Sashe 6
Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read
Zumbur na miƙe na rarumo hijabina na saka na bayyano waje, tana tsaye a baranda ta cika ta yi him da dukkan alamu ƙiris take jira ta fashe. Na durƙusa a gabanta sai dai tsoron da ya yi mini katutu a cikin ƙalbina ya hana ni furzar da zancen da ya maƙale mini a bakina.
"Uban me ye kike jira? Shegiya mai zubin aljanu".
Ta doka mini tsawan da ya tilasta mini runtse idanuna ƙirjina yana tsananta bugu. Ta rusunar da kaina ƙasa kafin na soma faɗin"daman tambaya na nawa ne zan yi". Da alama zancen nawa ya yi tasiri wajen ƙara rura wutan da yake huruwa a cikin ƙirjinta, ta yi ƙwafa tsabar takaici. Duk da idanuna suna ƙasa amma a jikina nake jin ni take kallo.
"Amatullah kina ƙure ni fa kina tuntsira ni. Ina jiye miki tsoron ranar da zan yi wasan kura da ke a cikin gidan nan. Dan ubanki na dubu ɗaya ne da ɗari biyar, idan kin ga dama ki dawo min da shi yadda na kika fita da shi. Tun da daman ke ba ki gaji abin azurki ba tsinanniya". Babu shiri na ɗago kaina"don Allah Umma ki yi haƙuri in ranki ya ɓaci ki dinga yin shuru. Kullum ana gaya mana a islamiyya cewar ba a son a dinga yi wa ƴaƴa irin waɗannan kalaman".. Kallon da ta tsare ni da shi ya sani yin shuru tare da mayar da kaina ƙasa ƙwalla suna ciko mini kurmin idaniyata.
Fahimtar abin da shurunta yake nufi ya sani tashi na naɗa gammo na ɗaura bokitin kunun a kaina, numfashi mai zafi na fesar daga bakina ina ƙarewa layin namun kallo. Don ban ma san inda zan nufa na sayar da wannan kunun ba. Amon muryar Auwal da suka yi wa ƙofofin kunnuwana sauƙan bazata.
"Amatullah kenan! Ƴan mata adon gari matar manya, irin ta gaban mota".
A tsorace na waigo ina bin sa da kallo cike da son ƙarin haske, kamar ya san abin da yake cikin raina ya ci gaba da magana kansa tsaye ba tare da tsoro ko shayin komai ba.
"Allah ya yi miki zubi da tsari uwa uba ga diri kamar ke kika zana kanki, wallahi ba namijin da za ki wulga ta gabansa bai ji wani abu a cikin ransa ba. Ni da sai yanzu ma na fahimci na yi zaɓen tumun dare, sam Ummi ba ita ce kalan matan da nake so ba sai dai ance da babu gwara ba daɗi. Amatullah na yi miki alƙawarin matuƙar kika amshi soyyayata a shirye nake da na yi watsi da Ummi daga cikin zuciyata, daman can ba shiga can ciki ta yi ba".
Sakeke na tsaya ina kallonsa raina cike fal da mamakin furucinsa da yadda yake ya wani kanne ido guda ana lashe leɓan bakinsa kamar maye.
Na gyara tsayiwata kafin na harhaɗo jarumta har na sama ƙarfin gwiwan iya furta"Auwal babu abun da ya haɗa ni da kai saurayin Ummi ne kai kowa ya shaida hakan, na roƙe ka don girman wanda yake yi mana ruwa da ƙanƙara ka fita daga harkana ko har ka manta abin da ya faru ne? Ba na son na ƙara tsoma kaina cikin wani masifan". Na ƙarisa zancen cikin sigar roƙo da magiya sai da dukkan alamu roƙon nawan bai ɗaɗa sa da ƙasa ba.
"Tun ranar da na yi ido huɗu da ke Allah ya ɗaura min sonki a cikin zuciyata, ba yin kaina ba ne ni ma Amatullah. Kuma ina mai ba ki haƙuri akan abun da ya faru, ban yi da wani manufa ba kuma ban yi tunanin lamarin zai yi ƙamari har haka ba, ki yi haƙuri ya ke Sarauniya". Yana rufe bakinsa muka yi ido huɗu da Salmanu ƙanin Ummi ya dawo daga aiken da aka yi masa, ina ganin sa na sha jinin jikina. Don na san na yi shuka ne a idon makarwa tun da ya ganni da Auwal sai ya je ya isarwa Ummi.
