← Book details Ciranin Amana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 58

Sashe 54

Ciranin Amana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Amana da bacci a idonta tace rabu dashi ni Bazan je ba,Sakeena tace Anty ki tashi kawai,Badriyya ma ta mike tace kin san dai mazan nan akwai son kai kar yayi fushi ki tafi, ni da Huzaifa ne da tuni na tafi,
To a tsohon daren nan fadin Amana ....wayar Asiyace ta kara daukan ruri Alim ne again,Amana tace ita kam sai gobe zata koma,
Minti 5 saiga Alim ya shigo har cikin gidan Asiya ya gani ta fito zata koma dakinta yace tana wanne room?tace tana wannan room din,ai kuwa fuu ya bubbuga kofar,Amana ta zata yan biki ne ta bude ya figota waje da karfi,Amana ta zille tana hakki tace sai gobe fa zan dawo,kizo nan nace miki ko,Amana tace naki din,zagayowa yayi ta jikin kujera zai kamata,ta gudu jikin dayar kujerar,ya kara biyota,
Suka fara zagaye kujerun palon,ko wanne dake gidan nan yan biki kasa bacci sukayi suka tashi zaune Sabo da yanda ake ta guje guje da ture ture a palon wasu ma sun zata aljanune suka kara buya a room,

Alim ya kama Amana da kyar duk haki sukeyi,ya safa ta a kafada, kara bubbuga kofar room din da Amana ta fito yayi, Badriyya ta leko tana dariya,yace Sis miko min hand bag dinta da komai da tazo dasu,Ai kuwa Badrriya ta miko masa ya rike gyalen da Hand Bag suka bar gidan yasata a mota har gidansu yana masifa.

Suna zuwa ya kaita har Bedroom sannan yace nayi niyyar kyaleki kije Amma ni zaki raina ki tafi ba tare da Umarnina ba kan Mum tace kije,kin ma rainani ko? Shi yasa naje na dawo dake ta karfi naga kuma ta tsiya,ya karasa yana hucin masifa.

Amana taga ransa ya baci sosai tace to kayi hakuri shike nan ta juya ta kwanta shima haka can dai ya matsa jikinta tare da manneta tsam a jikinsa,Amana tana kwance ta kifa cikinta ta dago gwiwar hannunta tawa Alim elbow daya,da sauri ya matsa tare da rike wajen kirjinsa,harda Elbow ma akan kina Jin haushi na,Amana dai bata ce komai ba,taci gaba da kwanciyar ta,bai hakura ba ya kara daura hannunsa a saman bayanta,ba bata lokaci ta jawo hannun ta cikinta tare da ganya masa cizo,ba shiri ya dauke hannunsa,
Jira yayi aka dan dauki lokaci tunaninsa tayi bacci ya koma ya kara rugunmeta,kafarta ta buga masa a kansa kamar me magagin bacci,
Ba shiri Alim ya koma karshen bed ya kwanta yana murmushi a ransa yace masifaffiya akan na hanata kwana gidan biki,

Washe gari da safe Mum ta fara salati ganin Amana tana jera abinci a dining,amma bata ce komai ba har Amana ta duka ta gaisheta, Alim ya fito sanye cikin tsadajjiyar shadda kamar a saceshi sai kamshi yakeyi yana ta kallon Amana yanda take cika tana batsewa shi kuwa dariyar mugunta yake mata kasa kasa, tana kallonsa ta kara cika fam.

Mum kuwa abincinta ta Eba ta koma room dinta,Alim yana ganin ba Mum yace shirya na kaiki masifaffiya karki cinyeni akan biki,Amana cikin fushi tace bana so kuyi bukinku bazan je ba ka daina nuna mun ba yan Uwa na bane akan naje bikin gidanku duk duniya sai ta sani ka je ka daukoni cikin talatainin dare.

