← Book details Ciranin Amana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 58

Sashe 29

Ciranin Amana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Badriyya Na gefe tana haki tausayin Amana ne ya lullubeta wajenta ta tsugunna tana ta lallashinta,sannan ta cire mata doguwar rigar dake jikinta, Amana daga ita sai bra da pant,
Ruwan zafi Badriyya ta Tara cikin baho me zafi rau ta zuba gishiri,pant ta kama zata cirewa Amana,Amana ta bige hannunta cike da shagwaba tace Allah sai na fadawa Mijina,Dariya Badriyya tayi tace inye kaga masu miji, wlh Amana kin iya shagwaba dole Alim ya manne miki.

Allah gasaki zanyi zan rufe idona wlh trust me Badriyya ta furta tana cirewa Amana Pant tare da rufe idonta kam tana baki da kamata Amana nice taki babu yanda zakiyi kuma nasan baza ki iya wanka da kanki ba tunda kinyi famu,
Idon Badriyya a rufe ta cirewa Amana kaya ta tsomata a ruwan zafi tare da dannata a ciki ta bude kafafunta,ihu Amana takeyi amma Badriyya ta kafa ta tsare tace dama nasan wlh yanda Ya Alim ke kaunarki bazai taba yi miki gashi me kyau ba gwara da Allah ya kawoni lagos.

Amana tana ihun zafi tace zan mareki,dariya Badriyya tayi kimin shuru ko yanzu na jibgeki kar ki jawo na kara famu,
Saida Badriyya ta yiwa Amana gashi da ruwa har sau Biyar tana zubarwa tana sake sabo,wata Ni'imace da karfin dadi suka dinga ratsa Amana.
Amana tace sis wlh kin iya wa ya koya miki?Badriyya tace wajen kawarmu Bilkisa ta gidan Baba Tsoho,itace take mana lecture akan aure idan mukaje wasa gidanta,har kawata Maimuna ni na gashe shegiya minjinta ya mata daga daga.

Allah shiryeki cewar Amana, Badriyya tace rufe min baki ba gashi kin amfana ba,yanzu zauna cikin Bahon na miki wankan sabulu kuma kafin na bude idona.
Ba musu Amana ta zauna aka cudeta tana Badriyya kiyi a hankali mana zaki cire min fata,
Da Allah uwar kwailo duk karfinki kina badani.

Dai dai kirjin Amana tazo Ba ruwan Badriyya ta dirjesu da soso sosai,kara Badriyya ta saki kutmar....shege Alim dole yayi mukus a bed munafuki... Ashe rashana yake kwasa,fusge soson Amana tayi fita zan karasa kina tabawa Alim sirrinsa, wlh saina karasa ko na fama miki ciwonki,da sauri Amana ta bata soson mayya kawai ungo.
Tas Badriyya ta wanke Amana tare da daura mata towel sai lokacin Badriyya ta bude idonta. Har daki ta kawo Amana ta bata mai da nightwear sannan itama tayi,Alwala sukayi suka jero nafeela da karatun Qurani da sauransu sannan sukayi ta jera adduoi wa komai da ya damesu na duniya Dana Lahira.
Yau bed daya suka kwanta suna hirar zuminci,sai tausa Badriyya kewa Amana tana kwantar mata da hankali.

Asiya kanwar Alim tayiwa Abbanta waya cewar ta fitar da miji Sadiq yayan Huzaifa kenan dan kanin Abban Alim dake kano,shima kanin su Alim auta dake karatu a Cairo ya kammala karatunsa gaf yake da dawowa shima tace ya samu matar aure yar Adamawa state ce Zahra tare sukayi karatu amma Mum tayi tsalle ta dire tace wlh bai isa ba ita zata zabar masa mata.
Itama Asiya tace bata yards da zabin Asiya ba domin Saddiq ma'aikacin Gomnatine bashi da gadon arziki da Gomnati ya dogara ita kuma tace dole itama Aliya ta auri zabinta wato Sageer dan gidan Gomnan Kebbi tubabben Bayarabe ne,
Kuma baya da haka ma Mum bata kaunar dangin mijinta.

