Sashe 46
Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Take zuffa ya soma tsatstsafo mini daga dukkan mafitan gashin da yake jikina, sai da na aro jarumta na yafawa kaina kafin na sama damar sarrafa abin harshena da ya cika mini bakina.
"Umma zame wa na yi a banɗaki na faɗi. Shi ne ƙuguna ya bugu". Ta ɗago ido tana ƙare mini tanadin kallo har sai da na tsargu na rusunar da kaina ƙasa.
"A ina kika zame É—in? Wannan kayan kuma fa na jikinki?".
"A gidan Hajiya Tasalla, kayan kuma ita ta ba ni na sauya don nawa sun jiƙe na shanya su". Sai da ta salwantar da wasu mintuna kafin can ta ce"Allah ya sauwaƙe ki je ki kwanta". Ban ce da ita komai ba na wuce cikin ɗakin ina shiga na fire hijabin kaina na yi jifa da shi kamar jaka haka na zube akan gado ina wani irin matsanancin kuka mai matuƙar cin rai da haifar da zogi da ƙaiƙayi a cikin zuciya. Na cire kallabin kaina na tusa a cikin bakina a ƙoƙarin hana sautin kukan nawan fita, har sai da na ji numfashina yana ƙoƙarin sarƙafewa kana na tashi na zauna na zabga tagumi ina tunanin makomar rayuwata, tabbas ɗan Adam baya taɓa gujewa ƙaddararsa amma na yanke hukuncin ba zan ƙara zuwa gidan Tasalla da sunan kwana ba, na gwammace na kwana ko da a soron gidanmu ne don sai na fi samun kwanciyar hankali da nutsuwar ruhi. Take na ji jikina ya ɗauki zafi zazzaɓi ruf-ruf ya rufe ni na koma na kwanta ina ta rawan ɗari.
A cikin wannan yanayin Umma ta shigo ta iske ni, ta kai hannunta saman goshina ta ji zafi gau hakan ya sa ta faÉ—in"Ke Amatullah lafiyarki kuwa? Mene ne yake damunki haka?".
"Kaina ne yake ciwo".
"To ki tashi ki sha magani mana sai ki kwanta da ciwo haka ba tare da kin sha magani ba". Na tashi ta fito falo inda ake ajiye maganin na duba na ɓalle paracetamol ƙwara biyu na fito waje na ɗebo ruwa na afa ina jefa ƙafana a cikin falon na ji jiri yana ɗeba tare da ƙoƙarin nanayi da ƙasa. Na yi hanzarin dafe kaina da yake juyawa tamkar sitiyarin mota a hannun ɗan koyo. Ban yi aune ba na ji ni shirib na zube a ƙasa na yi warwas, ina jiyo amon Umma ta zo kaina tana tambaya ta ko lafiya amma na gaza samun bakin da zan ba ta amsa. Daidai lokacin Amira ta shigo ɗakin suka haɗu ita da Umma suka ɗago ni suka kwantar da ni a bisa kujera suna yi mini fiffita don fankan da yake aiki a cikin falon bai hana ni fitar da gumi b ya yi mini lajab kamar wacce aka watsawa ruwa.
"Ki tashi ki daure ki ci wani abu sai a kai ki chemist ɗin Halilu ya yi miki allura. Don zazzaɓin bana sai an tare shi tun da wuri in ba haka ba sai ya tsotse mutum tsaf". Furucin Umma kenan da ya sanya hawaye zubowa daga idanuna ina jin a raina ina abin da take tunani ne watau zazzaɓi ba wannan abun ba. Amira ta taimaka mini na tashi na zauna Umma ta dama mini koko da ƙosai kunun kawai na iya zuƙa na koma na kwanta na yi luf, Umma ta ce Amira ta raka ni chemist ɗin Halilu ya yi mini allura. Haka muka fito tare da ita tana riƙe da hannuna muka wuce Ummi da Auwal zaune a zaure suna hira, suka zaro mana idanu lamarin da ya fusata Amira har ta furzar da takaicin da yake cikinta.
"Wannan kallon fa bayin Allah? To sai dai ku ci kanku wallahi mu kam nan gani nan bari É—umamen mayya".
"To ma me ye za mu gani a jikinku? Har ina abin yake wai maye ya ci jariri?". Ummi ta mayar mata da martani a zafafe. Amira ta yunƙura za ta tanka mata ta kwaɓe ta, sai da muka doso chemist ɗin Halilu na ja na tsaya, Amira ta juyo tana kallo na alamar lafiya.
"Anya kuwa ba a gane abin da ya faru ba? Ni fa duk a tsorace nake".
Ta jijjiga mini kanta"babu wanda zai gane matuƙar ba ke kika faɗa ba". Tana dire zancen ta ja hannuna muka shiga ciki chemist ɗin Amira ce ta yi masa bayanin wai zazzaɓi ne yake damuna da kuma ciwon kai, ya rubuta mini magunguna sannan ya yi mini allura ya ce da dare na dawo a yi mini. Har muka iso gida ban ce da Amira komai ba, duk da kuwa yadda ta dage tana lallashina da roƙona akan kar na faɗa kuma kar na bar kowa ya gane halin da nake ciki.
Koda muka dawo ɗakinmu na shige na kwanta lamau ba tare da na yi aune ba nake jin wasu tsiraran hawaye suna kwance mini fuskata. Ina jin ƙirjina yana yi mini wani zafi tamkar ana watsa mini garwashin wuta. Ban san sa'ilin da wani wahalallen bacci ya yi awun gaba da ni ba.
