Sashe 30
Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta tafa hannu gami da tsarin shewa kafin ta ce"ai kuwa magana tana nan daram har sai zuwa lokacin da na rama irin É—iban albarkan da kika yi min a cikin gidan". Na buga tsaki na juya zan tafi ta koma cakumo ni daga lokacin da Abbanmu da Baba Habu suka shigo cikin gidan suka buga salati kafin Abba ya nema jin ba'asin abin da ya afku, na kwashe komai na sanar da shi.
"Yanzu ke Ummi tun da an gama magana me ye amfanin tayar da shi yanzu?". Tambayar da Baba Habu ya jefa mata kenan kafin ta amsa Ummanta ta yi caraf ta amshe zancen.
"Ko sama da ƙasa za ta haɗe sau Ummi ta ɗauki fansar abin da Amatullah ta yi mata".
Kansa kawai Abba ya yi kafin ya furta"Uwata wuce ɗaki, ga salla ma yanzu ake ƙira".
"To Abba".
Na amsa da shi a taƙaice ina jin wani takaicin a cikin raina da ta tokare mini ƙirjina. Ban san sa'ilin da hawaye ya zubo daga idona ba yayin da nake shigewa ɗaki kai tsaye na wuce na je na sauya kayana, na fito na ɗau alwala na zo na yi salla. Sai a lokacin na lura da cewa Umma ba ta cikin gidan don haka na wuce wajen Amira ta ɗauke fuskana na yi mur don ba na so ma ta tare ni da wani zancen, tare muka fara aikin abincin da ita fried rice muka yi da soyayyar kazar da muka yi mata miya ta sha kayan lambu. Haka muka yi muka gama duk jikina babu ƙwari kuma na ƙi ba wa Amira fuskar da za ta yi mini wata tamnayar.
Ina zaune a É—akinsu ina latsa wayarta ta shigo ta dire plate É—in abincin da ta shigo da shi a gabana, tare da fizge wayar tana faÉ—in"to Madam Bismillah mu ci abinci".
Na sauƙe gwauron ajiyar zuciya kafin na sama zarafin cewa"wallahi kin ga ni kam ko yunwar ma ba na ji". Ta watsa mini harara"saboda me ye?".
Kafin na ba ta amsa ta É—aura da faÉ—in"kin ga Amatullah in zan ba ki shawara ki É—auka to tun wuri ki cire damuwar komai daga cikin ranki. Kar ki je ki ja wa kanki wani matsalar na daban akan wasu mutane can daban, yanzu dai ki daure ki ci abincin sai mu yi magana daga baya".
Ban ce da ita uffan ba na saka hannu muka soma cin abincin har muka gama ban yi magana ba, duk da yadda take ta ja na da ita, da uhm ko umm kawai nake amsa mata wani sa'ilin kuma na saki taƙaitaccen murmushin da iyakar sa leɓena.
Haka muka gama cin abincin na baro ta akan za ta shiga wanka don sun yi waya da Mansur ya ce ya ma shigo garin, wajenta kawai zai nufa. Sakakken ajiyar zuciya na sauƙe lokacin da na shigo ɗakinmu na iske har yanzu Umma ba ta dawo ba wanda ban san inda ta je ba, alwala na fito na yi na koma na yi salla ko da na iddar na gaza tashi daga inda na yi sallan na zaune na zagba tagumi da hannu bibbiyu tamkar wacce aka aikowa da saƙon mutuwar uwa da ubanta.
"Uwata lafiya kuwa ina ta sallama ki zauna kin yi tagumi, ko amsawa ba ki yi ba?".
Tamkar a cikin mafarki na tsinkayo amon Abba a tsakiyar kaina, da hakan ya tilasta mini cira kaina ina dubansa na miƙe na amsa baƙar ledar da ya shigo da ita ina yi masa sannu da zuwa.
Na kawo masa ruwa ya sha kana na ce"ba ri na ɗaura maka girki kafin Umman ta dawo". Ya yi saurin faɗin"ba na jin yunwa sai dai ki dafa iya cikinki, Ummanki kuma na san ko ta dawo ba lalle ba ne ta ci wani abu". Tsimi-tsimi na koma na zauna kusa da ƙafafunsa tare da sadda kaina ƙasa, shuru ya ratsa wajen na tsawon wasu mintuna kafin Abba ya kawar da shi ta hanyar faɗin"walimar sauƙanku tana ta gabatowa ko?".
"E akwai Æ´an kwanaki ma yanzu kam suka rage".
Ya yi É—an jim kafin ya ce"kuma za ku yi wasu hidimomi ko?".
"Hijabi ne kawai sai ankon da za mu yi. Kuma Umma ta ce za ta yi mini hijabin".
"In Sha Allah kafin lokacin ma zan yi iya ƙoƙarin na ga na yi miki ankon, su makarantar takun me ye suke shirya muku na ga ana gayyato mutanen".
Sai da na haɗiye wani miyau mai kauri daga bushashshen maƙoshina kafin na sama lasisin faɗin"Sheikh Dawood za a gayyato".
Tun kafin na gama maganar ya tari numfashina"kai! Ai kuwa ya zama dole na halacci wannan taron nakun ko don na yi ido huɗu da Sheikh Dawood. Amma gaskiya sun yi ƙoƙari da suka gayyato shi don a malaman yanzu da wuya a sama kamarsa, mai ƙoƙarin hidimtawa addini da ziyartar duk wani wajen taron addini".
Jikina gabaɗaya ya yi sanyi ƙalau tamkar kazar da aka jefa da ruwan gishiri, na yi shuru kamar wacce ruwa ya cinye ta. Ban ƙara cewa komai don na gaza samun abin da harshena zai sarrafa.
