← Book details Ciranin Amana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 58

Sashe 20

Ciranin Amana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Baba yanzu baza a kaini a matsayin Amarya ba?ke ya isheki Amana tafi gashi duk angwaye sun tafi mijinki ne kadai ya rage a garin nan.
Amana tana cin magani tare da kukan gulma wai dan kar ace batayi kuka ba ta fito har jikin motarsu taje Har khaleed driver yabi wata motar sun tafi cikin kano city,

Alim ne kwal a wajen,key din mota ya mikawa Amana me kuka,a ranta tace wato baima daukeni Amarya ba kenan, karbar key din tayi Alim ya Shiga gaba,ta zauna mazaunin driver ta fara tuki har suka bar garin Amana tukinta takeyi Hawayen karya nata sharara a fuskarta harda shesheka,
Har sukazo airport Amana bata daina kuka ba,Alim yana ta satar kallonta,ga driving ga kuka,frnds tuni suna jirgi ango da Amarya ma shiga jirgi sukayi khaleed ya juya gida da motar,
Amana ana lungu a kujerar jirgi har yau kuka takeyi tare da cewa Ashe tana kaunata,me sonace,Ashe kaunace zunzurutu Na dinga zaginta a banza,Ashe uwata ce nima,
Nima ina kaunarki ta kara fashewa da kuka,Alim bai gane kan zancen Amana ba,

Ashe Amana duk kukan takaici takeyi rannan da taji Mum zatayiwa Alim aure ta kwana tana zaginta kala kala,ashe ma itace amaryar,ashe Mum din Alim tana matukar kaunar Amana tunda har ta iya hada jininta da Na Amana.

Amana tunanin halin Mum ta shigayi yanda take sa Alim yana auri saki,kawai sai Alim ya kara jin kukanta tace shikenan bazanyi lasting ba,bazanyi inganci ba,
Shi dai baya gane me Amana take nufi,masu kula da cikin jirgi sai lallashin Amana sukeyi tunaninsu ko bata da lafiya,

Har suka zo lagos bata sani ba,motocin Alim Jere sun kai bakwai su suka kwashe tawagar ango,har gida wajen Mum dinsa aka rakasu,Har Amana sai wani rufe fuska takeyi saboda kunya
Mum cike da nuna murna da farin ciki Na karya ta tarbi Amana,

Yata kiyi hakuri kinji anyi aure ba tare da amince warkiba Na yaba da halayenki matuka shi yasa naji kwadayin hadaki da Dana,kuma shima Alim ya fada min yana sonki,haka Mum Alim ta dinga shiryawa Amana zancen karya iri iri,har sai da Amana taji ta yarda da Mum,

Su hajiya Talatuwa kawar Mum sun dawo suma,Talatuwa ita kadai tasan dalilin da yasa Mum tasa Alim ya auri Amana,Aabid yana makale a jikin amarya Amana, Mum ce ta sa ma'aikata suka fito da lefen Amana Na gani Na fada har akwati 9 babu abinda babu,wasu ma a Holland Mum ta hadosu,har mota aka shigar da akwatuna,Mum ta kalli Amana tare da kallon ledar da Amana tazo da ita,da wasa da dariya Mum tace wannan kayan fa daughter,Amana murmushi ta saki tare da cewa Umma Na ce ta bani nima ban San mene ba, Mum ce ta karba tare da dubawa kayan gyara Na mata ta gani,ingatattun magunguna,fakar idon Amana tayi ta dalla mata wata uwar harara tare da maka mata banzan kallo,a ranta Mum tace za a mallakemin yarona tsinanniya zaki ga yanda zan mai da rayuwarki,a fili kuwa cewa tayi yata wannan ai sunyi araha da yawa sai su lalata miki mahaifa,ki bari ki zauna yanda Allah yayiki sai mijinki yafi sonki,Amana baiwar Allah to Mum kawai tace,

Bayan sunyi sallar isha Abban Alim ya nemi Alim da Amana yayi nasiha ta gaske sannan yayiwa Alim tasu ta sirri,Asiya ma sai yabon irin kyan Amarya takeyi har sai da Mum ta maketa,

