Sashe 31
Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tabbas indai ba idanuna ne suka sama matsala ba ko kuma suka daina aikin su yadda ya dace, to babu shakka Umma na ga ni tana tsaye a kan Abba da yake kwance a bisa gado yana bacci huce gajiyar da ya kwaso, ƙaramin almakashi ne a hannunta tana yadda gashin gemunsa tana zubawa a cikin wani kwalba.
Ban yadda ta ganni ba na yi wuf na koma don da farko ban ya ma tunanin cewa Abba yana cikin ɗakin ba da ba zan shigo ba, zama na yi a ƙasa dirshan na tallafe kuncina yayin da numfashina yake sarƙafe mini a ƙirjina, zuffa ya soma jiƙa miji jiki lajaf tamkar wacce aka juyewa bokatin ruwa a kanta. Na dulmiye cikin kogin tunanin dalilin abin da Umma take yi, sannan me ye za ta yi da gashin gemun Abba da take yadda take sanyawa cikin wannan kwalban?.
"Amatullah".
Na tsinkayo muryar Umma a tsakiyar kaina, na yi figigi na miƙe tsaye ina goge ƙwallan da ya ɓata mini fuska wanda ban san lokacin da suka zubo ba.
"Ki samo min garwashi".
"Umma ai ba a hura wuta ba ma. Amma me ye za ki yi da garwashi a daren nan?". Kallon da ta tsare ni da shi ya sanya ni rusunar da idanuna ƙasa jikina a sanyaye tamkar jinjiran kazar da ruwan sama ya yi wa ɗan banzan duka.
"Ba na son yawan tambayoyi ki wuce kawai ki nemo min abin da na buƙata". Ban kuma cewa komai ba na fice jikina gabaɗaya babu kuzari kamar wacce aka zarewa laka.
Ko da na fito na gaza assala komai na tisa munkubarin a gabana na zagba tagumi tunani kala-kala babu wanda bai kawo wa ƙwaƙwalwata ziyara ba.
"Ƴar uwa lafiya kika zauna kika zagba tagumi haka?".
Babu shiri na ɗago kaina saboda ba kaɗan ba sauƙar furucin a ƙofofin kunnuwana ya razana ni, Anty Amarya ce matar ustazu Abdulwahab ta yi maganar tana tsaye kusa da ni. Ganin ban amsa mata ba ya sanya jan kujera ta zauna kusa da ni tana ƙara faɗin"ko dai akwai wata matsalar ne wanda kike ganin bai dace kowa ya sani ba, ba zan matsa miki sai kin faɗa min sirrin zuciyarki ba amma in Sha Allah zan taya ki addu'a. Allah ya kawo miki mafita ta inda ba ki taɓa zato ba balle tsammani".
"Amin na gode". Na amsa da shi a taƙaice kasancewar tun da suka shigo gidan ba mu taɓa wani dogon magana da ita da ya wuce gaisuwa ba. Har ta tashi za ta tafi na yi hanzarin dakatar da ita ta hanyar faɗin"don Allah na ga kamar girki kike yi ko?".
"E girki nake yi yau na yi dare ban gama ba".
"Don Allah garwashin wuta nake so ko guda biyu ma. Za mu sa turaren wuta".
Ta faɗaɗa fara'ar fuskarta kafin ta ce"ba damuwa ina kaskon na zuba miki". Na ji kamar an sauƙe mini wani ƙaton dutse daga kaina, na tashi da sauri na shiga na ɗauko mata kaskon na ba ta. Ta karɓa ta je ta ciko mini shi na karɓar ina ta zuba mata godiya kafin na yi mata sai da safe na shiga ciki. A falo na iske Umma na ajiye kaskon a gabanta.
"Umma ga garwashin".
Ba ta tanka mini ta É—auka ta shiga cikin uwar É—aka, babu jimawa ta fito mini da abun shimfiÉ—i ta ce na yi shimfiÉ—i na kwanta a falon na amsa tare da yi mata sai da safe wanda ba ta ko amsa ba ta yi shigewarta ciki.
Shimfiɗi na yi na ɗauko alƙur'ani da tocila a kusa da ni na zauna, sosai na mayar da hankalina kacokam ga karatun don so nake yi na hana kaina faɗa cikin tunanin da yake addaban kwanyata. Na daɗe ina karatun don aƙalla na yi awa guda ina yi ban gushe ina yi ba har sai da na yi wani sanyi ya soma ratsa sashin ruhina kana na rufe alƙur'anin.
Na kwanta akan bayana ina kallon rufin ɗakin da ya zamo shamaki tsakanin ganina da sararin samaniya, ajiyar numfashi na koma sauƙewa wani na bin wani tamkar wacce ta yi gudun ceton rai tunanin abun da na ga Umma ta yi shi ya tsaya mini a rai kwatankwacin yadda ƙayan kifi yake tsayiwar ƙiƙam a maƙoƙaro.
A bayyane na furta"Ya Allah ina roƙonka tare da tawassali da sunayenka tsarkaka guda ɗari ba ɗari da ka shirya mini Ummata ka dawo da ita kan hanya madaidaiciya mai ɓulewa. Ka kuɓutar da Abbana daga dukkan abin da take shiryawa ka kuma tsaretar da shi daga dukkan ƙullin da take ƙullewa".
Cikin wani irin yanayi na mutuwar jiki na ƙare zancen ina jin wasu tsiraran hawaye masu ɗumi suna bin gefe da gefen fuskana. Haka na ƙarar da kusa rabin daren ban runtsa ba abubuwa da dama sun taron sun yi mini yawa sai da na yi sallan asubahi kana na sama runtsawa.
