← Book details Ciranin Amana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 58

Sashe 7

Ciranin Amana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai satar kallon yaron da ta Goya a bayanta da towel yakeyi Wanda yake bacci hankali kwance,da hannu ya tambayeta wannan dan natane?ai kuwa tace ae tare da murmushi tana kara jijjigashi,shareta yayi still tana tsaye a wajen sai buga game dinsa yake
cike da nishadi ko wannensu,gashi ta gama kasheshi da dariya kamar wata namiji yanda takeyin abu,a ransa yana gata me kyau she need to change her character wa zai aureta a haka,
Yaron dake bayanta Wanda take cewa little boy shine ya farka daga bacci,
Ido 4 sukayi da me kyau da yaron nan yaron ya buga kara tare da cewa Daddyna kayyi(kalli) nayi new Anty tace na daina zagin mutane,ta hau dani keke,da yifan(Lifan) har ma zaneni tayi Dana jageka(zageta), murmushi me kyau yayi Wanda ya jawo hankalin Amana kansa ta kura masa ido tare da jinjina kyau irin na wannan mutumi.
Yaron dake bayanta ta kwance ta saukeshi,da gudu ya tafi wurin me kyau,me kyau kuwa sai kallon yaron yakeyi yanda Amana ta fasa masa Baki tare da kumbura masa fuska,
Da sauri Amana tace my boy ina zuwa Jakarta ta dauko ta zaro wasu chocolate masu dadi guda 4 da sweet ta mikawa yaron,sai murna yaron yakeyi yana new Anty zakijo jidanmu?murmushi tayi tace yes,yace mu dinga kwana taye kina kaini cukul(SCHl) OK my Boy zanzo insha'allah,bye Amana ta dagawa yaron hannu tayi tafiyarta gabanta sai faduwa yake sakamakon me kyau da take gani kusa da ita,sai da ta bar wajen ta samu saukin zuciyarta ta daina bugawa.

Wurin Manager ta koma shima ya gama game dinsa suka wuce take away ya siya itama Amana ya siya mata ya sauketa a gida kana ya wuce. Shi kuwa me kyau securities ya wa Umarnin su zo akai yaronsa hospital a dubashi, ana ta jin labarin me kyau,
waye me kyau?

Me kyau dai Amana ce ta sa masa suna amma asalin sunansa ALIM USMAN MUSA,Babansa USMAN MUSA DA MAHAIFIYARSA FATIMA asalinsu yan Ethiopia ne,shi yasa idan ka gansu kamar wasu larabawa don a Ethiopia ma su daban ne kalar nasu kyau ya wuce na kasar Ethiopia,
Gaba daya dangin Fatima da iyayenta du suna kasar Ethiopia,

yayin da family Usman na jini suke a Nigeria,sabo da su dama su Usman Baban Alim da kannensa su Biyu a kano aka haifesu,anan suka taso suka girma har Sukayi karatun degree suka gama,dukiyar su ta gado ce tun asali su masu kudi,sun gaji dukiya,basa aikin Gomnati sai zallar business,Usman duk yafi yan uwansa kudi nesa ba kusa ba,sabo da yafi yan uwansa neman kudi,
Babar Usman wato kakar Alim,da kannen Usman Haj Sameera da Alhj Ishaq da iyalansu suke zaune a birnin kano cikin shahararriyar g.r.a shi kuwa yayansu Usman Musa sabo da harkokin tafiye tafiye da business ya koma Lagos da zama tare da matarsa da yaransa, Haj sameera tana auren wani engnr da yaranta maza uku mata biyu, sai Alhj Ishaq yaransa bakwai maza 5 manyan samari sai mata biyu,ko wannensu mata daya daya garesu,babu me biyu,kuma alhmdllh suna zaune lfy suna zumunci cikin so da kaunar juna,kasancewar matar Ishaq yar kano ce basa shiri da fatima matar Usman,

Sameera ma kanwar Usman basa shiri da matar Usman saboda da bata kaunar dangin mijinta kaf,Fatima bata son kowa ya rabesu har Babar Usman wato Haj khadija,suna kiranta Hajja, Usman zuwansa ethiopia wajen sauran danginsu a nan Allah ya hadashi da Fatima kyakyawar mace ya aureta har Allah ya azurtasu da yara.

