← Book details Ciranin Amana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 58

Sashe 10

Ciranin Amana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Alim da jerin motocinsa ne sukayi parking a gidansu,bayan an bude masa kofa ya fito cike da tafiyar nan tasa ta izza da kasaita sanye yake cikin wata farin yadi kal dinkin fitted ya amsheshi yasha kyau hannunsa dauke da wayoyinsa guda biyu yana latsawa,cike da yanga kamar bazaiyi magana ba yayi sallama a palon Abbansa,nan ya samu Abba yana shan fruits,har kasa ya gaishe da Abbansa,Asiya kanwar Alim ce ta shigo cikin shiga ta alfarma,wata shadda ce maroon a jikinta tasha aiki,laaa Ya Alim sannu da zuwa kallonta Alim yayi ke kuma yaushe kika dawo daga kano?jiya Na dawo,bro ina Aabid? Yana schl mana,ya Alim Ya Nura yace ya kiraka wayarka a kashe,zan kirashi later, ok ,Ya Alim? Tsawa ya buga mata ke kin dameni ban son surutu,shidai Abba yana jinsu har Mum ta Shigo,
Harara ta zabgawa Alim wato da ban shigo ba Abbanka kawai zaka gaisar ka wuce ko?am sorry Mum tsaki taja, nan Abba yace sarkin kishi aikinki kenan kishi.

Shuru tayi daga bisani tace dama haka zakace mana tunda sun nuna sunfi sonka, kallon Alim tayi tare da cewa Ina jikana? Murmushi yayi tare da cewa yana nan lfy yana schl.
Hirar Nura dake Finland suka farayi Mum kuwa daure fuska tayi bata kaunar ayi mata zancen Nura saboda ya gudu da matarsa yana Nuna mata so,sun kwace mata yaro suna cin kudinsa a banza ya daina sonta.

Alim shikam halayen Mum dinsu mamaki ke bashi,Asiya ma Sam bata kaunar halayen Mum dinsu,
Yau Sunday yaune Alim ya shirya domin kai Aabid wajen Amana saboda ya dameshi kan yaje wurin Antynsa.
Amana kuwa yau bala'i ya sameta sunyi fada da wani Igbo yayan manager sosai sukayi fada akan ya shafa mata wuyanta,
Zaginsa ta farayi Wanda ya fusata ya cafki boobs dinta a taron mutane,nan take Amana ta dauki kujera ta kwada masa a kai,sai jini tako ina,

Ba tare da Manager yayi tunani ba ya fesawa Amana mari har Uku tare da korarta daga wajen aiki. Ita Amana ba korar ce ta sata zub da hawaye ba illa irin yadda bro din manager ya shafa mata breast agaban mutane Wanda ba a taba kwatanta mata hakan ba,

Tun Saturday da yamma tana gida tayi kuka ta gaji har yau Sunday idan ta tuna Babansu Sulemanu Harka shi ya ja musu sai kaga Hawaye Na sintiri akan fuskarta idonta ya kumbura yayi jajir bata da wani kuzari,gashi wani marar Imani yana binta bashin dubu sittin 60 gashi kudin hayarta ya kare Dan Uzuri ba mutunci,abincinta saura kadan ya kare dama da aikin ta laru zata biya wasu don Dashi take son shiga dama sai ta samu ta rage wasu to gashi aikin da ta dogara ma dashi an koreta.

Addua takeyi sosai da nafeela kan Allah ya kawo mata mafita a wannan Al'amari,11am tana zaune a dakinta tayi tagumi hawaye Na zuba Dan Uzuri ya rufto dakin ko lura da Kukan da takeyi baiyi ba yace ke yar chakwaskwas kizo inji masu lokaci me kudin nan yana waje ya bar dakin da sauri kamar zai kifa.

Fuska Amana ta wanke idon nan a kumbure jajir dashi ta fito, Wanda ke binta bashi taci karo dashi,yana busa sigari yace ke yayane?kwana 2?ina kudin ne? Fuska a daure Amana tace kasan bazan ci ma kudi ba dama lalura tasa Na karba, ke yarinya naga kina wani masifa ne,mu zakiwa Jan ido dan me cin uwarki yanzu Na makeki kuma wlh gobe ba mutunci dole kibiyani,dalla ware banza, Amana yau dan tana cikin Bakin ciki ne da tuni an kwashi yan kallon,Alim dake mota sauran jerin motocin suna bayansa yana kallon Abinda ke faruwa, kuma da Alama fada sukeyi.

Tunda ta taho yake kare mata kallo yau salab salab take tafiya fuskarta ba annuri, ido ya kumbura Jajir haka ta karaso jikin motar kanta a kasa tana wasa da zoben azurfarta me matukar kyau.

AsmaBaffa
✳CIRANIN AMANA✳

35-40

By
AsmaBaffa

Ina ganin sakonninku ta ko ina readers ina godiya sosai.

Tun kafin a bude motar Aabid ya fara ihu da murna yana kiran New Anty,idonta cike da kwalla ta daga masa hannu,ganin zata iya fara kuka yasa ta yi saurin bude motar tare da daukan Aabid ta juya cikin sauri ta bar wajen,Alim kuwa yasan tabbas da gani tana cikin damuwa ba haka ya saba ganinta ba.
Motocinsu suka juya suka wuce direct office ya nufa,ita kuwa Amana yini sukayi da Aabid yana debe mata kewa,bakin cikinta ya yaye sai dai in ta tuna sai kaga tayi shuru kwalla Na Neman zubo mata,karfinta ya gaza,mace me raunice tunda ta taso cikin wahala take tunda ita ke ciyar da kanta,Sana'a kala kala da rayuwa duk tayi,gashi yanzu ba uwa ba uba ba wani Wanda zai taimaka mata ko tana kusa dasu baza su amfana mata komai ba,sai bacin rai da bakin cikin halayyar su,a rayuwa ta ya mace ace babu Wanda ya dau nauyinta,ita kewa kanta komai ,dole yanzu ta gaza kuma dole ta shiga wani yanayi.

