Sashe 15
Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Na kai mata duka a kafaɗarta"ke dai kam ki godewa Allah don Baba Habu bai rage ki da komai ba". Ta sauƙe numfashin da har sai da na jin sautinsa kana ta ce"Amatullah ba za ki gane raɗaɗin irin ciwon nan. Babu wanda yake maye gurbin iyayen sai dai kawai a kamanta". Tana gama maganar ta yi gaba ta bar ni.
Na fita a baya muka je wajen Mansur yana tsaye a jikin motarsa tana latsa wayarsa yayin da wani abokinsa take kusa da shi, da sallama É—auke a bakinmu muka isa wajen su suka amsa mana yayin Mansur yake tattara dukkan hankalinsa kan Amira.
"Gimbiya kin fito?".
"Ai ka san ba zan zo na bar Sarkina a tsaye ba". Ta saki murmushin jin daÉ—i zai yi magana na katse shi.
"Tun da na ga alama idanunka ita kaɗai yake gani, babu amfanina gwada na ja ƙafafuna na koma".
"Afuwan ranki ya daÉ—e. Idanuna sun ganki amma zuciyar ce gabaÉ—aya tana tare da ita. Ya kike ya gidan?".
"Lafiya ƙalau ka zo lafiya".
Ya amsa cike da kulawa"lafiya sai dai na tabbatar da zaran na bar nan zan zama majiyanci ne". Amira ta yi masa wani kallo da hakan ya sanya sa cewa"e mana tun da sai na shafe sati guda ban yi tozali da ke ba. Wallahi Amira ba don Alhajinmu ya matsa min akan lalle ni zan wakilce sa a wannan taron ba, babu wani dalilin da zai sa na yi nisa da ke". Jim ta yi gabaÉ—aya jikinta ya mutu yanayinta ya sauya ta kasa cewa komai illa kallon juna da suke yi.
Ba su dawo duniyar zahiri ba sai da abokinsa ya yi magana"ni ma tun wuri bari na san inda dare ya yi min. Don na ga alama an manta da ni ".
Mansur ya ce"Haba kai kuwa Mukhtar ni na isa na manta da kai. Kawai dai ka san an ce sawun giwa ya danne na raƙumi". Dukkan mu muka fashe da dariya sai da muka tsagaita Mukhtar ya kallo ni yana cewa"kin ga ƙawarmu waɗannan mutanen ba ta mu suke yi ba. Ya fi dacewa mu matsa mu ba su wajen".
"Ai kuwa na ga alama". Na yi maganar yayin da nake bin bayansa muka matsa gefe, mun ɗan yi hira jifa-jifa kafin Amira suka yi sallama da Mansur. Da ya buɗe bayan boot ɗin motarsa ya fara sauƙe mata manyan ledodi sai da abin ya ba ni tsoro aƙalla sun kai bakwai a ƙidayen da na yi kuma dukkannisu shaƙe suke da kaya. Har da kukanta da Mansur zai tafi shi ma duk yanayinsa ya sauya haka ya shiga mota ya tafi bayan ya yi mata alƙawarin ƙiran ta da zaran ya isa garin da zai je.
Muka kwashi ledodin wanda za mu iya muka shiga da su ragowar kuma muka saka yara suka shigo mana da shi. Ina cikin lallashina Amira a ɗakinsu Umma ta aiko ƙira na na tashi da hanzari na je.
[7/19, 7:42 PM] Maimunatu Iyam: *DAFIN HARSHE*
Â©ï¸ Maimuna Tijjani Iyam
______________________________________
Page 1ï¸âƒ£2ï¸âƒ£
Tana zaune a falo ta ɗaura ƙafa ɗaya bisa ɗaya ta kwantar da kanta a jikin kujera ta lumshe idanunta kamar mai bacci. Gaban ta wani baƙin leda ne a ajiye. Sai da na nema waje na zauna kafin na ce"sannu da dawowa". Ba tare da ta buɗe idanunta ba ta amsa mini tana ci gaba da cewa"ki haɗa wuta ki ɗaura min ruwan kunu". Na ɗan jim kafin na ce"Umma lokacin islamiyya fa ya yi". Sai a sa'ilin ta buɗe idonta tana kallona"ai tun da ba ki da safe ba to tabbas sai kin fita na rana".
"Ranan nan ma fa ban sama zuwa, da kin yi haƙuri yau ɗin na je ko da yamma inna dawo sai na fita da kunun". Ba ta ce da ni komai ba ta ta shi ta ɗauki ledar ta shige cikin ɗaki ba ni da zaɓi dole na tashi na fito na huta wuta na ɗaura ruwan da ta umarce ni na zauna na zabga tagumi sai da ruwa ya tafasa na je na sanar da ita ta fito ta dama kunun yayin da na shiga ciki na gabatar da sallan zuhr. Na fito na yi wanka na fara shirin fita idona ya raina fata lokacin da ta miƙo mini kwallin ta ce na saka a idona bayan ta gama turare bokatin kunun da hayaƙi.
Zuciyata kamar za ta tsago ƙirjina ta bayyano waje tsabar bugawan da take yi duk kuka da magiyar da nake yi wa Umma hakan bai yi tasiri ba, dole ƙanwar naƙi na karɓa kwalli na saka a idona. Na ɗaura bokatin a kaina na fita ina tafe ne kawai amma ban san inda nake cilla ƙafafuna ba mussamman da na ga duk layin da na wulga sai jama'ar wajen su bi ni da kallo. Gabaɗaya sai na ji ni duk a takure na kasa sakewa.
