Sashe 51
Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ai ba kai kaɗai ka haifa yarinyar ba Manniru don haka babu inda zan je, komai a gaba na za ku tattaunawa. Ai ni ma ina da iko akanta kamar yadda kake jin kai ma kana da cikakken iko akan ta". Umma ta yi zancen cikin isa da izgilanci da ƙyar Umman Amira ta shawo kanta ta yarda ta fita daga cikin ɗakin, ya rage daga ni sai Abba a cikin ɗakin har zuwa lokacin kuka nake yi duk da ban san abin da yake faruwa ba amma na yi imanin duk abin da zai sanya Abba shiga makamancin irin wannan tashin gami da furta zafafan kalamai ba ƙaramin abu ba ne.
Ya zauna a kusa da ƙafafuna ya kafe ni da ido lamarin da ya ƙara sanya jikina yin sanyi ƙalau don bai taɓa yi mini irin wannan dogo kallon ba.
"Amatullah".
"Na'am Abba". Na amsa muryata a kashe tamkar wacce aka sanya igiyar kirtani aka shaƙewa wuya tamau.
"Amatullah ki na ɗaya daga cikin jerin matan da na yarda da su a cikin rayuwata kuma na yi imanin ba za su taɓa cin amanata ko su kunyata ni ba. Tun ranar da kika zo duniya aka cirewa mahaifiyarki mahaifa sakamakon irin wahala da azabar da ta sha tun daga rainon cikinki har izuwa lokacin haihuwarki. Ya tabbatar ba za ta sake haihuwa ba a duniya haka ni ma inda ba wata macen na aura to ba zan sake haihuwa ba tun da an raba ta da mahaifa, tun daga lokacin na yuƙurce a raina cewar zan tarbiyyartar da ke na ba ki kula na ba ki ilmin addini ta yadda za ki zame mini madadin ƴaƴa goma a gare ni, kuma alhamdulillah haƙiƙa na cika da farin cikin a yau ganin kin haddace littafin alƙur'ani akan ki babu abin da zan ce Allah sai dai godiya. Amma me yasa kika zaɓi ki jirkita min wannan ranar ta farin ciki zuwa ta baƙi ciki da kasance rana mafi muni a gare ni?".
Bai ba ni daman cewa wani abu ba ya ci gaba da cewa"Allah ne shaidana domin ba ya bacci yana ganin duk abin da yake na zahiri da na baɗili. Ya san na kula da amanarki da ya ba ni daidai da rana guda ban taɓa barin ki kin sauƙa daga tafarkin addinin da Manzon ya zo mana da shi ba. Amma Amatullah me yasa kika zaɓa ki saka min ta wannan hanyar? Me yasa kika zaɓa ki shayar da zuciyata raɗaɗin baƙin cikin da ba zai taɓa bari na yi rayuwa cikin farin ciki da walwala ba?". Na tuntsire da wani irin kuka mai ƙarfi numfashina har ɗaukewa yake yi.
"Amatullah likita ya tabbatar mana da cewar ki na ɗauke da ciki a jikinki na tsawon sati biyu, Uwata wa ya yi miki ciki?". Mutuwa zaune na yi don cak numfashina ya ɗauke na wucen gadi na dawo da ni da gawa ba mu da maraba. Na ji duniyar gabaɗaya tana juya mini ban dawo daidai ba sai na ji sauƙan wani abu mai zafi a fuska da ya ratsa dukkan sassan jikina wanda ina da tabbacin ruwa Abba ya watsa mini a fuska. Na ci gaba da wani irin kuka wanda ya yanayin da irin zafin da nake cikin a ƙirjina ba na jin akwai kalmomi da za su wadatar wajen fassaruwansa. Duk yadda na so na yu magana baki ya ƙi ba ni haɗin kaina furta abin da yake yi mini ƙaiƙayi a cikin raina. Hankalina ya kai ƙololuwan tashin ganin hawaye suna zuba daga idanun Abba ya sukunyar da kansa ƙasa ba tare da ya ƙara cewa da ni komai ba. Tun ina yin kukan idanuna suna zubar da ƙwalla har sai na da idanuna suka kafe tsiyayar da komai.
"Abba". Na furta cikin wani iriyar muryar mai cike da rauni haɗi da maɗaukakin tashin hankalin da ya jirkice da rashin nutsuwa, shuru bai tanka mini na ƙara ƙira a karo na biyu nan ma shuru ina jijjiga shi na ga ya faɗi a ƙasa idanunsa sun kakkafe bakinsa ya koma gefe guda.
Na É—aura hannu aka na fasa ihun da ya sanya su Umma faÉ—owa cikin É—akin tamkar an jefo shi.
"Innalillahi wa inna ilahirin alaihir raji'un! Me ya same shi?". Anty Sawwama ta jefa mini tambayar da na gaza amsa wa illa kukan da nake ji jikina yana rawa.
Yaya Alhassan da Malam Aminu suka ɗaga shi suka kwantar da shi akan gadon da na tashi, Umman Amira ta fita ta ƙira likita ya shigo ya umarce mu da duk mu fita. Sai dai ni kam na kasa motsa ƙafafuna daga inda nake tsaye duk da jan hannuna da Amira take yi kamar za ta fincike shi daga gangar jikina. Ganin halin da nake ciki ya san likitan da kansa cewa a ƙyale ni haka suka fita suka bar ni a wajen, na ja saƙararran gangar jikina na isa na durƙusa gaban gadon da Abba yake kwance na riƙe hannunsa ina murzawa a hankali. Likitoci suka rufu akan sa suna ta ƙoƙarin ceto rayuwarsa domin har jijjiga ya fara aka ɗauko wani abu kamar dutsin guga ana danna masa a ƙirjinsa.
