Sashe 52
Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Muna sanya ƙafarmu a cikin filin tsakar gidan Umma ta tare mu tamkar daman jiran shigowarmu take yi.
"Kar ki sake ki nufo ɗakin nan shegiya tsinanniya kawai. Amatullah kin ja min abin magana da yamaɗiɗi a cikin gari ki jawo min abin kunya, kar ki matso inda don babu makawa matuƙar muka haɗa wajen zama da ke zuciya za ta iya ɗiba na na murɗe miki wuya".
"Subhanallahi! Haba Hafsatu idan hankali ya gushe ai hankali ake sawa a nemo shi. Ki yayyafawa zuciyarki ruwan sanyi sai a zauna a nemo yadda za a ɗinke wannan ɓarakar da ta same mu gabaɗaya".
Kalaman Anty Sawwama kamar aka fusata Umma suka yi ta cika ta yi fam.
"Maman Umar ki fitar da yarinyar nan daga cikin gidan duk kafin na biye zuciyata na aikata abin da daga ni har ke za mu zo muna cizon É—an tsaya daga baya".
Anty Sawwama ta dafe kai"innalillahi wa inna ilahirin raji'un". Idanuna suka daina gano mini komai illa gilmawar baƙin duhu duk da haka na ja jiki na isa gaban Umma na riƙe ƙafafunta.
"Umma idan ba ki rufa mini asiri ba waye zai rufa mini asiri a cikin duniyar nan. Umma ki ba ni dama na yi miki bayanin abin da ya faru wallahi ba laifina ba ne ƙaddara ce ta Ubangiji ta faɗa mini". Ta sanya kafa ta yi kutufol da ni sai da na yi tanbulin goshina da aka yi wa dressing ya bugu da ƙasa, jini ya soma zuba da goshi da hancina. Anty Sawwama ta yi saurin ɗago ni sai dai na kasa tsayiwa akan ƙafafuna sai da ta riƙe ni kam. Duk rashin tausayin mutanen gidanmu a ranar sai da na tausayina kwance a fuskarsu.
Matar Uszatu ta ce na je ɗakinta na zauna Umma ta daka tsalle ta dire a duk wanda ya ba ni wajen rakaɓewa sai ta yi masa ɗiban albarka mai wasali, haka Anty Sawwama ta riƙo ni ina kuka ita ma tana yi haka nan ma Amira da ƙyar aka ɓanbare ta daga jikina muna kuka wiwi muka fito daga cikin gidan.
Muna fitowa idanuna suka sauƙa akan Muhammad Taukif ya na ganin mu ya yi saurin fitowa daga cikin motarsa ya fito.
"Hajiya lafiya na ga kun shiga kun fito?". Maimakon ta amsa masa sai ta ƙara jefa masa wata tambayar"kana nan ba ka tafi ba?".
"Yanzu nake son tafiya sai kuma na ga fitowarku. Lafiya kuwa?".
"Lafiya ƙalau yanayin jikin natan ne ƙawa babu daɗi, shi ne za mu je gidana da ita".
"To ku shiga na kai ku mana".
"A'a kar ka damu za mu nema abin hawa". Da hanzari ya katse ta"Hajiya umarnin mahaifina nake cikawa, don yana girmamawa da mutunta duk wanda ya haddace littafin mai tsarki yana musu hidima da ƙarfinsa da kuma aljihunsa. Don Allah ku shiga na kai ku".
Ba ta musu ba ta ja hannuna muka shiga cikin motar har muka isa kuka nake yi, mu fito za mu shiga cikin gidan nan na ji ya ƙira sunana na tsaya cak.
"Amatullah".
Na waigo muna kallon juna"Allah ya ba ki lafiya".
Na kasa amsawa da kalmomin baka sai a cikin zuciyata na amsa. Na muka ƙarisa shiga cikin gidan ina shiga cikin ɗakin na zube akan katifanta ina ta kuka.
