← Book details Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 58

Sashe 5

Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kai ɗin fa Munniru. Wani irin masifa ce wannan? Kai komai na yi a idanunka ban fita ba. Ka ƙwammace ka goyi bayan matar wani akan ka goyi bayan matarka ta sunna har kake ƙiran ta da baiwar Allah. Duka kuma ba ni na ce ya sake ta ba tashin hankalinta ne ya jaza mata, ƴan uwanta kuma da ta kwaso ba a haifi shegiyar da za ta zo har inda nake ta gaya min magana na ƙyale ta ba. Kuɗi kuwa ko sau dubu sai ɗauka ya ba ni billahillazi sai na amsa ai ba tursasa masa na yi ba shi ya yi niyya, kai ba ka ba ni ba kuma ban ga dalilin da za ka hana ni karɓa ba".

Sai mintuna suka shuɗe kafin Abba ya ce"ki kiyaye harshenki, ki dinga tauna lafazi kafin ki furta shi. Domin da zaran ya fita to ba a iya dawo da shi. Shi yasa Annabinmu da kansa ya ce kuffa alaika haza ma'ana ka kiyaye wannan a gare ka watau harshe, dafinsa ya bi na bakin maciji. Ke komai ya fito daga bakinki za ki yaɓawa mutum ba tare da tunanina ba, Hafsatu ina guje miki ranar da za ki yi dana sani".

"Babu dana sanin da zan yi Munniru, bakinka ya sari guntun gashi".

Ta yi zancen tana banko labulen ɗakin ta fito falo. Kamar wacce aka tsigara wa matsilli haka na zabura na tashi, kallon da ta tsare ni da shi ya sani saurin rusunar da ƙwayoyin idanuna ƙasa.
"Watau kin na zaune a nan kin kasa kunne kina sauraron abin da muke tattaunawa ko?".

Na girgiza kaina"ban daÉ—e da shigowa ba ma". Ta doka mini tsawan da ya haifar mini da rawar jiki.
"Dalla rufe min baki munafukar banza munafukar wofi. Duk ba ke kika ce ummul abasin faruwar komai ba. Shegiya ƴar iska mai jinin tsiya". Kafin na ce wani abu tunin Abba ya fito falon cikin matsanancin ɓacin ran da ya bayyana ɓaro-ɓaro a bisa kammalalliyar fuskarsa da farin gashi su ka yi masa ƙwawanya a saman harbarsa. Ya nuna ta da ƴar manuniyar ƴatsarsa da hakan yake tabbatar da ya kai ƙololuwan ɓaci rai da faɗa wa cikin tarin takaici.

"Na hane ki da jifan Amatullah da waɗannan munanan kalaman amma kin liƙa wa kunnuwanki gayan tuwo. Shin ashe idan wani ya ce da ita shegiya ko ƴar iska abin ba zai yi miki ciwo ba kenan?. Ke uwa ce ki zama mai tausasa lafazinki akan Amatullah. Ba na son mins sa'in sa dake amma ke kike jan komai".

"Mtscheew".

Umma ta ja dogon tsaki tana yi wa kanta mazauni a kujerar da na tashi daga kanta, jinjina kansa kawai Abba ya yi kafin ya maido da duban sa gare ni yana faÉ—in"Amatullah ki kai min ruwan wanka".

"To Abba".

Na amsa da shi yayin da nake fita daga falon na ɗauki bokiti na cika da ruwa na kai masa bayi. Kana na zo na sanar da shi. A uwar ɗaka muke kwana tare da Umma yayin da shi kuma Abba yake kwana a falo, tun da na yi girma na yi wayo muke yin hakan wannan dalilin ya sa kullum sai na yi addu'an Ubangiji ya buɗa wa Abba ya yi gidan kansa ko da kara ya kewaye mana mu koma. Mu huta da wannan baƙin masifan takuran. Kamar a mafarki haka nake jiyo sautin maganar a tsakiyar kaina na mirgina ina murtsike idanuna tare da buɗe su kana na maida su na lumshe. Duk da haka ban daina jin sautin yana tashi ba dole ƙanwar naƙi na tashi ina yin miƙa daidai lokacin limamin masallacin kusa da gidanmu ya rangaɗa ƙiran sallan assalatun cikin zazzaƙan muryarsa mai sanyi.

Na tashi zan fita falo na jiyo Abba da Umma ne suke magana na koma na zauna, don ba na ƙaunar sauraron abin da suke tattaunawa wanda ina da tabbacin zai iya zama sirrinsu ne wanda bai dace na ji ba. Ina nan zaune Umma ta shigo tana ta bambamin da ban gane takamanmen akan abin da take yi ba, na tashi na fita domin ɗauro alwalan sallan asubahi na tarar da an haɗa wani rigimar a filin tsakar gidan.
Maman Rayyan ce take ta surfa masifa Asabe tana taya ta, a nan na tsinci kan zancen wai a daren jiya ne gandaderen ƙato ya shiga har uwar ɗakinta yana shafa jikinta, kasancewar mijinta ba mazauni ba ne ya kan yi watanni biyar zuwa shida ba ya gida.
Har hantsi ya fito masifa da bala'in bai lafa ba abu kamar wasa har ya kai gaban mai unguwa da wasu manyan unguwan, ina kwance a ɗaki ina fitan karatun islamiyya Amira ta shigo sai da na kai ayar ƙarshe da nake karantawa na cikin suratul tagabun kafin na rufe ƙur'anin ina duban ta fuskana cike da murmushi.

