← Book details Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 58

Sashe 49

Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ina ƙare zancen na shige ciki ta rufa mini baya tare da shan gabana.
"Me yasa kike haka ne Amatullah? Ai ko ba za ki ce da shi wani abu ba ya dace ki saurare shi ki ji da abin da yake tafe. Wanda ya damu da ke da halin da kake ciki da ai a tunanin ya wuce wulaƙanci a gare ka".

"Wai da wani yare kike so na yi miki bayani ki fahimta ne? Na gaya miki ba na son ganin wani alaƙa ta ƙara haɗa da wani ɗa na miji ko da kuwa ta gaisawa ce matuƙar shi ɗin ba wai ya kasance muharramina ba ne". Na yi zancen ina ƙoƙarin wuce ta riƙo hannuna gam ta riƙe.
"Kar ki manta fa ke kika ba shi dama. Kar ki zama mai ƙarya alƙawari mana". Na ɓanɓare hannunta daga jikina"ki je ki ba shi haƙuri don ba zan iya sauraren sa, ina ji a jikina ma kamar wannan ce haɗuwar mu ta ƙarshe da shi". Ban jira abin da za ta ce ba na ya wucewa ta ciki kai tsaye na nufi ɗakinmu bakina ɗauke da siririyar sallamar.

Na tsuguna har ƙasa na gaishe da Umma da na iske zaune a falon tana irga wasu kuɗaɗen masu yawa, ba ta amsa mini na har na gaji da tsayiwar na tashi zan shiga ɗaki kana ta yi magana a gajarce.

"In kin shiga ɗaki akwai saƙon ki akan katifa".

"To".

Na amsa dashi duk da kuwa ina buƙatan ƙarin bayani sai dai sam ban ga fuskar yin hakan ba. Na wuce cikin ɗakin ina shiga fige hijabina na ajiye na suri ledar da na gani akan gado na buɗe. Hijabi ne a ciki sai kuma ɗinkin doguwar rigan da aka watsawa stone ya fito ya yi ɗasar da shi, wani ihun daɗi da farin ciki na saka a lokaci guda ina faɗawa kan gadon ina tsalla tsabar murnar da na tsinci kaina a cikin sa. Na rumgume hijabin ina ta washe haƙwara tamkar wacce aka biyawa kujerar hajji, tabbas Umma ta faranta mini don na daɗe da cire tsammanin cewa zan yi ankon hijabi da atamfar walimarmu tun bayan abin da ya faru lokacin da Yaya Alhassan ya kawo mini waɗannan kayan.
Sai da na ƙarishe murnata na fito na yi wa Umma godiya bakina har kunne, rabon da na tsinci kaina cikin makamamcin irin wannan farin cikin tun kafin wannan iftila'in ya faru da ni. Sai dai kalaman da ta tare ni da su suka sanyaya mini jikina matuƙa.

"Ki dai maida hankali akan karatunki sosai da sosai. Daga ni har mahaifinki mun yarda da ke ne shi yasa muka tura ki wanga islamiyyar, Amatullah...". Kafin ta ce wani abu na tuntsire da kuka har jikina yana rawa. Ta yi sakake tana kallona kamar ba ta taɓa ganina ba.
"Kukan kuma na me ye ne? Ki tashi ki ba ni wani waje idan ba za ki rufe min baki ba". Haka na ci gaba da kukan har aka yi ƙiran sallan magriba tun Umma tana mamakina har ta tashi ta bar ni wajen. Na tashi da ƙyar na je na yi alwala na dawo na gabatar da salla tun kafin na yi iddar nake jin wani zazzaɓi mai zafi yana ƙoƙarin riƙe ni. Ina iddar da sallan na ɗauko alƙur'ani na soma karanta cike da shauƙin abin da nake karanta haɗe da sanin fassaransa, haka kawai ranar na tsinci kaina cikin wani irin matsanancin kwanciyar hankali da wanzuwar nutsuwar ruhi. Ji nake yi kamar gari ba zai waye ba balle har mu taro a filin walimar, ranar mitsitsi na kafe akan ba zan je gidan Hajiya Tasalla ba saboda shirye-shiryen walimar man gobe.

Abba ya kawo wake kwano biyu da wasu kayan miyan ya ce a yi alala na sauƙan, sannan ya ba ni naira dubu biyu ya ce na yi zoɓo. Duk yadda na so hana Amira sanar da Mansur labarin walimar sai da ta zagaya ta sanar da shi. A daren ranar ya zo shi ya yi mana siyayya sosai sannan ya ce zai halacci walimar da iznin Allah. Haka muka surfa wanken muka shanya sa muka je muka sayo kayan haɗin zoɓon, ba mu kwanta ba sai ƙarfe sha ɗaya saura na yi wanka na ɗauro alwala na zo na gabatar da salla raka'a biyu, na dinga zagba godiya ga mahaliccina a cikin sujjadata na ƙarshe. Ina ɗagowa na ɗauko alƙur'anina na buɗe na soma karanta ban dakata ba har ƙarfe biyun dare kana na rufe alƙur'anin. Duk yadda na so na runtsa bacci ya gagari idanuna haka na yi juyi har aka ƙira sallan assalatu, ladanin yana ƙwala ƙiran sallan na yi zumbur na tashi na zauna. Na fito na yi alwala ina ƙoƙarin koma ciki Amira ta fito ta dalle mini idanuna da hasken tocilan wayarta tana yi mini tsiya.

