Sashe 50
Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Lokaci guda na ji wajen ya ɗauki kabbara ana faɗin isowan Sheikh Dawood Gaskiya dokin ƙarfe tare da shaƙiƙin ɗansa na miji ɗaya tilo. Duk yadda na so ganinsa cincirindon mutanen da suka kewaye sa sun hana ni ganinsa.
Sai da Malam Aminu ya yi magana cikin lasifika kana wajen ya nutsu, ya ƙira Rauda Salisu a matsayin ɗalibar da za ta buɗe taro da addu'a. Sai a lokacin idanuna suka sauƙa akan Sheikh Dawood take ƙirjina ya buga na ƙura masa idanuna, tabbas shi ne wanda na ga ni a tasha har ya yi mini maganar banza da ƙoƙarin taɓa jikina. Haka zalika yanzu ma shi ne zaune cikin kamala da nutsuwa, duk wanda zai gaishe shi sai ya durƙusa har ƙasa.
"Ga can Anty Sawwama da su Yaya Alhassan sun iso, Abba ma ya iso tun ɗazu. Umma ma su a hanya tare da Ummanta mun yi waya da ita ta ce sun kusa isowa". Na tsinkayo amon Amira ta yi zancen a daidai saitin kunnena, na yi kamar zan tashi na je wajen su Malam Suleiman ya yi mini ido akan na koma na zauna, babu yadda na iya haka na koma na zauna. Sai aka gabatar da jawabi sosai sarakuna da ƴan siyasa suka tashi suka yi nasu jawabin kana Malam Aminu ya fara ƙiran Aliyu a matsayin wanda zai fara gabatar da karatu.
Ya tashi ya yi karatun cikin tsantsan nutsuwa da fitar da haƙƙin ko wani harrafi, wajen ya ɗauki kabbara aka ayyana shi a matsayin wanda ya zo na uku kuma ya kasance ɗaliba mafi ƙwarzo na shekara. Aka ƙira wani basarake ya ba shi kyautarsa da makaranta ta tanada masa sannan shi ma ya ƙara masa da kyautar zunzurutun kuɗi har naira dubu ɗari tare da fatan alkhairi da addu'o'in da ya dinga yi masa.
Har na yi shiri don na sa a raina cewar ni za a ƙira a matsayin ta biyu, haka nan ma sauran ɗaliban don duk sai waigowa suke yi suna kallona. Kwatsam muka yi an ƙira sunan Al'amin jikin kowa ya yi sanyi, hatta shi Al'amin ɗin da kansa don bai fito ba har sai da aka ƙara maimata sunan a karo na biyu kana na tashi. Ya je ya yi karatun jikinsa gabaɗaya babu ƙwari, shi aka ayyana a matsayin wanda ya yi na biyu aka ƙira dan takaran kansilan yakinmu da ba shi kyautarsa da makaranta ta tanada domin shi aka yi musu hoto. Daga haka ya dawo ya zauna gabaɗaya yanayinsa ya sauya.
"Amatullah Munnir".
Malam Aminu ya ƙwala ƙiran sunana a cikin lasifika take zuffa ya keto mini ina ɗago kaina muka haɗa ido da Abbana. Fuskarsa a washe cikin tsantsan farin cikin da har sai da na hawaye a idanunsa. Na tashi na isa kan munbarin ina karantu auziya da bismillah wajen ta kaure da kabbara na ci gaba da karatun suratul Maryam cikin sanyin murya wajen ya yi shuru ina cikin karanton na hango shigowar Umma da Umman Amira. Sai da na karance suran tas kana aka yi kabbara da alama hatta su Malam Suleiman sun ji daɗin karatun da na yi fiye da na sauran.