Wajen magrib sukayi wanka ta shirya Aabid ta mayar masa da kayansa da yazo dasu tare da fesa musu turare,wani cornflakes ta hada musu ita da Aabid suka sha suka koshi,sunayin Sallar Isha wani ya shigo tare da sanar da ita ana kiranta a waje,

Aabid ta goya suka fita dan tasan bazai wuce Daddynsa ba,tana fita ta hango wata bakar mota me shegen kyau da tsada guda daya,da alama shi ya kawo kansa,wajen ta karasa yana zaune a mazaunin driver cikin shiga ta alfarma,kamshi da kyalli yakeyi,ba bata lokaci ta bude gaban motar ta zaunar da Aabid Wanda ke kuka shi wajenta zai kwana,da kyar ta lallabashi,haka kawai taji bakin cikin dake damunta ya dawo sabo dal,nan take ta fada tunanin rayuwarta bata da wani plan,bata ma San inda ta nufa ba,ita ba karatu ba,ita ba aure ba to waye ma zai aureta a haka,ga shi bata ma gaban iyayenta su Burunsu ta nemo musu kudi,ba ruwansu da halin da zata shiga,
Nan take zuciyarta ta kara karyewa ita waye ma zai so ta a haka yanda take kamar namiji,wani hawaye masu dumi da zafi ne suka shiga ambaliya a fuskarta,sheshekar kuka ta farayi ba shiri ta rungume Aabid kam kamar zata Fasa masa kashi taci gaba da kukanta a hankali,duk inda taso danne hawayenta da zuciyarta abin yaci tura,

Shuru kakejin motar babu Wanda yace ko ehem,kukanta kawai ne ke fita kadan.
Alim kuwa wani tausayinta ne ya lullubeshi da alama akwai Matsala babba tare da ita,bai ce mata komai ba illa bundle Na 1k dubu Dari kenan ya mika mata,Aabid kuwa shima kukan ya fara,yana Anty wane ya dakeki?

Ki fadawa Daddy ya fadawa sojoji,murmushin yake Amana ta farayi ga hawaye Na zubar mata har ta samu saukin zuciyarta,ba tare da ta kalli Alim ba cikin rawar muryar me kuka tace Na gode Allah kara budi ta juya tare da barin wajen tana share Hawaye.Alim yayi tunanin bai kamata yanda take kula da dansa ba ya kyaleta haka iya kudi kawai ya bata bai ji matsalarta ba,

Horn ya danna mata Wanda ba shiri ta juyo a firgice tare da dawowa wajen motar budewa Alim yayi tare da kiranta ta side din kofar sa,ya kai 5mnt tana tsaye gabansa ba tare da yayi magana ba,da kyar ya furta what's wrong with u?meke damunki?da kyar ta kalleshi kadan sannan tace ba komai Na tuna iyayena ne,suna ina parent din naki?ko sun rasu Alim ya tambaya.
Hawaye ne ya zubo mata sannan tace suna kano state, CIRANI aka turo ni lagos Neman kudi,
Da Sauri Alim ya zaro ido waje Ci...ra...ni? Kai ta daga masa tare da cewa yes,mamaki da alajabi ne suka cika Alim,yace aikin da kikeyi fa yau naje bakya zuwa?ae an koreni munyi fada da wani yana son taba min jiki that's y.

Tausayinta Alim yaji tare da cewa wannan Unguwar da kike a lagos bata mutanen kirki musulmai bace,gidan da kike zama Na karuwai nai,hmmmm aini na jawowa kaina tunda da yarda Babanmu ya kawoni cirani, Amana tace tayi shuru.

Damace tazowa Alim dan haka yace ko zaki Bini gidana Na baki aikin kular min da Aabid?matarkafa?cewar Amana,ta Dade da rasuwa,eyya Allah ji kanta, ameen cewar Alim,jeki gobe zan turo driver ya daukeki kiyi shiri.OK tnx Allah kaimu.
Nan ta wuce shima ya bar unguwar cike da mamaki.

Amana tana komawa dakinta tsalle, rawa,sannan tayi nafeela ta godewa Allah cike da murna ta fice kudin da Alim ya bata ta je a Daren ta biya bashin da ake binta,
Bayan ta dawo gida Dan Uzuri tayiwa bayani sannan ta bashi kyautar dubu goma sai murna yakeyi.

Washe gari da wuri Amana tayi shirin komai iya kayan sawa Dana kwalliya ta dauka kawai ta zuba a wata trolley da Manager ya siya mata kafin suyi fada,kayan girki etc kuwa duk ta bawa Dan Uzuri su.

Har kayan sawa ta bayar da wasu iya sababbi ta eba,har boutique taje ta kara siyo inner wears da wasu kayan ta shirya komai irin zata koma gidan yan gayu masu kudi.

Yau Abincin da Amana taci ma me tsada ne,tun 3pm take jiran azo a dauketa amma shuru har tayi la'asar shuru,sai wurin 5:30pm sannan wani driver da motarsa daya me kyan gaske yazo Duk Wanda Amana ta sani dake unguwar sai da tayi musu sallama,da ance unguwa zaki canja da zama? Sai ta yatsine fuska tana yanga sannan tace wlh kuwa Na gaji da zama a nan unguwar tayi min kauye da yawa,Na samu babban aiki a company, haka Amana ta dinga sambada karya kala kala ita dole big girl kar a rainata.
Chapter 10 · 0% Book details