Alim yana kallonta har ta gama masifarta yace tooo Allah ya baki hakuri ni ba fada nake nema ba,shirya mu tafi,yatsina fuska Amana tayi Alim yace kinga kyan da kike min kuwa idan kina yatsina fuskar nan taki me kyau,
Fuska Amana ta hade tare da fashewa da kuka, wai tunda Alim yace tana kyau da yatsina fuska,shine ta koma kuka,Alim yace kaiiiii kinga kyan da kukan nan,ai ban San haka kike kyau da kuka ba kullum zaki dinga yi min?
Amana najin haka ta kama dariya,Alim yace kash kin cuceni mene zakiyi dariya ni nafi son kukan kinfi kyau dan yi min,ai Amana sai ta dinga murmushi me kyau wai dan kar Alim yaji dadi yaganta tayi kyau.

Alim baiji dadi ba ganin Amanansa na fushi dashi sai yayi dana Sanin daukota jiya,suna gama break yace je ki shirya mu tafi Amana ta makale kafada,bata rai yayi ban son musu jeki shirya na kaiki,
Amana da sauri taje ta shirya ta fito suka tafi,suna zuwa zata fita Alim ya riketa ki tsaya muyi Sallama mana,shuru tayi tana kallonsa,kiss ya manna mata a goshi tare da tambaya anan zaki kwana? Amana tace eh,kiyi hakuri kinji nazo da dare na daukeki kinji? Make kafada Amana tayi wai ita kwana zatayi,kin San bana iya kwana ba ke,kunkuni Amana ta kama masa cike da shagwaba,ni bana gane wannen kunkunin naki wa ya sani ko zagina kikeyi,kallonsa Amana take baki bude cikin shagwaba tace ya zanyi na zageka,naji to dan Allah nazo na daukeki? Alim ya fada cikin shagwaba tare da yin kalar tausayi,
Amana tace a'a ni gaskiya kwana nake so,
Alim ya kara magana nine fa Babynki ni din? Amana ta make kafada,kwafa yayi tare da cewa to fita ki tafi sai da safe,Amana ta fice,Dear Alim ya kira ta har zata shige gidan ta juyo daga nesa yace nine fa? Amana ta kama sheshekar kuka,ajiyar zuciya ya sauke yace to jeki jeki daina kuka,nine?ta daga kai wai eh,yace to bazan dawo na daukeki ba sai gobe jeki...yana kallonta ta shige gidan.

Alim kuwa driver ya tura airport ya dauko su Umman Amana da kishiyoyinta dasu Hamza harda zaliha da Salma.

Direct gidan Abba aka wuce dasu nan su Amana suka dinga murna aka basu masauki,sunci sun Sha sun huta sannan aka kaisu wajen Abba suka gaisa cikin girmamawa,su Nura da sauran dangi duk sun gaisa an San juna,
Mum ma gidan ta taho suka hadu da sauran dangi ana ta shagali,sannan ta bawa dangin mijinta hakurin abinda tayi musu wai su yafe mata,

Washe gari su Umma gidan Amana suka dunguma suka Sha kallon aljannar duniya,kwana biyu Alim baiga Amana ba,har gidan yaje sau nawa bata nan wai sun fita shirya wajen dinner,anjima kuma ace sun wuce gyaran jiki da lalle,

Haka aka gama biki lafiya aka kai Amarya Asiya kano a jirgi,su Umman Amana da sauran dangi kaf Amare suka bi a jirgi suka koma kano,

Kowa ya shirya ya koma gidansa,Mum kuwa idan suka hadu da Abba ma harara yake Dalla mata,ba fuska bare ta sa rai zai maidata dakinta,har hakuri taje ta bashi amma Abba ya kara ci mata mutuncin da ba shiri ta hada nata ya nata tace zata tafi kasarsu,Alim yace ta zauna dasu Nura ko a bata gidanta daban ta zauna su kai mata yar aiki da kyar Mum ta yarda,

