Sashe 33
Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Wallahi da zarar na tunkaro hanyar gidan nan sai na yi gabana yana faÉ—uwa. Haka nake jin ba na son komawa cikin wannan gidan saboda tashin hankalin da zan tarar a cikinsa ko na sakan guda ba na samu farin ciki".
Ta riƙo hannuna dukkan biyun ta sanya cikin nata kafin ta soma magana da laulausan amon mai ratsa ƙalbi.
"Amatullah sai fa kin cire damuwar komai daga cikin ranki, kin ga rayuwar nan kowa da irin na shi ƙaddarar da kuma ƙalubalen rayuwarsa". Na yi saurin tarar numfashinta"Amira ni fa ba dogon magana nake son ji ba. Kawai ba na son komawa gidan nan ne a yanzu na fi so sai lokacin tafiya islamiyya ya gabato kafin na koma, ni wallahi gwara mu koma tashar ma mu yi zamanmu".
A tsorace ta waro idanunta ta buÉ—e su tar a kaina"tasha kuma Amatullah?".
Ba tare da tsoro ko shakkan komai ba na ce"ƙwarai kuwa, zaman cikin tashan nan ya fi mini kwanciyar hankali fiye da zama cikin gidan nan".
Ta riƙe haɓa cike da mamaki tare da faɗin"tirkashi! Lalle lamarin ya girmama. Amatullah yau ke ce da bakinki kike furta kin fi son zaman tasha fiye da gida". Na yi shuru na gaza ba ta amsa don na rasa ƙwarin gwiwar buɗe bakina. Take wani tunanin ya faɗo mini a rai tamkar faɗuwar aradu na yi caraf na ce"ko dai mu je gidan Anty Sawwama ne?". Ta yi sakeke kawai tana kallona kafin can ta yi magana a taƙaice.
"Indai har za ki sama nutsuwa a can É—in, to mu je mana".
Murmushi muka sakarwa juna kafin na ja hannunta muka fice daga layin, tudun nabawa muka nufo da yake bayan layinmu, tun daga zaure muke zabga sallama har muka isa cikin gidan, gidan wayam da alamun Umar ya tafi makaranta don daman shine mai zama a gida.
"Wa alaikussalam sannunku da zuwa".
Muka tsinkayo muryar Anty Sawwama daga bayan mu da hakan ya sa mu juyawa dukkanmu. Anty Sawwama ce da alama daga banÉ—aki ta fito ta ajiye bautar da ke hannunta kafin ta yi gaba muka bi ta a baya har cikin É—akinta. Sai da muka zazzauna kafin muka gaishe ta ta amsa mana fuskarta babu
yabo babu fallasa.
"Daga ku kuwa kuke da wannan ranar?".
"Daga wajen tallla muke". Na amsa mata a gajarce, sai dai na lura da yanayin fuskarta ta sauya gabaÉ—aya ta yi É—an jim kafin ta can ta ce"Allah dai ya kyauta, ki je kitchen ki É—auko muku by ragowar abincin safe ku ci".
"To". Na amsa da shi yayin da nake tashi na nufi kitchen na É—auko Mana abincin na ajiye mana muka ci tare da Amira sai da muka gama ci tas, kana na tambayi ko akwai wani aikin da za mu yi mata ta ce sai dai mu haÉ—a mata wutan abincin rana.
Kamar yadda ta buƙata haka muka fito muka fara aikin, na soma haɗa wuta yayin da Amira ta ɗauko doyan ta soma ferewa. Sai da muka haɗa komai har ruwan ya tafasa muka zuba doyan kana na tashi na shiga ciki wajen Anty Sawwama yayin da na bar Amira tana zaune tana waya da Mansur.
"Sannu da hutawa Anty Sawwama".
Ta gyara kwanciyarta daga gishingiÉ—an da ta yi kafin ta amsa muni cikin faÉ—in"yauwa uwata sannunku da aiki".