Aabid Alim da Amana haka aka rakasu har mota suka tafi gidan Alim,kowa yana murna da fatan alkhairi banda Mum da kullum cikin kulla sharri take,
Ma'aikatan gidan Alim kaf sun sa ido suga an kawo amarya su ga kalarta su sami abin gulma,sai sukaji shuru kawai Amana suka gani da Aabid da Alim,sai suke tunanin ba yau za a kawo Amarya ba,amma wasu maza daga ma'aikata sunzo da gulmar cewar sunji ance Amana itace matar da Alim ya aura,amma aka karyatasu ba a yarda ba ganin babu wata alama data nuna Amana Amaryace,kuma sunga da safe da ita Alim ya tafi gidan biki,

Amana kuwa suna shiga Palo Alim yace ina ledar hannunki da aka baki a garinku? Mum ce tace Na bata basu da inganci Amana ta fadi,mene a ciki?Alim ya tambaya,hmm nima ban sani ba amma naji Mum tace wai kayan gyaran matane,nan take Alim ya gano wato Mum kwacewa tayi dan kar ma ko ya kusanci Amana yaji wani dadi,

Baki ya tabe tare da cewa ke kuma sai kika tsaya sototo ta karbe ko?gaki da wayo amma kuma baki dashi,sai kiyi tayi ai.ga Aabid karbeshi yayi bacci zanje Na huta

Wanka sukayi gaba daya suka kwanta baccin gajiya Kowanne a dakinsa yake,washe gari dukkansu babu Wanda ya fita,haka sai ga yan aiki sun shugo da lefen Amana gaba daya,Suna zaune sai ga Mum da sassafe tayi sallama a gidan,da sauri Alim yacewa Amana dauki Aabid ki koma dakinki,saida ya tabbatar Amana ta shiga dakinta sannan ya budewa Mum kofa ta shigo tana faman baza ido,ko gaisawa basuyi ba tace ina Amarya,yatsina fuska Alim yayi tare da tabe baki yace Mum pls ki daina hadani da wannan yarinyar bana kaunarta,

Tana can dakinta nifa Mum duk cikin matan da kike aura mun babu wacce Na tsana kamar wannan yarinyar,bana kaunar ganinta Sam,da nasan zakisa Na aureta da bazan taba daukanta aiki a gidana ba,yanzu wlh kin jawo mata masifa da bala'i aiki zata sha ta zama baiwata kawai,.
Wani sanyi da dadi ne ya ziyarci zuciyar Mum,nan take tayiwa Alim sallama driver ya maidata gida,

Wata ajiyar zuciya Alim ya saki tare da kwankwasa dakin Amana ta fito tana fitowa ya sakar mata kayataccen murmushi tare da cewa Amarya yau bazaki hada mana break ba ko hutun Amarcinne,Amana dai kunya ce ta lullubeta,harda nunawa Alim Aabid karfa yajika tare da fadawa kitchen sai Murna takeyi

AsmaBaffa

Ina godiya kwarai readers luv u all,ina ganin sakonninku ta ko ina tnx.
[6/27, 9:25 PM] ‪+234 808 968 1079‬: ✳CIRANIN AMANA✳

75-80

By
AsmaBaffa

Alim suna ta game da Aabid har Amarya Amana ta gama shirya girke girkenta a dining sannan ta koma dakinta ta shige toilet ta feso wanka tare da cancada kwalliya cikin shigarta ta yau da kullum amma yau ta dabance wani burmemen wando 3qtr red da wata Riga T-shirt karama ko dankwali bata daura ba ta fito,su Alim ta hango a dining tun kafin ta karaso wajen Alim ya mata alama da hannu cewar ta juya ta canja kaya,