NURA shine na farko 38yrs yake yana da mata zainab da yara biyu mace da namiji,yana zaune a Finland can yake aiki tare da iyalansa, sai ALIM me kyau yaro da kudi yafi kowa kyau a gidansu,ga dukiya da Allah ya azurtashi dasu,yayi degree da masters nasa a harkar kasuwanci a Germany, 31yrs yake, ASIYA 25yrs take wata uku kenan da gama degree dinta a London, sai Ameer Wanda yake Finland wajen Nura yana karatunsa yana level 2,21yrs yake kuma shine auta.

Ranar da yan fashi suka tare Alim kano yaje wajen danginsu ya dawo yan fashi suka taresu har Amana ta taimakeshi,
USMAN MUSA Baban Alim dattijon arziki ne,me hakuri da kyauta tare da son talaka,duk inda ake Neman mutumin kirki to azo wajen Usman Musa,
HAJ FATIMA kuwa Sam bata da mutunci ko kadan,bata son talaka,bata kauna wani ya rabi yaranta musamman Alim da yake me kudin gaske,
Bata kauna taga yaranta maza suna son wata mace don kar ma ta kwace mata yara,kishi takeyi sosai da matan yayanta maza,Nura ita ta zabo masa mata yar gidan wani kusa a Nigeria, bata kauna taga Nura na nunawa matarsa soyayya wai zata kwace mata yaro,sai ta dinga kishi,da farko da ta sa Nura ya auri Zainab sai murna takeyi ganin Nura bai son Zainab,kasancewar zainab ta gari ce sai ta sace zuciyar Nura,ganin Nura na nunawa zainab so tace lallai sai ya saketa,Nura kuwa yaki yarda haka Abbansu ya nemawa Nura aiki a Finland ya turashi can da iyalinsa,sai bakin ciki Mum Fatima takeyi,

Amma tace duk ranar da Nura ya dawo Nigeria dole ya saki matarsa Zainab,shi yasa Nura yaki dawowa Nigeria,yana son zuwa amma halin Mahaifiyarsu bazai barsu ba,Abbansu ma ya ce kar ya dawo,shi kanshi halin Fatima matarsa na damunsa,yanda take wulakanta danginsa da Wanda ya rabesu gashi yana kaunar matarsa,addua kawai yake mata Allah shiryeta.

Alim yaro da kudi,babban dan kasuwa ne na gaske,sosai yake neman na kansa,bai dogara da kayan wani ba,da kudinsa yake harka,me kwazone da basira tare da zafin nema,ya mallaki dukiya da kadarori masu matukar yawa tun yana 17yrs yake Neman nasa yana karatu yana business.dan Jari Abbansu ya bashi me yawan gaske ya fara juyawa,kafin kace me Allah ya albarkaci abin.

Kyakyawan gaske ne na karshe,fari ne sosai sai kace dangin turawa,idanunsa ma dara dara masu kyau wasu Golden kamar irin kalar na mage shi ba na mage ba,irin dai na turawa,gashinsa kuwa baki ne sosai me santsi da kyalli,girarsa kuwa wow har hadewa takeyi,hancinsa siriri ba sosai ba,normal hanci me matukar kyau,bakinsa karami da shi red, habarsa yar doguwa,dauke da siririn saje da dan gemu kadan,sumar kansa ya tarata da dan yawa gyaran gashin sa ma abin kallo ne,

jikinsa me yar kiba ba ramamme ba kuma ba me kiba ba,gashi karkarfa da damatsa,kirjinsa me fadi sumul dashi,gashi dan dogo dashi ba da yawa ba,yatsunsa kansu abin kallo ne da birgewa,namiji ne na gaske ko ina Alim ya shiga sai ya haske wajen,Amana idan ta tsaya kusa dashi duk da cewar itama yar farace amma sai ta tashi a chocolate me hasken gaske lol,

