← Book details Ciranin Amana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 58

Sashe 18

Ciranin Amana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Baba yaso yayiwa Amana dukan tsiya kan ta karbi kudinsa amma sai ya tuna alkawarirrikan da tayi masa sai yayi shuru da bakinsa, yaune ranar da Amana zata bar garinsu,kananan kayanta duk ta rabawa su Badariya,su Umma ma sun samu T-shirt dai dai,Aabid ya dami Alim rigimar a kaishi wajen Antynsa ba shiri Alim ya turo driver guda daya da mota da safe da wuri yazo daukan Amana,sai kumburi Amana takeyi sai wajen 5pm sannan ta dauko akwatinta tabi driver suka taho cikin kano city.karfe takwas Na dare suka karaso gidan.
Aabid yana jin sallamar Amana ya fanfaro da gudun tsiya ya dafalfaleta,mutan gidan duk suna Palo banda Alim Wanda sun fita gari da Frnd dinsa khaleed,
Gaishesu Amana tayi ta tafi wajen Kaka can ta ya da zango sai hira sukeyi da Kaka,har tayi wanka Kaka ta kawo mata abinci sukaci tare da Aabid,
Alim kuwa tun safe yake jiran dawowar su Amana amma shuru har khaleed yazo suka fita.Amana har tsarabar Goro ta kawowa Kaka,sai murna Kaka takeyi Goro lafiyayye me yawan gaske,Matar Abba Ishaq kuwa da Haj Sameera kayan miya irinsu su kuka,kubewa bushashiya,gyada danya etc duk Amana ta kawo musu da yawa.

AsmaBaffa
[6/27, 9:25 PM] ‪+234 808 968 1079‬: ✳CIRANIN AMANA✳

65-70

By
AsmaBaffa

Tunda Alim ya dawo yaga ba Aabid yasan Amana ta dawo,washe gari da safe ma Amana bata fito ba a dakin Kaka taci abincinta,
Har yamma lis Huzaifa yaje yasa Amana tayi shiri sosai cikin wata arniyar shadda sky blue,suka fito sai kyalli sukeyi,khaleed da Alim suka gani a compound,
Da fara'a tace Daddy barka da yamma,ta kalli khaleed kadan tace ina yini tayi gaba abinta ba tare da ta jira amsarsu ba, Alim a ransa yace lallai ma yarinyar nan,
Khaleed yace wannan kyakyawarfa?yar uwarku ce? A Ina ka zama Daddy dinta?

Tabe baki Alim yayi tare da cewa Nanny din Aabid ce fa,Aabid yana ce min Daddy shine itama take fadamin,lallai ka iya zaben Nanny cewar khaleed,sai wurin 9pm Amana ta shigo ita da Huzaifa,yayi mata siyayya sosai,Alim suka gani shi kadai a Palo,ko me yake jira oho,
Yana ganin Amana ya sauke Ajiyar zuciya me karfi hade da mikewa ya bar palon,washe gari 6am escorts dinsa suka kwashi motoci suka dauki hanyar lagos, da Aabid jirgin karfe 5na yamma suka bi,Amana sai murna akeyi ana zare ido an hau jirgi,

Mintuna kadan suka sauka a Lagos wani Frnd din Alim Kamal yazo ya daukesu a airport,ya kaisu har gidan Alim ya wuce abinsa.
Gidan neat kal kal suka samu ko ina kasancewar yan aiki sunayin gyaransu,
Tunda Amana ta dawo ta shige dakinta suka sha bacci da Aabid washe gari ma haka Alim bai ganinsu Sam,

Kwanansu Uku da dawowa amma Amana bata kara sa wani atamfa ko lace ba damunta sukeyi,kayanta ta koma sawa,yau shirin wanka sukayi Amana sanye da Wando legins tight iya gwiwa da rigar ta tshirt armless irin doguwar nan ta kai Rabin cinyarta
Aabid kuwa dan pant ta sa masa ta jashi sukayi bangaren sweeming pool din gidan,
Alim suka gani zaune a kujera daga shi sai short ko Riga babu,yana karanta jarida yana kora lemo,towel dinsu Amana ta ajiye gefe,da fruits salad da ta hada musu,Aabid ta Goya ta shige cikin ruwan nan ba tare da suncewa Alim ci kanka ba,

