Sashe 55
Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Amira me ye ya faru da ni ne ki sanar da ni. Ganin komai na ke yi tamkar a cikin mafarki, don idan mafarki nake yi ki taimaka ku tashe ni tun kafin na zauce".
"Babu abin da ya faru da ke Amatullah faɗuwa kika yi aka kawo ki asibiti kuma yanzu kin ji ai da kunnenki cewar babu wata matsala. Sai dai kuma wani abu....". Ta yi shuru ba tare da ƙarisa ba suka haɗa ido da Anty Zulaihatu take na ga duk su biyun sun fashe da kuka, hakan ya ba ni tabbacin cewar akwai wani abun da suke ɓoye mini.
"Don Allah Anty Zulaihatu kar ku ɓoye mini komai ku sanar da ni abin da ya faru da ni komai munin sa, babu abin da zai same ni yanzu babu wani labarin da zai tayar mini da hankali fiye da rasuwar Abba. Don Allah ku sanar da ni". Na ƙare zancen cikin karyewan zuciya. Sai da suka ɓata wasu mintuna kafin Anty Zulaihatu ta riƙo hannuna ta sanya cikin nata tana murzawa a hankali ta ke faɗin.
"Amatullah kin shiga cikin jarabawa da yawa wanda sai mai ƙarfin imani ne kawai zai iya jure su ba tare da ya rasa tauhidinsa ba. A yanzu ma ina so ki yi haƙuri da abin da za ki ji daga gare ni". Na gyaɗa mata kaina alamar ina sauraran duk abin da take faɗa da hakan ya ba ta damar ci gaba daga inda ta tsaya.
"Sakamakon dukan da Ummanki ta yi miki cikin da ke jikinki ya bi rariya". Na ware dukkan girman ƙwayan idona"ya zube kenan?".
"Babu yadda za mu yi Amatullah haka Allah ya ƙaddara". Na sauƙe tagwayen ajiyan zuciya na rasa a tsakanin farin ciki ko baƙin ciki wanne ya fi dacewa da ni a yanayin da nake ciki. Yaya Alhassan yana zuwa asibitin aka sallame mu sai dai maimakon mu wuce can gidanmu sai na ga sun wuce gidan Anty Sawwama.
Na yi kuka iya kuka har sai da idanuna suka kafe, na ji gabaÉ—aya duniyar ta ishe ni babu abin da yake yi mini daÉ—i a cikinta. Wai ace mahaifina ya rasu amma ba ni da ikon zuwa wajen makokinsa ni kam ba san abin da ya fi wannan ciwo da raÉ—aÉ—i ba.
[10/29, 10:08 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE*
Â©ï¸ Maimuna Tijjani Iyam
________________________________________
Page 3ï¸âƒ£9ï¸âƒ£
Haka na kwana na tashi da zazzaɓi a jikina garau kamar garwashin wuta ake watsa mini a cikin jikina. Ji nake yi tamkar a mafarki wai yau Abba ba ya raye cikin duniya ya rasu ba tare da na sanar da na kore masa kokonton da share masa zargin na aikata abin da ake zargina da shi. Ban taɓa sanin haka mutuwa take da matuƙar zafi da ciwo ba sai yanzu da ya juyo kaina, ji nake yi kamar ni ma ba zan yi tsawon rai a duniya ba ko da kuwa na yi to haƙiƙa zan zauce ne na fita daga cikin hayyacina.
Tun ina yin kukan da hawaye har suka daina zuba ƙirjina ya yi miji nauyin gaske tamkar an yi mini ajiyan dutsin dala ta Kano a saman ƙirjina, idanuna har sai da suka daina buɗuwa saboda tsabar kumburan da suka yi. Kafin gari ya waye ko magana ba na iya yi haka nan ba na gane wanda yake tsaye a kaina sai dai kawai na tantance muryan.
Ina kwance tamkar ruwa don ko Æ´atsan hannuna ba na iya motsawa jikina ya yi lamus ko kaina ban iya É—agawa, ranar da aka yi sadakan ukun Abba yayin da Anty Sawwama ya ce a haÉ—a har na bakwai kowa ya watse aka kuwa yi hakan. Aka bar mu daga mu sai ya mu sai kuma halinmu, har zuwa wannan lokacin Umma ta Antyaihatu ta shigo cikin É—akin ta zauna a kusa da ni ta É—aura hannunta a bisa goshina da ya É—au zafi gau.
"Ya subhanallahi! Amatullah jikin ne haka? Don Allah ki tashi ki ci wani abun ko kaÉ—an ne sai ki sha magani".
"Anty Zulaihatu mutuwa zan yi ni kam ba zan rayu ba mutuwa ni ma zan yi". Na zaro maganar da ƙyar saboda yadda numfashina yake cukurkuɗewa waje guda kamat mai lalurar cutar numfashi.
"Amatullah duk wanda kika ga ya mutu ai lokacinsa ne ya yi. In sha Allah ba za ki mutu ba sai lokacinki ya yi, za ki ci gaba da rayuwa har ma ki yi dariya ki yi mu'amala kamar kowa. Don Allah ki kwantar da hankalinki komai ya faru da Bawa muƙaddari ne daga Allah ne kuma Bawa baya wucewa ƙaddararsa balle ya guje mata".
Na ɗaya kaina ina ganin ta dishi-dishi ga numfashina yana sama yana ƙasa na yi ƙarfin halin faɗin"Anty Zulaihatu rayuwata ta zo ƙarshe ni kam". Ban ƙarisa ba ta rufe miji bakina da tafukan hannayenta.