"Ka ga ni dai babu ruwana. Ina zaman zamana ba za ka ja mini bala'i da masifa ba, ka ga tafiyata". Ina dasa aya a nan na juya na bar ƙofar gidan da sauri har ƙafafuna suna sarƙafewa, sai da na cire daga layin gabaɗaya kana na sauƙe wani wahalallan ajiyar zuciya.
Sai da na yi tafiya mai nisa amma ko ciniki naira biyar ban yi ba na nema waje na zauna ina huta gajiyar da na kwaso. Na tallafe kuncina ina bin bokitin kunun da kallo. A ƙalla na yi zaman mintuna ashirin kafin na yi cinikin naira ɗari biyu na kuma yin naira ɗari, har hantsi ya fito ba a ƙara saya ba, hakan ya sa ni tashi na ɗaura a kaina na fara bi gida-gida. Gida guda ne suka saya na hamsin. Cikin fargaba na nufi gida ganin ranar ta fito ta take ta yi ƙwal, da ƙyar nake iya ɗaga ƙafata saboda gajiyar da na yi lis tun daga nisa idanuna suke gano mini wata shirgegiyar mota a fake a ɗan nisa da gidanmu. Na lumshe idona na buɗe don tabbatar da sahihancin abin da suke gano mini.
Sai na yi kusa kafin na gane Amira ce da wani tsaye a jikin motar suna fuskantar juna sun ƙurawa junansu idanu kamar za su cinye juna. Kai tsaye zuciyata ta fassara irin kallon da irin kallon da malamin littafin ahalari ya faɗa mana, kallon da addini ya haramta. Gefe guda kayan tallanta ne a kusa da ita. Jikina ya yi sanyi ƙalau ganin har ta sayar da duk tulin wainar da tun fitowa ta alwalan asubahi Sahura take tuyawa.
"Amatullah".
Ta ƙira sunana yayin da nake gab da shiga cikin gidan, na juyo jikina a sanyaye. Ta yi mini ishara da hannu akan na zo na isa wajen tare da sallama ɗauke a bakina suka amsa na gaishe shi ya amsa yana kallona.
"Masoyi ga aminiyata ko ma na ce ma Æ´ar uwata sunanta Amatullah". Ya jinjina kansa"ma sha Allah, Amatullah sannu". Kafin na amsa Amira ta riga ni faÉ—in"Amatullah ga Mansur wanda nake ba ki labarinsa".
Na ɗago kaina ina satan kallonsa caraf idanunmu suka sarƙafe na yi hanzarin janye nawa kafin na ce"sannu da zuwa, ai kuwa ta na yi mini labarinka. Allah ya wanzar da alkhairi a cikin alaƙarku".
"Amin ya Allah". Duk suka haɗe baki wajen amsawa da shi kafin ya ce"ya kuma kika dawo kunun nakin bai ƙare ba?".
"Na yi mantuwa ne na zo É—auka". Na ji bakina ya furta ba tare da ya yi shawara da zuciyata ba.
"Amatullah kenan ke dai akwai zurfin ciki. Ba kya son kowa ya san halin da kike ciki". Na wurgawa Amira da ta yi zancen harara kafin na zarce da cewa"kin ga ni ba na son dogon magana. Sai kin shigo, Mansur na bar ku lafiya". Ya washe baki har kunne ya zaro wasu kuɗi daga aljihunsa ya miƙa mini"to ƙawarmu ga wannan a sayi kayan kwalliya".
"A'a na gode Allah ya ƙara azurki".
Na furta ina juyawa na bar wajen don na gaji da kallon da yake mini, na shige gida daidai sanda ake ƙiran sallan zuhur da Umma muka fara yin kato za ta fita gani na ya sa ta komawa da baya tana ƙare mini tanadin kallo.
"Me nake gani haka? Amatullah yaya da haka kuma?".
Na sauƙe bokitin daga kaina na miƙa maka cinikin da na yi ina ƙara wa da cewa"Umma an saya fa wallahi, kin ga ma cinikin da na yi". Ta firge kuɗin ta na irga su kafin ta yi magana yaro ya yi sallama ya shigo da kayan tallan wainar Amira Umma ta bi robobin da kallo da ina da tabbacin ganin su wayam babu komai a ciki shi ya fi komai jan hankalinta.