Tunanin Alim Amana bata iya ruwa ba kawai sai ya hangota ta Goya Aabid tana iyo a ruwa kamar wata kifi,a ransa yace ita wannan komai ta iya kenan.
Aabid kuwa dariya yake ta bangalawa yau ya shiga ruwa,dama bai taba shiga ba,sun Dade ciki sannan ta fito zasu huta su koma,gaba daya bata sa bra ba rigarta duk ta manne a jikinta.
Alim gaba daya ya rude ya shiga wani yanayi ganinta a haka,kafe kirjinta yayi da kallo,yanda ko ya tayi motsi kadawa sukeyi,ji yake kamar ya cafkosu ya shafa,gasu shape dinsu gwanin birgewa,Amana fruits dinsu suke sha bata San me Alim yakeyi ba,Alim gani yayi Amana zata koma cikin ruwa kallonsa zai kare,kiranta yayi da sauri,
Amana! Wani iri Amana taji a jikinta babu abinda ke birgeta a rayuwarta irin taji Alim ya kira sunanta,sai taji kamar ta shide,cikin tafiyarta ta gadara da zafin nama ta karasa wajen Alim,shi kuwa Alim kallonsa yake ta sha yanda Na shanunta suke juyawa,

Ya kwashi wajen 10mnt baice mata komai ba,ita kuwa sabo da tasan yanayinsa baya magana a kan lokaci sai bata damu ba ta tsaya tana juransa,shi kuwa ba haka bane kallon kirjinta yakeyi a hankali saboda ya daga jarida nufinsa ita yake karantawa Ashe wayo ya hada kawai idonsa Na kan Amana ta saman jaridar.

Mikewa yayi daf da Amana kamar zai shige jikinta a zuwan shi tafiya zaiyi,Amana ganin kyaykyawar surar Alim yana kyalli yasa ta jin wani dummmmmm a kwakwalwarta,ta rasa gane mene domin bata taba jin hakan ba,

Alim yana sani yayi luuuu ya tafi zai fadi tare da dafe kansa yace ouch...da sauri Amana ta taroshi ya fado jikinta ragwajaf tare da sakar mata nauyinsa ai kuwa yafi karfin Amana nan take suka fada cikin ruwan gaba daya,
Sai lokacin hankalinsa ya dawo jikinsa sai ya fara tamke fuska yana cin magani tare da tsaki ya fice daga pool din,yana ta faman masifa,aikin banza daga kiranki sai ki jefani cikin ruwa,komai bakyayi A hankali kamar wata sakarai yaja tsaki tare da barin wajen cike da kunya.

Amana kuwa bata kawo komai ba tace masifaffan mutum,shuru shuru dashi sai masifa,Aabid ne yace Antyna Daddy baya masifa fa,to naji muje muyi wankanmu,komawa ruwan sukayi suna ta wankansu har suka gama,
Yau sati biyu kenan hutun makarantar su Amana ya kare sun koma schl,Mum Alim tun safe take damun Alim kan yazo fa akan maganarsu,haka ya hakura yaje har dakin Abbansa,

Bayan sun gaisa Abba yace Alim wata magana nake jin cewar wai ka tsayar da mata za a je Neman aure,kallon Mum Alim yayi,Mum kuwa ta daka masa harara ba shiri yace yeah Abba,amma a kano take shike nan Alim ka turo min driver ka jibi za muje nemo maka aurenta,cike da takaici Alim yace to Abba ya musu sallama ya bar gidan kamar ya kashe kansa tsabar bakin ciki,

Kwana tsakani Abba ya shirya tare da Amininsa da Mum Alim,sai driver dan rakiya,flight suka bi har kano suka dauki Alhaji Ishaq sukaje can garin da za a nemowa Alim aure,

Suka nemowa Alim aure kuma an basu yarinya tare da sa ranar aure nan da 1mnth domin Mum tace bata so a day lokaci sabo da shedan,
Mum Alim koda sukaje Neman auren mutuniyar kirki ta zama tare da kaunar talaka haka ta nuna,gidan Amarya sai yabon halinta sukeyi,basu San Mum tana da dalilinta,akwai abinda ta boye a kasa.su kuwa Allah sarki sai murna sukeyi gida ya rude sabo da jin dadi zasu shiga gidan Naira.

