Sashe 33
Ciranin Amana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Nasan komai fa ba sai ka fada min ba Allah zai kawo mafita kaji sai hakuri,kwalla Alim ya share da sauri kar Amana ta gani,ita kuwa Amana ta gani amma sai tayi kamar bata gani ba,Naushinsa tayi kadan a kirji ba shiri ya saki kara ouchhhh.....be a man,u have to be strong fa muje ta kama hannunsa oya muje kawai,
Sun kara tafiya me Nisan gaske kamar zasu bar garin sannan suka isa wani dandasheshen wani gida dan karami harda gate yasha tiles da flowers.
Gidan ta kwankwasa wata dattijuwar mata ta bude tare da fitowa nan take matar ta washe baki tare da cewa barka da zuwa Hajiya,
Amana tace yawwa suka gaisa,matar Sa'adatu tace Hajiya lafiyar gidan kikazo dubawa domin nasan mun biya kudin hayarmu
Amana tace Sa'adatu wannan miji nane shine me gidan nan mun dawo zamu zauna a saman benen tunda dama iya kasan na Baku haya nace Ku dinga hawa kuna gyara min sama kar a bar mana gida da dirty,
Murmushi Sa'adatu tayi tace hakane komai yana nan tsab a part dinku wato upstairs,bari na kira mijina,
Malam Salisu ne ya fito suka gaisa cikin mutunci sannan Amana ta masa bayani ta kama Alim suka haura sama part dinsu,domin gidan part biyu ne,kasa 3 bed room ko wanne da toilet,sai Palo kitchen da toilet,saman ma haka take komai da komai. Sa'adatu da Malam Salisu sai yaransu 3 babbar macece yar 20yrs Iklima,kamal da Yahaya suna part din kasa.
Alim shi kam mamaki yakeyi Amana yaushe take da gida bari su huta zai tambayeta,
Suna shiga abin mamaki latest dubai furniture ne a saman yasha Alatu,sosai an kawata part din da kaya na Alfarma amma komai a rufe da ledarsu.
Amma Sabo da Sa'adatu na gyara shi kullum ta kulle da key kal kal komai suke sai kamshi ko ina ke yi kasancewar Sa'adatu me tsafta ce.suna shiga ya shige bedroom kalar bed din sun birge Alim tafiya yayi da niyyar fadawa bed din domin ya gaji caraf Amana ta damkoshi tare da jawoshi baya tare da kakkabe masa rigarsa wai zai bata jikinsa,
Ledar dake lullube da katifa ta kwaye nan ta leka kasan bed din fes dashi Sa'adatu na daga katifa ta share da moping,sip ta bude ko ina bedsheet ne kalakala sun kai 5 masu kyau ko wanne room da kalolinsu,duk ta da musu turaren ajiya a ciki sai kamshi sukeyi,share room din tayi tare da moping cikin zafin nama dan babu abinda babu a part din na amfanin gida komai Sabo kamar sabuwar Amarya nan ta shimfida bedsheet wani Mai kyau na gaske,room freshner ta fesa da turaren wuta ta kunna, toilet ma ta kara wanketa fes fes, kafin kace me room din ya dau kyau, palo ta fito Alim ta hango a tsaye yana ta layin gajiya sai rufe ido yakeyi gashi Amana ta hanashi zama wai zai bata kayansa,
Ido suka hada ta kashe masa ido daya tare da jan hannunsa ta kaishi har kan bed din riga ta cire masa da wando daga shi sai tight da singilet sannan tace oya slip kafin sallar isha bari na kara sa aikin,sai binta yake da kallo wani farin ciki ya cika masa zuciya.
Ficewa tayi haka tabi ko ina a upstairs part dinsu ta cire ledar kayan ta gyara komai ta share ta goge ta kunna kamshi sannan ta kunna Ac ta duka dakunan kasancewar da wuta tuni gida ya dau kamshi,waje ta fita ta siyo taliya spagetti da kayan miya hade da danyen kifi harda indomie da kayan shayi da wasu abubuwan na amfani da babu,direct kitchen ta shige kamar kitchen din Amarya komai na harkar kitchen akwai kayan abinci ne kawai babu fridge ta kunna ta zuba lemuka da ruwan robar da suka siyo sannan ta fara girki, ko gas babu sai kerozine da ta siyo ta cika katona resho ta,ta kunna miyar jajjage tayi tasha kifi ta dafa taliya sai coffee da ta hada ta cika musu flask ta shirya abincin a dining sannan ta gyara kitchen din kamar ba a ciki tayi girki ba,toilet ta fada a dayan bed room din wanka tayi sosai,
Ba sallah takeyi ba tana fitowa gashinta ta busar da hand drier da ta taho da ita a jakarta sannan ta shafa lotion dinta ta shirya cikin wata gaunt iya gwiwa me dogon hannu peach color toilet ta koma ta wanke kayan data cire tare dana Alim data cire masa ta Shanya su.
Zama tayi ta rangada kwalliya sai kamshi takeyi sannan ta dauki jakarta ta koma dakin da Alim ke ciki,tana shiga ta tadda shi ya tashi sai mika yakeyi da salati bakinsa dauke da addua
Sabulu da sabon soso ta kai masa toilet sannan ta dawo ta zauna kusa dashi ta zo zata rungumeshi Alim ya buga tsalle ya ja baya,
Tana dariya tace lfy? Murmushi yayi yace rana ta dake ni dazu ga tafiya munyi da kafa nayi dirty ai sai ki shafi dirty na,
Amana tana murmushi ta karaso kusa dashi suna facing juna tace see u kaji kamshin da kakeyi kuwa zaka ce kayi dirty,babu me cewa kayi wani tafiyar kasa,come here joooo ta afka tare da hugging Alim harda cusa kanta a kirjinsa tare da manna masa kiss normal babu wani canji saima kamshi da yakeyi,
Brush da toothpaste ta mikawa Alim to maza yi wanka ka fito tare da mika masa towel ya shige ta rufo masa kofar.