"Don Allah ki daina faɗin irin wannan maganar babu wanda ya san gobe sai Allah". Na sauƙe tagwayen ajiyan zuciya mai ɗumi ina lumshe kumburarrun idanuna da kamar za su faɗo ƙasa. Sama-sama na soma jiyo amon Yaya Alhassan a masarrafan naɗan sautina, kafin na ji muryar dab da ni.
"Amatullahi".
"Na'am". Na amsa a taƙaice da hakan ya ba shi damar ci gaba da maganan da yake yi.
"Wannan damuwar duk na mene ne haka ƙanwata? Abin da ya faru ai riga da ya zama tarihi sai dai ayi ƙoƙarin gyar gaba. Kawu yanzu addu'armu yake buƙata ba wannan koke-koken ba, na san abin da ciwo amma ina so ki daure ki yi ƙoƙarin cire komai daga cikin ranki ki fuskanci rayuwarki ta gaba ka shagala wajen ingantata".
"Yaya Alhassan ni kuma me ye ya rage mini a duniya ai rayuwata kam ta gama rushewa ta rugurguje".
"Har yanzu ki na da sauran daman da za ki ɗinke ɓarakar da ya ɓullo a cikin rayuwarki. Amatullah rayuwa jarabawa ce mai girman gaske, duk munin halin da kike ciki idan kika ga wani ko kika ji halin da wani yake ciki sai kin ji tamkar ke ɗin ki na cikin gidan aljanna ne". Na yi lamau na kasa cewa da shi komai zuciyata tana turara kamar talgen masarar da aka aza bisa murhu.
"Tashi mu yi magana".
"Ba zan iya tashi ba".
Muryarsa babu alamar wasa ya furta"tashi ki zauna magana za mu yi da ke". Na cije leɓe na tashin na zauna saboda duk inda na motsa a gaɓoɓina ciwo yake yi mini. Shruu ya ratsa ɗakin kafin ya kawar da shurun ta hanyar faɗin"Amatullah da waye kika keɓe har ciki ya shiga cikinki?".
Zuffa ya jiƙa mini jikina tsam jikina ya soma rawa sai da na fizgo numfashina da ƙarfi kafin na iya faɗin"Yaya Alhassan wallahi ba laifina ba ne ƙaddara ce ta faɗa mini......
....". Na irge masa komai duk abin da ya faru tun daga faru har ƙarshe.
Ya zabga mini wani gigitaccen marin da ban san lokacin da na sake ihu ba. Ya tashi tsaye yana cije leɓansa tare da kai wa iska naushi.
"Amatullah me yasa kike ɓoye faruwar wannan abun? Shin ba kya kishin kanki da har wannan abun zai faru amma duk da haka ki zaɓi ki ɓoyewa kowa hatta iyayenki da ƴan uwanki. Wanda kika san cewa duk wuya duk tsinki suka rufa miki asiri. Ina ma kin sanar tun a lokacin da lamarin ya afku da duk abin da ya faru bai faru ba". Ya ƙarishe zancen cikin matuƙar takaici daidai lokacin da Anty Sawwama take shigowa ɗakin cikin tsananin damuwa da alamar ta saurari duk abin da na muka faɗa.
"Allah ba ka jarabtan Bawa da abin da ba zai iya yi. Ya Allah don ƙarfin zari da ikonka ka ba mu juriya da haƙurin jure wannan jarabawan da ka jarabce mu da shi".
"Amin ya Allah".
Duk suka haÉ—e baki wajen furtawa amma ni kam sai a zuciyata na amsa don bakina ya kasa motsawa.
"Umma yanzu ya ya za a yi?". Anty Zulaihatu ta tambaya muryarta tattare da tarin damuwa.
"Dole mu je mu yi magana da mahaifiyarta don yadda ta yi watsi da Amatullah a wannan yanayin da take ciki abin yana damuna matuƙa. Zuwa yamma in sha Allah za mu je gabaɗayanmu mu same ta". Duk suka yi na'am da abin da Anty Sawwama ta furta ni kam na yi shuru tamkar wacce ruwa ya cinye ta. Zuwa bayan sallan asr suka sauƙa daga napep a ƙofar gidanmu.
Na waiga na hango masallacin da Abba yake salla kuma yake yawan zama a bakin wajen, na ga tarin dattawa zaune a wajen sai dai duk cikin su babu Abba, mutuwa kenan mai raba zumuci da daɗaɗɗan alaƙa.
Sai da Anty Zulaihatu ta ja hannuna kafin na ja ƙafafuna muka shiga cikin gidan, yara da manya suka taru suna ganina kamar ba su taɓa ganina ba kaina a ƙasa tun da muka shigo amma hakan bai hana su magana ba.
"Wannan ce annobar kenan? Ni kam da haihuwar irin wannan ai gwara ka zo duniya har ka gama rayuwarka ba tare da ka haihu ba". Cak na tsaya bisa sauƙan furucin da na ji a kunnuwana da ya damalmala mini dukkan lissafina ya farraƙa nutsuwa da gangar jikina.
"Amatullah ke ce haka duk kika lalace kamar mai cutar ƙanjamau?". Maman Adnan ta yi zancen tana iso ta tsaya a gabana kafin na ba ta amsa ta ci gaba da zancen tana taɓe baki.
"Ai daman ƙarya fure take yi ba ta ƴaƴa kuma komai nisan daren dole gari zai waye haske ya mamaye ko'ina, ashe duk sintirin da kike yi da sunan da zuwa islamiyya fakewa ake yi da guzuma a harɓi karsana to an yi walƙiya mun gan ku".