ci shiga ciki za ki ji daɗin jikinki". Ba ta jira abin da za mu ce ba ta tashi a hanzarce ta fice tamkar za ta kife akan hancinta.
"Na shiga uku ni Amira yanzu da wani idon zan fuskanci Abbanki da wannan zancen, bayan ya damƙa amanarki a hannuna. Ya yarda da ni tare da yaƙinin matuƙar kina tare da ni ba zan taɓa bari wani abun ya cutar da ke ba". Furucin Amira kenan da ya ƙara saka ni kuka daga ni har ita kukan muke yi da dukkan ƙarfinmu, tamkar wanda aka aiko da saƙon mutuwar iyayensu uwa da uba tare da dukkan ahalinsu.

Har Hajiya Tasalla ta dawo ba mu daina kukan ba, ta je ta rufe gidan ruf a cewarta kar wani ko wata ya shigo ya tarar da abin da ya faru asiri ya tonu, ta kuma sallami duk masu kwanan ranan suka tafi. Tare da Amira suka cicciɓe ni zuwa waje na shiga cikin ruwan ɗumin wani azababben zafi na ji ya ratsa ƙoƙon kaina na yi zumbur zan tashi Hajiya Tasalla ta maida ni.
"Ki yi haƙuri ki koma ki zauna a cikin ruwan nan, domin shi ne samun lafiyarki a yanzu".
Haka ina kuka ina cije leɓe na koma na zauna na aƙalla mintuna talatin kafin na fito ta kai mini ruwan ɗumi banɗaki na yi wanka na fito ina ɗingisa ƙasa. Wani kayan ta ba ni na saka na kifa kaina da gwiwa ina ci gaba da kukan tausayin kaina da iyayena da nake yi. Amira ma ta zo ta jona ni muna yi tare.
Cikin durshashewar murya da sarƙafewar harshe na ce"Amira gida zan tafi ba zan iya kwana a nan ba, ki taimaka ki mayar da ni gidan. Ko mutuwar ce ma na fi so ta ɗauke ni a can".

"Amatullah ki yi haƙuri yanzu idan muka koma gida ai asirinmu ya gama tonuwa a idon duniya. Dole mu tsara yadda lamarin zai tafi". Ban tanka ba na miƙe tsaye ina cije leɓe na yunƙura zan fice daga cikin ɗakin ta sha gabana tana yi mini magiya.
"Don girman Allah Amatullah ki yi haƙuri ki rufa mana asiri kar ka fita cikin wannan daren". Runtse idanuna na yi ina jin wasu hawayen da na gaza samun ikon akan su suna kwaranya daga koramar idanuna.

"Ya na ganku duk kuna tsaye cirko-cirko?". Na tsinkayo amon Hajiya Tasalla na buɗe idona ina kallon ta da wutsiyar idanuna, ji nake yi tamkar na yi tsalle na je na shaƙe mata wuya.
Ta dire wannan abinci da kofin da ta shigo da shi kana ta zo ta riƙo hannuna za ta taɓo jikina na zame. Ina ci gaba da kukan da nake yi.

"Ki yi haƙuri mana ke kuwa abin da ya faru ai ta riga da ya faru, sai dai a kiyaye gaba". Na galla mata harara kamar idanuna za su faɗo.
"Hajiya an cuce ni a cikin gidanki ai dole ki ce mini haka. Me yasa tun farko ba ki sanar da mu cewar kowa yana da ikon shiga kowani ɗaki ba a kowani lokaci? Me yasa kika bari aka cutar da ni cutarwa mafi muni da raɗaɗi da zai ci gaba da bibiyar rayuwarta har zuwa ranar da numfashi zai yi bankwana da gangar jikina?. Hajiya me na yi masa ya aikata hakan a gare ni?". Na ƙare zancen ina sulalewa ƙasa saboda gaza ɗaukana da ƙafafuna suka yi na durƙushe ina kuka da tun sautinsa yana fita har ya dishashe.

"Amatullah ki tambayi kowa a cikin unguwan nan zai faɗa miki cewar gidana akwai tsari da kuma dokoki daki-daki. Na fi zargin kin taka sawun ɓarawo ne kawai domin nan ɗakin Ramlatu ƴar gold ne sai dai in wani jagwal ɗin ta haɗo kai kuma ya faɗi akan ki. Tabbas Ramlatu ƴar hau ce ta bugawa a jarida". Na yi zumbur na miƙe tamkar wacce aka tsigarawa matsilli.
"Wace ce Ramlatun? Don yanzu haka tana ina?". Ta ja dogon numfashi ta fesar kafin ta ce"ita ce mai ɗakin nan kuma yanzu haka tana can ƙauye amma bari na ƙira ta a waya". Tana ƙare zancen ta shiga latsa wayarta bugu biyu aka ɗauka ta soma magana.