"Anty daman na zo ne musamman don na ba ki haƙuri akan abin da ya faru tsakaninki da Umma ɗazu da safe. Ina mai ba ki haƙuri a madadinta kuma ina so ki yi mata uzuri".
Ta jinjina kanta tana sakin taƙaitaccen murmushi kafin ta ce"tabbas albasa ba ta yi halin ruwa ba. Uwata ba komai ai ya riga da ya wuce, kin ga ni har na manta ma ai".
"To amma Anty me ye kuka tattaunawa haka da ya ki tafiya da wuri? Ko sallama fa ba mu yi ba sai fito na yi na iske har kin tafi".
Ta sauƙe tagwayen ajiyar zuciya mai matuƙar sauti da har da kunnuwana suka ji yo mini sautin.
"Uwata ba wata magana ba ce da za ki tada hnakalinki, daman na je na roƙi alfarman Manniru da ki dawo wajena da zama saboda yanzu kin girma ke ba yarinya ba ce, sannan a can gidan falo ne kawai ne da ɗaki dole ne wani lokacin iyayenki suna buƙatar yin sirri a tsakaninsu wanda babu damar yin hakan. Da a tunanina na ce idan ki gama haɗa haddarki sai ki dawo idan kin ga nan ɗin ma bai yi miki ba sai ki koma wajen yayarki Zulaihatu".
Na sauƙe ɓoyayyar ajiyar zuciya mai nauyin gaske, duk wasu gaɓoɓin jikina suka yi sanyi ƙalau. Anty Zulaihatu ita ce babbar ɗiyar Anty Sawwama sa take aure a cikin gari, kuma ita ɗiya ɗaya tilo mace sauran ukun duk maza ne. Yaya Alhassan shi ne yake bin bayan Anty Zulaihatu wanda yanzu haka yana aiki a ma'aikatan shinfaka yana samu sosai don hatta gidan da suke ciki shi ya saya musu, daga shi sai Yaya Walid wanda ya ci sunan Abbana aka ɓoye masa suna ana ƙiran sa da Walid wanda yanzu haka yake karatu jami'ar jiha sannan autansu Umar wanda tazarar tsakaninmu da shi kaɗan ne. Kalaman da ta ɗaura da su su suka yi silar dawo da ni izuwa duniyar zahiri daga na tunanin da na dulmiya a cikinsa.
"Amma tun da Ummanki ba ta amince da shawarar da na je da ita ba. Daman shawara ce ba komai ba".
"To Anty ki bari zuwa bayan kwana biyu mana sai ki ƙara komawa ki sama Abba shi kaɗai, ko a wajen aiki ne wataƙila ya amince". Na ƙare zancen cikin marairaice murya yayin ƙwalla suke ciki mini kurmin idaniyata. Kafin ta yi magana muka ji yo sallamar Yaya Alhassan muka amsa masa kafin ta shigo ciki na tashi na amsa ledar da yake hannunsa kana na gaishe shi. Ya ɗauke kansa gefe kamar bai ganni ba yana cewa"ai ni kam na yi fushi Amatullah. Na ma yi tunanin ko kin manta hanyar gidan namun ne ai".
Na girgiza kaina"Yaya Alhassan wane ni na manta hanyar gidan nan, akwai kwanakin nan ba na samun zama ne saboda sauƙarmu ta gabato".
Ya faɗaɗa annurin fuskarsa tare da faɗin"haka Umma take sanar da ni, yaushe ne sauƙar takun?".
"Yanzu sai saura sati uku". Ya jinjina kansa"Allah ya kaimu lokacin kafin lokacin ma kuma sai ki zo ki ƙara sanar da ni".
Cike da jin daÉ—i na ce"to in sha Allah, bari na je na duba girkin na bar Amira ita kaÉ—ai a waje". Har zan fice Yaya Alhassan ya dakatar da ni.
"Ai kuwa na zo a daidai ba zan tafi ba sai na ci girkin ƴar ƙanwata".