Aka bayyana ni a matsayin wacce ta yi na ɗaya. Aka ƙira wani basarake ya ba ni kyautata ya kuma ba ni wasu kuɗaɗen da ban san adadin yawansu, zan tafi aka ce na tsaya aka kara ayyana ni a mashin gwarzuwan shekara kuma ɗaliba mace ta farko ta yi sama iri wannan nasarar cikin shekaru goma da kafa islamiyyar. Sannan aka ayyana ni a matsayin ɗaliba mafi hazaƙa a cikin ajinmu. Malam Aminu ya ɗauko kyautar da za a ba ni ya ƙira sunan Sheikh Dawood a matsayin wanda zai karrama ni da kyauta ya taso cikin shirgar alfarma, tun da ya taso nake bin sa da kallo har ya iso wajen. Ya karɓa lasifikan ya soma jawabi.
"Yau na cika da murna da farin ciki ganin yadda aka yaye ɗalibai masu yawan gaske kuma duk sun haddace littafi mai tsarki. Ina jinjinawa malamanku ƙwarai da gaske da suka tsaya kai da fata wajen tabbatar da sun sama ilmi mai inganci. Wannan ɗalibar da ta yi na ɗaya kuma ina yi mata fatan alkhairi da addu'ar dacewa a cikin rayuwarta. Sannan idan mahaifi ko mahaifiyarta yana wajen wannan taron ina so a taso ya hau kan munbari domin na yi masa wani albishir".
Aka dinga kwarara kabbara har Abba ya iso wajen suka yi musaba kana Sheikh Dawood ya ci gaba da jawabinsa.
"Bawan Allah da farko ina taya ka murna domin Allah ya yi maka arzikin da ba kowa ne yake dacewa da irin sa. Wannan É—iya taka zinariya ce a cikin zinaru, idan akwai wani karatun da take yi ko kuma za ta fara to na É—auki É—awainiyyarta daga yanzu har ta gama shi, idan kuma daga nan aure za ta yi to na É—auki nauyin yi mata kayan É—aki da duk wani abun da ake yi mace yayin bikinta. Zan karrama ta cikin alkyabba mafi daraja da tsada".
Wajen gabaɗaya ya ruɗe ya sa aka ɗauko wata alkyabba mai tsananin sheƙi da ƙyalle wanda ko da daga kallo guda ka san cewa mai tsada ce balle kuma ace ka murza jikinta. Ya ɗaura mini ita a kaina idanumu suka sarƙafe cikin na juna, take na ji raina yana tafasa sakamakon wani irin kallon da yake yi mini da na kasa gano ma'anarsa.
Abbana sai godiya yake zuba wa yana yi yana ƙarawa, ɗan takarar kansila da sarakuna duk suka gaisa da shi tare da yi mini kyaututtuka masu tsoka.
"Ina taya ki murna matuƙa kuma ina addu'ar Allah ya sanya albarka a karatunki".
Da sauri na ɗago kaina don tabbatar da mamallakin wannan muryar da ta kasa gogewa daga cikin kaina. Caraf idanuna suka sauƙa akan sa yana tsaye a gabana fuskar ɗauke da maɗaukaki murmushi. Hannunsa riƙe da alƙur'ani da aka yi ado da wasu irin zare masu jan hankali. Ya miƙo sai dai mamaki ya hana ni karɓa balle na ce da shi wani abu.
Sai da na ja dogon numfashi na fesar kafin na ce"Muhammad Taufik ko?". Ya sakar mini da murmushin yana faɗin"karɓi mana kin tsaya ki na ta kallo na". Jikina a sanyaye tamkar kazar da aka kwararawa ruwan zafi na kai hannu na amsa alƙur'anin.
"Ina taya ki murna Allah ya albarkacin karatun da aka yi. Kafin ku tafi zan neme ki". Kaina kawai na girgiza masa kafin na ce wani abu Malam Aminu ya iso wajen ya ƙira gefe.
