← Book details Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 58

Sashe 48

Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Gaya mata dai wataƙila ta ji nakan". Amira ta yi zancen tana ƙunshe dariyar da yake ƙoƙarin kwace mata. Na galla mata harara kafin na yi wa Mansur godiya suka yi sallama da Mansur na ɗauki ledar muka shiga ciki. Muna shiga cikin gidan na ji gabana ya yanke ya faɗi lamarin da ya tilasta mini runtse idanuna ina karanto duk addu'ar da ta zo bakina.
Sharau muka tarar da gidan don masu kwana ba su fara zuwa ba a wannan lokacin, sai sun gamo sharholiyar su kafin suke dawowa cikin gidan idan dare ya tsala. Muka tarar da Hajiya Tasalla tare da wata matashiyar budurwar da fatarta ta sha bleaching har ta gaji ta yi jajir da ita duk fatan fuskar ya taƙushe waje guda tamkar an yi ɓarin garwashin wuta. Tun da na ɗaura idona akan ta na yi bugun zuciyata ya tssnanta. Har muka iso muka zauna ban ɗauke idona daga kan ta ba, muka gaisar da Hajiya ta amsa ta yi mana tayin abinci muka ce mun ƙoshi, haka nan kawai na ji zuciyata ta kasa nutusuwa don haka na tashi zan shige ciki.

"Hajiya ko wannan ce wacce tsautsayin ya faÉ—a mata?".

Cak na tsaya bisa sauƙar furucin a na'urar naɗan sautina. Kafin na waigo na ji Hajiya ta ba da amsa da faɗin"uhmm! Ke dai ki bari kawai ita ce ina gaya miki".

"Hajiya ita ce Ramlatun?". Na watsa mata tambayar hawaye suna ciki mini koramar idanuna.
"Ita ce, ita ma tun da tazo take tambayar ki". Take na ji jikina ya soma rawa duk yadda naso na furzo da zancen da yake ci min rai bakina ya ƙi ba ni haɗin kai wajen aiwatar da hakan. Jikina ya ci gaba da rawa ƙafafuna suka nuna gazawar su wajen ɗaukar nauyina sai da Amira ta taso ta riƙe ni, na fizge jikina na shiga ɗaki da gudu. Shirij na zube akan katifa ina kuka tamkar raina zai bar gangar jikina.

Na ji an dafo kafaÉ—una haÉ—e da cewa"Amatullah kike ko wace ce?". Na ya banza da ita ba tare da na ce da ita komai ba, hakan ya ba ta damar ci gaba da maganar.
"Hajiya ta sanar da ni duk abin da ya faru kuma na ji baƙin ciki matuƙa musamman da ta sanar da irin kamun kanki da ƙoƙarin ki wajen ganin kin killace mutumcin kanki da kiyaye kima da martaban gidanku. Ki ɗaga hannu ma ki godewa Allah da ya kasance ba ke kika kai kanki ba ƙaddara ce ta faɗa miki wacce ba ta wuce ranar ta. Ko kin zo gidan nan ko ba ki zo idan Allah ya nufa faruwan hakan babu makawa sai ya faru a gare ki, Mus'bahu cikakken namiji ne na tabbatar ke ma kin ji daɗin kasance da shi...".
Kalamanta na ƙarshe suka daki zuciyata tare da baƙa mini ruhina. Na yi zumbur na tashi na zauna tare da buge hannunta daga jikina.

"Ki na matsayin mace kike furta wannan maganar? Shin ko kaɗan ba ki ji tausayina ya ɗarsu a cikin ranki ba? Wallahi don babu yadda na iya ne ba ni kuma da wani zaɓi balle mafita amma da tunin na daina zuwa gidan nan. Ba zan ce da ke komai kuma ba zan nema jin wani abu daga gare ki na yarda ƙaddarata ce ta zo a haka kuma ina neman sauƙi a wajen wanda yake da ikon sausauta lamurana".

Tun da na soma maganar take kallona har na akai aya, ta yi dariya ta ce"ba nufi na baƙanta miki rai ba ne baiwar Allah. Sai dai zan so na yi miki wata tambaya guda, a yadda kike da diri da kyawun suran nan ki na nufi babu wani na mijin da ya taɓa kusantark....".
"Ki tashi ki fita tun kafin na idanuna su rufe na illata ki ko kuma na yi miki raunin da har ki koma ga mahaliccinki ba zai bar jikinki ba".

Ya miƙe tsaye ta riƙe ƙugu tana ƙare mini kallo kafin can ta ce"zan fita kamar yadda kika buƙata, amma kafin na tafi zan ba ki wani shawarar da nake da yaƙinin cewar za ta amfane ki. Na ji an ce kina neman Mus'bahu to ba za ki taɓa samun sa don na tabbatar tun ranar da ya aikata wannan abun ya haɗa jakarsa ya bar garin nan wataƙila yanzu ba ya ƙasan nan". Tana gama faɗin haka ta fice daga cikin ɗakin ta bar ni da sakin wani gigitaccen kuka mai raunana zuciyar mai saurare. Ban gushe ina yi ba Amira ta shigo ta dinga rarrashi na, na amshi wayarta na soma karatun aƙur'ani da shi sai da dare ta raba kana na ajiye wayar na yi dogon addu'a na shafa a nan wajen bacci ya yi nasarar ɗauka ta sai dai ban yi nisa ba na farka a zabure.
"Lafiya kuwa?".
Amira ta jefa mini tambayar cikin damuwar da ya bayyana har a cikin furucinta, maimakon na ba ta amsa sai kawai na fashe da kuka.