Alim mutumin kirki ne na gari ga hakuri da kawaici,me kyauta,ba ruwansa da duniya,baya magana sai da dalili,idan zakuyi 1wk tare da Alim indai ba muhimmin abu bane to baza kaji maganarsa ba,ko a cikin danginsa iya gaisuwa ke hadasu sai su kwana 2 basu ji yace ko hi ba,yafi yin magana da hannu,ido,etc amma bakinsa baya magana sosai,shi yasa Wanda basu sanshi ba sai suce kurma ne,haka frnds dinsa sai su yini tare amma daga gaisuwa baya kara cewa komai,

Best Frnd dinsa Mubaraq shima wani hadaddan handsome chocolate ne yaso ya canja halin rashin magana na Alim amma ya kasa.Mubaraq dan gidan wani minister ne a Nigeria,kuma shi lawyer ne,sosai Alim yake kaunar Mubaraq, shima Mubaraq haka.
Halin Mum fatima kuwa abin yafi yawa a kan Alim domin kuwa sai da ta tursasa Alim Auren mata har guda biyar tana sawa ya sakesu dole,

Matarsa ta farko da mum dinsa ta aura masa Salma ce baya sonta yana kyautata mata,ganin haka Mum ta ce dole ya saketa ko ta tsine masa,haka ya saketa yanzu haka Salma ta auri wani mijin tana zamanta lfy, Ramlat Mum ta kara aurawa Alim itama baya sonta,amma tana hutawa,nan ma Mum ta koreta, Sakeena ma hakan take,sai Maryam itama tasa aka saketa, ta biyar itace Nusaiba itace wacce Alim ya dan fara Sonta har yayi saduwar aure da ita ta samu ciki,itace Alim ya hada dabara sai suka dinga nunawa Sam Alim azaba yake nuna mata,shi yasa Mum ta kyaleta tare da Alim,har cikinta ya isa Haihuwa ta haifi zankadeden yaronta me sunan Abba Usman suna ce masa Aabid,satinta biyu da haihuwa Allah yayi mata rasuwa,
Alim yayi bakin ciki duk da cewar ba wani sonta yakeyi ba Nusaiba yarinyar kirkice, shekarar Nusaiba daya da rasuwa Mum ta koma Ethiopia kasarta ta samowa Alim wata yar Uwarta Sageera,amma Sam Abban Alim yace wlh bazai aura ba,ya gaji da Halinta,tana sa dansa auri saki ganin Alim me hakuri ne,Abba yace idan ta sa Alim ya auri wata matukar bashi ya nemo da Kansa ba to taje ya saketa,shike nan Alim ya samu lafiya,
Sai dai Mum ta kulle a ranta baza ta bari wata ta kwace mata danta ba,haka kawai wata tazo ta cinye mata dukiyar yaro ba,

Yayinda take burin Asiya yarinyar kirki yarta ta auri miji na gari me sonta kajifa son kai.Aabid dan Alim a wajen Mum yake zama shi yasa Sam Aabid bashi da tarbiyya,saboda yanda take kaunar jikanta bata yi masa fada,
Ko kukansa taji ta dinga zage zage za a kashe mata jikanta,ko makaranta idan yace baya so to baza ta bari yaje ba,

Aabid ya gama lalacewa tun yana karami ya iya zagi da cin mutunci iri iri,shima baya son talaka wajen kakarsa Mum duk ya koya,Alim abin da ya dameshi wajen Mum yaje yace ta bashi Alim su zauna tare sabo da ya samu abokin zama a gidansa so bored yake.

Sabo da son da Mum kewa Alim ta yarda da kyar ta bashi Dansa Aabid,watan Aabid Uku kenan tare da Alim suna rayuwa tare,yau da suka hadu da Amana yaune birthday na Aabid ya cika 4yrs da haihuwa,yaune kuma Amana tayi maganin rashin kunyar Aabid,

Har ga Allah Alim yaji haushin Amana irin dukan da tayiwa dansa amma sabo da hakuri da kawaici irin nasa bai nuna ko ransa ya baci ba,kuma dama rashin kunyar Aabid ta dameshi ya rasa ya zaiyi dashi,amma gashi ya hadu da Amana ta koya masa hankali.

Ci gaban labari
Chapter 7 · 0% Book details