Bayan sun dawo Abba ya sanarwa Alim komai tare da yabon dangin Amarya,Abba yace son sai watarana kafin biki ka kawo min sirikata Na ganta,domin Mum dinka tace kana sonta sosai,Asiya kanwarku ma naji yanda take yabon halinta,haka Nura da Auta Sadiq ma naji sunce sun Santa yarinyar kirkice.
Alim dai cike da mamakin makircin uwarsu yace Hmm kawai,shi kuwa Abba ya zata kunya Ce kawai.

Amana kuwa harkar gabanta takeyi kawai daga schl sai karatu,zama da kawarta Rufaida yar gayu yasa Amana ta fara dan canja halinta ba laifi,
Mum tace baza ayi biki ba kawai aure za a daura amarya ta tare,

Biki ya matso Amana a bakin yan aiki taji ogafa zaiyi aure, wannan matar yana sonta ba zabin Mum dinsa bace,nan Amana taji tarihin Alim har auri saki da Mum ke sashi yi saboda bata so wata ta ci arzikinsa sai ita uwarsa da ta haifi abinta,
Ko yan uwansa Na jini bata kauna Alim ya musu kyauta sai ta dinga nuna kyashi da bakin ciki,

Bare Abbansa bata so ko hira taga sunayi da Alim saboda kar ya bashi wani abu,Abban Alim kuwa shima me arzikine, hassada ce tayiwa Mum yawa,shi yasa bata taba yarda Alim ya auri wacce yake so,shi yasa duk wacce tasan Alim bazai taba kauna ba har a bada to ita zata nemo ta aura masa.

Amana tana gama jin labarin taji wani bakin ciki da bata San Na mene ba ya taru ya cushe mata a zuciya,hankalinta ya tashi ta nemi farin cikinta ta rasa,a ranta saida ta tsinewa Mum Alim yafi dubu kan wanne dalili zatayiwa Daddy aure, bakin cikin Amana kenan.

Amana tana shiga Palo bata kula da Alim ba ta jefar da Jakarta a palon ta cire takalminta ta watsar cike da tsananin bakin ciki ta ja tsaki,nan ta fara zagaya Palon,da karfi tace a'a...wai mene haka ne eh....ina ruwana ma aikin banza aikin wofi,
Minti kadan ta buga kafafu tare da miko hannu kamar damisa zata damki nama tace saina ehhhhhhhhhh......shake tsohuwar nan.....can wani lokaci ta dakko ruwa ta kafa kai kwat...kwat...ta shanye tare da jefar da robar tace sai naci uwar tsohuwa wlh...tambadaddiya.....kodaddiyya.....sokayayya....me suffar hanjin ligidi.... Tayi dakinta da sauri ta fada bed dinta,Aabid ne ya shigo daga baya shi kam yaga Daddynsa wajensa ya nufa.

Ihun Amana su Alim sukaji sai karaji takeyi a dakinta,da sauri Alim ya bude dakin nata a kan bed ya ganta kawai wutsil wutsil takeyi tana karajinta tare da tsine tsine,Allah ya baki lfy cewar Alim yayi waje abinsa.Aabid yana a kafadarsa,
Ranar Amana da kyar ta iya yin wanka haka ta kwana ba bacci,sai asuba ta samu bacci,Aabid sai driver ne ya kaishi schl,amma Amana tace Sam ita bata da lfy.haka Amana ta yini da zazzabi,ga period tanayi,harda su amai tsabar bacin ran za a yiwa Daddynsu aure.

Alim kuwa tun yana damuwa har ma ya gaji gudun kar ciwo ya shigeshi a banza,frnds dinsa ma sun jajanta masa, sun tabbatar auren babu inda zaije.
Yau daurin aure saura 1wk Amana duk ta rame ita kanta bata San dalili ba,Alim kuwa ko a kwalar rigarsa indai irin wannan aure ne ya rigada ya saba dashi.
Mum kuwa burinta ya kusa cika,
Chapter 18 · 0% Book details