← Book details Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 58

Sashe 29

Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tsam Maman Ummi ta sha ruwan jikinta ta koma yin wasu ƙananan maganan, ta zo ta ɗaga Ummi suka wuce ɗaki suna cin alwashi akaina. Kaina kawai na jijjiga har yanzu ban sauƙo daga dokin zuciyar da na hau ba na wuce ɗaki, na wuce Umma ba ta ce da ni komai ba shiryawa na yi na fice islamiyya.

Kaina a ƙasa tun da na fito daga gida har na isa islamiyya ban ɗago ba, raina cike da takaicin da kuktun abin da Ummi ta yi mini. Babu shiri na saki wata doguwar tsaki mai matuƙar sauri tunawa da na yi zancen Abba na barin mu gidan izuwa yanzu kam ya sha ruwa. Ban yi aune ba na ji dirar wata baƙuwar murya a cikin dodon kunnena da ya tursasa mini tsayawa cak tamkar gunki.
"Ke uban waye kike yi wa tsaki?".

Na bi mutumin da kallo cike da tsoron da ya yi wa birnin zuciyarta dirar mikiya. Muryata a shaƙe na ce"ba da kai nake yi ba bawan Allah".
Ya yi ƙwafa"Allah ya taimake ki". Daga haka ya ja zugan ƙafafunsa ya bar ni cike da tarin mamaki da al'ajabin da ya tsaya mini a rai. Lalle sai yau na ƙara gaskata cewa mafi yawan mutane yanzu a fusace suke ainun.

Haka na wuce islamiyyar na samu har Malam Suleiman ya shiga ajinmu, da hanzari na ƙarisa na shiga na zauna na ciro alƙur'anina na soma karatu. Haka muka fito salla muka koma ajinmu har mun fara karatu Malam Suleiman ya aiko ya ce duk ƴan ajin sauƙa su je filin salla yana son ganin su. Duk muka ɗauki jakakkunanmu muka nufi filin kasancewar an kusa tashi ma a lokacin, ba mu daɗe da haɗuwa ba ya zo shi tare da Malam Aminu, Malam Suleiman ya fara yin jawabi mai kama hankali.

"Mun tara ku ne a nan akan sauƙarku da kullum yake ƙara gabatowa, akwai abubuwan da makaranta ta shirya yi muku domin taya ɗalibanta murnar haddace littafi mai tsarki. Cikin abin da makaranta ta shirya har gayyato manyan malaman domin su zo su yi muku nasiha da nusar da ku hanyar da za ku yi amfani da ilmin da kuka samu ta hanyar da ta dace, hukumar makaranta ta zauna ta yanke hukuncin turawa Sheik Dawood Gaskiya dokin ƙarfe a matsayin babban malamin da zai halarci walimar sauƙan ku".

Ras! Na ji gabana ya yanke ya yi wani mummunan faÉ—uwa. Babu shiri na É—ago kaina ina kafe Malam Suleiman da idanu tamkar magiji ko kuma yau ce rana ta farko da na fara yin tozali da shi a cikin rayuwata.

"Sheik Dawood Gaskiya dokin ƙarfe".

Na maimaita a cikin raina zuciyata cike da tarin fargaba. Babu shiri na dafe ƙirjina da dukka hannayena saboda tsananin bugun da yake yi, take na ji zuffa ya soma keto mini. Idanuna suna hasko mini zanen hotonsa tar ina gani tare da wassafa kalamansa da ya furzo mini a cikin kwanyata. Maganar da Malam Suleiman ya ɗaura da shi shi ya yi silar fizgo hankalina da ya yi nisa daga gangar jikina zuwa gare ni.
"Babban mutum ne a ƙasan nan da ma nahiyar Afrika gabaɗayanta. Mutumin kirki ne ƙwarai da gaske kuma mutunci da dattakunsa sun kai matuƙa ba ya wasa da duk wani lamarin da ya shafa addininsa komai uzurin da yake cikin idan aka yi masa irin wannan gayyatar haƙiƙa yana amsar ta. Ta yadda ko mai sama damar halalta ba ya kan wakilta ɗansa ɗaya tilo namiji ya zo a madadinsa, sai da ku kun yi sa'a shi da kansa zai zo walimar yaye ku ba aike zai yi ba, don haka muna son ranar ku fitar da mu malamanku da kuma makaranta da kanta kunya".

Take wajen ya rikice aka soma yin kabbara babu ƙauƙatawa, ni dai ina zaune inda nake rungume da jakata ko motsin kirki na gaza yi balle na bi ayarin masu yi kabbaran.
"Za mu ware ɗalibai uku da za su yi karatun littafi mai Tsarki a ranar daga cikinku, wanda kuma suka kasance masu ƙwazo ne da basira haɗi da mayar da hankali akan karatunsu. A cikinsu kawai Al'amin Yakubu, Aliyu Shehu sai kuma Amatullah Munnir".
Ras! Na ji gabana ya yi wani mummunan faɗuwa da hakan ya haifar mini da runtse idanuna, wajen ya ɗau shewa abokan karatunmu suna cike da farin ciki don a ganin su wanda aka zaɓa ɗin duk sun cancanta. Na buɗe idanuna a hankali ina kallon maza biyu da suka fito suka tsaya kusa da Malam Suleiman wanda ni ko sanin fuskokinsu ban yi ba, kasancewar ajin maza daban haka nan ma na mata, wajen alwala da salla ma nasu daban da na mu ba ma haɗuwa da su sai in an tashi yayin tafiya gida.

"Amatullah ki tashi mana ki je ke ma".

