Sashe 10
Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Sai kuma aka ce miki da ke nake yi Hafsatu? Lissafi ne ya ɓarce min kin ga kuwa dole na yi abin da ya ci uwar tsaki ma. Babu uban da ya isa ya hana ni don daidai nake da uban kowa a cikin gidan nan yadda ake biyan kuɗin haya haka ni ma nake biya babu raran ko ficika".
Shewa Umma ta saka har da tafa hannu kafin ta furta"Allah na gode maka. Daman an ce makashinka yana tare da kai kuma hassada dai aka ce mungun ciwo ce a zuciyar mai ƙula shi. Mu zuba ni da ke Sahura tsakanin ni da ke ɗan halak ka fasa".
"Tun da haka kika ce to mu zuba ɗin wallahi sai na tabbatar da in kika zuba ba ki kwashe ba Hafsatu". Sahura ta yi zancen tana miƙe wa tsaye Amira ta riƙe ta tana ba ta haƙuri suka shiga ɗaki, nan Umma ma ta ƙarishi banbamin ta ta gama.
Jikina a saɓule na tashi na shiga ciki a falo na tarar da Abba da Anty Sawwama duk su biyun sun yi shuru alamar duk abin da yake wakana a filin tsakar gidan suna saurara, na durƙusa na gaishe su Anty Sawwama ce ta amsa Abba kuma maimako ya amsa sai ya jefo mini tambaya.
"Yau ma kin je tallan ne?".
Kafin na amsa masa Anty Sawwama ta tari numfashina"kunun ma yana tafiya kenan? Daga fitarki har kin dawo ko awa biyu masu kyau ba ki yi ba". Ƙirjina ya harba ɓat! Kamar yadda alburushi yake fita daga cikin bindiga, gabaɗaya na riɗime na daburce na soma kame-kame har izuwa lokacin da na ƙara tsinkayo amon Abba a karo na biyu.
"Ina kika kai tallan ya yi saurin ƙarewa haka?".
"Bakin titi ne Abba, masu tafiya makaranta da gona ne duk suka saye". Shurun da ya yi ya tabbatar mini da hashashen zuciyata na cewar bai yarda da abin da na faɗa ba. Zancen da Anty Sawwama ta yi ya ƙara jefa ni cikin kogin firgici har na kasa magana da motsi na tsawon wasu mintuna.
"Ya kamar shatin Æ´atsu ne a fuskarki Amatullah? Ko dai dambatuwa kuka yi a wajen tallan?".
"Ba-ba-ba- ba abin da ya faru, shatin kwanciya ne kawai. Don jiya ban kwanta ana matashi ba".
Ta gyara zamanta tana fuskantar Abba da kyau kafin ta sa furzar da takaicin da yake kwance a ƙasan ranta"Allah ya jiƙan iyayenmu ya sabunta rahama a gare su, tabbas bango Ya faɗi don na tabbatar da ɗaya daga cikin iyayenmu suna raye ba za su taɓa zura ido jikarsu ta yi talla ba komai talauci da matsin rayuwar da muke ciki. Don an shaide su da wadatar zuciya da kuma kare mutunci da martaɓan ƴaƴansu mussamman ɗiyoyinsu mata, har muka girma iyayenmu mata ba za fita ko'ina iyayenmu da yayun maza suke fita domin samar mana da abin da za mu gudanar da rayuwa da shi. Amma yanzu kai Manniru ka ga dacewar wannan tallan da Amatullah take yi? Zankaɗeɗiyar budurwa da ita a ɗaura mata talla tana yawon layi-layi, kororo-kororo, lungu-lungu da sunan neman kuɗi. Wanda ina da tabbacin ba ku rasa ci da sha ba balle suturar da za ku rufe tsiraicinku, ya kamata ka farka daga baccin da kake yi kai ne na miji a gidanka kuma kai kake da alhakin gyara shi da daidaita shi. Ka sani fa akwai ranar Allah zai tambaye ka amanar da ya ba ka a ranar da babu lauyan da zai kare ka".
Numfashi mai zafi Abba ya furzar daga bakinsa sai da ya musguta kafin ya ce"wallahi ni ma har cikin zuciyata ba na son wannan tallan da Amatullah take yi......".
"Kar ka wani rantse min Manniru. Kai ne fa namiji a cikin gidanka kuma da Amatullah da uwarta duk a ƙarƙashin ikonka suke, idan suka lalace sai Allah ya tambaye ka don haka zaɓi ya rage gare ka".
"Ba shakka Maman Umar dole ka sa shi a gaba kina yi masa huÉ—ubar banza. Ke ki fara gyara naki gidan auren mana kafin ki wa gidan wasu katsalandan".
"Ke Hafsatu ki iya bakinki idan kina cin ƙasa ki kiyayi ta shuri. Zan jure komai akaina amma ba zan juri cin mutumci ga ƴan uwana ba. Maman Umar kamar uwa ce a gare ni zan iya ƙarya duk hannun da ya nuna mata ƴatsa".
"Dole na furzar da abin da yake cikin raina Manniru, ko yaushe ƴan uwanka gani suke yi kana ɗaukar duk ɗawainiyyarmu bacin ba haka ba ne. Talla dole na ɗaurawa ƴata don na rufawa kaina asiri ina da yaƙinin ko aurenta ne ya tashi babu wanda zai tsinana mana komai daga kai har dangin nakan". A matuƙar fusace Abba ya soma magana kamar zai yi aron baki.
