← Book details Ciranin Amana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 58

Sashe 51

Ciranin Amana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nan Amana take fadawa Alim yace ba matsala,haka kuwa akayi Alim ya tura kudi tsoho yazo lagos aka daukoshi har gidan Su Amana,sai kalle kalle yakeyi,
Abinci me aiki ta kai masa yaci ya koshi yayi Sallah,Sannan Amana tare da Alim suka fito wajen tsohon,suna ta masa kallon sani kamar sun sanshi.
Gaisawa sukayi da tsoho,Alim yace make tafe dakai? Kamar na taba ganinka,
Tsoho ya karkace yana goge hawaye tare da furta ba kama bace Dannan,yaro ba kama bace kun sanni idan zaku iya tuna Baba tsoho dake haskaku da fitila a lungun duhu,har na maka ihun kwarto aka biyoku,
Amana tace yes mun tuna mun ganeka amma lafiya Baba? Tsoho yace labarin me tsawo ne,sanda muke haduwa kece baki sanni ba amma ni na sanki nasan komai na rayuwarki,kuma nasan kuna da aure tun tuni,zuwa nayi na roki gafara Ku yafemin na yi muku babban laifi,zuciya da shedan suka sa na kasa hakuri,
Labari ya fara basu,watarana ke Amana tun kina budurwa kina kauye sannan kina fama da kuruciya kuma bakya barin ko ta kwana.
Ni na kasance tunda nake ban taba haihuwa ba a duniya har na tsufa,ina cikin bukatar haihuwa Allah yasa na auri wata kwatsam ta samu ciki ta haifamin Namiji,
Bani da kamar yaron nan na dauki son duniya na dora masa,ko zaginsa bana bari ayi,watarana ya tsokaneki kika biyoshi har gida kika lakada masa duka tare da farfasa masa jiki,readers idan baza Ku manta ba farkon novel din nan Amana yaro ya tsokaneta ta bishi har gaban uwarsa ta hada masa jini da majina,to wannan yaron Baba tsoho ke magana shine dansa.

Bana gida na dawo na tarar da yarona ance ke kika masa haka,raina ya baci nayi niyyar shiga malamai domin naga bayanki sai na fasa na shiga bibiyarki har Allah yasa naji labarin kin dawo garinku da zama ke da mijinki,
Ina sani nake muku magana har na gano gidan da kuke Zama dalilin ihun kwarto da nayi muku,
Muka biki har gida dan naga gidanku,hakan yasa na tafi Adamawa nayo hayar yaro na biyashi kudi yazo har gidan ya shige dakinki ya fito ya kulla miki sharri don naga na cusa miki bakin ciki sabo da naga duk duniya kin fi son mijinki da komai,

Yaron yana Adamawa yanzu ya shiryu sanadiyar wata yarinya da yake so,
Sai laifina na biyu wata baiwar Allah tazo garin neman gidan Babanki cewar Sulemanu yayiwa Yarta fyade ni na mata jagora ta ga gidanku,da dare ta dawo da matasa yan daba tasa sukayi wa Sulemanu duka suka karairayashi.

Nayi hakane sabo da son dana son kai da son zuciya,yanzu kuma nayi nadama naga banyi dai dai ba nazo Ku yafe min,domin yanzu dan nawa ya kangare yaro karami yanzu ya fada shaye shaye dalilin son dana ke nuna masa bana masa fada sai gata danake nuna masa,

Amana ce tayi ta maza tace sanda kace anyi maka haihuwa fa?har mijina ya baka kudin rago,tsohon yace yarinya mace aka haifar min,yanzu kuma duk wanda muka aikata muku ba a Dade ba sun rokeni idan na ganki na fada musu zasu zo neman gafara,dan Allah yarinya ki yafe min,Alim zuciya ta cika da takaici ji yake kamar ya masa mugun duka,
Sai dai ka karbi hukunci a koti domin baka ma da hujjar yi mana haka,ka zaluncemu kasa na zargi matata,da ace na saketa fa,kuma bayan yaron shi ya tsokaneta wannan hujja ce?kawai bakar zuciyarka dama can mugun halinka ne,kasa mun zargi mutane da yawa wanda Ashe basu suka aikata ba sai wanda kai bamu sanka ba,bamu damu da kai ba,mun manta dakai Ashe kai sharri kake kulla mana to baza mu yafe ba itama baza ta yafe ba kuma sai kasha dauri tsohon banza,bakaji dadin halinkaba cewar Alim....tsoho yaci gaba da magana.

