← Book details Ciranin Amana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 58

Sashe 24

Ciranin Amana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Saude kuruwar kuka kawai takeyi,amma Amana ba tausayi tana jibgar Saude tana fadin maganin irinku kenan dattijan banza munafuka,bazan taba daga miki kafa ko in saurara miki ba kika sani kuka,kika sa Mum ta sa aka min sharri aka koreni daga schl,zaki kashe min Aure ki rabani da Mijina kisa Na zama bazawara,dama tuntuni ina sa ido akanki duk abinda kikeyi ina kallonki,dama bari nayi sai na kamaki,kuma wlh a dakin nan zaki ta rayuwa ba fita ba shiga,baki San wace Amana Suleiman Harka ba,wlh har hajiyan darajar Alim takeci da Baku isa kun ko da nuna ni da yatsa ba.

Saida Amana tayiwa Saude jina jina sannan ta kwace wayar Saude ta kulleta a dakin gashi window akwai ragar rodi ba dama mutum ya iya fita.

Amana Na fitowa Alim Na sallama,Oyoyo Daddynmu cewar Amana kamar yau ta fara ganinsa tahowa Alim yayi da Niyyar rungume Amana amma da sauri ta ja baya tana dariya,Aiki nayi fa ya Alim jikina maiko da zufa,

Bashi kika ci,ae jeka ina zuwa,kitchen ta shiga ta fara girke girkenta har ta gama ta shirya a dining,Alim yunwa tasa ya ja kujera ya fara ci ba jira,Aabid ya dawo kamashi tayi ta wankeshi tas ta shiryashi yaci abinci ya huta sannan ya wuce Islamiyya,

Wanka tayi sosai sannan ta shirya cikin wani riga da skert Na lace dark brown da milk,tayi kyau matuka,sai kamshi takeyi taci kwalliya lips yasha janbaki red,
Room din Alim ta shiga da sallama,dankwalinta a hannu,

Yana zaune a sofa Amana ta karasa kusa da Alim ta wani turo mazaunanta saitin fuskarsa sannan ta zauna a cinyarsa, wai su Amana anwaye za a nunawa Alim bariki,sosai ta bawa Alim dariya,
Ido daya ya kanne tare da dage mata gira daya yana cije lips,jikinsa ne ya fara rawa idonsa ya koma ja harda hawaye kamar kwalla ta taru ciki,

Da sauri Amana ta daga cinyar Alim tana kallonsa lfy kake kuwa zazzabi ne ya dawo,shuru Alim yayi tace Kuka zakayi? Wai mene ke damunka? cikin sigar rada Alim ya jawo Amana ta kwanta a kirjinsa yana shakar kamshinta itama haka sannan ya furta kece matsalar,
Tana saman kirjinsa ta dago da kanta suka kurawa juna ido cike da shauki,a hankali ta zaro harshenta ta lashi nasa cike da kunya ta sauka daga kan kirjinsa da gudu zata bar wajen jawota Alim yayi ta fado jikinsa, sannan yace ga iya shege ga kunyan tsiya ko? Dariya tayi tana rufe fuska tare da cewa Daddy Allah kunyarka nakeji sosai.

a hankali Alim ya hade bakin su waje daya yana aikin tsotsarsa tare da aika mata zafafan murza a jikinta,da kyar ta kwaci kanta,zata arce ya riketa yana maida numfashi sama sama,
Mene zaki gudu kullum ko romance baki bari nayi Na kirki why?
Cike da shagwaba tace to ni wai...so kake haka kawai ka maidani bazawara ka sakeni,ok wannan shi kike ganin masalaha,mufita ce wannan? Ae ai sakina zakayi watarana,
Hmmm baki da wayo ciki da haihuwa kadai zaisa mu kasance tare da juna ki bari Na baki Baby ajiya shikenan,