Sun ɗau lokaci a haka har sai da komai ya daidaita aka maƙala masa roban numfashi.
"Ki yi haƙuri ki tashi ki fita waje, in sha Allah zai sama lafiya kamar yadda kike gani ma ai yanzu da sauƙi". Likitan ya furta cikin sanyin harshe da sassauta amonsa. Na cira kai ina kallonsa"don Allah zai tashi kuwa?".
"Me zai hana shi tashi? In sha Allah zai tashi ya sama lafiya ya ci gaba da gudanar da rayuwarsa tamkar babu wani abun da ya taɓa faruwa".
Ban ce da shi komai ba na kuma fashewa da wani kukan ina murza hannun Abba da yake cikin nawa. Lokacin guda har fuskarsa ta faɗa tafin hannunsa ya yi sanyi ƙalau kamar wanda aka ɗaurawa ƙanƙara.
Aka bankaɗo ƙofar ɗakin na waigo ina ganin Umma da ta faɗo cikin ɗakin a fusace tamkar kububuwa tsoro ya mamaye mini ƙalbina, kafin na yi wani yunƙuri na ji ta rufe ni da duka da ko'ina ana ƙoƙarin raba ni da numfashina. Ta buga kaina a jikin ƙarfe gadon take jini ya ce sallama Alaikum ya fara malala kamar da bakin ƙwarya. Da ƙyar likitotin suka ɓanɓare ta daga jikina duk da hakan bakinta bai fasa furta mini mungayen kalmomi ba.
"Allah ya isa tsakanina da ke Amatullah. Da haihuwarki irin ki gwara na rayu har na koma ga mahaliccina ba tare da na yi ko ɓatan wata ba, da na san haka za ki zame min annoba da tun ranar da kika zo duniya na murɗe miki wuya kin mutu kowa ya huta, na tsane ki na tsani kallon ki. Da wannan abun kunyar da kika ɗauko mana gwara a kawo min gawarki a gaba na hankalina sai ya fi kwanciya".
Na rarrafo na zo na riƙe ƙafafunta"don girman zatin Allah Umma ki yi haƙuri kar ki furta mini kalmar da za su jirkita tunanina. Umma ki ba ni dama na yi miki bayani wallahi ƙaddara ce ta faɗa mini...". Tun kafin na ƙarisa ta sa ƙafa ta yi bol da ni na faɗi gefe guda, babu shiri na saki ihu saboda zafin da na ji ya ratsa har cikin ƙoƙon kaina.
"Ke ba ki da hankali ne? Idan kika ji mata ciwo fa? Ko me ta yi ai kamata ya yi ki bari sai kun je gida ko kin manta cewa nan asibiti kuma a cikin ɗakin majinyaci kuke kike wannan hayaniyan. Ku tattara ku fita waje don ba ma buƙatar hayaniya da ɗaga murya a nan".
Likitan ya yi zancen cikin ƙololuwar ɓacin rai da takaicin abin da Umma ta aikata, Umman Amira da Anty Sawwama suka shigo suka fitar da Umma Amira ta ɗago ni likitan ya ce na fito a bar Abba ya huta muka je wani waje a cikin asibitin aka yi mini dressing ɗin goshina da yake zubar da jini. Ana gamawa Anty Sawwama ta ce mu tafi gida Yaya Alhassan zai zauna a wajen Abba kafin a ga abin da hali zai yi.
"Anty don Allah ku yi haƙuri ku bar ni a nan...". Kafin na rufe bakina ta katse ni"kar ki yi gardama da ni Amatullah ki wuce mu tafi". Ban ƙara cewa komai don ban ga fuskar hakan daga gare ta ba. Malam Aminu da Yaya Alhassan da Muhammad Taukif suka iso wajen a tare duk su ukun suka jefo mini wani matsanancin kallo. Ba kamar Malam Aminu da har cije baki yake yi, shi ya fara tafiya bayan Anty Sawwama ta zabga masa godiyar ɗawainiyyar da ya yi.
"Anty na ga kamar ku ma tafiya za ku yi ko zan sauƙo a gida. Daga nan ni ma sai na wuce". Muhammad Taufik ya yi zancen idanunsa akan Anty Sawwama.
"A'a É—an nan tun da lamarin nan ya faru kake É—awainiyya da mu, kai ka kawo mu asibitin nan mai tsada a cikin motarka sannan ka biya kuÉ—in komai da komai, É—awainiyyar ai sai ta yi yawa ka yi tafiyarka kawai za mu hau motar hanya".
"Mahaifina ya umarce ni da na tsaya akan lamarin wannan baiwar Allahn nan har sai na tabbatar da cewar komai ya warware. Don haka ina roƙonki da ki taimaka mini wajen cika umarnin mahaifina". Shuru Anty Sawwama ta yi kawai tana jijjiga kanta kana ta ce"shikenan to mun gode". Suka yi sallama da Yaya Alhassan bayan sun yi musayar lambar wayan juna ya yi gaba muna biye da shi a bayan, a Umma da Umman Amira tunin sun tafi gida.
Kamar motar gawa tun da muka shiga babu wanda ko tari har muka isa gidan, Anty Sawwama da Amira suka yi masa godiya ni kam na kasa cewa komai illa kallon juna da muke yi ni da shi.