← Book details Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 58

Sashe 11

Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sautin ƙiran sunana da Amira ta yi ya fizgo tunanina da ya yi ƙaura daga gare ni izuwa gangar jikina. Na gyara zamana a ƙoƙarin daidaita nutsuwata.
"Amira yaushe kika zo kika zauna a nan?".

"Lokacin da kika yi nisa cikin kogin tunanin da kika faɗa". Na sauƙe ɓoyayyar ajiyar zuciya ba tare da na tanka mata ba.
"Wai me ye yake damunki ne? Tun da kika shigo na fahimci akwai tsoro da firgici a tattare da ke".

"Ina Ummanki?".

Ta murmusa kafin ta ce"tana cikin ɗaki tana bacci ki kwantar da hankalinki na san abin da kike tsoro. Kafin ta kwanta sai na tabbatar ta manta komai, kuma ina da tabbatar ko musayar alburushi suka yi da Ummanki Ummata ba za ta taɓa hana ni zuwa inda kike ko mu'amala da ke ba, a wajenta laifin wani ba ya shafan wani, don haka ki sanar da ni kawai me yake faruwa?". Tiryan-tiryan na kwashe komai na faɗa mata da ita kaɗai na ji zuciyata ta nutsuwa da ita, ta ƙura mini ido kafin can ta soma maganar da ya ƙara sanya hankali tashin gauron zabuwa.

"Don É—an wannan abun shi ne duk kika bi kika tashi hankalinki? Indai har wannan abun zai É—aga miki hankali to ai ba ki shirya yin talla ba ne Amatullah. Wannan su ne abubuwan da suke faruwa yau da kullum kuma duk wacce ta amsa sunan cikakkiyar Æ´ar talla ya kamata ta san da su ta kuma tanadar wa kanta mafita".

"Kin ga haukan da ta yi kuwa Amira? Ni wallahi ta ba ni tsoro har na yanke shawarar ba zan ƙara zuwa wajen talla ba". Ta hanzarin katse ni"ai kuwa yanzu ma aka fara ɗaura ɗamarar yaƙi da su za ki yi, ki nuna musu duk abin da suke taƙama da shi kin dama su kin shaye. Ki fito a cikakkiyar ƴar tasha ki yi musu hauka da naɗe-naɗanta, hatta shi mai gidan nasun ki yi duk yadda za ki yi ki dawo da hankalinsa gare ki ta yarda za ki gasa musu aya a tafin hannunsu".
Sakeke na yi ina bin ta da kallo har ta kai aya kafin na iya magana.

"Wallahi Allah ma ya sani ni kam ba zan iya ba".

"Za ki iya kuma in har kika gwada ina da yaƙinin ke ce da riba. Ai ko a addini ma an ce ka kare kanka daga wanda zai cutar da kai, kuma ai raba cuta ga macuci ibada ne".
[7/13, 1:19 PM] Maimunatu Iyam: *DAFIN HARSHE*

©️ Maimuna Tijjani Iyam

___________________________________

Page 0️⃣9️⃣

Wuri-wuri na yi ido ina bin ta da kallo tamkar na sama majigi raina cike fal da mamakin zantukanta tsoron da yake cikin zuciyata ya bayyana ƙarara a bisa fuskana.
"Ki nutsu ki nazarce abubuwan da na faɗa miki. Don matuƙar tallan za ki yi da gaske to sai kin shafawa idanunki toka kin rikiɗa kin koma ƴar tasha ko ma na ce ƴar bariki. In ya so in kika dawo gida duk ustazancin da za ki yi sai ki yi".

"Ba na ma fatan na ɗau tsawon lokaci ina wannan tallan Amira. Allah ya sani ba zan iya yin waɗannan abubuwan ba". Dariya ta bushe da shi mai matuƙar sauti sai da ta tsagaita kana ta ce"lokaci ne kawai zai tabbatar da hakan Amatullah amma ina da yaƙinin sanda za ki fara ma ba za ki sani ba".

"Ke Amira a uban waye kike yi wa dariya?".

Muka tsinkayo muryar Ummi kamar daga sama duk mu biyun muka miƙe muna kallon juna. Amira ce ta yi magana don ni kam bakina ya rufu kiruf.
"Da uban wanda ya tsarku nake yi. Inda abun da za ki yi kuma to bismillah".
"Billahillazi ki fita daga idona Amira ba ni da daÉ—i, yanzu zan yi wasan kura da ke hakan ba damuwata ba ne".

"Don girman Allah Ummi ki yi min abin da Allah bai yi min ba yanzu-yanzun nan. Idan kin cika Æ´an halak kar ki bar ni da numfashi". Amira tana rufe bakinta Ummi ta cakumo ta da kokuwa suka kaure da faÉ—a kamar ba za su bar junansu da rai ba.
Duk yadda na so raba su hakan ya gagara sai da Baban Adnan ya fito daga É—aki ya raba su, duk da hakan Ummi ba ta lafa sai sura take kai wa Amira.

"Malam ka matsa ka ba ni waje yau sai na koyawa yarinyar nan hankali. Sai na nuna mata bakin rijiya ba wajen wasan mahako ba ne kuma wallahi na gaba ya yi gaba na baya sai dai labari".

