← Book details Ciranin Amana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 58

Sashe 47

Ciranin Amana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Murmushi tayi a fili tace dan duniya kenan harda bacci a hankali ta cire masa hular tare da ajiyeta gefe,kafarsa ta kalla duk rabi a kasa karfinta tasa a hankali gudun kar ya tashi ta gyara masa kwanciyar saida ta hau dashi bed din sosai,Amana da karfinta to, Amma duk da haka tasha wahala dama tasan Alim din nata idan ya fara bacci to sai ka saceshi bai farka ba,

A nutse ta shirya tsab cikin riga da skert na material black tayi kyau matuka nan ta fara Barin turaruka a jikinta harga Allah a zuciyarta dan Alim tayi kwalliyar Amma a fili wai sai tace badan shi nayi ba dama nayi niyyar kwalliyata,idan zuciyarta ta tabbatar mata dan Alim tayi sai ta karyata,tunani Amana tayi ta shiga kitchen ta dafa masa abinci amma kuma idan ta shiga kitchen kwalliyarta zata baci duk da cewar da Gas suke amfani amma ai aiki zaisa kwalliyar ta lalace tun Alim bai gani ba,

Fasa shiga kitchen tayi tace idan ya tashi na hada masa,wata zuciyar tace idan yaki tashi da wuri fa har sai kwalliyar ta baje,tace kai bari na tasheshi na masa wayo ya gani sai ya koma baccinsa,

Toilet ta shiga tare da ebo ruwa a hannunta ta yarfa masa a fuska zumbur ya bude ido tare da mikewa ya zauna,
Kallon Amana yayi gaba daya kwalliyar Amana ta tafi da hankalin sa sai kallonta yakeyi bai ce komai ba,
Amana ta kara tamke fuska irin ba wasa ta kara gyarawa tayi tsaiwar daukan hoto ta gama Zuko da matso kyau tare da kallon saitin Alim,tunowa tayi baiga bayanta ba sai ta juya tare da kallon mudubi tana neman wani abu a kan Mirror dan Alim ya ga bayan,Alim kuwa ai tuni ta gama kashe masa jiki da kwalliyarta sha'awarta ce ta taso masa,
Sai da ta tabbatar ya kalli bayan ma sannan ta juyo tare da tamke fuska ta furta malam lafiya ka sani a gaba,nayi maka kara,na maka tauna,nayi maka hadiya ina jira naji me kazo yi a gidanmu harda shigo min daki ka kama bacci?

Shuru Alim yayi baice komai ba,Amana ta kara magana jibeka simi simi kamar mutumin kwarai,Alim dai baice komai ba,Amana tayi mamaki shi da yake tsokanarta ma,

Alim a hankali ya furta am so sorry abinda na miki kiyi hakuri kinji,Amana wani tausayinsa taji kamar tace ta hakura amma sai ta daure tace ka daina bani hakuri haka ya isheni me zaka ce Dani yanzu na yarda,kai harni zaka Zarga,da masifa Alim yace taya bazan zargekiba ko kece kika shigo kika sameni wata tayi min haka exactly abinda na gani ya zakiyi? Dole ki shiga kokonto,ni waye da bazanyi laifi ba?Sufi neni?dan Adam ajizine Kuma na fada miki na baki hakuri uncountable ya kikeso nayi kashe kaina zanyi?na biki na biki ok to zo ki cinyeni ko ki yankani,ko sati biyu bamuyi ba da rabuwa sai da na nemeki,ranar da Baba ya rasu zuwana nawa?ance miki da bana sonki zanzo inda gidanku yake ne?abinda yasa ban ce a kira min ke ba nasan kina cikin wani Hali kuma banson ganin damuwarki tunda Baba ya rasu,ki tambaya zuwana nawa gidanku bakya garin nan,kafin ma ki tafi Adamawa, ni fa ko a waya kin nemeni? Ko text kin taba yi min na tunanin wanke kanki ko kimin bayani ko kiji halin da nake ciki,ko namiji shine marar aji?shi ba mutun bane? Gidanku nazo ki fada min abinda kika ga dama kuma dole ki koma gidana yarinya amma kisan me zaki fada min banson raini ya karashe fadan da kinyi kyau dai badon halinki ba,

Amana dake tsaye sannan ta fara nata itama ka dakeni ka hanani kuka,daga yin abu Baka tsaya ka saurareni ba kayi tafiyarka,harda zazzagina kuji sharrin Amana,
Alim yace kiji tsoron Allah yaushe na zageki?Amana ta gwada muryar Alim tace haka fa kace ke din banza ni nafi karfinki talaka,wawiya,doluwa,bahuwa,kuchaka kuma saina ballaki idan na kara ganinki sai na karya miki wuya,
Salati Alim ya saki sannan yace kiji tsoron Allah,Amana ta kara hade rai tana Hawaye Alim yace to mene na Kukan kuma?,Amana tace ai kaci mutuncina da yawa dole idan na tuna nayi kuka,Alim dai sharrin Amana ya isheshi yace to yi hakuri kinji.

