Sashe 2
Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tana rufe bakinta ta jayo ni ta rufe ni da duka kamar ba za ta bar ni da rai ba, matan gidan duk suna tsatstsaye suna kallo amma cikin su aka rasa samun wacce za ta kawo mini ɗauki. Tun ina ihu da kururuwar neman taimako har na gaza samun ƙarfin yin hakan, Anty Maryam ce kaɗai ta kawo mini agaji da ƙyar ta ƙwace ni daga riƙon da Umma ta yi mini tana tambayar ba'asi, Umma ta daka mata tsawa.
"Ki kauce ki ba ni waje kafin ke ma na haÉ—a da ke. Ki ba ni waje na lillisa
wannan ƴar iskan yarinya mai baƙar zuciya. Kowa yana abin kansa amma ban da ni, kunun dubu biyu kacal ki kasa sayarwa ban da lalaci da mutuwar zuciya".
Umma ta yi bayanin tana ƙoƙarin kai mini mari na kauce, Anty Maryam ta mai da ni bayanta.
"Haba ke kuwa Maman Amatu ki yi haƙuri mana ki fara sauraran dalilin da ya sa ta dawo kafin ki yanke hukunci. Sannan kin ga wannan furucin da kike yi mata sam bai dace ba a matsayin na uwa. Yau idan ta zama ƴar iskan sai kin fi kowa shiga damuwa".
Kafin ta kai aya Umma ta dakatar da ita"kin ga Malama ba zamanki nake yi balle ki zaunar da ni kina faɗa min abin da zan yi ko wanda zan bari. Kuɗin haya mijinki yake biya ni ma haka mijina yake biya don haka babu abin da za ki nuna min. Ki ji da abin da yake gaban ki, ban da lalacewar zamani da samun wuri wai har wacce ba ta taɓa haihuwa ba ce za ta faɗin yadda za a yi tarbiyan ƴaƴa".
Cikin tushewar numfashi Anty Maryam ta ce"Allah ya ba ki haƙuri, ga Amatullah idan kin ga dama ki ɗauko wuƙa ki daddatsa namanta ki zuba a tukunya, ki sulala".
Tana gama maganar ta bar wajen ya koma É—akinta. Umma ta hau bambami kamar za ta yi aron baki.
[6/11, 11:58 AM] iyammaimuna: *DAFIN HARSHE*
Â©ï¸ Maimuna Tijjani Iyam
_________________________________________
Page 0ï¸âƒ£2ï¸âƒ£
Ina tsaye a wajen hawaye suna wanke mini fuskata tsabar laushin da jikina ya yi mini na gaza motsa ko da ƴatsun hannuna. Sallamar Baban Adnan shi ya dakatar da Umma daga feshin masifar da ta yunƙura za ta furzo mini. Cikin rawar jiki ta zube har ƙasa tana yi masa sannu da zuwa. Fuskarsa a washe yake amsawa kafin ya tambayi dalilin ganin mu cirko-cirko da ya yi Umma ta kwashe komai ta labarta masa.
"Na wane kuÉ—in kunun gabaÉ—aya? Sai na ba ki kuÉ—in gudun kar ayi asararsa".
"A'a Baban Adnan ayi haka? Ai kawai ka bar ni da ita tun da ita ƴar duniya ce zan nuna mata na dame ta na shanye". Ya yi saurin taran numfashinta"A'a ai ba za a yi haka ba". Yana dasa aya ya zaro wasu kuɗi daga aljihun uniform ɗinsa ba tare da ya irga ba ya miƙa wa Umma yana faɗin"ga wannan na san zai isa".
Bakinta har kunne ta miƙa hannu za ta karɓa sai dai kafin ta kai ga yin hakan aka fizge kuɗin. Duk muka ɗaga kai muna duban Maman Adnan da ta faɗo cikin gidan kamar an cillo ta ko kallabi babu a kanta balle hijabi, rabin kanta a kitse rabi a tsefe. Asabe da take bayanta tana zarrare idanu ya tabbatar mini da hashashen zuciya na cewar ita ta bi Maman Adnan har gidan kitso ta shaida mata abin da yake faruwa kasancewar gidan kitso muna kusa da shi.
"Me nake gani haka Ibrahim? Yaushe ka dawo gidan? Sannan wannan kuɗin mene ne kake ba wa wannan matar?". Sai da ya ƙare mata kallon tsaf kafin ya ba ta amsar da ta ƙara tunzura ta ta cika ta yi fam tamkar kwaɓin fanken da ya ji yis rana ta buge shi ya tashi ya yi fum.
"Kunun da ta yi ne na saye gudun kar a yi asararsa".
"Me ye haÉ—inka da ita ta balle kunun da take sayar wa? Ko kuma kai kaÉ—ai ne ka san zafin asara da kake gudun ta yi sa? Idan sau gudu É—ari za ta dama kunun ya yi kwante sai me ye Ibrahim".
Ya tsoka mata tsawar da ta tilasta mata yin shuru ba tare da ta gama furzar da takaicin da ya ƙunsa mata ba.
"Ke Safina! Me ye haka za ki tara min mutane kamar wanda ya yi sata. Ko wani aikin ashsha kika ga muna aikatawa da ita iya tijarar da za ki yi min kenan".
"Ai da wannan munafurcin gwara ma ku aikata komai".