"Hafiza Amatullahi".

Na murmusa ina kare hannuna daga hasken tocilan haÉ—e da faÉ—in"in za ki yi sallan dai ki yi ki fito mu zo mu yi aiki".
"An gama ranki ya daÉ—e"
Ta amsa da shi ban tanka mata ba na koma ciki na yi sallan sai da na ƙara tilawar karatun da zan gabatar a wajen taron kana na fito, muka wanke waken tare da Amira muka kai niƙa muka dawo muka soma ƙulƙulawa kafin garin ya yi haske tunin ya dahu, muka ɗauko lemukan da Mansur ya kawo muka sassaka a leda muka alalen bibbiyu, sai da muka sama leda hamshin da uku.

Muka ƙula zoɓon ma, Amira ta ce tun da mun saka lemo a ledan na bar wannan na ba wa baƙina. Zoɓon kuma nawa da na ƙawayena na yarda da hakan, muna cikin aikin zoɓon Baban Adnan ya fito cikin shigar kayan aikinsa yana karkaɗe hularsa yayin da matarsa take biye da shi tamkar jela.
Amira ta taɓo ni"ga mutanan fa. Wallahi sai na ya masa magana ko don na ƙular da ita da safiyar nan".

"Ki rufawa kanki asiri dai". Ba ta ji abin da na ce da ita ba don sai da ta aikata abin da ta yi niyya. Ta lanƙwashe murya tana faɗin"Barka da fitowa Baban Adnan, har an fito ke nan? Allah dai ya saka muku da alkhairi don wannan aikin nakun ba kowa ba ne zai iya yin sa".
Take ya washe baki kamar gonar auguda" barka dai Amiratuwa ku na ta aiki ke nan da safen, biki kuke da shi ne ko suna?".

"Au! Wai daman ba ka sani ba? Amatullah ce za ta yi sauƙa yau".

"Sauƙa dai irin wacce na sani na izu sittin ko kuwa?". Ta gyaɗa kanta"ƙwarai kuwa shi fa". Zai yi magana Maman Adnan ta amshe zancen"ya dai kamata ka wuce ka tafi aikin gabanka". Ya juyo ya wurga mata wani mungun kallon da ya sanya ta saurin yi wa bakinta limzami.

Ya zaro wasu kuɗi daga cikin aljihunsa ya irgo guda biyar ya miƙawa Amira"ga wannan to ku ƙara ayi hidima, don ina da aiki da yawa ne ma da zan halatta amma yanzu ma dai bai ɓaci ba sai a yi hotuna a kawo mana mu kashe ƙwarƙwatan idonmu".
Kafin Amira ta kai ga amsar kuÉ—in Maman Adnan ta yi wuf ta kai hannu ta wafce.

"Wallahi ba za ku yi amfani da kuÉ—i nan ba, me ye haÉ—in kifi da kaska da har za ta É—auki kuÉ—i ka ba su...". Tana rufe bakinta ya wanke ta da mari.
"Ba ta kuɗin nan tun kafin na tattaka ki a nan wajen". Babu girma babu azurki ta miƙawa Amira kuɗin ta koma ɗaki tana kuka da faɗin magauta sun shiga tsakanin ta da mijinta. Tun da aka fara dramar har aka ƙare ta ban tsoma bakina a ciki ba har sai da Baban Adnan ya fita kana na ce"yanzu me ye amfanin abin da kika yi kenan? Suna zaman zamansu ki haddasa musu rigima". Ta sheƙe da dariya kafin ta ce"ko banza dai mun sama dubu biyar a ɓagas kuma ta yi asarar hawayenta a banza". Na jinjina kaina cikin takaici ba tare da na ce da ita komai ba.

Haka Ustazu Abdulwahab ya fito ya same mu muka gaishe sa Amira ta shelanta masa cewar yau za mu yi walimar sauƙan alƙur'ani, ai kuwa ya nema waje ya zauna ya soma zubo mini ruwan addu'o'i da yi mini fatan alkhairi. Ya kuma nema da na yi masa kwantacen islamiyyar in Sha Allah amaryarsa za ta je na yi masa. Kafin ƙarfe takwas mun kama komai har na yi wanka na kimtsa cikin sabuwar atamfa da hijabina da ya amshe ni sosai. Abba ma sai da ya yaba da shigar da na yi na ɗauko niƙab na ɗaura a kai, tare muka tafi da Amira abincin kuma su Umma za su taho da shi idan za su zo.

Muna isa cikin islamiyyar Malam Suleiman ya aika aka ƙira mu ni da Al'amin da Aliyu da suka suka sha ankon faran shadda da rawani sai sheƙi da ƙamshi suke bazawa.
Sai da muka yi bitan karatun da za mu yi a wajen su, suka gyagygyara mana inda ya kamata kana muka fito lokacin waje har ya É—au harama. Filin makarantar ya sha ado an kafa rumfuna da kujeru babban taro aka shiyar mana kasancewar an haÉ—e murnar waliman namun har da na bikin murnan cikar islamiyyar shekaru goma da kafuwa.
Muka zazzauna a inda aka tanada domin su masu É—aukan hoto sai hasko muke yi, na ji kaina ya sara jikina ya É—auki zafi tsabar zumuÉ—i ko abincin ban tsaya ci ba haka na taho.
Chapter 49 · 0% Book details