Sahura ta fito daga ɗaki tana rangaɗa kuɗa"Allah kai ne abun godiya. Maraba da ke ƴar azurki irin albarka har kin sayar ki dawo". Ta yi furcim sa'ilin da Amira take shigowa tana tafiya ɗaɗɗaya tana taunar cigam da yake ba da sautin ƙas ƙas.
"Umma ni ce fa ko kin manta alƙawarin da na yi miki ne? Ai waina ko na dubu hamsin za ki yi min sai na sayar da ita". Ta ƙare zancen tana miƙa mata kuɗin ta irge su a filin tsakar gidan cas ta lale su, lamarin da ya baƙanta ran mutane da yawa ciki har da Ummata da take ta faman ciki tana batsewa. Na tabbatar takaicin da ya zo mata har wuya ya yi mata tsayiwar ƙayan kifi a maƙoshi shi ya hana ta furta ko da baƙi ɗaya illa ƙwafan da ta yi, ta fice daga gidan. Na bi ta da kallo har ta fice kafin na ɗauki bokitin na shiga ɗakinmu na cire hijabina na fito na yi alwala na koma na yi salla nan kan sallayar na zauna don na san yau kam babu batun zuwa na islamiyya tun da Umma ta sa ƙafa ta fice.
Ban san lokacin da bacci ya sure ni ba sai da na soma jin ana bubbuga ni tare da ƙiran sunana. Na buɗe idanuna a hankali har suka yi tar akan fuskan Amira da take tsaye a gabana. Da ƙarfi ta miƙar da ni tsaye ta ja ni zuwa cikin uwar ɗakanmu, na fizge hannuna ina murtsike idona.
"Wani irin wulaƙanci ne haka Amira? Ina baccina za ki zo ki tashe ni ki wani jawo ni ɗaki".
"To jarabu ki yi haƙuri mana taimako za ki yi min". Ban amsa mata ba na ja tsaki na zauna na kafe ta ido. Ledan hannunta ta zazzage akan gadon Umma ta ɗago dogayen riguna biyu.
"Ta ya ni zaɓan wanda ya fi kyau da tsaruwa za ki yi a cikin waɗannan. Mansur ne zai zo mu fita shan ice cream". Ta ƙarƙare zancen tana wani lumshe idanunta.
Ta kufule na ce"akan wannan shi ne za ki tashe ni ina baccina? To ki saka duk wanda ya yi miki". Na miƙe zan fita ta riƙo hannuna.
"Ki tsaya mana haushinki fa nake ji ma in ba ki sani ba, amma duk da haka na zo neman shawaranki". Na ware idanuna akan ta"haushin me ye? To ma me ye na yi miki?" Na ƙwace hannuna daga riƙon da ta yi mini.
"Mussamman na zaɓo ki kamar tumu, a yaran gidan nan gabaɗaya ke kaɗai na ba wa damar ganin Mansur amma kika zo kika wani haɗe rai. Har ya yi miki kyauta ki ƙi karɓa don wulaƙanci".
"To kuma sai aka ce dole in ya mini kyauta zai na amsa? Na ga dai kar addu'a na yi muku da fatan alheri. To me ye kike so bayan hakan?".
"A bar maganar nan, ni dai yanzu ki duba min rigar da zan sa". Na wafce rigunan ina jujjuya su kafin na ce"ki sa wannan shuÉ—in za ta yi miki kyau sosai". Ta daka tsalle"haka Mansur ma ya ce da ya kawo min su".
"Kina nufin shi ya saya miki?".
Ta ɗaga mini gira guda"ƙwarai kuwa". Kafin na dawo daga mamakin da na faɗa ta kuma cewa"bari na je na saka na dawo". Ba ta jira abin da zan ce ba ta karɓa rigar ta fice cikin zumuɗi da tsantsan farinciki. Mamaki ya hana ni motsawa daga inda nake har sai da na jiyo sallamar Umma na fito ina yi mata sannu da zuwan da ta yi kunnen uwar shegu da ni.
Na ɗauki hijabin da ta cire ina ninkewa na furta"Umma ina kika je kuwa da ranan nan?". Kaman ba za ta amsa ba sai kuma can ta ce da ni"gidan Malam mai laƙanin sa'a na je". Na dakata da abin da nake yi"Umma ke kuwa me ye kika je yi?".
"Kukana na kai gidan mutuwa, na je na ƙarbo taimakon buɗewar ƙofar nasara akan sana'ata. Don ina da tabbacin Sahura ma a nan ta karɓo na ta laƙanin".