Sallamar Amira shi ya dawo da ni cikin hayyacina daga duniyar tunanin da na yi nisan ciwo a cikinsa, na amsa mata kana ta shigo ta durƙusa har ƙasa ta gaida Abba tare da yi masa bayanin zan raka ta ƙofar gida ta amsa saƙo.
"To kar dai ku daÉ—e kuma ku lura, ni ba na son wannan hirar daren nakun wallahi".
Amira ta fashe dariya har da rufe fuskarta saboda kunya kafin ta ce"Abba saƙo ne kawai za mu karɓa".
Ya murmusa tare da cewa"to na ji, Allah ya kiyaye sai kun dawo".
"Amin mun gode". Muka haɗe baki wajen amsawa kana muka tashi muka fita a zaure muka dakata ina ƙarewa Amira da ta sha doguwar rigar shuɗin kamfala an mata wani masifaffen ɗinkin da ya fito da duk wani suran jikinta. Ta kashe ɗaurin ture ka ga tsiya yayin da ta watsa sumarta zuwa bayan wuyanta.
"Ma sha Allah! Wallahi kin yi kyau kamar a sace a gudu. Anya kuwa in Mansur ya ganki zai iya motsawa".
Cike da matuƙar jin daɗi ta yi fari da idanunta gami da buga tsalle.
"Na gode ta kusa da ran". Ta amsa da shi tana jan hannuna muka fita wajensa, yana tsaye a inda ya saba tsayuwa inda ya zo a jikin motarsa da duk da duhun dare hakan bai hana sheƙin da take yi ɗaukar ido ba. Da sallama muka isa wajen bai amsa ba illa kafe ta da idanu da ya yi wanda ita ma ɗin shi take kallo.
"Barka da fitowa tauraruwata hasken idaniyata, filitar dake haskaka birnin zuciyata da kewaye. Na yi kewarki yadda ba ki ba zai iya misaltawa ba, wasu lokutan har ji nake yi kamar na yi tsuntsuwa na zo don kawai na gan ki sai dai hakan ba mai yiyuwa ba ne".
"Ni ma nan kullum da kewarka nake kwana kuma nake tashi a cikin raina Masoyi".
Na naɗe hannayena tsam a ƙirjina ina kallon su"to masoya tun da ba a gani ba babu amfanin tsayiwata a wajen. Don na ga alama iya junanku kawai kuke gani".
Murmushi Mansur ya yi yana haɗe hannayensa waje guda alamar ban haƙuri.
"Afuwan ranki ya daɗe, mun yi kewar juna ne irin sosai ɗin yadda baki ba zai iya furta wa ba". Na taɓe baki ina cewa"to har shekara dubu nawa kuka yi ba ku ga juna ba?".
"Ai duk kwana guda jin sa muke yi tamkar shekara muka yi ba mu ga juna ba". Amira ta yi furucin fuskarta tamkar gonar auduga.
"To sannu masoya yanzu kam ai ga ki ga shi. In kun ga dama ma ku cinye juna ƙarshen soyayya". Dukkan su suka tuntsire da dariya kamar waɗanda aka ba su wankan gardi, sai a lokacin muka sama damar gaisawa da Mansur na yi masa sannu da dawowa mun ɗan taɓa hira na wani lokaci kafin na ce zan shiga ciki, Amira ta yi tsalle ta dige akan babu inda za ni. Dole na tsaya ba don raina yana so ba jifa-jifa nake soma baki a cikin hirar tasun kafin can na hango Umma ta doso gida. Da alama ba ta gan mu ba don kai tsaye ta wuce cikin gidan ba tare da waiwaye ba.
"Amira kin ga Umma ta dawo bari na wuce gida".
Ta galla mini harara"babu inda za ki je yadda muka fito tare to haka za mu koma. Sai ka ce cizon naman jikinki ake yi a nan ɗin". Ban ce komai ba illa murmusawan da na yi, ba su ja hirar da yawa ba don hatta shi kansa Mansur ɗin ya fahimci cewar na ƙosa na bar wajen, ya zagaya ya buɗe bayan motarsa ya fito da wasu manyan ledodi biyu ya zo ya dire su a gabanmu.
"To Babe ga tsarabarki".
"Ranka ya daÉ—e ba na so ka na wahalar min da ajihunka". Amira ta yi zancen cikin karya harshe da sausauta amonta.
"Rufe idonki ki miƙo min hannunki". Mansur ya furta a dake don kar ma ta kawo masa wargi. Kamar yadda ya buƙata hakan ta yi, ni dai ina tsaye ina kallon ikon Allah buwayi gagara misali. Ya ciro wani kyakykyawan agogo daga ajihunsa ya ɗaura mata a hannunta kana ya ce ta buɗe idonta. Ta cika da farin ciki da murna yayin da ta ya tozali da agogon ta dinga jeranta masa godiya wani na bin wani ni ma ina taya ta. Haka suka yi sallama ya tafi mu kuma muka shigo gida kai tsaye na wuce dakinmu don haka kawai na ji ƙirjina yana bugawa fiye da kima a kimiyance.
Babu kowa a falon don haka na wuce uwar ɗaka na yi turus bisa tozali da mummunan ganin da na yi, take ƙafafuna suka soma rawa suffa ta soma keto mini daga dukkan mafitan gashin dake jikina.
[9/30, 7:07 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE*
Â©ï¸ Maimuna Tijjani Iyam
_____________________________________
Page 2ï¸âƒ£4ï¸âƒ£