Wasu sabuwar farar jallabiya da sabuwar singlet da boxers ta dakko cikin wanda ta siyowa Alim da taje cikin Kano hospital kai Baba shine suka je ShopRite ita da Sakina sai ta ajiyesu da nufin idan ta koma lagos zata bashi.
Yana fitowa ta mika masa mai me tsada da kamshi ya shafa sama sama,turarukanta ta mika masa ya shafa sannan cike da mamaki tambayoyi cike a zuciyarsa yasa kayan da ta bashi dai dai shi kamar an auna yayi kyau sumarsa sai sheki takeyi,comb dinta ya karba ya taje kansa,
Tunes ce ke kwakularsa Bai gama Shan mamaki ba saida Amana ta jawoshi Palo saman dining food flask hadaddun gaske nan suka ci suka Sha suka godewa Allah,
Kwanikan ta kwashe suka koma Palo ya jawo Amana jikinsa suka kwanta a kan 3seater suka mamuki juna domin a kan jikinsa ta kwanta,
Ga plasma TV Amma ba a hada kayan kallonba
Gashin Amana dake matukar fidda kamshi ya fara shafawa a hankali kana ya fara magana kasa kasa Amana tashi zaune muyi magana,ba musu ta Mike tare da Zama suna gugan juna,yace tambayarki zanyi duk wannan Abubuwan ina kika samosu wai I mean gida,food,kayan jikina etc.
Murmushi tayi sannan ta Mike tace ina zuwa bedroom ta shiga handbag ta bude ta ebo wasu takaddu guda uku ta fito dasu ta zauna kusa da Alim tace Babyna ba Abin mamaki bane,
Wannan gidan daka gani gidanka ne,sanda ina gidanka ina Kula da Aabid dina kana bani kudi masu yawa haka duk wata a accnt dina kana biyana kudi kafin a daura mana aure
Numfashi ta ja tace to da kudin da kake bani na sai maka wannan gidan har kayan dake ciki dalilina kuwa ko Mum tace ka sakeni nasan baza ka iya ba idan ma ka sakeni kaga sai na fada ma na dawo gidan nan da Zama har Allah ya dai daita komai,Ko iyayena basu San da gidan nan ba,Badriyya da Ya Hamza ne kadai suka sani domin su na turawa kudin nace su sai min gida,to sai suka ga wani ya gida wannan wai baya son gidan garin ya masa kauye da yawa shine suka fada min nace su siya min da shedu,
Takardar shedar gidan ta mika masa da sunan Alim da komai a jiki daya takardar ta kara mika masa ga wannan shi kuma takardar kayan da aka zubane gashi,kayan sawa dana Baka shekaran jiya munje kai Baba hospital Kano city na siya ma da niyyar na Baka idan na koma lagos suna cikin akwati da yawa gobe zan dauko ma a gidanmu
Abinci kuma kana bacci na siyo kayan dafawa na yi mana duk cikin kudin da ka bani dazu a gidanmu,
Mamakin Amana ya cika Alim gaskiya Amana macece ta gari duk da basu da kudi amma gashi Abin duniya Bai dameta ba,da wasu ne ai iyayensu da yan uwansu zasu bawa komai har cutar mijin zasu dingayi
Firgigit ya rufe bakinsa sakamakon Amana data hade masa su waje daya.
Mika mata takardar yayi yace wannan gida ni Alim na mallakawa mata ta halak malak shi ga takaddu rikesu,
Amana cike da shagwaba tace Allah Baka isa ba yaro dankwali yaja hula,kaza ta janye zakara kayi gida a garinmu wooooo
Dariya Alim yayi yace bazan karba ba kukan shagwaba Amana ta fara dole sai ya karba ita me zatayi da gida,ai bata fatan ta zauna ba a gidan mijinta ba,dole Alim ya karba sabo da rigimar Amana,sallar isha yayi da nafeela yaja Amana suka fada Bed nan Alim ya shiga romancing dinta ya fara magana da.....
Mum ce zaune gefen Abba ga su dan Auta,Abba ya kalleta yace Ina Nura ki fada masa gobe ya dauki matarsa su koma gidansa an karasa masa ginin gidansa anyi komai,nan take Mum ta hade rai tace yanzu duk Fadin gidan nan Alhaji sai kace sai sun koma gidansu fisabilillah,Aabid ne ya shigo room din tare da Islam yar gidan Nura,
Mum ce ta dauki jikokinta tace ai Ku muna nan tare daku ko? Aabid cikin masifa da kuka yace ni Bana sonki Momyna new Anty nake nema da Daddyna,make masa baki Mum tayi ta jefoshi kasa Ku fita yan iskan yara kunyo halin iyayenku.
Abba ne ya jawosu jikinsa ya fara lallashinsu sannan ya fara balbale Mum da masifa sosai,Dan Auta yace gaskiya Mum wlh bakya kyautawa ki dinga dubawa dan Allah.
Zakinsa Mum tayi ya tashi ya bar dakin amma Mum tace dole Nura da matarsa ma a gidanta zasu zauna baza su taba komawa gidansu ba,matar Nura har kuka tayi tace dan Allah Mum kiyi hakuri ai nan Mum ta kurma ihu da kukan karya tace matar Nura ce ta zageta babu wanda ya saurareta.