Kuka ta sa ta hada kanta bango wlh bazan yarda ayi min ciki ba aje a sakeni a banza nasha wahala,ok haka kikace?ae din cewar Amana, to shikenan ni kuma wlh ta karfi zan miki fadar Alim,dariya ta kyalkyale dashi har wani karfi gareka malalaci irinka ni da Na fika karfi wullu....tayi masa gwalo,kuma nace bazanyi cikin ba ehe tayi fari da ido harda murguda baki,

Dariya Alim yayi to naji sarkin karfi zo kiji wata magana muhimmiya,kusa dashi ta zauna sannan ta rike yatsunsa tana wasa dasu,
Alim ne ya fara magana jibi zanje London 2wks zanyi wani aiki zanyi ba dadewa zanyi ba,

To ka tafi dani dan darajar Allah Na hau jirgi naji irinsa,kin San Mum dai ko?matsala zata faru fa,au eh hakane kash mu an takura mana dande kawai Mum ce dole ayi mata biyayya cewar Amana,Allah kaika lafiya ya dawo da kai lfy dan Daddynmu,amma kafin Na tafi ai za a baki ajiyar Baby ko?
Nifa bana so gwara ma ka cire a ranka, yawwa Daddy Kasan..ki daina fada min Daddy Na gaya miki tam,to ba yanzu zan daina ba sai nan gaba,

Kasan Na kulle Saude A room Na jibgi shegiya,nan Amana ta bawa Alim labarin komai,da kyau cewar Alim ki kulleta karki budeta idan tana gidan Dole sai ta bawa Mum labarinmu,idan na koreta ma dole Mum sai tasa Na dawo da ita,best solution a kulleta kawai,
Ai Daddy kullum sai Na jibgeta da safe shine first breakfast dinta,da lunch sai dinner,dariya Alim yayi yace ayi mata a hankali,ai so nake Na koya mata hankali fadin Amana,

Muje Na ganta cewar Alim tare suka shiga har Alim Saude tayi miki miki,Amana duk tayi mata jina jina,hakuri ta shiga basu tana rokon Alim,Alim yace tunda ke munafuka ce matata kadai ta isheki sai yanda tace dan haka ba ruwana,Amana sabo da Saude Na wajen taje ta rungume Alim kam tana shinshina shi,Ruhina muje ka bani ajiyar Babyn nan Na matsu naji kukan jaririna,suna fitowa ta sawa Saude key sukayi gaba,Alim yasan karya Amana takeyi ba wani Baby da take nema,riketa yayi har room dinsa,da kyar Amana tana rusa ihu ta gudu daga room din ta bar Alim da wahala saboda matsananciyar sha'awar da ke damunsa.

Alim Mum da Abba da sauran mutanensa yayi musu sallama zaiyi tafiya ranar tafiyarsa London Amanace ta kaishi Airport Amana harda kuka,da kyar ya lallasheta.

Amana da Aabid suna zaune a Palo taji karar door password ma"ana suna da baki,hijab ta nemo kato tasa sannan ta bude kofar,Mum Alim ce ta bayyana tunda tasan Alim baya nan kome tayi Alim bai sani ba bare ya fadawa Abbansa ya dau mataki kanta.

Yatsina fuska ta shigayi tana watsawa Amana kallon banza,cike da ladabi Amana tayi mata sannu da zuwa ta tsugunna har kasa tana gaisheta amma ko amsawa Mum batayi ba,

Mikewa Amana tayi taje ta kawo mata kayan motsa baki,sannan ta koma dakinta ta canja shigar rashin tarbiyarta ta da,wandon wizzy kato da riga T-shirt,gashinta ta baza ta fito,asalin tafiyarta ta da da komai shi ta fara acting.a zuciyarta tana dama darajar danki kikeci ni danayi gadon rashin tarbiyar ba duka ba zagi zanyi maganinki. Siyasa zan miki kuma sai nayi nasara da yardar Allah.