"Ya ishe ki haka kar ki wuce gona da iri. Ki ɓace min daga gani kafin na yi miki abin da zuƙata da yawa za su raunana". Tanadin kallo ta ƙare masa tas kafin ta buga tsaki ta wuce cikin ɗakin bayan ta ba ni umarnin tashi daga wajen a cewarta a daga wajen su nake koyan baƙin hali da gardama. Muna shiga ɗaki ta tsare da ido tamkar mai son gano wani gaskiya a tattare da ni.
"Kar ki ba ri kalamansu su sama matsuguni a cikin kanki balle har zuciyarki ta amshe su. Ke ganau ce ba jiyau ba cikinsu gabaɗaya waye yake taimaka mana da ko da tsinke ne? Ko yaushe gani suke yi kamar duk duniya babu namijin da yake ƙoƙarin sauƙe haƙƙoƙin iyalinsa da wadata su da komai na rayuwa kamar ɗan uwansu don zuzurutun son kai. Dole na yi sana'a haka zalika dole ki je min talla don mu rufawa kanmu asiri".
Tun da ta fara zancen kaina yake ƙasa har ta gama kana a hankali na furta"in sha Allah Umma zan ci gaba da zuwa matuƙar ba Abba ba ne da kansa ya dakatar da ni". Ba amsa mini ba illa ɗauke kanta da ta yi gefe guda, na fito na yi alwala na koma na yi sallan zuhur a ƙuraran lokaci babu jimawa aka yi ƙiran asr na yi su gabaɗaya. Na janyo jiki na zauna a ƙasa kusa da ƙafafunta.
"Umma kin ga ikon Allah ko? Ga shi yau na sayar da duk kunun ba tare da ko sisi ya yi ciwon kai ba. Daman na gaya miki idan Allah ya so kuma ya datar da mu ko ana so ko akasin haka zan sayar da kunun, Umma shi Allah mai nuna iko da isarsa ne akan komai kamar yadda ya nuna mana a yau ko da laƙanin nan ko babu idan ya nufa wallahi ko a cikin gidan nan ne sai kin ga an saye kunun, ina roƙonki da mu haƙura da wannan abun ki watsar da duk zantukan da Malamin bogin nan ya zuba miki a cikin kanki, ni kuma na yi miki alƙawarin zan yi iya ƙoƙarina na ganin ban dawo da kwantan kunun ba".
Tun da na soma maganar take bi na da wani irin kallo da na gaza gane ma'ana da maƙasudin yin sa. Ta taɓe baki kafin ta ce"ki daina ɓata bakinki don babu abin da za ki ce min na fasa aiwatar da abin da na yi niyya musamman yanzu da hassadan Sahura ya fito ƙiri-ƙiri akan mu. Dole ne na tashi na tsaya akan ƙafafuna don na san ba za ta taɓa bari na haka banzan ba".
"Don Allah ki yi haƙuri ki tura mata mungun nufinta".
"Ke Amatullah". Ta doka mini tsawan da ya tursasa mini yi wa bakina linzami nan take.
"Kar ki ƙara yi min wannan maganar don na riga da na gama yanke shawara". Haƙuri na ba ta na ja bakina na gimtse har izuwa lokacin Anty Sawwama ta soma shirin tafiya a sa'ilin Abba ya tafi masallaci bai dawo ba.
Fuskata É—auke da annuri nake faÉ—in"Anty har tafiya za ki yi ga shi ko abinci ba ki ci ba". Kafin ta yi magana Umma ta yi caraf ta amshe zancen kamar jira take yi na ce kule ta ce da ni cas.
"Ai dole ta tsaya jiran abinci tun da shi ɗan uwan natan ya kawo ya ajiye. A kan idonta ya dawo ai haka ya shigo siƙau hannu na dukan cinya, don haka ba abin da za mu ɗaura balle har ta sa tsammanin ci".
Sosai kalaman suka daki zuciya na ji wani ɗaci a bisa maƙoƙarona yana tasowa har izuwa cikin bakina. Satan kallon Anty Sawwama na yi na ga gabaɗaya jikinta ya yi sanyi da alama ita ma zancen ya baƙanta mata ruhi sai dai ba ta bayyana shi a fuskarta ba.
"Ba komai Uwata zan tafi, daman na gama abin da ya kawo ni kuma mun yi sallama da shi kafin ya fita masallaci. Kin ga kuwa ai babu abin da ya rage". Ta yi zancen yayin da take miƙewa tsaye kafin na ce wani abu har ta fice daga falon na yi wuf na rufa mata baya muka fito daga gidan tare, har ƙarshen layinmu na yi mata rakiya kasancewar ranar babu islamiyya kana muka yi sallama a dawo gida.
Ganin har lokacin Umma ba ta ce da ni na haɗa wuta ko kuma ga abin da za a girka ba, ya sani shimfiɗa tabarma a ƙofar ɗakinmu na ɗauka jakar islamiyyata na soma tilawa. Kamar faɗuwar aradu haka abin da ya faru da ni ɗazu a wajen talla ya faɗu mini a rai na ja dogon numfashi na fesar ina lumshe idanuna.
Na sha jin ana cewa ƴan talla ba su da kunya kuma ba sa tsoron ta mutuwa balle ta yi rayu wanda wasu suke amfani da wannan dalilan suke yi wa duk wata mai talla kuɗin goro. Ban taɓa yarda kalaman da ake faɗa akan su ba sai yau da na ga zahiri ya kuma faru a kaina. Tabbas akwai babbar matsala matuƙar aka ci gaba da tafiya, zuciyata ta harba yayin da na tuno irin musayan kalaman da Zaina da Mai aska suka yi da irin ikirarin da alwashin da ta yi a kaina. Gabaɗaya sai na yi gwiwoyina sun sake zuciyata ta karaya yayin da raunina ya bayyana.
"Amatullah".