Hayaniyar da nake ji kamar a cikin mafarki shi ya yi silar farkawa na ba don baccin ya ishe ni ba. Na soma buɗe idona a hankali kafin na buɗe sa tar ina ƙarewa ɗakin kallo, tashi na yi na zauna ina murtsike idanuna tare da ambaton addu'ar tashi daga bacci kamar yadda addinina ya tanada.
Ƙananun maganganu nake yi suna tashi daga ɗakin wanda ina da tabbacin Abba da Umma ne suke magana, numfashi na sauƙe mai karfi kafin na tashi na soma tattare shimfiɗana. Don na yi wa kaina alƙawarin indai ba bisa kuskure ba ba zan taɓa sauraron zancen da suke tattaunawa a tsakaninsu ba, ko da kuwa ya shafe ni.
Tattare falon na yi tsaf na yi shara na kimtsa ko'ina na fito na haɗa wuta na ɗaura farar shinkafa, ina girkin ina duba alƙur'anina ina ƙara tisa karatun da aka yi mana jiya. A haka Amira ta zo ta same ni ba ta katse ni ba har sai da na kai ƙarshen ayan da nake karantawa na rufe ƙur'anin, kana muka gaisa da jin lafiyar juna.
"Wannan ledar fa?".
Na jefa mata tambayar ina jawo ledar da ta ajiye a gabanta na soma buɗewa, atamfa ne guda biyu da sarƙa da ɗan kunne.
"Wai har kin manta kenan? Tsarabar da Mansur ya kawo ne". Na yi mata kallo guda ina fiddo da atamfar ina ƙare musu kallo.
"Ai kuwa ga su ma sha Allah! Allah ya saka masa da alkhairi ya ƙara buɗi. Amma dai wannan ɗawainiyyar ta yi yawa kar ki manta fa ko gabatar da kansa bai yi a gaban magabatanki ba".
"Amin! Matsalata da ke kenan ba a yi miki gwaninta ko kaɗan. Bawan Allahn duk ƙoƙarin da yake yi a kaina in ba a sa masa albarka ba ai bai dace a kushe sa ba, ke yau da safen nan ma da muka yi waya cewa ya yi na kusa na daina fita wannan tallar sai ɗauka dukkan ɗawaniyyata da ta mahaifiyata".
Babu shiri na ware dukkan girman idanuna a kanta tare da sake leɓɓe ina bin ta da kallon mamaki, kafin na yi magana muka jiyo sallamar Anty Sawwama da hakan ya tursasa mini haɗiye zancen da na yunƙuro da nufin furtawa. Muka haɗe baki da Amira wajen amsa sallamar muna yi mata martaba da zuwa, falo muka shiga muka zauna kana muka gaishe ta ta amsa fuskarta ɗauke da yalwataccen annurin da ya ƙara taimaka wajen fito da tsatsar kaman jinin da suke yi da Abbana.
" Na yi muku sammako ko?". Na yi murmushi tare da girgiza kaina alamar a'a hakan ya ba ta damar ci gaba da maganar.
"Ina son na yi magana da Abbanki ne shi yasa na yi wannan sammako don kwana biyun nan da damuwar nan nake kwana nake tashi a cikin raina. Ina dai suna ciki ko?".
"Ga mu me ye muka yi ake nemanmu da wannan farar safiyar?".
Martanin da Umma ta mayar mata kenan cikin kakkauran murya tana isowa cikin falon ta zauna tare da ɗaura ƙafarta ɗaya bisa ɗaya.
"Hafsatu kenan kun tashi lafiya, Mannirun yana ciki kuwa?".
"Da ba mu lafiya ba ai ba za ki zo ki tadda mu haka ba. Manniru kuwa yana ciki amma na yanzu zai fito ba sai ki jira shi".
Gabaɗaya ji na yi jikina ya yi sanyi ƙalau na sadda kaina ƙasa ina jin zafin furucin da Umma ta yaɓawa Anty Sawwama. Fitowar Abba ya sani ɗago kaina ina bin sa da kallo har ya zauna haka kawai na ji tausayinsa ya cika mini raina ba tare da na san dalili ba.
"Maman Umar ke ce tafe da safiyar nan? To ya gidan ya kuma yaran?".
"Wallahi ni ce tafe gida da yara kuma duk lafiya lau. Daman na zo mu tattaunawa wata magana ne da kai shi yasa na yi sammako kar na zo na iske ka fita wajen aiki".
Shewa Umma ta saka har da tafa hannu kafin ta ce"su aiki manya, yo wannan aikin har wani abun ne? Aikin da ba ya tsinana masa komai shi kansa balle kuma wanda suke kewaye da shi".
Ƙwalla suka ciko mini kurmin idaniyata cikin rauni na ce"don Allah Umma ki yi haƙuri mana".
Amira ta riƙo hannuna tana faɗin"Amatullah mu je daga waje mu ba su waje su tattaunawa". Ban yi mata musu na tashi muka fita muna fita wani kuka mai ƙarfi ya kubce mini na kifa kaina a bisa gwiwa ina rero sa cikin durshashewar murya. Duk ƙoƙarin da Amira ta yi na ba ni haƙuri da lallashina na gaza sarrafa kaina kukan ne kawai nake jin yana yi gaban kansa yana fitowa. Har sai da Ummanta ta fito ta nema jin ba'asin me yake faruwa Amira ta yi mata bayani ita ma ta lallashe ni sosai ganin ba ni da niyyar tsagaita kukan hakan ya sanya ta jan hannuna zuwa ɗakinsu, ta umarci Amira da ta ƙarisa girkin da na aza bisa wuta.
Ko anan ɗin ma hawayen sun kasa tsayawa da ƙyar Umman Amira ta lallashe ni ta zubo mini wainar da take toyawa sai dai na kasa kai ko da loma guda cikin bakina. Haka har Amira ta zo ta iske ni .