AsmaBaffa

Godiya nake readers.
✳CIRANIN AMANA✳

190-195

Official

By
AsmaBaffa

Ku yafe min sharrin shedan ne,Amana nayi hakan ne a nufina dan na koyawa zuriarku hankali saboda abinda kukeyi a gari baku kyale kowa ba a garin nan mutanen gari,yan uwanku ma gudunku sukeyi domin da Sulemanu ya rasu da kyar suka zo gaisuwa saboda su Kansu baku kyalesu ba,sai gashi hukuncin Allah ya canja muku rayuwa,

Ku yafe min gafararku nazo nema domin idan ma a kotu an yanke min hukunci kwana nawa zan kara a duniya,
Nasan banyi dai dai ba,Alim cike da takaici yace pls ka kyalemu haka ni na zata mutumin kirki ne kai har nayi asarar kudina aka kawoka gidana,bana kaunar ganinka,kuma dole ka karbi hukunci dai dai da abinda ka aikata,Amana dai tana jinsu ta kasa magana sabo da mamaki daya lullubeta,Alim sai faman masifa yake saukewa tsoho,

Amana ce tayi magana ba komai Baba kanka ka cuta ka ganni dai baka rageni da komai ba domin mijina Bai sakeni ba Kuma Bai jira ya tsaya dogon bincike ba saboda ya yarda Dani muka ci gaba da zaman aurenmu,
Ka bani mamaki tsoho wlh da ace dane da nake Amanar Sulemanu Harka da a nan wajen saina bajeka,duk tsufanka saina barar da kai,a kan son yayanku Ku dinga mugun abu,wato na wani banza naka dukiya ko,Danka kuma ko yanzu ya min rashin kunya kaji da kyau saina ballashi ni matar Alim yar Sulaiman ba a ja Dani,murmushi Alim yayi yanda Amana take zabga kuri,
Ita kuma wacce ta yi sanadin Babana ina jiranta ka kawota,da yaron daka tura yamin sharri harda kwasheni da mari ina matar aure,ya gyara kumatunsa domin Idona idonsa sai mijina ya rama min Marin daya min.

Kaikuma sanadin tsufanka kaje halinka ya isheka amma ni na yafema har Abada,
Alim da sauri yace ke mene haka wa yace ki yafe,karka damu gashi munci riba tunda kaga na yafe kawai ka kyale maganar,ai na gaba yayi gaba na baya sai labari Allah yanason me yafiya kyaleshi kawai,
Alim yace to shike nan Baba an yafe ma ka kiyayi gaba,ba haka akeyi ba daga anyi ma abu ka rike mutum a zuciya har sai ka yi masa mummunan sharri.

Baba tsoho godiya ya dinga yi sannan ya danna waya tare da kiran Matar da ta ragar gaza Sulemanu Harka,da yaron da yaje gidan su Amana,adress ya basu na gidan Alim yace Suzo yana gidan ma.
Tashi Amana tayi tare da komawa sama cike da mamakin tsoho a fuska kamar mutumin kirki.

