Sashe 16
Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Lafiya kuma kika koma kika zauna?".
Cike da tsoro na ce"Malam wata alfarma nake nema daga wajenka". Ya tattaro dukkan hankali da nutsuwarsa gare ni"to ina sauraronki".
"Malam so nake yi a yi wa mahaifiyata nasiha da kuma tsoritarwa akan wani aikin saɓon Allah da take aikatawa wanda ba zan iya faɗawa kowa ba. Sannan alfarma ta biyu tambaya ce da ni da na daɗe ina buƙatar amsarta na rasa wanda zan tunkara da lamarin. Malam mahaifiyata ta kasance mai kaifin harshe irin mutanen da komai ya fito daga bakinta za ta furzar da shi ga ko waye ba tare da tunanin abin da kan je ya dawo ba. Tun kafin na yi wayo take jefa da mungayen kalamai tsinanniya, shegiya wani lokacin har ta suffata ni da ƴar zina. Kuma ni kaɗai ce ƴarta a duniya balle na yi tunanin son da take yi wa sauran ƴaƴanta ne ya rinjayi wanda take yi mini. Yayin haihuwata ta sama matsala har sai da aka cire mata mahaifa wanda hakan yake nuni da ba za ta sake haihuwa ba bayan ni. Tun abin baya mini ciwo har an kai munzalin da nake kasa bacci saboda damuwa".
Na tsagaita saboda kukan da ya taso mini a lokaci guda na yi na yi son raina ba tare da ya lallashe ni ba kana na É—aura daga inda na ka burki.
"Malam ba yabon kai na sama tarbiyya daidai gwargwado daga wajen mahaifina, ina da kamun kai da nutsuwa. Duk layinmu da ni ake buga misali wajen kyakykyawan hali da ɗabi'un ƙwarai. Amma tsorona ɗaya kar bakin da mahaifiyata take yi mini ya yi tasiri a kaina, ya wargaza duk shiri da tanadin da na yi wa rayuwata. Mahaifina ya sha nusar da ita da fahimtar da ita illar abin da take aikatawa amma kamar ana watsa ruwa a bayan ƙwarya".
Jikina ya soma rawa saboda kukan da ya gama galaitar da ni duk da bai ce da ni komai har lokacin amma na ji sanyi a cikin raina. Ko ba komai yau na fitar da damuwar da ta daɗe tana yi mini kai kawo a cikin ƙalbina.
Sai da aka shafa wasu mintuna kafin Malam Suleiman ya ja dogon numfashi ya fesar daga bakinsa da har da na ji sautin fitarsa. Kana ya soma magana cikin jimami da tarin damuwa.
"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un! Amatullah ko wani bawa kika ga cikin wannan duniyar yana da tashi irin damuwar. Da za a ba ki tahirin rayuwar wasu mutane sai babu shakka da sai kin yi mamakin yadda aka yi har yanzu suke dariya, rayuwa ce lokaci shi yake warkar da komai. Yanzu kin ga lokaci ya ƙure ki tashi ki je gida gobe idan kin zo sai mu ƙarisa maganar".
Cike da girmamawa na ce"na gode sosai Malam na gode da lokacinka da ka ba ni ka saurare ni". Ina gama maganar na tashi na É—auki bokitin na É—aura a kaina zan fita ya tsayar da ni.
"Ki cire damuwar komai a cikin zuciyarki. Sannan a duk lokacin da za ki fita talla ki dinga saka hijabi mai girma da zai rufe miki jikinki".
"To in sha Allah, na gode Malam". Na amsa cike da kunya ina sadda kaina ƙasa. Lokaci da na fito kowa ya watse daga islamiyyan kafin na iso gida har an ƙira salla, bayan cinikin da Malam Suleiman ya yi mini a hanya na ƙara yin cinikin naira ɗari uku jimillan kuɗin gabaɗaya ya kama dubu ɗaya da naira saba'in haka na koma gida a gajiye ina ajiye bokitin kunun, na yi alwala na yi sallan magrib na fito na haɗa wuta na ɗaura mana abinci kana na koma ɗaki na kai wa Umma cinikin da na yi.
Ban ga damuwa ko tashin jin daɗi a fuskarta ba duk da kuwa ban sayar da kunun gabaɗaya ba. Ki irgawa su ba ta yi ta ajiye su a ƙasan matashi har na tashi zan fita ta ce na koma na zauna na koma na zauna ina sauraronta.
"Mun yi magana da Sahura akan za ki dinga tafiya talla tare da Amira don na ga ta fi ki wayewa da sanin harkan. Da zaran kin kammala haɗa haddarki sai na fara yi miki soyayyar doya da ƙwai kina fita da shi bayan sallan isha'i'.
Na É—aura hannu a ka"na shiga uku Umma. Amira kuma?". Ta gallo mini wata banzar harara"ita ta ko tana da wani aibu wanda ni ban sa ni ba? Da za ki kafa hujja da shi".
"Wallahi inda take kai talla duk maza ne a wajen marasa É—a'a. Umma kin gan su kuwa? Duk ba su da kamun kai kuma ba sa kunyar haÉ—a jiki da mace, ko ita Amirar ma ki tambaya za ta faÉ—a miki". Ta yi sauri katse mini numfashi.
"Inna fahimce ki kina so ki ce ita ma kanta Amirar ba ta da kamun kai kenan ko? Idan da kuwa haka take to ina tabbatar miki ke ce ta farko wacce za ta fara gurɓatawa tun da ba ki da wata ƙawa ta kusa sama da ita kullum kuna tare da ita".