"Amira an ya ba haukacewa zan yi ba kuwa ni kam?".

Cikin sanyin murya ta soma cewa"babu abin da zai faru da ke in Sha Allah". Ta jawo ledar kayan da Mansur ya kawo ta fito da kayan ciki kayan marmari ne sai kuma wasu manyan cakuleti masu sanyi sa'annan lemonka gora har kala biyar. Ta matsa mini akan sai na ci wani abu ba don raina ya so ba na sha lemon da wasu daga cikin kayan marmarin. Washe garin ranar a islamiyya Malam Suleiman ya aiko aka ƙira ni ya zaunar da ni ya dinga yi mini nasiha tare da ba ni wasu shawarwari, ban iya daurewa ba har sai da na zubar da ƙwalla. Ko da a fito daga wajen Malam Suleiman lokacin har an tashi ban ga su Rauda da Ammi don daman sun ce daga islamiyyar wajen ɗinki suka nufa za su je su karɓo ɗinkin ankon waliman.
A hankali nake tafiyar tamkar wacce take jin tsoron taka ƙasa na fito daga cikin islamiyyar, zan tsallaka titi na ji an ƙira sunana na waiga da sauri.

"Yaya Alhassan". Na furta kalmar cikin mamaki don ban yi tsammanin ganin sa a wannan lokacin ba.
[10/24, 10:06 AM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE*

©️ Maimuna Tijjani Iyam

_______________________________________

Page 3️⃣5️⃣

Da saurina na iso inda yake tsaye a jikin mashinsa É—in tare da wani abokinsa da tun ina tahowa idanunsa yake kaina har na iso wajen bakina É—auke da sallama. Suka haÉ—e baki wajen amsawa kana na gaishe su suka amsa.
"Kun tashi kenan?". Na gyaɗa masa kaina ina zarcewa da faɗin"daman ma ina so na je gida wajenka na ba ka haƙuri akan abin da ya faru game da waɗannan kaya...". Ya yi saurin ɗaga mini hannu alamar ba ya son sauraren ragowar zancen.
"Abin da ya faru ai ya riga da ya wuce sai dai a kiyaye faruwarsa a gaba, na ji wai ba ki da lafiya tun lokacin nake so na zo na duba ki amma ina gudun abin da zai je ya dawo shi yasa ma ban zo ba, shi ne na zo islamiyya. Me yake damunki ne haka Amatullah? Duk kin rame kin faÉ—a tamkar ba ke ba, me ya yi zafi haka?".

Na sauƙe tagwayen ajiyan zuciya kafin na sama zarafin faɗin"zazzaɓi ne kawai sai kuma yanayin karatu".
"Amatullah kar ki faɗi saɓanin abin da yanayin fuskarki ya riga ya nuna. Tabbas akwai wani abun da yake faruwa ko in ce akwai abin da yake damunki". Na yi shuru ba tare da na ce komai tare rusunar da ƙwayoyin idanuna ƙasa.
"Alhassan don Allah kar ka yi sanadin zubar hawaye daga fuskar wannan kyakykyawar halittan". Furucin abokinsa kenan ya ƙara sausauta amon muryarsa ya ci gaba da cewa"ƙanwata me yake damun ki?". Na ɗaga idona na yi masa kallo guda na janye a hankali na ce"babu komai".
Yaya Alhassan ya amshe zancen"shikenan ba zan matsa miki amma ko ma mene ne ina miki fatan samun mafita cikin gaggawa, ranar yaushe ne walimar takun".

Na yi murmushin ƙarfin hali"gobe ne da ƙarfe tara na safe". Ya jinjina kansa"me kike so na taho miki da shi, tun da Umma ta hana ni yin wancan aikin alkhairin da na yi niyya".

"Zuwanka ma kaÉ—ai ya wadatar da ni ba sai ka zo mini da komai ba".

Ya tsuke fuskarsa"idan ba za ki faɗa ma ba ai kuwa duk abin da na yi niyya shi zan saya na kawo miki, in ya so in kin ga dama inna ba ki ki watsar ko ki kyautar wannan kuma ra'ayinki ne". Na saki taƙaitaccen murmushi"to shikenan na bar maka zaɓi duk abin ka taho mini da shi ina maraba da shi".
"Ni ma da za a yi na'am da nawa kyautar da na yi " Furucin abokinsa kenan da ya sani É—aga idona na yi masa kallo guda na mayar da idanuna.
Na kawar da maganar ta hanya cewa"yaya Alhassan don Allah ka sanar da Anty Zulaihatu ma don ban sanar da ita ba".

Ya riƙe haɓa"ai duk dangi babu inda ban shelanta cewar ƙawata ɗaya tilo za ta yi sauƙa ba. Don haka ki kwantar da hankalinki gayya guda za ki gan ma ranar, yanzu dai ga wannan ki wuce ki hau abin hawa ki wuce gidan na ga magriba tana kawo kai". Ya ƙare zancen yana miƙo mini naira ɗari biyar ɗin da ya zaro daga cikin aljihunsa, na amsa tare da yi masa godiya sai da na tsallaka titi na shiga napep kana na ga sun tafi.
Ina sauƙa a layinmu na hango Amira tsaye da Bashir a ƙofar gida duk suka zubo mini na jiyamunsu, na sa kai zan shige cikin gida tamkar ban gan su ba Amira ta dakatar da ni.

"Amatullah ba ki ga kin yi baƙo ba ne?".

"Amira don Allah na gaji don Allah ki bar ni".
Chapter 48 · 0% Book details