Washe gari da wuri sai ga matar ta shigo gidan Alim harda sanda tana dogarawa kayan jikinta duk sun yage,
Itama an bata abinci da ruwa taci ta koshi,da karfe biyu saiga Saurayin nan da yaje gidan su Amana,shima an masa saukar mutunci,har yau su Amana basu leko ba kuma gaba dayan bakin nasu suna bangaren masu aikin gidan nan aka basu masauki,
Shuru suna jiran su Amana shuru suna can suna soyewa sun manta da baki,har wurin 3pm sannan Suka fito makale da juna tare da bada Umarnin a kawo musu baki part dinsu,

Baki dai sai kalle kalle sukeyi sunga gidan da basu taba gani ba,Amana ta fara magana sannunku da zuwa,nan baki suka gaishesu kai a kasa,
Jin muryar ta yasa Saurayin nan ya dago tare da kallon wace wannan me muryar masoyiyarsa matar aure,
Ai kuwa karaf suka hada Ido da Amana ba wani bane face Deeni kwaro dan Adamawa wanda ya kai Amana asibiti,to wai ma ya Akayi Amana bata ganeshi ba time din da suna Adamawa,
Deeni Kwaro cewar Amana dama kaine ya Akayi ban ganeka ba? Mamaki da zufa ta ketowa Deeni,yana ina...Ina fara magana,lokacin kin shiga cikin tashin hankali ba tani kike ba ta mijinki kikeyi shi yasa ba ki Kula ba har nazo na kwada miki Marin daya gigita ki na fita da sauri,ni kaina wlh ban taba yin irin wannan aikin ba saida Baba tsoho ya rokeni sosai ina yin aiki kala kala a biyani kudi amma ban taba yin irin wannan ba,shi yasa ni kaina a tsorace nayi aikin,
Amana tace shi yasa nake ma kallon sani a Adamawa,Alim abin ya daina bashi mamaki magana yayi yace ni kam ina ganinsa na ganeshi,ko a ina na ganshi wlh sai na ganeshi amma ba komai rayuwa ce,Deeni har kasa yana bada hakuri,tare da furta na Dade da tuba kuma kin Sani a sanadiyarki na tuba wlh na daina komai sanda nake ganinki a garinmu,
Lokacin ban San ke matar wani bace kuma harga Allah ban gane kece ba sai yanzu,ki yafe min dan Allah Ku yafe min,
Amana murmushi tayi tare da furta ai ka cancanci na yafe maka,na yafe maka Deeni,Alim yace wai ke meke damunki ne yanzu ni gaskiya Amanata ta farko nake so bata yanzu ba,gwara Amana me Zafi da masifa ta,ke wannan Amanar ta yanzu ban gane miki ba,Dariya Amana sukayi gaba daya harda su tsoho

Matar ce tace gani nima dan Allah a yafe min,ni kun Sanni farin sani Saude ce,duniya ta dawo Dani haka,Amana tace na Dade da ganewa kece Saude,ko dan dukan da kikaci a hannuna na yafe miki,Alim ne ya kwalawa Amana Biro a kanta na gaji da wannan abin naki komai kice na yafe,

Amana tace idan bamu yafe ba mene ribar mu kawai ka kyalesu,Allah ma yana yafiya bare wasu mu,duniyar nawa take kowa yaje da halinsa,Halinka jarinka babu abinda dan Adam zai hanaka ko yi ma a rayuwa face da Sanin Allah,
Deeni kuwa shi ya taimaka min da tuni na mutu ya kaini asibiti ya biya kudin magani lokacin da bani da kowa bani da ko sisi lokacin da cikina ya zube,
Ka kusa aure kuwa?Amana ta tambayi Deeni,Alim ina ruwanki dashi kuma,Amana cikin rada suruntunta ya kaita tacewa Alim da fa sanda Ina Adamawa so na yakeyi sosai,sunansa Na me Kunu,bai San ni matar Aure bace,amma da na fada masa ya hakura,har address dinmu na bashi,niyya ta na bashi kanwata Salam tunda ta girma,

Kafin kace me Alim mood dinsa ya canja gaba daya ya bata rai sai muzurai yakeyi hannu yasa ya gyarawa Amana hijab dinta sosai sannan yace to Alhmdllh duk mun yafe muku,ke kuma Saude kin makara Baba da kika sa aka sassara ya rasu shariarku sai a lahira sai dai kiyi tuba Allah ya yafe miki nasa laifin, Allah kiyaye gaba,kuje driver ya kaiku wajen shiga mota Ku koma gida Allah kiyaye gaba,
Chapter 51 · 0% Book details