← Book details Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 58

Sashe 24

Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cike da gamsuwa da zantukansa na ce"in sha Allah Malam ina godiya sosai". Haka na tashi na baro cikin staff ɗin jikina duk a sake, na koma aji har aka tashi ban dawo daidai ban tsaya jiran su Rauda ba na yi tahowa ta, ina tafe kaina a ƙasa
na ji ana yi mini sallama. Da farko ban amsa ba sai da aka ƙara yi a karo na biyu kafin na amsa tare da waigawa bayana.
Na yi turus na tsaya ganin mutumin da muka haÉ—u da shi É—azu da zan taho ne kafin na yi magana ya riga ni.

"Na ƙara tsorita ki ko?"

Na jijjiga kaina na juya zan ci gaba da tafiyata ya kuma tsayar da ni.
"Har kun tashi daga islamiyyar kenan? Ai tun É—azu nake tsaye a nan ina jiran dawowanki".
"Don Allah bawan Allah kar bar ni haka nan".

"Zan bar ki ne kawai idan har na tabbatar da cewar kin isa gida cikin ƙoshin lafiya, ba tare da wani ya ƙara firgita ko tsoritar da ke ba".
Na ɗaga kai ina kallonsa ganin ya bar motar ya soma bi na da ƙafa.
"Ba ka tsoron a É—auke motan ka baro ta a can?". Ya murmusa kafin ya ce"na bar ta a hannun Allah, na yarda kuma duk abin da ya zartar babu kuskure a cikinsa".

"To ka koma kawai na gode da rakiyar". Ya ɗan ranƙwafo da kansa ya rage tsayinsa ya ce"don Allah kar ki hana ni aikin lada. Ni ma fa ina da ƙanne mata kuma na san yanayin rarurarsu, yanzu haka a gajiye kike".

Taƙaitaccen murmushin gefen baki na yi kafin na furta"babu alamar gajiya ni kam".
"Kar ki faɗa abin da ba shi ne a cikin zuciyarki ba don fuskarki ta riga da ta bayyana gaskiyar da kike ɓoyewa".

"Wai me yasa mutane da yawa suke cewa fuskana yana bayyanar da labarin zuciyata ne?".

Ya ɗage girarsa guda"wataƙila zuciyar ce ba ta son a zarge ta da kasancewa daga cikin maƙaryata". Babu shiri na ji dariya mai sauti ya ƙwace mini na sake ina yi babu ƙauƙƙautawa. Sai da na tsagaita don kaina kafin na ce"kai dai da abin dariya kake".
"ÆŠabi'ata ce son ganin wani yana farin ciki a sanadina. Yanzu dai mu je na raka ki ko". Ban ce da shi komai ba muka fara tafiya yana ta ja na da hira ina amsa masa har muka isa farkon layinmu na dakata a nan.
"To rakiyar ta isa haka kar na ja ka da nisa. Kuma ka ce tafiya ce a gabanka".

"Tafiya ce kam a gabana mai nisa amma na zaɓi na tsaya na fara sauƙe haƙƙin da yake kaina".

Na ɗage masa ido ɗaya alamar ban fahimci zancen ba haka ya ba shi damar ci gaba da zancen"haƙƙin tabbatar da cewar wani bai sake razana ki ba mana".
"Da ba ka fasa tafiyarka ni kam babu wani matsala, ni da ko sani na ma ba ka yi ba".
"Ina ji a jiki zuwa gaba zan zama É—aya daga cikin mutanen da suka fi kowa saninki, yanzu dai mun iso ne kika tsaya a nan?".

"Ba mu iso ba amma ga can gidan mu daga nan ma ina hango sa". Na ƙare zancen ina nuna masa gidanmu da ƴar manuniyar ƴatsata.
"To tun da kin hana ni aikin lada bari na tsaya daga nan, sai dai har za mu rabu ba ki tambayi sunana ba alhalin ni kuma na san naki". Na ware idanuna"a ina ka san sunana bawan Allah?".
"Zuciyata ce ta sanar da ni".
"To me ye ta sanar da kai?".
Ya juya manyan fararen idanun"Safiyya". Na jijjiga kaina"tun da na É—an ji tausayinka bari na sanar da kai. Sunana Amatullah".

"Ni kuma sunana Muhammad Taukeeq".

Na jinjina kaina"ina godiya, Allah ya kiyaye hanya". Cike da jin daÉ—i ya ce"Amin na gode, ki fara wuce wa tukunnan". Murmushi kawai na yi na wuce izuwa gida har na isa annuri bai gushe daga fuskana ba.
[8/4, 8:52 PM] Maimunatu Iyam: *DAFIN HARSHE*

©️ Maimuna Tijjani Iyam

_________________________________________

Page 1️⃣9️⃣

Kai tsaye na wuce ɗakinmu ba tare da na mayar da hankali akan tunkoson jama'ar da suke tsaye cirko-cirko a cikin gidan ba. Sauya kayan jikina na yi na fito na soma haɗa wuta saboda wani irin masifaffan yunwan da take ƙwaƙulan hancin cikina da tun suna kukan yunwan har sun saduda. A wajen na tsinci kan zancen wai sata aka shiga ɗakin Maman victor aka yi mata na turamen zannuna da kuɗi. Sosai aka yi dambarwa kamar ba za su bar juna da rai ba, sai da wasu biyu daga cikin manyan dattijan unguwa suka shigo suka tsawatar saboda hayaniyar ya ƙai ƙololuwar yawa. Taliya na tafasa fara na ci na zuba mata mai da yaci na ci nawa na bar wa Umma da Abba na su a kula, ina gamawa na fito na yi alwala na koma ciki na gabatar da sallan kasancewar yau ba mu da karatu da yaran da nake koyar da su, hakan ya sa ina iddar da sallan na ɗauko alƙur'ani na soma karanta ban gushe ina yi ba har sai na haɗa izu biyu cif-cif. Na yi sallan isha'i na fito falo na zauna don har yanzu Umma ba ta dawo ba haka nan ma Abba tun da na shigo ban shi ba, kuma a sanin da na yi masa tun runtsi ba ya wuce ƙarfe taran dare a waje.