Kamar daga sama na jiyo muryan Umma tana ƙiran sunana tare da bubbuga matashin da kaina yake kai. Na yi figigi na farka ina sumbatu.
"Don Allah ka yi mini rai ka taimake ni kar ka raba ni da......".
MuÉ—uk na haÉ—iye ragowar zancen yayin da idanuna suka washe a bisa fuskar Umma, jikina sharaf da gumi saboda mungun mafarkin da na yi da ya gigita ni ainun.
"Ke lafiyarki kuwa sai ka ce mai shafar aljanu? Ki na bacci kina ta battutuwa".
Sai da na daidaita nutsuwata kafin na yi ƙarfin halin faɗin"lafiya ƙalau Umma, yanzu ƙarfe nawa?". Sai da ta ƙare mini kallon tsaf kana ta ce da ni a taƙaice.
"Ƙarfe biyu saura".
"Innalillahi wa inna ilahirin raji'un!".
Na furta ina dirowa daga oan gado na fito waje na yi alwala na koma ciki na yi salla, duk yadda Umma da Amira ta suka matsa mini akan na ci abinci kasa ci na yi, da ƙyar na sha kunu shi ma bai wuce ludayi uku na yi ba. Ranar ko islamiyya ban je ba duk son da nake yi mata kuwa, haka na wuni a ɗaki inna fito waje to alwala zan yi ina kammalawa nake koma na kwanta tun ina hawayen har suka daina tsiyaya. Tun da na kwanta nake ta biya karatun alkur'ani a cikin zuciyata har wani baccin ya kuma ɗauka na, ba ni na tashi ba dab ana ƙiran sallan magrib na fito na shiga banɗaki da nufin yin wanka amma na fi mintuna talatin ina durƙushe ina kuka, da ƙyar na yi wankan na fito na ɗauro alwala na koma ciki na yi salla, ban tashi daga kan sallayan ba har sai da na yi sallan isha'i ina zaune Amira ta shigo lokacin Umma ta fita.
"Ya jikin nakin?".
"Da sauƙi".
Na amsa mata da aa taƙaice da hakan ya ba ta damar ci gaba da magana.
"Ki tashi mu je ayi miki alluran daren daga nan kuma sai mu wuce ko?".
Na ware dukka girman idona akan ta"mu wuce zuwa ina ke nan Amira?".
"Gidan Tasalla mana". Baƙi ciki da takaici ya hana ni cewa komai illa bin ta da kallo da na ci gaba da yi ina cije leɓena. Ta riƙo hannuna na zame.
"Na san abin da kike tunani a cikin ranki Amatullah, amma idan kika ce kin daina zuwa to ina tabbatar miki da cewar kin kafawa kanki alamar zargi kenan. Dole su Abba su bincika dalilin da ya sa kika ce ba za ki koma ba alhalin ke da kanki kika zo masa da buƙatar". Ta sauauta amon muryarta kana ta ci gaba da cewa"ki ɗauri abin da ya faru a matsayin ƙaddara".
"Na yarda da ƙaddara mana Amira na yarda da ƙaddara. Amma ba zan iya komawa gidan nan ba". Na yi zancen cikin raunin da yake fitowa tun daga ƙasan zuciyata.
"Ni ma ba wai na ce ki ci gaba da zuwa ba ne, na É—an wani lokaci kawai saboda mu kawar da zargi. Ki daure ki rufa mana wannan asirin". Na fashe da kuka ina faÉ—in"Allah na tuba idan laifi na yi maka ka jarabce ni ta wannan hanyar. Allah na tuba ka yafe mini".
"Ki yi haƙuri ki daina wannan kukan Amatu ya isa haka. Kar ki ja wa kanki wani ciwon na daban don Allah".
Kafin na amsa mata muka tsinkayo sallamar Abba, na yi zumbur na miƙe ina gyara ɗaurin zanin da yake jikina na goge fuskana da bakin hijabin da yake jikina. Na fito falon Amira tana biye da ni. Muka haɗe baki wajen yi masa sannu da zuwa ya amsa yana tambayata ya ya jiki na ce da shi da sauƙi.
Ya ba ni wani magani ya ce ma sha na ciwon jiki ne, a take a wajen na ɓalla na sha ba mu tafi ba sai da Umma ta dawo muka yi mata sallama muka tafi. Sai da muka tsaya a wajen Halilu mai chemist ya mini alluran kana muka tafi.
Ko kallon azurki ban yi wa Hajiya Tasalla ba duk da kuwa kulawar da take ba ni don tun da muke je ta kasa zaune ta kasa tsaye sai hidima take yi da mu har sauya mana É—aki ta yi.
"Hajiya ina ita Ramlatun ta dawo?". Na yi tambayar fuskata a É—aure kamar hadarin gabas.
Ta soma inda-inda"ki yi haƙuri an yi rasuwa ne a can ƙauyen shi yasa. Ni ma saboda na san za ku zo ne shi yasa ban je ba. Amma in Sha Allah da zaran an yi sadakan bakwai za ta dawo ku yi haƙuri".
Ban ce da ita komai ba na tashi da sauri na har ina harɗewa na shige ciki ina tare hawayen da suke ƙoƙarin zubo mini daga idanuna. Amira tana shigowa muka rufe ɗaki na ciki na amsa wayarta na buɗe application ɗin alƙur'ani ina karantawa tun Amira tana zaune har sai da ta kwanta bacci ya soma fizgan ta don daren jiya ba mu runtsa ba.