Babu magiyar da Aliya da Auta basuyi ba Amma Mum ta kekasa kasa taki abinda ya tashi hankalin dan autanta da kuma Aliya,Aliya tana can kano taki dawowa sai kuka takeyi,dan Uwan Abba kuwa sai tausarta yake yace addua itace mafita sabida idan aka matsa to Mum zata tsinewa yaranta wanda hakan barazana ce ga rayuwarsu.

AsmaBaffa
✳CIRANIN AMANA✳

125-130

By
AsmaBaffa

Ina matukar godiya fans duk naga sakonninku na Kuma Ji yanda kuka nemeni na gode da nuna kaunarku. Kuyi hakuri ba kuji ni ba,ina kaunarku sosai ina jinjina muku.

Page din nan naki ne MARCYCOOL my sweet and lovely sis.

Basu zarce ko ina ba sai gidan Alim direct Amana Jan Badriyya tayi har cikin Palon part dinsa nan take Badriyya ta sukukuce wajen kallon asalin haduwa, Badriyya batayi kasa a gwiwa ba tace Amana yanzu wanna kata'in gidan ne gidan mijinki, anan kike zama?ina Kallon gidan Mum Alim hadadde Ashe akurkin(cage)kazane ban sani ba,Amana dariya Kawai tayi yanda Badriyya ke zuba kauyancinta, Badriyya taci gaba Amma Mum ta cuce ni da tuni anan aka saukeni ko?

Kaf saida Amana ta zagaye gidan Tana nunawa Badriyya komai na gidan har sukaje part din Ma'aikatan gidan mata sai gulma Sukeyi Ashe oga Amana ya aura, Badriyya har yanga take musu ita ga kanwar matar gidan,
Sama suka hau a part din me gida Alim Sautin kidane ke tashi a manyan speakers dake girke a Palon Alim,Huzaifa zaune yana chat Alim yana latsa computer system,Badriyya kamar idonta zasu zubo tsabar kallon tsaruwa, volume suka rage a nutse suka karasa suka gaisa da Juna suka zauna,Alim kamar zai cinye Amana saboda Kallo,Huzaifa ma rudewa yaya ganin su Badriyya an dau wanka,

Alim ne ya radawa Amana baby kinyi kyau,wani yarrrr... Amana taji a cikin jininta sakamakon irin salon da Alim yayi wajen mata
Magana cikin kunne, nan take ta lumshe Ido,kasala ta sakko Mata,ba abinda takeso kamar tajita rungume jikin Alim musamman yanda kamshinsa ya cika mata hanci me dadin gaske,

Bari mu shirya Cewar Alim,kai kawai ta gyada,Huzaifa ma ya mike ya nufi shiryawa yana bin Badriyya da mayen Kallo.
Amana taja Badriyya zo muje kiga Saude yanda na kulleta,me gadi ne ya bude musu Dakin da Saude take suka shiga,Saude Tana ganin Amana ta fara lailayo manyan zagi Tana watso musu,
Haushi Badriyya taji tace kinji ko Amana, Saude tace tsinannu gadon tsiya, bakar haihuwa, haihuwar gefen kwalta, haihuwar tsakar Rana,wacce da Rana ubanki yayi cikinki,wlh nice ajalinki Dan ubanki Tare da Danno ashar lafiyayya.

Amana ta harzuka tace ki daina zagin iyayena nasan darajarsu,Saude tace Ubanki Ma yaci Uwatas, Uban Uwarki na fada yan tsinannu.
Amana tace Baba me gadi dauko min sandar nan me kamar kulkin yan sanda,aifa Baba da gudu ya kawo ya bar wajen,Amana ta mikawa Badriyya sanda jibgi rabonki Sis,Badriyya tace yanzu naji manana wannan shine aha...
Shiga Tayi ta Fara lugudar Saude,Amana kuwa kofar ta rufe musi Tana jin yanda Badriyya ke tafkar Saude,Saude kuwa bata fasa zagin da take ba.saida Amana taga lallai Badriyya zatayi kisan Kai sannan ta koma ciki Badriyya wai wanne hauka ne haka ki kyaleta haka ai dukan yayi yawa kina ganifa ko magana Saude ta Kasa,

Badriyya tace yo ni ina ruwana idan zata yini to wlh zan kwana akan zagin iyayenmu, Amana tace banason musu fa ke halina dake banza ce baki san kadan ba,Badriyya ta kalli Amana wlh kin lalace Amana, wai ke kikewa wani fada akan dukan wani.
Naji muje Kawai komai Ai sai ana hangen nesa
Sandar ta kwace ta kira me gadi ta bashi kudi da yawa sannan tace ya bata abinci da ruwa yaci gaba da tsare Saude.