Na zube ina yi mata rantsuwa"wallahi tallahi Umma kullum muka zauna da ita sai na yi mata nasiha akan abin da take yi ba daidai ba ne".
"Amatullah na gama yanke shawarar dole ki fara bin Amira kuna fita tare har izuwa lokacin da ke ma kanki zai waye".
Wani irin zafi da tafasa zuciyata take yi mini na cire leɓena hawaye suna zuba daga idona da ƙyar na iya furta"Allah ya sa hakan ne mafi alkhairi". Ban jira abin da za ta ce ba na tashi na fita, har na gama girkin hawayen idona bai tsaya ba.
Yanayin da nake ciki ya sani sallamar yaran da nake yi wa karatu don babu abin da zai iya aiwatarwa a halin da nake ciki. Ina yin sallan isha'i na kwanta raina gabaÉ—aya babu daÉ—i.
Kamar a cikin mafarki na soma jiyo wani tashin sauti da ya sani buɗe idanuna da ƙyar saboda ciwon kan da ya addabe ni. Na laluma gefena ban ji alamar Umma tana kwance a gefe na, na yi zumbur na tashi na jawo tocilan da yake ƙasan matashi na kunna na haska ɗakin ban ga Umma ba. Kuma har lokacin ban daina jin tashin sautin ba.
Haka ya sa na fito falo na haska tocilin daidai inda kunnuwana suke jiyo mini sautin. Babu shiri na yi zaman Æ´an bori saboda munin abun da na yi tozali da shi.
Umma ce tsaye tana kewaye Abba riƙe da kw turaren wuta tana yi mass hayaƙi, ɗaurin ƙirji ne a jikinta yayin da ta ware kitson kanta ta bar gashin haka ba tare da kallabi ba. Tana wani irin suturai da yaren da tun da na zo duniya ban taɓa jin sa ba balle na san nau'in sa.
[7/20, 1:53 PM] Maimunatu Iyam: *DAFIN HARSHE*
Â©ï¸ Maimuna Tijjani Iyam
_________________________________
Page 1ï¸âƒ£3ï¸âƒ£
Ƙarar faɗuwar tocilan daga hannuna shi ya fizgo hankalinta zuwa gare ni take na ga ta rikice irin rikicewar da tun da ta haiho ni ban taɓa ganin ta cikin makamancin sa ba. Jikinta gabaɗaya ya soma rawa zan iya rantsuwa da Sarkin da ba shi da abokin tarayya ban taɓa ganin ta cikin wannan halin ba, sai dai bushashshiyar zuciyar da take ta shi ya hana ta sa fasa abin da ta yi niyya ba ta dakata da abin da take yi ba har sai da ta gama, wani ƙarin abun mamakin da ya hana ni tashi daga zubewan da na yi shi ne har lokacin Abba bai tashi ba yana nan kwance kamar gawa.
Sai da ta ƙara zagaye shi sau uku tana ƙiran sunanta tare da busa masa hayaƙin kafin ta ajiye kwasko a gefe ta nufo ni tamkar kububuwa. Cak ta ɗago ni ta dige ni akan dugadugaina ta finciki hannu kamar za ta raba ta da gangar jikina ta ja ni zuwa cikin ɗaki muna shiga ta cilla ni kam gado ta rufe ƙofar ɗakin kiruf.
"Me ya fito da ke cikin wannan daren?".
Ta watsa mini tambayar babu alamar wasa a tattare da ita yayin da ta dalle mini idona da tocilan da ta ɗauko kafin ta rufe ƙofar ɗakin.
Ruɗu da riɗimewar da na yi ya sani kasa cewa komai illa numfashin da nake sauƙewa a wahala. Ta zo dab da ni ta zauna kafin na yi aune na ji ta damƙo gashin kaina da na tufke ta bayan wuyana ta riƙe gam tana gindaya mini sharaɗi.
"To billahillazi bari na ja miki kunne, ki manta da duk abin da kika gani ki É—auka tamkar mafarki kike yi kuma har yanzu ba ki tashi daga baccin da kike yi ba. Idan kika sake na ji labarin nan a wani wajen sai kin yi mamakin abin da zan aikata gare ki, ki burne duk abin da kika gani a yanzu don na tabbatar da cewar sai kin fi kowa amfanar abin da na aikata a nan gaba kaÉ—an".
Na buÉ—e baki zan yi magana ta katse mini numfashi.
"Ba na so ki tambaye komai ki dai kawai ki yi abin da na ce da ke". Cikin wani irin yanayi da ya zarce a ƙira sa da tashin hankali ko firgici na ce"in sha Allah". Na ja bargo zan kwanta duk da na san ko da na kwantan ba zan iya baccin ba.
"Amatullah idan har kika fallasa wannan sirrin babu shakka sai na tsine miki kuma sai kin biya ni ɗawaniyyar da na yi dake". Zumbur na miƙe tsaye jikina yana wani irin matsanancin rawa duk yanda na so na yi magana amma hakan ya gagara, babu shiri na zube ƙasa sakamakon gazawar ƙafafuna na kifa kaina jikin gadon ina rera wani irin kuka marar sauti.
Ko gizau Umma ba ta yi ta haye gado ta yi kwanciyarta ba tare da ta damu da nake ciki ba, babu abin da yake sanya zuciyata tafasa da hana ruhina samun sallama da nutsuwa kamar idan na tuna ban san turaren me ye Umma take yi wa Abba ba.