Bai yi wata-wata ba ya ɗauke ta da marin da ya ba da sauti mai ƙarfi ya nuna ta da ƴar manuniyar ƴatsarsa. Sai dai bakinsa ya gaza cewa komai illa rawar da jikinsa yake yi. Ya fizgo hannunta ya ja ƙofar ɗakinsu sai da ya sa makulli ya buɗe kana ya wurga ta ciki ya rufa mata baya ya turo ƙofar. Ihu da kururuwarta ya cika wa kowa kunne jibgarta yake yi da dukan ƙarfinsa kamar ya sama baiwa ko kuma jaka, Adnan ya zo ƙofar ɗakin yana bubbugawa yana kuka. Kamar gidan babu kowa babu wanda ya yi yunƙurin taimakawa Maman Adnan kowacce mata ta gama harkan gabanta, ga wanda ihun ya dame su kuwa suka ja hijabi suka fice wasu suka shige ɗakunan su.
Tausayin Adnan ya kama zuciyata na ja ƙafafuna da ƙyar na nufi wajensa kafin na ƙarisa Umma ta dakatar da ni cikin kakkauran amo.
"In kika ɗaga ƙafarki guda kika isa wajen yaron nan sai na saɓa miki kamamnin. Munafuka mai baƙin hali sai an yi magana ki yi fiƙi-fiƙi da ido kamar shege a rabon gado".
Simi-simi na juyo zan shige É—aki kalamanta a karo na biyu suka sanya ni yin mutuwar tsaye.
"Ina kuma kike ƙoƙarin shiga? Wannan kunun da kika bar ni da shi gidan uban waye zan kai shi?. Ai wallahi tun da na dama kunun nan sai ki sayar da shi kin kawo min kuɗina cas babu gara bin zago".
Hawaye suka ciko mini kurmin idanuna muryarta a dushashe na soma cewa"Umma na ga yanzu Baban Adnan ya saye gabaÉ—aya kuma ya ba ki abin da ma ya fi karfin kuÉ—in kunu...". Hararar da ta watsa mini ya tursasa mini haÉ—iye raguwar kalaman ba tare da na furta su ba.
"Maman Amatu halin nan yana burge ni. Wani lokacin har mamaki nake yi anya ba ki haɗa jini da yarabawa ba kuwa? Don son kuɗina kin dama ni kin shaye". Furucin da Sahura ta yi kenan da ya sanya Maman Ebuka ɗago labulen ɗakinta tare da yaɓa wa Sahura magana.
"Ko wani ƙabila suna da son kuɗin ba sai yarabawa ba. Ko hausa ma akwai mutanen da suka fi ku son kuɗi, ku da har mutum kuna iya
yankawa akan kuÉ—i".
"A'a Allah ya ba ki haƙuri ba ni na kar zomon ba rataya aka ba ni". Sahura ta furta tana wurga mata harara a faƙaice, ba ta ce komai ba ta saki labulen ta koma ɗakinta. Sallamar Amira ɗiyar Sahura da take fita tallan waina da miya ya dakatar da Umma daga zancen da ta yunƙura za ta furta.
Tsam! Sahura ta miƙe tamkar wacce aka yi alluran doki ta sauƙar wa Amira kulan dake kanta, ta ja mata kujera ta zauna kafin ta ce"ya na ga yau kin dawo da wuri? Ko dai dawa ce ta yi nama?".
"Mama ai na gaya miki ko wainar dubu É—ari kika yi min sai na sayar ta ita cas. Ina fita ko awa guda ban yi ba na sayar, daman mun haÉ—u da Bilyamin ne shi yasa amma da tun É—azu na dawo".
Guɗa Sahura ta rangaɗa yayin da Amira ta sinco kuɗi daga gefen zaninta ta miƙa mata. Ta karɓa tana riƙa su ƴan dubu-dubu da su. Tsabar murna rawa ce kawai ba ta daka ba amma ta rumgume Amira da ci mata albarka ya fi a irga.
"Allah kai ne abin godiya daman an ce da haihuwar gwamna gwara haihuwar matarsa. Duk da Allah bai azurta ni da haihuwar É—a namiji ba ya ba ni mace mai kamar maza wacce za ta huce min takaici ta share min hawaye. Ni kam na yi farar haihuwa ko yanzu kasuwa ta watse É—an koli ya ci riba".
Sake da baki Umma take bin Sahura da ido kuÉ—in da Amira ta kawo kuwa cas sai da ta irga su, duk kusan tare suka irga da Sahura. Kamar kububuwa ta juyo kaina.
"Dan ubanki za ki É—auki kunun nan ki tafi ko sai na lahanta ki? Shegiya Æ´ar iska mai mataccen zuciya. Kowa yana abun kansa amma ban da ni, ni kam na haiho ruwan dafa kaina gantafalalla É—an kurciya da gashin baki".
Babu shiri ya suri bokitin na ɗaura a kaina har ina ƙoƙarin cin karo da Baban Adnan da ya fito fu ya fice daga gidan kamar iska. Har yanzun Ummi da saurayinta suna zaune a zaure ina jin ta tana tambayata lafiya na fito ina kuka ko kanzil ban ce da ita ba sai tsaki da na ja saboda mau kallon da Saurayin natan yake bi na da shi na yi ficewa ta. Tun da na fito daga gida na rasa takamanmen inda zan nufa a saye kunun haka na yi gararamba a titi daga ƙarshe da na gaji na nema gefen hanya na zauna na tisa bokatin kunun a gabana na zabga tagumi.
Ko dai maganar da Umma take faɗa na cewar ina da matacciyar zuciya gaskiya ce? Tun da gashi tun fitowata daga gida babu wanda ya sayi kunun ko na sule biyar. Sauƙe ƙatuwar ajiyar zuciya ina bin bokitin kunun da kallo har na kai hannuna na taɓa ya yi sanyi ƙalau yanzu kam ina da tabbacin duk wanda ya saya ba zai ji daɗi sha ba.