"Amatullah mu je Sheikh yana son magana da ke". Take na ji ƙirjina ya buga ya yi gaba ina bin shi a baya har gaban Sheikh na durƙusa a ƙasa, ya ƙura mini idanu kamar zai cinye ni ɗanya ya ɗauko wasu littattafai ya miƙo mini na miƙa hannu zan karɓa caraf na ji ya riƙe hannuna gam. Babu shiri na ɗago idona ina kallonsa sai dai ko a jikinsa sai murza mini hannuwa da yake, sai da na sa ƙarfi kafin na kwace hannuna. Na yi zumbur zan tashi wani jiri ya ɗauke ni duk yadda na so tsayiwa akan ƙafata lamarin ya ci tura, Malam Aminu da yake kusa da ni ya yi saurin karɓan alƙur'anin da yake hannunsa da sauran kyaututtukan.
Luu na yi baya na faɗi a ƙasa ina jin kaina yana juyawa jikina gaba ya sake, mutane suka cika a kaina ina ganin su dishi-dishi.
"Amatullah lafiya kike kuwa?". Muryar Yaya Alhassan kenan da ya kasance abu na ƙarshe da na ji kafin hankalina ya gushe, aka ɗauke ni ridi-ridi sai asibiti. A hankali na soma buɗe idanuna da na ji sun yi mini matuƙar nauyi ina ƙarewa ɗakin da nake cikinsa kallo. Sai da na ƙarewa ɗakin kallo na tabbatar da cewar asibiti ne. Ummata, Umma Amira, Anty Sawwama da kuma Amira, Anty Zulaihatu su kenan a cikin ɗakin. Suka fara jeranta mini sannu wani na bin wani kafin na kai ga amsawa Abba, Yaya Alhassan, Umar da Malam Suleiman suka shigo cikin ɗakin cikin wani irin matsanancin firgici da tashin hankali, na lura idon Abba har da hawaye ya kafe ni da idanuna kamar ya ga wata sabuwar halitta.
Kafin na yi aune ko na ce wani abu tunin Abba ya wanke ni da mari, ina ɗagowa ya ƙara wanka mini wani marin. Su Umma duk suka tattaso suna tambayar ko lafiya.
[10/25, 8:15 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE*
Â©ï¸ Maimuna Tijjani Iyam
_______________________________________
Page 3ï¸âƒ£6ï¸âƒ£
"Munniru lafiya kuwa? Za ka ɗauke yarinya da mari alhalin tana gadon asibiti cikin jinya". Ta juya tana duban Yaya Alhassan da tun da suka shiga kansa yake ƙasa ya gaza ɗago ido balle ya kalli kowa.
"Alhassan wai me ye likitan ya shaida muku ne? Me yake faruwa da Amatullah É—in?". Bai É—ago kansa ya kalle ta ba kamar yadda bai amsa mata ba.
"Ba fa zai yiyuwa a tisa min ɗiya a gaba da duka ba akan wani dalilin? Tana cikin jinya idan ba a lallashe ta ba ai ba za tada mata da hankali ba, wallahi ba za ta saɓu ba wai bindiga a ruwa".
"Hafsatu ki rufe min baki tun kafin na yi sassaɓa miki a nan wajen nan. Kin cuce ni kin cuci rayuwar ƴarki. Hafsatu kin wargaza min duk tanadi da shirin da na yi wa rayuwar Amatullah, kin jefa ni cikin kunya da tsoron haɗuwa da mutane balle har na shiga cikin su na yi mu'amala da su, tsakani na da ke Allah ya isa ban yafe miki". Gabaɗaya wajen ya ɗauki salati da sallallami Umma ta hau hayagaga ta inda ta shiga ba ta nan take fita ba, sai da Umman Amira ta taso ta riƙe ta tana ba ta haƙuri da tunatar da ita cewar a asibiti fa muke.
Kuka nake yi da dukkan ƙarfina jikina gabaɗaya yana rawa tamkar mazari haƙwarana suna karabɗiya da juna kamar jinriran kazar da ruwa ya yi wa ɗan banzan duka.
"Don Allah ku ba mu waje ina son ganawa da Amatullah ita kaÉ—ai". Abba ya yi zancen cikin tsantsan tashin hankali da ruÉ—ewan da ya bayyana har a cikin muryarsa.