Na tsinkayo amon Ammi yayin da take zare jakata daga runguman da na yi mata, tamkar kazar da ƙwai ya fashe mata a ciki haka na tashi duk jikina babu ƙwari na fita na tsaya wanda hakan ya ba wa Malam Aminu ɗaurawa daga inda ya dakata.
"Waɗannan su ne ɗalibai uku da za su yi karatu yayin walimar yaye ku, kuma a cikin su muke saka ran samu na ɗaya, na biyu da kuma na uku". Kan ka ce kabo wajen ya ƙara kaurewa da kabbara ni dai ina tsaye ne kawai a wajen amma hankali da nutsuwata ba sa tare da gangar jikina.

Kafin a watse Malam Suleiman ya ce gobe yana buƙatar ganin mu da wuri kafin a shiga aji, muka amsa da to. Kafin ta sallame kowa har muka fito daga cikin makarantar babu abin da ake tattaunawa sai batun zuwan Sheikh Dawood. Ko jiran Rauda da Ammi ban tsaya yi ba na yi tafiya don ji nake tamkar ba zan isa gida ba, ina so wa kuwa kai tsaye na wuce ɗakin su Amira na iske Ummata zaune a ƙofar ɗakin na tsuguna har ƙasa na gaishe ta kafin na shiga ciki.

"Amira na shiga uku".

Na furta a razana cikin rawar murya da take bayyanar da tsoron da ya yi wa ƙalbina naɗin huhun goro. Tsam ta tashi daga inda take zaune ta kamo hannuna muka shiga uwar ɗaka.
"Sanar da ni me yake faruwa Amatullah? Rasuwa aka yi?". Na girgiza mata kaina alamar a'a.
"To me ye faru?".

Tiryan-tiryan na kwashe duk abin da ya wakana na sanar da ita daga farko har ƙarshe, ba tare da tsallake ko da jimla guda ba. Dogon tsaki ta saka kafin ta soma furzar da takaicin da na yi silar cusa mata.

"Yanzu akan wannan abun ne kika bi duk kika É—aga hankalinki?".

"Dole hankalina ya tashi Amira ko kin manta yadda muka yi da shi, a tasha ne?".

Ta musguta kafin ta furta"ban manta komai ba, amma yadda malamanku suka suffanta muku kirki da mutumcinsa a ido duniya shin hakan kaɗai bai isa ya wanke zargin da zuciyarki ta ɗisa miki akan sa ba?. Ya kamata fa izuwa yanzu ki manta da duk abin da ya faru, babban mutum ne a ƙasan nan kuma yana da girma a idanun mutane, ko zuwan da zai yi walimarku ma ai ya isa ya sa ki ji kin nutsu akan kasancewarsa mutumin kirki".

"Amira babu wani zancen da zai sauya abin da na gani da idanuna kuma na ji da kunnuwana. Tabbas akwai wani ɗabi'a da mutumin nan yake aikatawa a ƙarƙashin ƙasa wanda ba ya son duniya ta sani, ko kuma in ce yana amfani da girmamawan da mutanen suke yi masa wajen lulluɓe wannan sirrin".

"Wani mutum kuke magana akai? Kuma wani sirri yake ɓoyewa?".

Zancen Umman Amira suka yi wa ƙofofin kunnuwanmu dirar mikiya. Duk muka cira kai muna dubanta tana tsaye a ƙofar ɗakin ta kafe mu da ido tana jiran amsan tambayoyinta.
"Umma ba fa wani abu ba ne, wai wani malamin islamiyyansu ne fa ta gani tare da wata budurwa anan bayan layin nan suna tsaye. Shi ne fa duk ta bi ta tada hankalinta wai ta ji an ce yarinyar ba ta da halin ƙwarai".

Ta É—an yi jim kafin ta ce"Allah ya kyauta, ki tashi ka ga gawayin an kawo sai ki É—aura girkin kafin ya iso".
"To Umma yanzu zan fito". Ba ta ce komai ba ta juya ta fita hakan ya ba wa Amira daman faÉ—in"yanzu dai ki tashi ki je ki cire kayanki ki zo mu yi wa Mansur girki, don ya kusa isowa". Ban iya amsa mata da kalmomin baki ba illa gyaÉ—a mata kai da na yi na tashi na fita.
[9/29, 3:41 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE*

©️ Maimuna Tijjani Iyam

____________________________________

Page 2️⃣3️⃣

Kamar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki haka nake ɗaga ƙafafuna da ƙyar tamkar wacce ke tsoron taka ƙasa, kamar daga sama na ji an jawo hijabina ta bayana ya zarge mini wuya har sai da tari mai ƙarfi ya sarƙafe ni. Babu shiri na waiga don ganin wanda ya aikata hakan a gare ni bayan na yi kici- kicin fizge hijabina da aka damƙe.
Na yi turus ganin Ummi tsaye a bayana ta sha ɗamara a ƙudunta tana cika tana batsewa kamar saniya za ta kai bugu, sai da na yi ƙoƙarin daidai nutsuwa da numfashi da yak tsaya mini a ƙirji kafin na iya harhaɗo kalmomin da bakina ya furta cikin tsananin takaicin da ta yi sanadiyar cusa mini.

"Ummi lafiya? Me ye na yu miki haka?".

Ta galla mini wata uwar harara kafin ta furta"aw! Wai har kin manta kenan? To ba ri na yi miki tuni wallahil azim duk wanda ya ci tuwo da ni sai na tabbatar masa da cewar miya ya sha, tun da har kika yi kuskuren shiga cikin gonata sai kin yi kuka da idanunki".
Raina ya harzuƙa zuciyata ta soma tafasa take jikina ya soma rawa saboda tsabar ɓacin rai da kalamanta suke jefa ni, idanuna suka soma cikowa da ƙwalla.

"Ummi magana ta riga da ta mutu a tsakaninmu, don haka ki bar ni haka na sarara. Babu ni babu ke babu ruwan biri da gada".
Chapter 29 · 0% Book details