Saude wacce ta gama jikata bayan su Amana sun tafi tace shegu ammafa wannan kanwar ta Amana har tafi Amana mugunta, saidai dukan Amana yafi zafi Domin duka daya na Amana shine goman na Badriyya.
Suna komawa Ciki Alim ya fito cikin shiri ya dau wanka na kece raini cikin pencil jean brown da riga Sea blue irin color na kayan Amana.
Yasha kyau suma taci Kudi sai shining yakeyi hade da kamshI.
Wani agogon Gucci ne me tsadar gaske a hannunsa,

Huzaifa ma ya hade cikin kanan kayansa black nd white,Alim ya kalli Amana wacce ta ke satar kallonsa domin ya mata kyau. Kamar dazu ina wanka naji ihu a gidan nan cewar Alim
Huzaifa ma yace nima haka wlh naji kuma na Mace,Amana sun san ihun Saude Ne Amma sai tace munje ai masu aiki matane wai sunga ga kadangare shine suke ta ihu amma an fitar dashi.

Huzaifa yace kai mata kenan Alim yace lets go zamuyi Missing flight,akwatunan guards Suka zuba musu a mota nan Suka wuce sai Airport dake Lagos.

Suna cikin Airport kafin a fara musu screening wata kyakyawa yar gayu bahaushiya suka hango ta taho tana yanga tana taku dai dai hade da juya mazaunai irin na yan duniya.
Alim ta kafe da kallo wanda shi bai ma san da ita ba domin Amana yake ta faman Kallo yana lallabata ta sha fresh milk tunda ba wata lafiya ce da ita ba.
Amana kuwa da Badriyya kallon wannan matar sukeyi Badriyya ta kama kunnen Amana ta mata Rada yanda ba wanda zaiji,Kalli wannan Amana wlh mijinki take kallo zatayi miki snatching,Amana itama ta yiwa Badriyya rada bar shegiya zanyi maganinta, Badriyya a basu show...
A basu show Sis,
a dauko manana yar Sulemanu Harka
CIRANIN AMANA

130-135

Official

By
AsmaBaffa

QUEEN MERMU WANNAN PAGE NAKINE,HAFCYCY DA SUBBY GODIYA GAREKU,OGA ASY BAN MANTA DA KE BA,INA TA WAJENA MAMAN WALEEDA ALLAH YA BAR KAUNA.
SAURAN READERS MA NA GODE

Har cikin garinsu kauyensu Badriyya ta kaisu, hamdala sukayi Allah ya kawosu lfy, a gurguje suka kwashi kayansu Amana ta sallami taxi Man ya tafi,kafin kace me anyi dandazo ana kallon yan gayu su Amana,kamar bakin larabawa ko indiyawa
Cikin sauri da zafin nama suka fada cikin dan gidansu me kyau,duk yan gidan tasowa sukayi ana tururuwar rungume su Amana,Amana hannu ta bawa yayyenta mata da maza manya da yara suna tafawa tas tas tare da share hawayenta,a tsakar gida bisa katuwar tabarma babba suka yada zango,
Cike da mutunci suka gaisar da iyayensu da kakarsu Iyya babar Sulemanu Harka wato Iyya.
Tambaya sukayi Ina Baba?Umman Amana tace suna asibiti daga nan zasu biya gidan me dori na Hausa,
Iyya tana sharar kwalla tace ai abokansa me Unguwa da Iliya su suke ta dawainiya dashi sun hana kowa zuwa sun dauki nauyi anjima zuwa dare zasu dawo daga asibiti.
Gwaggo tace ai wlh wannan tsinanannun yan Daba ne,
Iyya tace jarabar duniya asara ai basu da imani ko kadan,addua tsinuwa na dinga tsine musu kenan har ranar da mala'ikan mutuwa zai zare numfashi na
Chapter 29 · 0% Book details