Kamar an jefo ta haka Amira ta faÉ—o cikin É—akin ta manna mini waya kunne, na bi ta da kallo.
"Mansur ne za ku gaisa".
Na riƙe wayar ina yi masa sallama ya amsa, haka muka gaisa cikin girmamawa da mutunta juna kafin na miƙa mata wayar, ba su yi wani dogon magana ba ita suka yi sallama. Ta ajiye wayar tana kallona.
"Ba ni labari mana?". Na É—age mata gira"ban gane ba wani irin labari kenan?".

"Kar ki raina min hankali mana Amatullah. Wane ne wannan mutumin da É—azu kuka tsaya da shi a bakin layin nan, kuna ta hira kamar kun daÉ—e da sanin juna".

Fuskana ɗauke da mamaki ƙarara na furta"waye ya sanar da ke wannan labarin?". Ta sheƙe da dariya kafin can ta soma cewa"da idona fa na ganki, na so na je na tutsiye ki a wajen sai kuma na sauya shawara". Na yalwata fuskana da yalwataccen annurin da yake fitowa tun daga ƙasan zuciyata.

"Wallahi ni ma ban san ba ban taɓa ganin sa sai yau ɗin nan. A hanya muka haɗu shi ne ya tsaya jirana har muka taso daga islamiyya, ya dage wai sai ya rako ni gida saboda kar wani ya ƙara tsorita ni kamar yadda ya tsorita ni da horn ɗin motarsa". Na ƙare zancen ina baza murmushi kamar wacce aka yi wa alƙawarin kujerar makka na bana.
Sake da baki Amira take kallo na har na gama zancen kafin ta musguta tana faɗin"amma ai ba shi ne mutum na farko da ya taɓa nuna buƙatar yi miki rakiya ba, kika watsa musu ƙasa a idanunsu. Shi wannan me yasa kika amince masa har kika sake masa fuska".

"Wannan ya bambamta da duk wanda na taɓa haɗuwa da su akan hanya". Ta katse ni"me ye ya bambamta shi da sauran?".
"Saboda har muka rabu da shi bai yabi sura ko halittan jikina ba. Saɓanin sauran samarin da nake cin karo da su maganar farko da yake fara fitowa daga bakinsu shi ne yabon surana".

"Ki na da gaskiya da wannan fannin. To ba ni labari me ye kuka tattauna?". Na galla mata harara"ban sani ba uwar son gulma da bin ƙwaƙwƙwafi".
"Shikenan in ta yi tsami ai za mu ji".
Na gyara zamana na kawar da zancen ta hanyar sauya akalar maganar"wai ina Umma ta je ne ga Abba ma har yanzu bai dawo ba?".
"Umma ta dawo ta ƙara fita. Shi kuma Abba bai fita ba ma sai da aka yi ƙiran asr".

Na ɓoye mamakina na ce"Abban?". Ta gyaɗa mini kai alamar e tana ci gaba da cewa"me ye wani abin mamaki?".
"Babu daman ina so mu yi magana akan wannan malamin da muka haÉ—u da shi a tasha.......". Ta É—aga mini hannun na dakata haka.

"Ki rufa mana asiri Amatullah kar wani ya ji ki kina maimaita wannan maganar, ki manta da wannan mutumin ki sa a ranki kamar babu wani abun da ya faru. Wallahi idan kika kuskure wani ya ji ki kina irin wannan maganar sai É—an buzunki".

"Ki saurare ni ki ji abin da zan faÉ—a mana".

"Ina jin ki". Ta amsa mini a daƙile.
"Sheikh Dawood Nasarawa yana daga cikin manyan baƙin malaman da za a gayyata a lokacin yaye mu daga islamiyya, saboda ya sama halatta babu irin faɗi tashin da Malam Suleiman bai yi ba. Zuciyata ta cika da wasi-wasi akan sanin da mutanen gari suka yi masa da kuma fuskar da yau nuna mini a tasha". Tun kafin na gama zancen na ga ta haɗe giran sama da na ƙasa ta zuba mini na jiyamunta. A kufule ta soma furzar da takaicin da na yi silar cusa masa a cikin ranta.
"Ki yi maza ki cire wannan gurɓataccen tunanin daga cikin ranki kafin ki jefa kanki cikin wata masifar da ba za ki iya cire kanki ba. Kin san fa yanzu duniya ta sauya abu ƙiris za ka yi ko'ina ya ɗauka, yadda malamin nan ya yake kan lokacinsa idan kika ce diddiginsa za ki bi sai kin sama ma su tsigare ki ma daga cikin addinin. Don haka ki rufa mana asiri ki rufawa kanki asiri".

Sallamar Umma shi ya sanya ni haɗiye maganar da na yunƙuro da nufin furtawa, ni da Amira muka haɗe baki wajen yi mata sannu da zuwa ta amsa mana a taƙaice tana wucewa cikin ɗakin.
"Kin ga ni bari na je na karɓo awarata, na fita soya". Amira ta yi zancen tana miƙewa tsaye, na yi banza da ita na ƙi kallonta. Fahimtar abin da nake nufi ya sa ta ci gaba da magana.

"Na manta ban sanar da ke ba, ɗazu Bashir ya ƙira ni wai yana son jin muryar sarauniyar mata tauraruwar birnin zuciyarsa....".
Chapter 24 · 0% Book details