Anty Zulaihatu ta shigo ta yi mini dukkanin lallashin duniya amma na kasa daina kukan, Anty Sawwama ita ma ta shigo.
"Amatullah tashi ki zauna mu yi magana".
"Anty ba zan iya tashi ba".
Cikin kakkauran murya ta furta"Amatullah waye ya yi miki ciki?". Numfashina ya tsaya na lokaci guda saboda cakwakiyar da yake cikin tambayar da ta yi mini. Wanda ni ma kaina ban san wanda ya aikata mini hakan balle na sama kalaman kare kaina. Abu na sani kuma na yarda da shi shi ne ƙaddarata ta zo a haka babu yadda zan yi na guje mata.
[10/26, 3:09 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE*
Â©ï¸ Maimuna Tijjani Iyam
_______________________________________
Page 3ï¸âƒ£7ï¸âƒ£
Numfashi nake ta sauƙewa wani na bin wani ga jinin da yake sauƙowa daga goshina yana wanke mini fuskana, cikin taushin murya na ji ta ƙara faɗin"Amatullah ki taimaka ki sanar mu wanda ya yi miki ciki. Ki dubi halin da mahaifinki yake ciki, a cikin rayuwarsa kina ɗaga daga cikin abin da yake matuƙar alfahari da su tun da kika zo duniya ya kalle ki har kika girma farin cikinsa ya ninku. A lokuta da yawa darajarki mahaifiyarki take ci yake ɗaga mata ƙafa akan dukkan abubuwan da take yi, domin a cewarsa ita ma ta taka rawar gani ta haifa mata ɗiya sannan a dalilin hakan aka cire mata mahaifa yana ganin inya rabu da ita bai yi mata adalci ba. Amatullah iyayenki sun yi ɗawainiyya da ke irin ɗawainiyyar da fi ƙarfin baki ya suffanta shi cikin kalmomi, mahaifiyarki ta sha wahalar rainon cikinki lokacin haihuwarki ta yi dogon naƙudan da har sai da muka cire rai da cewar za ta rayu. Mahaifinki ya yi wahala da ke tun ki na ciki har kawo girmanki ya yi duk mai yiyuwa wajen ganin ya tanada miki more rayuwa daidai ƙarfin aljihunsa, ya ba ki ilmi har sai da yau aka wayi gari kin kammala haddan alƙur'ani. Amma ki rasa da me ye za ki saka musu sai da wannan abun shin sun cancanci hakan ne daga gare ki?".
"Wallahi ƙaddara ce ta faɗa mini ba da son raina ba, Anty ki yarda da ni ba zan taɓa wofantar da tarbiyyan da kuka har ni ko na sauƙa daga kan gwadaben da kuka ɗaura ni akai ba".
Ta katse ni"waye ya yi miki ciki?".
"Ban san shi ba ban taɓa ganin sa hasalima shi ma bai sanni ba, bai taɓa ganin fuskata ba". A fusace ta miƙe irin fusatar da tun da uwata ta kawo ni duniya na girma na yi hankali ban taɓa ganin ta cikin makamancinsa ba.
"Wani irin magana ce haka wanda hankali ba zai É—auke shi ba? Kamar ya ya ba ki san shi ba?".
"Wallahi tallahi ban san shi ba ba mu taɓa ganin juna ba ni da shi".
"Innalillahi wa inna ilahirin raji'un!". Ta furta cike da damuwa tana dafe kanta, Anty Zulaihatu ta tashi ta riƙe ta don tana ƙoƙarin faɗuwa. Ta zaunar da ita tana faɗin"don Allah Umma ki yi haƙuri a bi komai a sannu. Son samu ma a bar ta kar kowa ya ƙara yi mata maganar har sai ta dawo cikin hayyacinta nutsuwarta ta daidaita lamuran sun dawo daidai".