Kafin na yi magana ta datsi numfashina"karfe goma da rabi na dawo, na san abin da za ki tambaya kenan".
Na murmusa kafin na ce"ai ke da kan ki Amira ya kamata ki yi wa kanki faÉ—a, wannan daren da kike kai wa a waje ba mutuncinki ba ne a matsayinki na É—iya mace. Ko na miji ne ai duk inda goma zuwa sha É—aya ta yi daga lokacin ta fara neman hanyar gida balle kuma mace".
Ta yatsina fuska kafin ta ce"kin ga ni ba wannan ba ne ya kawo ni. Amshi ki buɗe ki ga". Ta ƙarishe zancen tana ajiye mini wani baƙin leda a bisa cinyata, ta bi ta da kallon mamaki.

"Mene ne a ciki?".
Na jefa mata tambayar ina juya ledar a hannuna.
"Ke kuwa ki buÉ—e mana idanunki su gane miki". Kamar yadda ta faÉ—a hakan na yi na soma ciki-cikin buÉ—e ledar. Kwalin waya ce sabuwa dal da ita Æ´ar shafai. Na kwasa ihu ta yi hanzari rufe mini baki da tafukan hannayenta na zame hannunta.
"Amira Ina kika sama wannan dalleliyar wayar nan? Ko wani ne ya ba ki ajiye? Ko aka aike ki da shi wani wajen?". Ta saki dariya har da riƙe ciki sai da ta yi mai isharta kafin ta tsagaita gami da faɗin"babu ko ɗaya nawa ce, daren jiya ta zo hannuna". Na watsa mata kallon mamaki da al'ajabi.
Cike da son tabbatar mini da sahihancin abin da ta furta ta ɗage mini idonta guda tana zarce wa da cewa"wallahi kin dai ji rantsuwa kenan ko, wayata ce". Na katse ta kafin ta ƙarisa zancen.

"Ina kika sama kuÉ—in sayan wannan wayar Amira? Ita wayar nan ce fa ta cikin shirin film É—in labarina, ta hannun Baban Sumayya. Kuma na san ko riba da jarinki gabaÉ—aya kika haÉ—a ba za su sayi wannan wayar ba". Ta kuma fashewa da dariya kafin ta ce.
"Ba ko sisina a cikin kuÉ—in wayan nan Mansur ne ya kawo min ita jiya, tukwuicin amsar tayin soyayyarsa da na yi".

Kamar saƙaho haka na saki baki da hanci ina bin ta da kallo tamkar yau na fara tozali da ita. Sai da na tattaro jarumta na yaɓa wa kaina kafin na iya yin motsin kirki har na iya furta wani abun.
"Amira anya kuwa kina da hankali? Haka siddan daga haÉ—uwa da mutum ya É—auki wannan wayar ya ba ki kuma ki sa hannu ki amsa". Ta galla mini harara tana fizge wayar daga hannu.
"Kin ga Amatullah kar ki ɓata min rai da sanyin safiyar nan, sanin kanki ne a kaf cikin gidan nan da ke kaɗai nake hira har na saki jiki na sanar da ke abubuwan da nake yi". Ganin tana ƙoƙarin ficewa ya sani riƙo hannunta.

"Kar ki ɗauka da zafi mana ke kuwa. Ki yi haƙuri".

"Ke ce ai kike ƙoƙarin ɓata min rai Amatullah". Ta koma mazauninta ta zauna ta murtuƙe fuska.
"Haba! Ke kuwa saki fuskar mana ta Mansur". Babu shiri ta ƙyalƙyale da dariya.

Ta gyara zama tana zubo mini bayanai"ban san inda yake ba amma dai a gajerin da nake kai tallar waina muka haɗu da shi ya kawo gyaran motarsa, ya saya waina ya buƙaci lambata na ce da shi ban da waya. A haka kusan kullum sai ya zo gajerin don kawai ta ganni har ya yi min tayin soyyarsa bayan na gara shi shekaran jiya na amince. Daren jiya kuwa ya same ni har ƙofar gida ina soyar awara ya ba ni ita, bayan p yi min juye".

Ƙwala mata ƙiran da mptessghaifiyarta Sahura ta yi mata shi ya hana ni furta zancen da na yunƙuro da nufin yi. Ta tattare kwalin wayar ta miƙe"bari na je na san yanzu Ummata ta kammala wainar, duk sauran ƙarin bayani inna dawo za ki ji shi". Da kallo na raka ta har ta fice na gaza cewa komai saboda giyan mamakin da ta shayar da ni, haka na zauna ina bitar zantukan Amira tare da yi musu tankaɗe da rairaya.

Ƙatuwar ajiyar zuciya na sauƙe ina tallafe kuncina lalle Amira ta kusa ta fi ƙarfina. A kwanakin baya sai da muka daina magana da ita don kawai na gaya mata gaskiya akan irin shigar banzan da take yi in za ta fita talla. Ko da na yi mata magana sai ta kaɗa baki ta ce da ni idan ba ta yi kwalliya waye zai kalle ta balle har ya sayi abin da take sayar wa. Yanzu ga halin biyewa samari da ta tsira.

"To maza malalaciya tashi gari ya waye. Ga kunu can ya kammalu".

Na tsinkayo amon Ummata da ya yi nasarar dawo da ni duniyar zahiri daga karatun wasiƙan jakin da na faɗa.

DAFIN HARSHE

©️ Maimuna Tijjani Iyam
_______________________________________

Page 0️⃣5️⃣
Chapter 5 · 0% Book details