← Book details Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 58

Sashe 37

Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka na ci gaba da juyi na kasa runtsawa har aka yi ƙiran sallan asubahi, da ƙyar na tashi saboda nauyin da gabaɗaya ilahirin jikina ya yi mini na fito na yi alwala na koma ciki na gabatar da zauna. Sosai kaina yake yi mini ciwo tamkar zai faɗo ƙasa ko zai rabu zuwa gida biyu, runtse idanuna na yi ina jin yadda ɗakin yake juya mini ina jin rufin ɗakin tamkar zai rikito a kaina.
Na kifa kaina akan gwiwa ina karato farkon suratul Maryam ban gushe ina yi ba har sai na ji sauƙin lamarin na zame ns kwanta akan sallayan babu jimawa wani bacci mai nauyi ya yi awon gaba da ni.

Tamkar a cikin mafarki na ji ana ƙiran sunana na buɗe idanuna da ƙyar ina jin ciwon kan ma tamkar ƙaruwa ya yi maimakon raguwa. Na tashi na zaune dafe da goshina da jijiyon kaina suka fito suka yi ruɗu-ruɗu ina kallon Umma da take tsaye a kaina dishi-dishi. Na yi ƙarfin halin jefa mata gaisuwa sai dai ko gizau ba ta yi balle ta amsa illa kallo na da ta ci gaba da yi tamkar yau ta soma tozali da ni.
"Ba ki da lafiya ne?".

"Kaina ne yake yi mini ciwo sosai". Na amsa mata da shi cikin dauriya da halin da nake ciki. Ta yi É—an jim kafin ta furta"ki tashi ki je ki É—eba kunnu ga shi can na dama, sai ki dawo ki kwanta. Na san yadda zan yi da kunun tun da na ri ga da na dama shi".
Na yi zumbur na ce"A'a Umma ai zan iya zuwa tallan ma". Kallon da ta katse ni da shi ya sani hanzarin haÉ—iye ragowar zancen ba tare da na gama amayo da shi waje ba.
"Ki fita daga idona na rufe Amatullah, in ba haka ba kuwa yanzun nan zan yi wasan kura dake a cikin gidan nan ƴar iskan yarinya mai halin dangin ubanta". Jikina ya yi sanyi ƙalau na sadda kaina ƙasa ina jin gabaɗaya jikina ya ɗauki zafi tamkar naman da yake wuta ake sulala shi.

"Ki tashi ki je ki yi abin da na saka ki".

Ban ce komai ba na tashi na fita na je na wanke bakina kafin na ɗeba kunna na zauna a ƙofar ɗakin ina sha a hankali, da ƙyar yake wucewa ta maƙoshina tamkar wacce take haɗiyar ƙarangiya.
"Amatutun Mama". Na ji yo muryan Amira ta tsakiyar kaina yayin da take jan kujera ta zauna kusa da ni. Ta bi ni da kallo"ya kamar ba kya jin daÉ—i? Na ga duk yanayinki ya sauya".
Na lumshe idanuna da babu komai a cikin su face bacci da gajiya kafin na buɗe su tar akanta ina faɗin"wallahi kar ki so ki ji yadda kaina yake yi mini wani masifaffen ciwo. Ko juya kaina ban so na yi balle wani motsi mai ƙarfi".
Ta jinjina kanta cikin kulawa kafin ta furta"Ayya! Sannu Allah ya ba ki sauƙi".

"Amin na gode". Na amsa da shi a taƙaice ina kurɓan kunun da ko kaɗan ba na jin danɗanonsa a bisa harshena.
"Amma yau kam ba za ki sama zuwa tasha ba ko? Don na ga jikin nakin ba ƙwari". Na caraf na mata amsa har ina neman ƙwarewa tsabar sauri.
"Me zai hana ni zuwa kuwa Amira?. Yanzu ma tashi zan yi na je na shirya na fito mu tafi". Ta kafe da wani kallon da ya fi kama da na al'ajabi don ya zarce a misalta shi da kallon mamaki.

"Ke Amatullah kin san komai sai da lafiya ake yin sa. Mene ne don yau kawai kin zauna a gida kin huta? In kin sama lafiya ai za ki je".

Na katse mata hanzari"ni fa babu abin da zai hana ni zuwa, bari ki ga tabbaci". Ina dasa aya na tashi na É—eba ruwa na shiga banÉ—aki na yi wanka na fito duk tana zaune a wajen na wuce ta na shige É—aki na sako kaya, na fito falo inda na wuce Umma tana zaune.

"Umma na fito zan tafi".

"Zuwa ina kenan?".

Na saci kallonta kafin na ce"wajen talla".

"Har kin ji sauƙi kenan haka da wuri?". Na rusunar da ƙwayoyin idanuna ƙasa kafin na ce"ban ji sauƙi sosai ba amma duk da haka dai zan iya zuwa". Ta jinjina kanta ba ta amsa mini ba har sai da na cire rai da samun amsa daga gare ta kafin ta ce da ni"Allah ya kiyaye".

"Amin sai na dawo".

Na amsa da shi annuri yana wanzuwa a bisa fuskata tsam na tashi na fita na faÉ—a É—akin su Amira na iske ta har ta shirya tana É—aura É—ankwali. Daga ni har ita babu wanda ya yi wa wani magana na jira ta ta gama muka fito tare tunin almajiran da suke É—auka mana kaya suka yi gaba muka bi su a baya.

"Daga jiya zuwa yau na gaza gane kanki Amatullah".