Ai kuwa gida karami flat me kyau Alim ya bata tare da me gadi da kuma yar aiki mace,Mum ta koma ciki suna zamansu lafiya,
Amana kuwa ranar da aka tafi kai Amarya ranar ta dawo gida da kanta,

Tunaninta Alim zaiyi fushi da ita amma sai taganshi sai murna yakeyi da dawowarta,
Rungumeshi tayi ta fara bashi hakuri me kikayi?ai ni naga dama na barki kema kin San da ace banyi niyyar ba ko yini daya bazan bari kiyi ba,
Na kyaleki sabo da ki samu nishadi da yan uwanki da iyayenmu shi yasa,ki daina bani hakuri ma,

Cike da murna ta fara kissing dinsa,bai direta ko ina ba sai saman Bed,
Tun daga yanda Alim ya fara murzata Amana ta raina kanta، tun daga yanda ya shigeta Amana ta fara bada hakuri ta gane mugunta ya shirya mata ba hakura yayi ba,
Saida tayi kuka sosai,ranar kusan kwana yayi,Amana cikin kuka tace da ka min irin wannan hukuncin ai gwara ka zaneni wlh,
Murmushi Alim yayi bana fada miki ba bana son musu,na barki kiyi kwana daya kwana nawa kikayi? Amana tace Uku,da naje kullum ina kike zuwa ba izinina kike bin yan mata kuna yawo,su Badriyya duk suna gida sabo da suna daraja aurensu,missed calls nawa na miki kinki dagawa dan kar nace ki dawo,atleast kin San kullum zan barki kije amma kin tafi kinma manta da aurenki,

Duk wannan Bai isheki ba da kukaje dinner kin zage har da rabon take away maza na kallonki duk abinda kikayi ina zuwa na ganki na tafi,bai kamata na kyaleki haka bama kin bata min rai da yawa,kara fisgota yayi tare da furta bari na kara goge miki rainin da kike min,Amana kuka ta fasa sosai tana bashi hakuri,
Wlh bazan kara ba na tuba,dan Allah mutuwa zanyi idan ka kara yi,
Ko tafiya da kyar zan iya,ke kika jawo ban so na miki horon nan ba Amma ba kya ji duk ranar dana ce kaza kika min musu saina miki wanda yafi wannan,
Da sauri Amana tace Bazan ma kara ba wlh na daina,dama tsautsayine.

Daukanta yayi tare da mata wanka ya gasata sosai sannan ya shiryata ya kawo mata abinci taci ya bata magani tasha ya kwanta tare da makalkaleta a jikinsa yana ta faman bata hakuri,

Washe gari da safe warkai Amana ta tashi ras da ita,Alim ta duba baya gidan,short note ya bar mata kan mirror,

Sweet heart dina na tashi kina bacci ban son tashinki, naje office ina da meeting,yanzu zan dawo,ki kular min da kanki, love u.

Murmushi ta tayi a hankali ta furta honey kenan jiya ya gama min muguntarsa amma na tsorata ni yanzu ma lallabashi zan dinga yi tunda idan ya fara mugunta Bai San ya bari ba.

Sati Uku da biki Alim ya samowa Amana private university me tsadar gaske take karanta microbiology,
Amana ta kara Zama classic girl tayi wata irin wayewa,murjewa hade da gogewa,
Yau watanta Uku tana zuwa schl bata da wata matsala burinta kawai ta ji ta dauke da ciki,ta haifo Aabid dinta amma har yau shuru kakeji.

Alim yanda yake gwadawa Amana so da kauna ga tattali,baya son bacin ranta,itama haka,Amman duk da haka idan tayi masa laifi sosai yake mata fada.
Itama Amana ba sanya idan ya mata tana hakuri sosai ta kyale watarana kuma yasha masifarta dole ya lallasheta,
Dama zaman tare watarana hakane dole a samu sabani amma an fi so farin cikin ya ninnika bakin cikin,sai da hakuri dole,
Chapter 54 · 0% Book details