← Book details Ciranin Amana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 58

Sashe 46

Ciranin Amana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

gyara zama tayi suka fara kokawa sosai,garin fada suka tugewa Kaka dankwali Kaka tana mene haka ku bari lfy?saboda taga Amana harda kuka,Alim kuwa yi yakeyi Amma dariya ta cika masa ciki yanda Amana ta zage,Kaka ta daura dankwalinta,Amana tace Kaka kiyi hakuri kinga dai laifinsa ne ko,Kaka kuwa manne kanta tayi a jikin kujera tana gefe suna ta faman yi,Amana tace kai kai kai kai dannamin kashin wuya uhmm....zaka gani Amana ta Yakushi Alim ta cijeshi yayi kara da karfi,Kaka ta matsa sosai gefe suna ta yi,ganin haka kaka ta rabasu a tsakiya ta zauna a tsakiyarsu wai ta shiga tsakani, sai gashi sun tsallake kaka Alim ta gaban kaka ya zuro hannunsa sai ya taba cikin Amana,Ita kuma taki yarda shine suke ta faman kokawa,

Amana ta rike hannun Alim kamar kunama sai fasa masa cizo takeyi yana ta kwalla kara,Kaka tace yawwa jikata yi maganinsa,
Alim ya karbe hannunsa da kyar yasa dayan ya cirewa Amana gogoron da tasha wahalar sakawa ya ja gashinta da karfi,tayi kara Kaka ta sa hannu biyu tare da Dukan Alim ka haba ka bar yarinya ta sake,Driver da Asiya dariya kawai sukeyi saboda kowa ya kalli abin yasan ba fada sukeyi ba,
Amana tace nafi karfinka ko banza na cijeka da yawa kaifa me ka iya yimin ta karasa tana hakki kamar tayi tsere.
Alim ganin Kaka ce shi yasa baya Jin kunyarsa

Alim yace sai na ballaki kika kara yi min magana,Amana tace na gaba yayi gaba na baya sai labari,gobe i yanzu na tafi gida ina zaka ganni kuma kafin na tafi sai na tabbatar dana yi maganinka.

Ina ma da ne yaro da kagane shayi ruwane,Alim yace kanki ake ji,
Har aka je cece kuce akeyi,amma Kaka tasan da wata a kasa idan sun koma gida zata hadasu taji me laifi acikinsu,

Amana da Alim ba wanda ya kula wani har akayi party suka dawo gida,Kaka tace kuzo muje dakina zanji dalilin wannan shirmen da kukeyi a matsayin fada.

Suna dakin Kaka zaune a kasa Kaka tana saman Bed tace ke fada min jikata mene matsalar ke da mijinki? Amana tace ki tambayeshi,Alim yace ke dai ki fada,k a fada dai kai da akayiwa laifi,Alim yace in zakiyi bayani kiyi,bazanyi ba nan suka fara cacar baki,ita Amana mamakin Alim takeyi har yaushe yake da baki haka yanzu,

Alim ne ya gyara zama tun farkon haduwarsu da Amana da halin Mum da abinda Sulemanu yayi musu da sanadin rabuwarsu duk Alim ya kwashe ya fadawa Kaka yace Amma kaka sirri pls kinji iya mu dake,Kaka tace kaine da laifi baka kyauta ba,kasan da halin Mum Dinka dana Saude amma ka zargi matarka ba tunani ba komai,kayi kuruciya Alim ga matarka ta gari,kuma yanzu gashi kasan kayi laifi ba bincike ba komai maimakon ka fara bata hakuri da lallashi sai ka dinga fada da tsokana da yakushi,

Ke kuma jikata nasan yayi laifi bai kyauta ba kiyi hakuri ki dauka kaddarace,nan Kaka tayi musu nasiha sosai tayi musu fada sannan tace kar na kara ji da gani ya wuce daga yau,Amana a ranta tace tab yaci banza ma kenan wlh Bai isa ba,a fili Amana tace ya wuce Kaka insha'allah bazai kara faduwa ba,

