← Book details Ciranin Amana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 58

Sashe 17

Ciranin Amana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Palo suka fito karo Na farko kenan da Amana taji kunyar mutane,kowa ya zubo mata ido,Baren ma Alim da yake kallonta kamar me,karasowa tayi a nutse ta tsuguna har kasa gaban Abba Ishaq da matarsa da Haj Sameera tare da cewa Ina yini Abba,kuna lfy?fuska sake ya amsa mata,haka tayiwa su Sameera ma,mazan samari da suke ta faman binta da kallo tace sannunku Ina yini,suma sun amsa da fara'a,ganin yan matan tayi ai sa'anninta ne koma ta girmesu,ga wani kallo da suke mata Na banza kawai sai ta sharesu ta mike tsaye,daya daga ciki wato Ikram tace mu baza ki gaishe mu ba?

Amana ce ta juyo a fusace tace hey mind ur tongue bana daukan nonsense,ta juya wajen Alim abinta sauran kuwa da mamaki suka bude baki lallai yarinyar nan masifaffiyace daga magana,su kuwa mazan birgesu Amana tayi ma,

Huzaifa dan gidan Abba Ishaq dake wajen yace bakuwace fa maybe ma ta girmeku Ku Baku kulata ba, tazo gidanku sai ita zata gaisheku,Kaka da Abba Ishaq sukace kyaleshu shashashai.
Amana kusa da Alim ta koma ta zauna a hankali tace ina Aabid,A hankali shima yace Aabid yayi fushi da ke,ni baza ki gaisheni ba?

Dariya tayi tace Daddy Kakace ta koya min fa,Kallonta Alim yayi yana jin wani farin ciki da ya rasa Na mene,ga kamshinta da kyan da tayi yana wani fusgarshi,
Alim da Amana hirarsu kawai sukeyi a palon an zuba musu ido kowa da abinda yake sakawa a ransa,

Abinci aka shirya kowa ya hau dining banda Amana da Kaka su basa zama a kujera,suna ci suna hirarsu,Huzaifa ma wajen Amana ya koma ya like musu,sai hira suke sha,Dan danan Amana ta saba da mazan gidan gaba daya banda matan,

Suna gama cin abincin Alim ya cillawa Amana Key din mota muje ki kaini gidan su khaleed Frnd dina ne.cafe key din Amana tayi tace wlh ni bacci nake ji ka nemi wani driver din, tun daga Lagos ko bacci banyi ba har kano kuma kace mu kara fita,

Palon gaba daya aka cika da mamaki mace ta tuko mota tun daga lagos har kano ansha mamaki tare da jinjina mata,Haj Sameera tace ke yan mata ya sunanki ma, sunana Amana, great name,Huzaifa yace lallai sunanki Na daban ne Baby Allah sa ki zama me Amana

Kaka tace ke kyaleshi muje kiyi baccinki,shi kanshi Alim fasa zuwa yayi yaje ya kwanta shi da Aabid,cikin dare Aabid ya dinga tsala ihu shi A kaishi wajen Antynsa,
Daukoshi Alim yayi har part din Kaka ya buga mata kofa ta fito,yace Aabid ke Neman waccen yarinyar,sai kaje ka kai mata tana waccen dakin,nan Kaka ta koma dakinta Alim ya shiga dakin Amana,

Da sauri ya runtse idonsa ganinta sanye da short wando da kadan ya rufe duwawunta,sai wata half vest a jikinta ta tale kafafu tana ta bacci,
da sauri Alim ya daura Aabid a bed din ya fice da sauri tare da rufo dakin.
Da kyar Alim ya iya runtsawa a ranar,washe gari da safe Amana ta hada kayanta Dana kaka ta fito can bayan gidan jikin wani panfo daga ita sai wata doguwar Riga me hannun vest,wankin kayanta dana Kaka take faman yi,

Mutanen gidan sai dadi sukeji tana girmamasu tsohuwa,Aabid yana kusa da ita,Alim yana sama yana kare mata kallo ta window,

Kwanansu Amana uku a kano,Alim yace tashirya zasuje ya kaita gidansu,Ta gama shirinta Na tafiya Garinsu wudil sai murna takeyi,
Motocin Alim gaba daya da escort suka jera zuwa gidan su Amana cikin yan tafiyar harda Huzaifa.