Tasan kayan da yake nufi dan haka ta cuno dan bakinta ta juya tana kunkuni ta canja shigar atamfa wata lemon green dinkin Riga da skert sosai tayi mugun kyau ta fito a Amaryarta,yau Amana cewa tayi sai ta daura dankwalinta nan ta fara kici ciki ta kasa kawai sai ta Dora dankwalin kawai a kanta kamar gyale ta fito haka,
Tana zuwa Alim yace ko kefa,zo...zo..da sauri taje wajensa,dankwalin ya zame a kanta,habawa nan yaga zallar baiwar gashi baki sidik yana kamshi da kyalli,
Amana kuwa gabanta sai faduwa yakeyi kasancewar namiji bai taba yi mata haka ba,

Shi kuwa Alim daurin dankwali ya shiga tsantsarawa Amana harda rera wakar barmani choge ....sakarai... bata da wayo,ai Amana dariya ta fara kyalkyalawa,Alim bai taba ganin dariyarta haka ba domin Amana ba komai ne ke bata dariya ba,
Tsayawa yayi har ta gama dariyar sannan ya daura mata daurin zamani kamar ta daura goggoro haka Alim ya Nada mata dauri,da sauri ta shiga bedroom din Alim ta kalli kanta yanda ta zama kamar sarauniya,

Fitowa tayi tare da cewa dan Allah a ina ka koyi dauri haka,ko a mata ban taba ganin wannan kalar ba,ba kin maida kanki namiji ba ta ya zaki San da wannan sakara kawai cewar Alim.tun daga wannan rana Amana ita ba abinda ke birgeta irin ta zauna taga Alim yana nannada mata dauri abin birgeta yakeyi yana bata sha'awa.sabi da haka yasa Amana kullum burinta tasa atamfa ko lace ko shadda ko material tazo wajen Alim tace Daddy ayi min dauri,shiko Alim ya zauna ya tsantsara mata dauri,kuma tayi tayi ya fada mata a ina ya koyi dauri yaki fada mata,

Amana tare da Aabid zaune a kujera tana taje masa gashi,Aabid ne yace Anty ki siyo min icecream gobe idan munje schl,Amana ce ta bige masa baki kar ka sake Na kara ji kace min Anty as from today Na zama your Momy, kunji fa Amana,Aabid kuwa ya rike gam Momy yake ce mata
Yau Amana sauri tayi kafin Alim ya fita Office tayi wanka tasha wani dakakken lace a cikin kayan lefenta ta fito main Palo Alim ma ya sakko cikin shirin sa zai wuce office da sauri tasha gabansa Daddy...Daddyn Aabid pls ayi min dauri,me zakiyi da dauri yanzu ke da Mum ke nemanki,kiyi sauri ki je wlh kafin ki shiga Matsala,cike da shagwabar da bata San ta iya ba tace to Daddy nifa kana gani ko schl banje ba yau saboda Mum tana nemana,kuma nace kamin daurin Na je kaki,kuma ma Allah ni bazan iya Driving ba yau muje ka saukeni a gidan,

Lallai yarinya baki San nufin Mum akanki ba,to ko driving karkiyi ta ganki a motata kinji Na fada miki,muje Jan hannunta yayi har dakinta,tsofaffin kayanta ya duba ya dakko wata doguwar rigar atamfa wacce take karama kuma ta kode ta jeme,yace sa wannan maza,ba musu ta yi hanyar toilet da sauri Alim ya jawota baya yace kut amma kinma raina ni dalla malama sa kayanki anan me zan gani,

Kunya sosai taji haka ta daura zani cikin dabara ta canja kayan,sannan ya dauko wani dark powder sosai ya shafa mata saiga Amana ta dawo baka baka tayi kalar wahala,kowa ya ganta zai rantse a cikin talauci take, oya yi kalar tausayi Na gani Alim ya furta,ai kuwa Amana ta wani langabe kamar Almajira, good ki yi acting ina zaluntarki,ina baki wahala a gaban Mum,karki bari Abba ya ganki a hakan,kuma zamu tafi amma zan saukeki ki hau taxi ta kaiki,duk abinda Mum zatace ki nuna wahala kike sha a hannuna,
Chapter 20 · 0% Book details