"Lalle kam! Yaushe rabon duniya da ayyaraye Alhassan? Ni ba zan iya tuna ranar da ka ci abincin rana a cikin gidan ba ko an ce ka saurara ka ci za ka kawo uzurin cewar kana sauri. Amma yau da yake Amatullah ce ta girka ko tayi ba a yi maka ba za ka tsaya".
Furucin Anty Sawwama kenan tana kafe Yaya Alhassan da ya sadda kansa ƙasa da ido, ni kam murmushi kawai na yi na fice. Har yanzu Amira wayar take yi na je fizge na kashe muka soma gyara kayan miyan da Yaya Alhassan ya kawo kan ka ce me ye tunin har mun ɗaura miyan akan wuta. Bai ɗau lokaci ba ya kammala muka sauƙe a lokacin Umar ya dawo daga makaranta.
"Ke yarinyar nan yaushe kika zo?".
Na wurga masa harara"ban sani ba É—an rainin yawo kawai, kuma da kake ce mini yarinya ka san dai da cewa na girme ka ko".
"Never wannan kuma zancen ne. Me ye kika jagwalgwala mana haka?". Ya ƙare zancen yana sunkuyawa ya ɗauki doyar da na sauƙe, na kai masa bugu ya zame ya yi ciki da gudu. Na kwafa na ci gaba da zubawa Yaya Alhassan abincin na kai masa ciki. Ya buɗe ya soma ci.
"Zan dawo na same ki a nan ne?".
"A'a ni kam yanzu ma tafiya zan yi, don zan je islamiyya". Ya É—ago kansa ya yi mini kallo É—aya kafin ya mayar da idanunsa kan abincin ya ci gaba da magana.
"To yaushe za ki dawo?".
"Sai an kwana biyu".
Ya yi shuru bai ce da ni komai ba sai can ya ce"ina son zuwa gidanku ko don na dinga ganinki ina kuma gaishe da Abba. Amma ba na jin daÉ—i abin da Umma take yi a duk sadda na je wannan dalilin ne ya sa na É—an ja baya da zuwa".
Na sauƙe ɓoyayyar ajiyar zuciya kana na furta"halin Umma ai sai haƙuri".
"Amma dai in Sha Allah zan yi ƙoƙarin na zo kafin lokacin sauƙanku sai mu tattaunawa akan abin da ya dace a yi muku".
"To". Na amsa da shi na fito na yi alwala muka shigo tare da Amira muka yi salla, kafin mu iddar tunin Yaya Alhassan ya kammala cin abincin har ya Yaya Alhassan ya koma wajen aiki, a gurguje muka ci abincin muka fara yin haramar tafiya Anty Sawwama ta ba mu dubu ɗaya ta ce mu hau napep ina ji Yaya Alhassan muka karɓa da godiya, tare muka fito da Umar ya rako har bakin hanya hana shi ma ya wuce wajen sana'arsa ta ɗinki.
Tun muna shawo kwana muke cin karo da taron jama'a har muka iso ƙofar gidan, muka iske mutane a cike maƙil ko hanyar wucewa babu.
[10/3, 1:12 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE*
Â©ï¸ Maimuna Tijjani Iyam
______________________________________
Page 2ï¸âƒ£6ï¸âƒ£
Mutanen ta ko'ina babu masaka tsinke, ba mu sama damar shiga cikin gidan ba muka soma jiyo jiniyar motar ƴan sanda ta nufo wajen, hakan ya sa mutanen wajen suka soma darewa. A ƙofar gidan motar ta faka wasu ƴan sanda biyu suka fito diro daga bayan motan yayin da Baban Adnan ya fito daga gaban motar.
Kai tsaye cikin gidan suka nufo hakan ya ba mu damar bin bayan su muka shiga tare, filin tsakar gidan ma ya cika da mata.
"Ina wacce aka watsawa ruwan zafin?".