Numfashinta ne ya soma sama da ƙasa na fita waje da sauri na ɗebo mata ruwa zan kai mata muka yi kiciɓus da Umar ya shigo gidan. Ya sha gabana"ina za ki je?".
Cikin rawan jiki da na murya na ce"ruwa zan kai wa Anty numfashinta sai sama-sama yake yi". Ya kwace kofin ruwan yana jifa na da wani matsiyacin kallo na bi bayan sa da sauri, muka shiga cikin ɗakin. Anty Zulaihatu ta karɓa kofin ruwan ta yi tofin addu'o'i ta ba ta sha ragowar kuma ta shafa mata a jikinta take ta koma sauƙe ajiyar zuciya wani na bin wani tamkar wacce ta yi gudun ceton rai. Anty Zulaihatu ta gyara mata zamanta ta kwantar da ita cikin ƙanƙanin lokaci bacci ya ɗauke ta. Duk muka sauƙe ajiyan zuciya muna hamdala da lamarin ya zo da sauƙi haka don tana da hawan jini mai sarƙarƙiya gefe guda kuma tana cutar numfashi.
"Anty wai me ye wannan take yi a cikin gidan nan ne?". Umar ya yi zancen cikin haÉ—e rai da zafin zuciya.
"Amatullah ce fa ko ba ka gane ta ba ne? Nan kamar gida ne a gare ta ai, tana da ikon zuwa a duk sanda take so kuma ta yi niyya".
"Anty a da kenan ba yanzu za ta watsa mana ƙasa a idanunmu ba. Cikin shege fa Amatullah waye ya yi miki ciki? Me ya sa za ki yi mana haka?".
Fayau Anty Sawwama ta ɗauke shi da mari ta nuna shi da ƴar manuniyar ƴatsarsa"Umar ba ka yi hauka ne ko kuma shaye-shaye ka fara yi ba mu sani ba?. Ashe ba za ka iya rufawa ƴar uwarka asiri a bisa ƙaddarar da ta same ta ba".
Ya dafe gefen kuncinsa da ta watsa masa marin"Anty ƙaddara? Ƙaddara fa kika ce? Amatullah ba yarinya ba ce ta ba wa shekaru goma sha biyar baya. In ma ƙaddarar ce me yasa tun lokacin da abin ya faru ba ta sanar ba har sai da ciki ya ɓullu a jikinta?".
Tana ada aya a nan tashi ya fice daga cikin ɗakin fu cikin saurin kamar mai tafiyan akan iska. Anty Zulaihatu ta dafe kanta"innalillahi wa inna ilahirin raji'un! Allahuma ajirni fi musifati". Kasa motsa na yi daga inda nake zauna izuwa yanzu kam ma kukan ma na daina illa kukan zucin da nake yi mai matuƙar ƙuna da raɗaɗi. Ina nan zaune har Anty Zulaihatu ta tashi ta fita babu jimawa ta dawo ta zauna a kusa da ni.
"Ki tashi ki je ki yi wanka, ki gyara jikinki. Ki sauya kaya sannan ki zo ki ci abinci sai ki kwanta ki huta".
Na ɗago rinannun idanuna ina kallon ta da shi sai dai bakin ya kasa furta komai. Ta dafa kafaɗata" Amatullah ki yi haƙuri na san ba zan iya kwatanta girman damuwar da kike ciki ba, amma tabbas ni ma ina cikin damuwa domin duk abin da ya same ki haƙiƙa kai tsaye ni ma ya shafe ni. Ki miƙa lmauranki ga Allah ki daidaita nutsuwarki sannan ki tanadi bayanan da za ki yi wa iyayenmu". Da taimakon ta na miƙe tsaye ta riƙo ni ta kai ni har ƙofar banɗakin na shiga. Na durƙushe a gaban bokatin ruwan da ta kai mini ina kukan zuci kaina har wani ciwo yake yi mini idanuna suka kumbura tsumtim.