Alim wani sanyi yaji da dadi a ransa marar misaltuwa,Amana ma taji dadi da sanyi sosai zuciyarta wasai saboda Alim baya zarginta yayi tunani ya San ta gari ce ita,

Alim ne ya kalleta tare da cewa Kaka kice ta biyani cikina,Kunne kaka ta toshe tace kai ban son shashanci,to wlh ta fadi inda ta kaimin ciki cewar Alim,Amana tace ciki ya zube ka auri wata ta haifarma ta Mike tare da ficewa,Kaka tace sai kayi aiki da lallashi fa,
Kaka yarinyar nan taurin kai gareta,nasan baza ta taba kulani ba shi yasa kika ga ina tsokanarta da fada,nasan tana da saurin zuciya shi yasa nake mata abinda zatayi magana in ba haka ba nine zan Sha wahala,
Koma me ta maka kai ka jawo ba tunani ba komai ka yanke hukunci cikin fushi,Kaka kishine wlh da shedan amma nasan Amana ba yar iska bace a virgin na samu abata cikin kwali a like,kaka tace tashi ka tafi marar kunya,

Fita Alim yayi tare da tunanin ta yanda zai bullowa Amana ta hakura,washe gari da rana Mum Alim ta sauka tana gadara da takama,

Amana ce ta shigo palon Mama tana neman Aabid,
Mum Alim ta gani zaune tana latsa waya,har gabanta Amana taje tare da tsugunawa har kasa ta gaisheta cikin ladabi,lfy kawai tace ta dauke kanta cike da mamaki dama jarabar yarinyar nan tana makale da Alim lallai aiki Bai kare ba,dole ta aikata lahira kowa ya huta.

Amana dama tasan abinda Mum zata mata kenan kawai sai ta Mike,Alim ta gani a bayanta ya harde hannaye yana ta murmushin Jin dadi an girmama uwarsa.

Ta gefen sa Amana zata wuce ya rukota tare da hadata da jikinta,wani so da shauki hade da shock sukaji gaba dayansu,Amana Hawaye ya cika idonta Alim ya kai bakinsa a kunnenta tare da cewa am so sorry ki yafe min kinji,missed u kwace jikinta tayi tare da ficewa daga dakin,Mum ta kalleshi tace kayi asarar halinka jibi yanda take tureka kana manne mata,Alim ficewarsa yayi baice komai ba,

Amana kuwa room ta koma tana share hawaye sosai ga wani sabon son Alim da yake azalzalarta,
Alim ma kasa Zama yayi ya rasa inda zaisa kansa matarsa yake so,kuma taki hakura
A ranar duk yanda Alim yaso suyi magana da Amana abin yaci tura,sam Amana taki ma yasan inda take,
Last party ma da zata je babu yanda baiyi ba ta kulashi ko ta saurareshi suyi magana ta kirki amma taki yarda
Duk hanyar dayabi ta tosheta, kukane kawai Alim baiyi ba,
Haka aka gama biki sannan suka dawo garinsu har Amare washe gari aka daura Aure tare da kai Amare abinsu shar komai yayi a gidansu.

Amana ta dawo gida washe gari da safe wanka tayi ta shirya tare da komawa baccin gajiya,Alim yazo gidan gaba daya sai da yabi dangin Amana da iyayenta wai su bata hakuri ta saurareshi,su kuwa kaf Alim nasu ne musamman yanda yake kyautata musu ba musu suka kwantar masa da hankali harsu Umma.

Gaba daya manya da yara tare da iyaye suka dungumo dakin Amana tana bacci suka tasheta,Amana gabanta ya fadi da ta gansu gaba daya,nan fa suka zauna zasu fara magana.