AsmaBaffa

Godiya masu comments daga yau zaku koma kullum page 1 zan baku.
[6/30, 8:56 PM] 0mmer Farouk: ✳CIRANIN AMANA✳

95-100

By
AsmaBaffa

Tunda Mum taga Amana ta fito ba hijab sai tayi tunanin dama can wannan kayan ne a jikinta,nan Mum taji sanyi a ranta ganin Amana bata canja ba yanda take da haka take yanzu sai haske kiba da kyau data kara,ta tabbatar Alim bazai taba son mace me kamar Amana ba mace kamar Namiji,Alim dinta da yake son classy girl ma.

Kallon Amana tayi shekeke tare da yatsina fuska sannan tace ke yanzu sabo da dabbanci,kauyanci da Jahilci har yau baki canja ba?
Me Dana ya rage ki dashi amma jiba shigarki,to ki jini da kyau in zaki canja ma ki canja dan idan baki canja ba sawa zanyi dana ya sakeki,
Dama Mum hanya take so ta nemo Wanda zata kafa hujja ta takurawa Amana da cin mutunci iri iri,
Ran Amana yayi mugun baci ta fusata da niyyar cin mutuncin Mum Alim,tunawa tayi surukarta ce fa kamar uwar tace,tunawa tayi mahaifiyar Mijinta ce wanda ya sota ya taimaketa,yaso danginta,ya tallafi danginta da iyayenta,ya canja musu rayuwa,mijinta Wanda takeson kasancewa dashi har karshen rayuwa,

Itace ta haifeshi da bata haifeshi ba da bata sameshi ba,kuma ita tasa danta ya aureta duk da cewa akwai manufarta amma ta taimaketa komene Na jin dadi ya sameta Mum da Alim sune sula a yanzu,
Tunani tayi idan ta wulakanta uwar mijinta kamar tayiwa uwarta ne, domin uwa uwa ce,ko uwarta akayiwa dole taji haushi Ashe idan tayiwa ta Alim shima dole bazai ji dadi ba,ko ya saketa ma ko ya tsaneta.

Shawara ta sake nan take ta fara kukan karya ta marairaice,ta dawo kalar tausayi,saukowa tayi ta durkusa gaban Mum tace kiyi hakuri Mum ba laifina bane,Alim baya kaunata,shine yace kar ya sake ganina da kaya irin Na mata ya tsaneni,baya kaunata,ni da namiji duk daya a wajensa sabo da haka ma ya sani a schl wai dan Na daina yini yana kallona,rannan ma amai ya fara yi daya kalleni,kara rushewa Amana tayi da kuka dan Allah Mum ki min rai ya sakeni Na huta,London din nan ma ban San ya tafi ba a wajen yan aiki naji labari.

Rannan ma saida ya mareni sau 5 ,wani dadi da farin cikine ya lullube Mum,amma sai a fuska ta bata rai amma Alim baya kyauta min kiyi hakuri zan yi maganinsa,

Mum ce tacewa Amana kira min Saude za muyi magana kwana biyu banji ta ba ina son bata sako,Amana murmushi tayi cike da ladabi tace ai Saude ta tafi kauye tun shekaranjiya yayanta ya rasu,

Ran Mum a bace tace amma wannan shashasha ce amma ai sai ta sanar min nayi mata alheri,Amana tace Allah sarki ai Daddyn Aabid yayi mata komai.

Mikewa Mum tayi cike da jin dadi Na ganin Amana cikin wahala,Ashe Saude duk karya take mata gashi nan Amana bata canja ba,har yanda take magana tana cijewa irin Na yan jagaliya.

Har mota Amana ta raka Mum,tana tafiya ta dawo tana sheka dariya,tare da fadin tsohuwa ki taka a sannu Na fiki iya shege,ke karamar kwaruwa ce,
Room din da ta kulle Saude ta shiga da bulalarta saida ta kara Zane Saude tas sannan ta bata abinci da ruwa ta kulle kofar ta fito,
Yau Amana dauke Aabid tayi suka koma dakin Alim nan sukayi komai Na shirin bacci suka kwanta,tana kwanciya Kiran Alim ya shigo wayarta ta Skype wato video call,
Chapter 24 · 0% Book details