Na ware idanuna akanta"me ye kuma na yi?"
Ta ja dogon numfashi ta fesar kafin ta ce"ke ma kanki kin san kin sauya ba kya buƙatar sai an sanar da ke hakan". Na matse yatsun hannuna waje guda na matse su har sai da suka ba da wani ɗan sauti kafin na sama zarafin cewa.

"Amira ba za ki gane ba wallahi ni ma kaina ban san me ye yake damuna ba. Haka kawai nake ji na a matuƙar takure a cikin gidan indai ba fita na yi ba na taɓa samun kwanciya hankali balle nutsuwar zuciya".
"Ina tsoron abin da hakan zai iya jawo miki. Don haka ina mai ba ki shawara tun wuri ki nema wa kanki mafitar da ta dace dake da kuma tsarin rayuwarki".

"Shikenan kuma ni ba ni da Æ´ancin jin daÉ—i ko kasancewa da waÉ—anda za su samar mini da farin ciki a cikin rayuwarta?".

"Amatullah kenan! Lokaci ne kaɗai zai ba ki amsar waɗannan tambayoyin nakin". Ban ce da ita komai daidai lokacin da muka karyo kwanar da za ta sada mu tashar har muka shiga muka zauna a wajen zamanmu ban daina jin ciwon kan ba, sai dai na gwammace da zauna a nan ɗin da na koma gida. Aƙalla mu shafa biye da mintuna arba'in amma ko wulgawar Bashir ban ga ni ba hakan ya sani furta abin da yake ƙunshe cikin raina ga Amira, da hakan ya ƙara jefa ta cikin mamaki.

"Amira kin lura kuwa yau ko wulgawar Bashir babu a cikin tashar nan?".

"To me ye abin mamaki a cikin hakan? Ke ma kanki kin sa direba ne to wataƙila an yi masa lodi ya tafi bai dawo ba". Na jinjina kaina tare da yi wa bakina sakata ba wai don na gamsu da abin da ta ce ba. Haka muka ci gaba da zama duk da azababben ciwon kan da yake ta'azzara na bai gani waige-waige ba ko zan yi tozali da Bashir. Lura da yanayin da na shiga ya sanya Amira soma furucin da ya yi silar jawo hankalina.
"Amatullah ba na buƙatar sai kin faɗa min da kalmomin baki yanayinki kawai ya nuna min cewar kin faɗa cikin soyayyar Bashir, sai dai kin yi zurfi da yawa. Tun yanzu har kin fara irin wannan abu to ina kuma idan soyayyar ta yi ƙarfi a cikin zuciyarki. Ina gudun abin da zai je ya dawo".

Ban san dalili sai kawai na ji na fashe da kuka mai matuƙar ƙarfi na kifa kaina da gwiwana ina rure shi da dukkan ƙarfin iyawana.
"Na shiga uku! Kuka kuma Amatullah? Me ya faru me ye aka yi miki?".

"Amira ni ma kaina ban san me ye ya faru, kuma zan fi kowa son jin abin da ya faru ɗin. Wallahi ni ma kaina ina ji a jikina cewar na sauya sai dai babu yadda na iya. Zuciyata tana gaya mini cewar ba ni da wani zaɓin da ya wuce na amshi tayin soyayyar Bashir, ko don farin cikina tun da kin ga Umma ba samun lokacinsa take yi ba balle har ta ji damuwar da yake cikin raina".

Ina iya jiyo sautin ajiyar zuciyar da ta sauƙe kafin cikin sanyin murya ta soma cewa"na fahimce ki amma fa dole sai kin iya sarrafa kanki, kar ki bari zuciyarki ta dinga sarrafa maimakon ƙwaƙwalwarki. Ko da ya ke zan yi miki uzuri guda na cewar wannan ne karo na farko da kika fara soyayya". Ban iya cewa da ita komai illa kukan da na ci gaba da shi jikina har yana rawa tsabar kukan ya gama galaitar da ni ban gushe ba na ji ta furta kalmar da ya sani saurin ɗago kaina babu shiri.

"To ai ga can Bashir É—in ma yana zuwa".

Na kafe shi da idanuna da suke tsiyayar da ƙwalla har ya iso wajen.
"Subhanallahi!Kuka kuma, me yake faruwa ranki ya daɗe?". Ya watsa mini tambayoyin a rikici yayin da yake ƙoƙarin zama akan bencin da yake kusa da ni.

"Yauwa! Na gode wa Allah da ya kawo ka a wannan lokacin. Tun ɗazu nake yi da ita amma ta ƙi jin lallashi balle lallami, ka ta ga ka kai m sai ka gwada taka sa'ar bari na je na dawo".

"Me ya same ta ne? Za ki tafi ba ki yi min bayani ba".
Ta yarfa hannunta alamar ita ma ba ta sani ba, ta É—auki masar Nasiru ta tafi kai kai masa.
"Don ki yi haƙuri ki tsagaita da wannan kukan da kike yi billahillazi ba ki ji yadda nake ji wani abu yana tasowa daga ƙasan ƙirjina yana sukan raina ba. Ki taimaka ki sanar da ni abin da yake damunki".
Na kai hannu na share ƙwallar da suka ɓata mini fuska kafin na furta"ba komai". Ya jijjiga kansa alamar bai gamsu ba.

"Kar ki ɓoye duk abin da yake cikin ranki, ni kuma na tabbatar miki da cewa indai bai fi ƙarfina zan magance miki shi". Na kafe da idanuna ko ƙiftawa ba na yi"Bashir ka tabbata inna sanar da kai za ka iya magance mini ita?".
Chapter 37 · 0% Book details