Sashe 18
Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da kallo na raka ta har ta ɓacewa ganina na sauƙe wani gawurtaccen ajiyar zuciya ina zabga tagumi da hannuwa bibiyu. Kafin maganganun da ta yi mini ya soma dawo mini a cikin kwanyata ina yi masa rankaɗe da rairaya. Babu shiri na zame hannuna daga tagumin da na yi ina ji har cikin ƙasan zuicyata ba zan taɓa iya aikata abin da Amira take ikirarin lokaci zai sa na koya ba.
"Ƴan mata me ye kike sayarwa ne?". Muryar saurayin ya dawo da ni cikin duniyar zahiri daga karatun wasiƙan jakin da na faɗa. Na cira kai ina ƙare masa kallon tsaf. Shigar ƙananan kaya ne a jikinsa da su da kansu suke bayyanar da tsadan farashin su, komai na shi tsaf-tsaf alamar baya haɗa hanya da ƙazanta ko mai aikata ta.
"Ko ba za ki yi min magana ai za ki tashi daga nan wajen kar zafin rana ya yi wannan kyakykyawan fatarta ki illa". Sai da ya yi maganar na ankara da har rana ya iso inda nake zaune na tashi na matsa gefe na zauna shi ma ya matso.
"Don Allah ki yi min magana mana ko da kuwa zagina za ki yi ko cin mutunci. Na tabbatar yanda kike da kyawun jiki da na fuska muryarki ma za ta kasance kamar sarewa a kunne".
A kufule na ce"me ye kake so daga gare ni? Idanunka dai sun gane maka kuma sun isa su ba ka amsar duk wani tambayar da kake tafe da shi. Ba shashashci ba ne ya kawo ni nan sana'a nake yi". Ya murmusa yana ɓalle murfin ruwan roban da yake hannunsa ya kurɓa kafin ya ce"tsarki ta tabbata da Ubangijin da ya tsagawa bayinsa baki kuma ya ba su ikon yin magana. Tabbas ki na da zaƙin murya mai rikitar da ƙwaƙwalwa tun da na hango ki daga nisa na ji zuciyata tana cewa na zo gare ki".
"Don Allah Malam ka yi haƙuri".
"A zuba min kunun na dubu biyu". Na É—aga kai na yi masa kallo guda kafin na kawar da kaina gefe ina faÉ—in"gabaÉ—aya sauran kunun bai kai na adadin wannan kuÉ—in ba".
"To yanzu a zuba min na sha sauran kuma sai ki yi yadda kike so da shi". Ban ce da shi uffan ba na zuba masa na ɗari biyu na miƙa masa ya ɗauka ya zauna ya soma sha.
"Kin san dai wallahi ita ce ƙarshen rantsuwa ga duk wani ɗan musulmi ko? To wallahi tun da nake ban taɓa shan kunun mai daɗin wannan ba. Don Allah zan roƙi wata alfarma daga gare ki idan ba za ki damu ba".
Ba tare da na kalla inda yake ba na ce"don damuwa kam dole na damu. FaÉ—i na ji wani irin alfarma ce".
"So nake yi a duk lokacin da kika kawo tallan kunu tashan nan, na zama mutum na farko da zan fara sha kafin kowa".
Na galla masa harara"ba zan iya ɗaukar abun da ba zan iya ba ka yi haƙuri". Ina ɗago kaina muka haɗa ido da shi na kuma watsa masa wani harara ina saki gajeren tsaki.
"Wallahi idan kina magana kamar kar ki daina. Yadda kike fassara leɓɓanki shi kaɗai ma abin burgewa ne". Ban ce da shi komai ba har ya gama kiɗansa kuma ya yi rawansa bayan ya gama shan kunun ya miƙe tsaye ya tsaro wasu kudaɗe daga aljihunsa ya raba biyu ya ajiye mini kashi ɗaya akan bokitin kunun yana faɗin.
"Ga kuɗin kunun". Ta ƙara ajiye mini ɗayan kashin yana ci gaba da cewa"wannan kuma ni ne na yi niyyan baki saboda gamsuwa da na yi da wannan daddaɗan kunun nakin".
"Malam na ɗari biyu ai kawai ka sha. Don haka iya ɗari biyun nake buƙata domin shi ne haƙƙina".
Kafin ya yi magana Amira ta iso wajen hakan ya sani miƙewa tsaye ina kallonta sai dai kafin na yi magana ta riga ni.
"Tuba nake yi na bar ki ke É—aya ko? To yanzu dai ga shi na dawo".
"Kin ga ni kawai ma mu tafi gida na gaji da wajen nan gabaɗaya". Ta yi sakeke tana kallona"ban gane mu tafi gida ba Amatullah? Ta yaya za mu tafi gida bayan kunun har yanzu akwai saura. Ai kawai haƙuri za ki yi mu zauna har ya ƙare".
"Babbar yarinya daman tare kuke da ita? Ai kuwa faɗuwa ta zo daidai da zama da ke zan yi kamun ƙafa". Ta murmusa tana fuskantarsa kafin ta ce"Bash ai ban gane ka ba kai ne haka? Duk ka wani canza ka sama duniya ka manta da mutane. Na ji ma ance wai yanzu babbar mota kake ja. Sai jifa-jifa ake ganinka a cikin tashar". Ya bushe da dariya har da tafa hannu sai da ya tsagaita kafin ya ce"ikon Allah! Ke ma kin sama labari kenan?. Wallahi ina gaya miki yanzu gabaɗaya ba na samun sama".
Cike da fara'a Amira ta ce"ma sha Allah ina taya ka murna".
"Ina godiya babbar yarinya. Wannan fine girl É—in fa?". Ta waigo tana kallona.