Amana tana ta driving dinta sanye take cikin wani rantsatsen lace Golden Colo tayi matukar kyau,Alim yasha arniyar shadda light blue fitted,Aabid kam English wear ne,Huzaifa ma ya chakare,jerawa sukayi har garin su Amana tun a hanya Alim ya fara sa ido yana dariya kasa kasa,zasu sha kallo yau.
Ana zuwa wata majalisa Amana ta tsaya da motar tare da sauke glass kasa tace hi guys Baaabaa Baabaa kuna sha'aninku,kallonta sukayi sosai da kyar suka iya ganewa Amana ce,Alim Huzaifa sai kallon ikon Allah sukeyi,ganin gungun samari sun yanyame motar ana ta kawowa Amana gaisuwa,haka Amana ta dinga tsayawa majalisa majalisa suna gaisawa,tace sai Na nutsu Baabaa akwai labari fa.

Har kofar gidansu ta tsaya sauran motocinma suka tsaya,Ko wa kallon irin rubewar da gidan yayi sukeyi,su Baban Amana suna waje sun zata shugaban kasane yazo wucewa,shi kanshi Baba kasa gane Amana Yayi su Alim gaba daya fitowa sukayi daga motar,mutane sun yanyamesu ana kallon turawa sunzo,wasu suce turawane zasuyi Titin kwalta,wasu suce ai makaranta zasu Gina,wasu sunce ruwan tuka tuka za ayi ko pampo,

Amana tace Allah taimaki Baba, Baba Amana ce fa,ai Baba kamar ya suma, Da karfi yace Amana yaushe kika zama haka ko takarar Gomnan Lagos kika fito kika ci bamu sani ba,ai Alim da Huzaifa Dariya suka kamayi,can sai ga Haladu da gudu yana haki yana zuwa ya dakumi Amana yace arniyar kasa wlh itace Dan ubanki ina wayata?

Matan gari sai leke sukeyi ta Katanga suna gulma gidan Baki sunyi kudi,Amana ta dawo da arziki harda sojoji masu take musu baya,Amana kafin ta shiga cikin gidan yan gidan kaf maza da mata yara da manya sun fito gaba daya kamar yaki,
Hamza babban yaya yazo wajen Amana yace shegiyar ban biyar Amana ta bashi hannu suka tafa tace How far man,Hamza a Abuja yake Cirani kawai sai ya juya harshe suka fara broken English pigeon shi da Amana,
Huzaifa da Alim dariya kamar su mutu,duk shuru shurun Alim kasa dannewa yayi.

Badariya yar kwalisa ita ta matso tace Banza yar kauye to ki shiga cikin gidan mana,kinzo da mutane kin barsu a waje,wajen Aabid Badariya taje tace kaga Bature amma wannan baya jin hausa,Fatar Aabid ta latsa da Sauri ta kalli Alim tace laushi wlh,dariya Alim yayi tare da cewa Badariya ko?tace laaaa dama kuna jin Hausa?a ina kasanni? Huzaifa ta kalla tace kuzo Na Baku wajen zama Ku kyale shashasha Amana,dariya Huzaifa yayi yace antynki cefa ko? Ae yayata ce amma Allah Amana bata da mutunci kaf garin nan an sani,yanzu ta balla mutum,
Amma fa tafi kowa hankali a gidan har Baba dasu Umma cewar Badariya, dauko mana tabarma mu zauna a waje kinga muna da yawa cewar Huzaifa

Wai wanne ne cikinku saurayin Amana?cewar Badariya,Huzaifa bai San me zai ce ba kawai sai ya nuna Alim yace gashi,harara Alim ya makawa Huzaifa,
Cikin gida Badariya ta koma dakin Babansu ta dauko manyan tabarmi sababbi dal dal guda uku musamman Baba ya siya sabo da bakinsa.