"Kina ina ne?". Daga ɗayan ɓangaren aka amsa da"ina ƙauye mana. Bashi ko tara kike yi min waɗannan tambayoyin?".
"Ramlatu akwai wanda kuka yi da shi za ku haÉ—u ne, a cikin É—akinki?". Ta É—an yi jim kafin can ta ce"babu wanda muka yi da shi, amma na san ko an zo nema na ma ba zai wuce Mus'bahu ba. Kin san shi kaÉ—ai ne yake zuwa har gida ai kuma ba shi da shamaki da É—akina".

Ta ɗaura hannu a ka"shikenan Musbahu ya cuce mu ya tona mana asiri. Duk abin da kike yi ki bar shi da asussubahin gobe ki dawo, don wata wuta ce ta kunno kai". Daga haka ta datse wayar duk muka zauna jigum-jigum, zaman dirsham na yi kukan ma na gaza samun ƙarfin yin sa balle wani motsi mai ƙarfi ina jin numfashina yana sama yana ƙasa. Take na ji kaina yana juyawa duk da ina zaune ne sai da na yi lu zan faɗi Amira ta yi saurin riƙo ni na faɗo jikinta.

"Hajiya ya kamata fa mu kai ta asibiti. Don wallahi ni kam lamarin nan ya fara ba ni tsoro, kin ga fa jijjiga take yi".

"Ƴar nan ai ba zai yiyuwa a kai ta asibiti a wannan yanayin, da zaran mun saka ƙafa mun fita to asiri fa ya tonu mutumcinta da na iyayenta ya zube. Kin kuma san ance mutumci madara ne in ya zube ba a iya kwashewa, akwai wani likitan da zan ƙira zai zo har gida ya duba ta". Ta ɗaga waya ta yi ƙira babu jimawa ta fits ta je ta shigo da mutumin, lokacin gabaɗaya na cire rai da ci gaba da numfashi a doron duniya, na fidda rai ga rayuwa. Da taimakon Amira na tashi na zauna bayan ta sa mini matashi na zauna a kai likitan ya duba ni kana ya soma jero mini tambayoyi.

"Da alama wannan ne karon farko da kika taɓa saduwa da wani ɗana miji a rayuwarki ko?". Na ji tambayar ta tsaya mini a rai kwatankwacin irin tsayiwar da ƙayan fiki yake yi a maƙoƙaro. Na haɗiye wani miyau mai kauri kafin na sama zarafin gyaɗa masa kaina alamar e da hakan ya ba shi daman ci gaba da tambayoyi.
"Hajiya ba wani babban abu ba ne da zarar ta juri shiga cikin ruwan É—umi kuma tana samun ishashshen huta, za ta dawo daidai. Sannan zan rubuta wasu magunguna sai a daure a neme su tabbas su ma za su taimaka".

"Likita ka tabbata za ta warware?".
Ya gyaɗa kai"za ta warware Hajiya wataƙila ma nan da zuwa safiya duk ciwon jikin da take ji zai yi sauƙi. Ga maganin sai a nemo mata su". Ya ƙare zancen tare da miƙa mata wata takarda ta karɓa jikinta har rawa yake yi, ya fita ta bi shi a baya.

Har ta je ta dawo ban gusa daga inda nake ba ta zo ta durƙusa a gabana. Na runtse idanuna don ba na ƙaunar ko da ganin fuskarta balle sauraren zantukanta.
"Amatullah ina mai ba ki haƙuri na san an cutar da ke, amma babu yadda muka iya ƙaddararki ce ta zo a haka babu yadda za mu yi mu sauya ta. Ina mai roƙon ki da ki rufe wannan maganar a nan inda ta faru kar ki bari kowa ya sani ciki kuwa har da iyayenki". Babu shiri na ware idanuna tar akan ta cike da son ƙarin bayani.

"Ƙwarai kuwa hatta iyayenki kar su ji wannan labarin don in suka ji to har su koma ga Allah wannan tabon ba zai bar cikin zuciyoyinsu ba. Sannan babu wani ɗa na mutunci zai dai fito neman aurenki, ko ya zo ma ƴan gulma za su tsegumta masa abin da ya faru. Ki rufa wa kanki asiri ki rufawa iyayenki".

Wasu tsiraran hawaye suka soma rige-rigen fitowa daga idanuna suna sauƙa har izuwa tudun wuyana. Na ji ta riƙo hannayena na yi saurin zamewa.

"Hajiya wace ce Ramlatu kuma me ye tsakaninta da shi Musbahun? Me ya sa zai aikata wannan abun a zuwan cewa akan ta ya yi?".
Chapter 44 · 0% Book details