"Au wai Amatullah? Ƙawata ce ko akwai magana ne?".
"Sosai ma kuwa sai dai ina ta yi mata magana ba ta tanka min. Kin san ba ni ban cika shiga harkokin mata ba amma ita É—in ta yi nasarar yin daidai da ra'ayina, da ita za a tafi".
Ta saka dariya kafin ta ce"to wannan kuma ai maganarku ce kai da ita sai dai ko na ba ku waje".
Na haɗe giran sama da ba ƙasa ina watsa mata harara da wutsiyar idona"Amira kin fi kowa sanin ba na son irin wannan wasan".
"Allah ya ba ki haƙuri ba ni na kar zoman ba rataya aka ba ni". Daga haka ta nema waje ta zauna ta zaro wayarta tana dandanawa ni ma na koma na zauna.
"To babbar yarinya ni dai zan wuce. Æarauniyar zuciyata ga kuÉ—in nan don Allah kar ki Æ™i É—auka". Ya Æ™are zancen yana maraicecewa lamarin da ya Æ™ara tuntsura mini zuciyata ta zo daidai wuya ta yi nuni tsayiwar Æ™aryan kifi a maÆ™oÆ™aro.
"Malam na ri ga da na gaya maka adadin kuÉ—inan ai ko? Me zan yi da wannan tulin kuÉ—in da ka ajiye mini?". Kafin ya ba ni amsa Amira ta yi caraf ta cafke zancen.
"Kar ka damu Bashir zan shawo maka kan komai".
Ya yalwata fuskarsa da yalwataccen annuri kafin ya furta"ina godiya ƴar gari, yanzu dai ki saka min sha ɗayanki tun da na ga kin ƙara da gari yanzu, kin dantsalo babbar waya". Da murmushi a fuskarta ta karɓa ta sanya masa lambarta ya ƙira a take ya ce ta yi saving kafin suka yi sallama ya tafi.
Ta watsa kuɗin ta irga su kafin ta soma cewa"kin ga dubu dubu huɗu ne dukka. Yanzu me ye za a yi da su?". Raina ya kai ƙololuwar ɓaci na yi mata wani irin mungun kallo ina furzar da takaicin da ta yi silar cusa mini cikin raina.
"Sai ki san yadda za ki yi da shi tun da ke kika É—auke su".
Ganin na ɓata rai ya sanya ta soma faɗin"ki saki ranki Amatullah abun da na yi shi ne daidai. Don idan ba ki karɓa ba ma wata can daban ce za ta ci kuɗin kin ga kuwa ban yi laifi ba don na ɗauka. Su da irin su Bashir kuɗinsu duk a wajen mata yake ƙarewa ba sa tsinanawa kansu komai gwara ma ki kwanki gara ki bar gara a inda kika same shi".
Ban ce da ita komai ba na tashi na na É—aga gammona zan É—auki bokitin kunun na É—aura a kaina ta dakatar da ni.
"Haba ke kuwa ina za ki da ragowar kunun? Ai almajirai za ki nema ki yi musu sadaka ki nema albarkar kasuwa". Na kasa cewa da ita komai balle na yi wani yunƙurin haka ina ji ina gani ta rabarwar almajirai kunun har da cewa wai su yi mini addu'a Allah ya sa na shigo tashar da ƙafar dama. Ta tattara kayan gabaɗaya tare da na ta almajirai suka ɗauka mana zuwa gida, suna gaba muna biye da su a baya.
"Amatullah sai fa kin watsar da waÉ—annan tsauraran É—abi'un nakin kafin ki iya zama cikin tashar nan har ki ci riban zaman. Kin ga mutanen sai ka musu abin da suke so kafin kai ma ka sama yadda kake so daga gare su".
Na yi hanzarin taka mata burki"ban gane sai ka yi musu abin da suke so ba?".
"Kwantar da hankalinki kar ki fassara zancena ta wani hanyar daban. Ki dinga sakar musu fuskar kuna yin ɗan hira nan ko da jifa-jifa ne. Matuƙar za ki yi haka to jauranki ba zai taɓa yin kwantai ba, kuma ina tabbatar miki babu wanda ya isa ya taɓa a tashar nan ya kwana lafiya".
Na yi É—an jim ina nazari da lalumen gurbin da zan aza zantukanta.
"Amma ai ce mini kika yi garejin mota kike zuwa kai talla".
"Kin manta Mansur baya gari ne? Idan yana gari ne nake zuwa gareji amma idan baya nan tashar nan nake zuwa".
"Me yasa?".
"Saboda haka kawai na yi ra'ayi". Na ja hannunta muka tsaya muna kallon juna.
"Amira ki ji tsoron Allah kin san da cewa Mansur yana sonki sosai kuma yana iya ƙoƙarin sa a kanki na gani ya biya miki duk wata buƙatarki da ta taso ɓangaren ƙudi. Amma me yasa don baya gari za ki nema cin amanarsa ta hanyar kula wasu mazan bayan shi? Ko rantsuwa na yi ba zan yi kaffara ba na san shi ne ya hana ki zuwa wannan tashar saboda baya son ki yi mu'amala da mazan wajen". Ta fizge hannunta ta fara tafiya na bi ta a baya.
"Shikenan don ina sonsa sai aka ce ba zan yi mu'amala da kowa bayan shi ba. Aure na ya yi ko kuwa ya zo gidanmu an ba shi ni ne da kike yi min wannan maganganun?. Amatullah idan na ce ba na son Mansur na yi ƙarya amma mu'amala da wasu mazan bayan shi ya zama wajibi". Ta yi tsaki daidai lokacin da muke karya kwanan shiga layinmu kafin ta ci gaba da maganan.