"Ke mahaukaciya ce wai? Ana raba ku har kina wani cewa a bar ki. To ka ga ki kashe ta in kin ga dama". Baban Adnan ya yi maganar cikin tsananin fusatan da ta bayyana har a kalmominsa.
Duk suka yi shuru sun yi zuru-zuru da ido, lokacin har an ca a kan su kowacce mata ta fito daga É—akinta don ba wa idanunta abinci.
"Na lura da ke yarinyar nan Ummi sam ba ki da kunya, har za ki kalla tsabar idona ki ce wai na matsa na ba ki waje ki koya mata hankali?. Ko kin manta wane ne ni? To a matsayina na ɗan sanda ba zai yiyuwa na zuba ido ayi ɓarna akan idona ba".

"Da yake Ummi ce marainiyar wayonka dole ka ce ita ce ba ta da kunya. In shari'ar gaskiya za ka yi ai kamata ya yi ka bar su su fitar da raini a tsakaninsu, ina kuma adalci za ka yi kamata ya yi la fara da tambayar abin da ya haɗa su". Furucin mahaifiyar Ummi kenan yayin da take isowa wajen ta riƙo Ummi kana ta zarce da faɗin"ba fa zai yiyuwa ace duk gidan nan an sawa ɗiyata ido ba. Babu uban da ya isa ya takura mata tun da kuɗi muke biya muna haka muke biya. Daga yau na ba ka damar ki ƙwaci ƴancinki duk wanda ya taka ki kema ki taka shi komai girma, shekaru ko furfurarsa".

"Ai kuwa da kin ba ta lasisin aikata kuskure mafi girma a cikin rayuwata. Don duk ranar da tsautsayi ya sa ta yi wa Baban Adnan tashin kunya ko kallon banza, sai na yi mata raunin da har ta koma ga mahaliccinta rabonsa bai bar jikinta ba".

Maman Adnan ta yi zancen daidai sanda take fitowa daga banÉ—aki. Ummi ta mayar mata da martani daidai da zancenta.
"Billahillazi ko iyayenki ne suka zo gidan nan suka shiga karkata sai na ba su amsa daidai da su, balle kuma wani banza".
"Banza? Ummi mijin nawan kike da ƙira da banza akan idona? To yanzu ni zan koya miki hankalin da ke kika gaza koyawa Amira". Tana rufe bakinta ta tunkaru Ummi kafin ta yi aune tunin ta rotsa mata bokitin ƙarfen da ta fito daga wanka riƙe da shi a hannunta. Kan ka ce kwabo jini ya ce sallama alaikum jini kamar an yanka saniya sai zuba yake yi daga gashin Ummi da ta zube a ƙasa tana burburko tare da rausa ihu.

"Wayyo Allah! Jama'a ku kawo min ɗauki za ta kashe min ɗiya. Shikenan ta tsiyayar mata da ƙwayan idonta".Mahaifiyar Ummi ta yi zancen tana fasa ƙara ta riƙo Ummi suka fice daga cikin gidan ko mayafi babu balle takalmi. Nan kuma wani faɗan ya kaure tsakanin Baban Adnan da matarsa. Ta hau masifa tana ikirarin duk abin da ake mata a cikin gidan shi yake ja mata, saboda shishshiginsa da tsoma baki a cikin abin da babu ruwansa a ciki sai ya yi wanka tsarki ya faɗa, sai da ya gaggaura mata mari kafin ta yi shuru.
Don shi a gare sa dukan mace akan abin da bai taka kara ya karya ba shi ne abu mafi sauƙi a wajensa wajen aikatawa.

Sai da ƙuran ya lafa kafin na sama damar ba wa Amira haƙuri tana buƙarewa akan za ta jira Ummi ta dawo su ɗora daga inda suka tsaya. Da ƙyar da suɗin goshi na shawo kanta ta haƙura. Sai da aka magarib kafin Umma ta ce na tafasa tafiyar murji kamar yanda ta ce haka na yi na ci nawa na kai mata nata ɗaki na zuba na Abba a kula na ajiye masa. Na yi sallan isha'i na kwaso littattafain da nake koyar da yara da su na fito gidan ya haɗe da gurmi. Don mahaifiyar Ummi ta lashi takori akan sai an bi wa ɗiyarta haƙƙin zubar mata da jini da aka yi ba gaira ba dalili. Ta ƙira Mahaifin Ummi da yake legas a waya tana shaida masa abun da ya faru ya fi sau shurin masaƙi.
Tunin na tarar da yaran da nake koyar da su a zaure suna jirana babu ɓata lokaci muka fara karatu har mun yi nisa Abba ya dawo na miƙe tsaye da fara'ata ina yi masa sannu da zuwa sai kafin ya kai ga amsawa wani yaro ya shigo.

"Wai ana sallama da Amatullah a waje".

Daga ni har shi duk muka yi mutuwar tsaye kafin ya tsayar da idanunsa a kaina tamkar yau ce rana ta farko da ya fara ganina. Cikina sai ƙugi yake yi haƙwana suka datse harshena lokacin da Abba yake tambayar yaron da har yanzu yana tsaye bai gusa ba.
"Waye yake sallama da ita?".

"Wani ne ya zo akan babur ya ce a ƙira ta".

"Ke waye ya zo neman ki?". Tambayar da ya watsa mini ta sanya hanjin cikina kaÉ—awa jikina ya soma rawa kamar mazari.
"Ba magana nake yi miki ba? Waye ya zo neman ki a daidai wannan lokacin?". Ya kuma maimaitawa a karo na biyu cikin tsantsan buƙatuwar sn jin amsar tambayarsa.
"Ka yi haƙuri Abba ni ake nema ba Amatullah ba. Wani ne muka haɗu da shi kuma ya ce min zai zo gidanmu, yanzu ma muka gama waya da shi, ni ce na ce masa sunana Amatullah saboda ya takura min a lokacin".
Chapter 11 · 0% Book details