Inuwar mangoro me sanyi dake kofar gidan ta shindidawa Alim da Huzaifa,suka ce ta mayar da sauran saboda guards basa bukata suna can jikin motoci,
Baba ne ya karaso wajen Su Alim a mutunce suka gaisa aka kawo musu ruwa pure water leda uku me sanyi,
Amana kuwa tana cikin gidan ana ta labarin duniya,dan ma Amana bata fiye surutu ba,Badariya duk ta fesa cewar Alim ne saurayin Amana sai kallonsa akeyu.

Suna zaune Amana ta fito tana kuyi hakuri Na barku kuzo muje ciki Ku gaisa dasu Umma,Aabid yana makale jikin Alim suka shiga suka gaisa dasu Umma,Alim a hankali ya cewa Amana wace Ummanki? Nan Amana ta nunana musu Ummanta wata fara kwal kamar kwara,suna kama da Amana,gashi yan gidan gaba daya ba laifi suna da kyau sosai Amana ce ta fisu gaba daya,
Alim zai tafi matan manya kowacce dubu hamsim,Umman Amana dubu Dari,Baba ma dubu Dari,sai kayan tsarabarsu yace Na Amana ne ta siyo musu,su doya,manja,dankali,etc harda wayar Haladu,Apple,banana da lemo,su guava, duk abinda suke fada a waya Alim ya siyawa Amana ta basu,gida da makwafta an rude,

Alim sunyi Sallama da Amana cewar jibi za a zo a dauketa zasu koma lagos,Amana tace to ka tafi ni idan nayi 3wks sai Na dawo lagos din,Aabid dinfa? Alim ya furta,baki ta turo gaba to shike nan ka turo jibin a daukeni, Kudi ya bata yace ga salary dinki,

Kin karba tayi to wannan kyautar da kayi a gidanmu ai yafi karfin salary kawai ka barshi,ban son iyayi karba malama kina bata mana lokaci,Karba tayi tare da godiya,baku ci komai ba,tabe baki Alim yayi mungode zamuci a gida, Aabid tayiwa bye bye tare da cewa dama nasan ba ci zakuyi ba Ku yan gayune,Huzaifa yace no ba haka bane Baby Amana, wuce gida tayi aka ci gaba da labarin duniya. Alim sai wurin dare suka koma can gidan su Kaka.

Amana kuwa bata basu labarin halin da ta Shiga a lagos ba,bata fada musu irin rayuwar da tayi a lagos ba,kawai labarin duniya ta basu,haka frnds dinta maza ta ba wasu Dari biyar,wasu 1k,tunda Amana taje take yiwa yan gidansu hudubar Ilmi,cikin kwana daya duk kannenta saida ta sa su a makaranta,
Har alkwari tayi musu indai sunyi karatu to zata sai musu motar hawa,sai murna sukeyi suka sami kwarin gwiwar zuwa Islamiyya da boko,suma yayyen nata sun shiga islamiyyar Matan aure suna jira Amana ta sai musu motoci,mazan kuwa Amana tayi musu alkawarin jari,suma har sun fara nutsuwa,
Iyayensu kuwa tace Makkah zata kaisu suma wannan dalilin yasa ba shiri suka shige islamiyyar matan aure,sunga fa lallai Amana da gaske take,
Baba halinsa yana nan Na banza sai Wanda ya karu a kai,har matan aure bi yakeyi,shi yasa kudin da Alim ya bashi Amana tayi masa wayo ta kwashe kudin ta bar masa iya 20k,sauran kuwa duk ta biya family schl,
Chapter 17 · 0% Book details