AsmaBaffa

Happy sallah to u all
✳CIRANIN AMANA ✳

175-180

Official

By
AsmaBaffa

Maza da mata iyaye harda yara ne suka sa Amana a tsakiya suka fara caccake ta, me fada nayi me masifa nayi me nasiha nayi da masu lallashinta yan yara kenan,
Amana tana jinsu a ranta tace lallai Alim ya gama siye dangina da kudi amma ai nafi sonsa daku ina son abina kuma nafi Ku farin cikin dawowar mijina wajena,a fili kuwa sai Amana ta fashe musu da kuka, Gwaggo ta hangame baki tace yau naji shashashar yarinya ana nema miki gata kina shirme, Umma ta hayayyako yo dan ubanta ma laifinsane ki duba sharrin da aka kulla miki har yau gaskiyar abin Bai fito ba amma ya dawo wajenki a haka zai mai dake amma kin tsaya shirme,

Hamza yace akwai me kaunarta irin wannan bawan Allah idan wani ne a take a wajen zai sakeki,yana da kudi ga mata nan ke kadai ce mace,
Kb ya fara ai ni wlh tana kin komawa wata rangadediya zan Nemo masa ya aura,Amana ce ta dago tare da gallawa Kb harara,Isa yace ga kannenta da yawa ai ya halarta ya rabu da ya mu bashi kanwa, Amana ta sigar wasa ta daki Isa a kirji,Haladu yace munafunfun ana so ana kaiwa kasuwa wai ke jan aji ko?

Wayar Hamza ce ta dau ruri Badriyya ce ta kira tana fada masa yanda Alim ke kiranta a waya ita da Sakeena akan su tayashi lallashin Amana.
Umma ce tace duk kuyi shuru zan yanke hukunci yanzu Amana dolene ki koma wajen mijinki jibi nace ya dawo jibi ya tafi dake kuma Umarni ne na baki a matsayina na mahaifiyarki,yanzu ma yana palo ki tashi ki shirya kije ko yanzu na turoshi nan,
Amana kamar zatayi kuka tace haba Umma wai mene haka.
Gwaggo tace kai kuzo mu fita karki koma idan kinga dama,mazan ma sai da suka tsaya tare da yiwa Amana nasiha sosai sannan suka fita,

Suna fita Amana ta Mike tsaye tare da daka tsalle ta fada kan Bed ta jawo pilo ta kanka me tana ta dariyar Jin dadi tare da furta Alhmdllh,ta kara mikewa tsaye ta daka tsalle tare da furta jibi sai lagos ko da kafar katako ne Allah kaimu,towel ta daura ta fada toilet,

Umma kuwa ganin Amana shuru taki fitowa taje wajen Alim kawai sai ta sa Kb ya rakoshi har dakin Amana,daga bakin kofa Kb ya juya,Alim daya shiga ciki karar ruwa yaji a toilet yasan itace take wanka,jikin kofar toilet din ya karasa tare da cewa na shigo? Amana tana jin muryarsa tace ya salam kai Umma,ji tayi ya kara magana nazo muyi wankan?Amana tayi banza dashi da wasa ya murda handle Amana cikin fada tayi magana basai ka shigo ba pls.
Murmushi Alim yayi tare da komawa kan bed ya kwanta yana shakar kamshin Amana.

Tana sani taki fitowa daga wankan ya dade yana jiranta har bacci ya daukeshi sosai sannan ta fito, saida ta leka fuskar sa taga bacci yakeyi sosai,ta fara kare masa kallo sanye yake cikin farar shadda dinkin Maza fitted domin Maza ma yanzu dai dai su suke dinki sai ya dan damesu,
Harda sa hula domin shi ba sosai yake sa hula ba Amma yau harda hula dai dai shi ya wani coko ta gaban goshi sawar yan gayu na zamani duk gashinsa me uban yawa gasu nan waje,yayi kyau sosai komai fari dama shi akwai sa farin kaya,
Chapter 46 · 0% Book details