"Amatullah Mannir".
Na tsinkayo amon muryar Malam Suleiman Malamin ajinmu a islamiyya kamar daga sama, a hanzarce na waiga ina kallonsa yayin da shi ma É—in ni yake kallo kallo irin na mamaki.
"Ina wuni Malam".
Na gaishe shi sai dai maimakon ya amsa sai ya ƙara dawo mini da wata tambayar.
"Ina za ki je haka bayan lokacin islamiyya ya yi?".
"Yau ba zan sama zuwa ba ne".
"Me yasa?".
"Zan je talla ne".
Ya yi shuru na tsawon wasu daƙiƙu kafin ya furta"waye ya sa ki tallan?".
Muryata tana rawa na ce"Ummata".
"To mu je islamiyya sai ki ajiye tallan a staff a wajena ki wuce aji, wataƙila a can sai ya ƙare".
"Malaman ba kayan islamiyya ba ne a jikina da kuma na baro jakata a gida". Ya ɗaure fuskarsa tamau"wuce mu je kafin na sassaɓa miki". Ban kuma cewa komai ba ya wuce gaba ina bin sa a baya har muka isa islamiyyan na ajiye kunun a staff kamar yadda ya ce. Ya ɗauko ƙur'ani ya ba ni ya ce da ni na wuce ajinmu. Haka na wuce ajin na je na zauna muka fara kara karatu, ko da muka fito sallan asr ban yarda mun haɗu da Ammi da Rauda ba don na san zan sha tambayoyi a wajen su, ina yin salla na koma aji na yi zamana ba mu tashi ba sai ƙarfe biyar muna yin addu'a na fito da saurina zan tafi Rauda ta dakatar da ni.
"Don Allah Amatullah ki tsaya".
Sanin girman wanda ta haɗa ni da shi ya sani tsayawa har ta iso gabana hannunta saƙale cikin na Ammi.
"Wai me ye yake faruwa ne kwana biyu ba kya zuwa? Yanzu kuma kin zo amma sam ƙi yarda ki haɗa inuwa ɗaya da mu". Ammi ta ci zancen cikin damuwar da ya bayyana har a cikin kalamanta, kafin na ba ta amsa Rauda ta karɓe zancen"kin san Allah yau muka ce idan ba ki zo ba daman za mu ke gidanku mu duba ko lafiya".
Cikin ƙosawa da sauraran zantukansu na furta"lafiyata ƙalau kamar yadda kuke gani ai babu alamar jinya a tattare da ni".
"Amma ai akwai alamar damuwa a tattare da ke".
"Don Allah Rauda mu bar maganar nan. Tun da yanzu kam na zo ai shikenan ko". Ina dasa aya na sa kai zan wuce wajen Malam Suleiman suka ƙara tsayar da ni.
"Wallahi Amatullah akwai wani abu da yake faruwa ko ma ya riga ya faruwa don ba haka kika saba zuwa ba. Kuma yaya Musbahu ya ce min ya gan ki kina talla a filin taurari, inda duk wata mai tarbiyya da kamun kai ba ta sanya ƙafarta cikin wannan filin. Me yake faruwa Amatullah?".
Ban yi aune ba na ji ƙwalla sun ciko mini kurmin idaniyata sai dai na yi jarumta da ƙarfin hali ban bari sun tsiyaya ba. Na ja dogon numfashi kafin na sama sararin faɗin"zan yi muku bayanin komai amma ba yanzu ba".
"Sai yaushe kenan?".
Na toshe kunnuwana"don Allah ku yi haƙuri ku bar ni haka. Na ce zan faɗa muku idan lokaci ya yi". Ina gama faɗin haka na bar wajen da matuƙar sauri na nufi staff wajen Malam Suleiman, shi kaɗai na samu duk ragowar malaman sun watse kasancewar lokaci ya fara ƙurewa. Sai da na yi sallama ya amsa kafin na shigo na tsuguna raina ya yi wani sanyi kamar an ɗaura mini ƙanƙara ganin bokitin kunun saura kaɗan.
"Amatullah".
Sautinsa ya dawo da ni cikin duniyar zahiri, na gyara tsugununan da na yi a nutse na ce"na'am Malam".
"Me yasa ba kya zuwa makaranta kwana biyu da suka wuce?".
"Malam ba na samun dama ne. Idan na fita talla ba na dawowa da wuri kuma idan na dawo da ragowa Umma za ta yi mini faÉ—a".
"Me yasa ba kya fita da wuri?". Na yi shuru don ba ni da amsar tambayar.
"Ban hana ki talla ba Amatullah kuma ba ina nufi kar ki yi abin da mahaifiyarki ta sa ki ba. Amma ina mai ba ki shawara da kar ki sake ki yi wasa da damarki, a wannan shekarun ne kawai ki ke da damar yin karatu sosai kafin abubuwa su sauya. Ke mace ce rayuwarki gabaɗaya ƙanƙanuwa ce saura ƙiris ku haɗa hadda ki dage duk runtsi ki na zuwa".
"In sha Allah zan daure ina zuwa". Na amsa a raunane.
"Ga kuÉ—inki an saya na É—ari bakwai da saba'in". Na sa hannu na amsa kuÉ—in ina yi masa godiya maimakon na tashi na tafi sai na koma na zauna, hakan ya sa shi zuba mini ido cike da zallar mamakin dalilin da ya sani share waje na zauna.