Ni Bazan hakura ba yanzu cewar Amana,Alim yace to sai yaushe? yayi maganar cikin sigar lallashi,Amana tace sai an gano wanda ya kulla min sharri,tsaki Alim yaja ke ban son shirme fa dole ki hakura kinji na fada miki, Bazan hakura ba to dolene,mikewa Alim yayi tare da furta bari na mike kika tsawona,tunkarota yayi sosai da gudu ta fice tare da cewa ka jira na sanmaka abinci amma ban hakura ba

Kwanciya Alim yayi bacci ya kara dauke shi,ya dinga yi har Amana ta gama hada masa jullop din taliya tasha hadi sosai,tana zuwa ta ciji yatsansa ya tashi firgit tare da rike wajen,
Kallonta yayi kana yace bashi kike ci,
Toilet din ya shiga tare da dauro Alwala sannan ya zauna yace to zuba min abincin tace ka zuba da kanka mana ai ban hakura ba bare na fara yima hidima,kyaleta yayi ya zuba abinsa tare da hada tea yaci yasha,
Amana ta kalleshi tace kwadayi anzo ana cinye mana shinkafarmu da taliya bai san sanda dariya ta kamashi ba sosai,Alim yace yimin kudi na biya mana,banza ta masa tana danna wayarta yace me kikeyi a waya Ba tare da ta dago ba tace Charting,idan da namiji ne wanda ba muharraminki bane bada yawu na ba, tashi ka tafi gidanku gaskiya ka takura min, basai kin koreni ba ya furta tare da mikewa tsaye
Kudi ya zaro Bundle biyu na yan dari biyar biyar yace dauki daya kallon kudin tayi dama bata da ko sisi sun kare a biki,hannu tasa ta kwace duka bundle biyun duka nake so kuma ka biyani kudin da ci da kaina da nayi yunda da aurena a kanka ka barni nasha wahala kasan hakkinka ne ka biyani duk kudin dana kashe,kudin sabulu da omo,kamo hannunta Alim yayi suka zauna gefen bed sannan yana murmushi yace sai ki fada min dalilin kenan na fushinki tuntuni na biyaki ashe da dalili to fada min komai na biya,Amana sai yanzu tayi dariya sannan tace dan kadan ne ma fa,banda wannan kudin da ka bani saboda wannan kyauta ka min,Alim yace ina Jinki,Amana ta gyara zama tace kudin Kukan dana sha da wahalar da ka bani na bacin rai,Alim yace daya,tace kudin ci da kai,kudin rainon ciki kafin ya zube,kudin kayan kwalliya dana siya nayi amfani dasu baka nan,kudin zirga zirga ta zuwa unguwa kasan dole zan kashe kudin Mota, sauran na yafe maka basai ka biya ba,
Dariya Alim yayi cikin jin dadi yace to ki jira zaki ga Alert ya mike zai tafi,Amana tace na manta kudin mintsini da Yakushi,sai kudin gyaran jiki kafin na bika mu koma lagos.

jagira (eye liner) baka da ja sun kare ka siyo,ko kuma kaga fuska ba kwalliya, jambakina sun zama tsohon yayi a siyo wasu, sannan sai ka sake min lefe zan koma kuma duk ka bayar dinki a dinka da kana nan kaya ka bani 2wks sannan kazo mu tafi,Alim yace an gama indai zaki koma ai shike nan,Amana tace kuma ka Aiko min da Mota ko na dinga hawa mashin dan acaba kasan kauye har yau ana hawa machine cinyata ta gogi ta dan achaba ba ruwana ni,
To karki hau dan Allah Huzaifa zai kawo miki Mota,Amana tace kuma aikin hajji da za aje bana sai ka biya min na sauke farali,Alim yace wannan me sauki ne, yawwa nima nasan me kudine mijina Amma kazo sai cutata kakeyi kana jin dadinka kai kadai cewar Amana
dariya Alim yayi sosai yace to zamuje,
Amana tace na karasa yafe maka sauran laifinka to,dariya Alim yayi sosai sannan ya jawo Amana jikinsa tare da rungumeta kam kam,
Baby so kike ki karar min da kudi ko?,Amana cikin shagwaba tace me teku tasan anyi dan an ebeta da cokali? Murmushi yayi tare da yi mata rada Baby danyi min kiss kinji,Amana tace naki din Ai dane muka dafawa jaka shayi ,Alim yana sheka dariya yace ina kika samo karin magana haka ni ban taba ji ba,

Amana tace ae mana kalli dai jaka wato donkey Amma a dafa mata shayi ai an bata dadi kuma gatan yayi yawa shine nima nace ai dane muka dafawa jaka shayi,
Murmushi Alim yayi tare da furta i love Amanata tare da kankameta i missed u,a hankali Alim ya hade bakinsu waje daya yana faman tsotsa kudin dake hannun Amana ta watsar daga hannunta tare da kara kankame mijinta,sosai suka shiga mirzar juna kamar zasu cinye kansu, kan bed suka fada Alim ya shiga zare mata kayan jikinta one by one,da kyar Amana tace ka bari na koma lagos dan Allah,Alim yace ina so ni dai ki kyaleni,zan fasa yin hakurin to naki yafe ma cewar Amana,Alim yace bakya tausayina dama na sani,to ka bari mana na kara warkewa har yaushe nayi Barin cikin ma da za ka kara min wani,ka bari idan na koma lagos sai kayi,na hakura to ai tunda bakya so nasan ko bari naji dadi Baza kiyi ba Allah kaimu ki koma zaki fada,

Gyara kayansa yayi itama ya mayar mata da zip dinta sannan ya mike tace to karka manta da motar kuma kudin gyaran jiki kwandalata Baza tayi ciwon kai ba don bani nace ka koreni daga gidanka ba sannan lefe Sabo in ba haka ba bazan ma kwalliya da masu kyau ba ehe,

Alim yayi murmushi tare da cewa Amma a Adamawa kika koyo rashin Imani ko?haushi ka bani da har ka iya zargina shi yasa Sabo da na huce zan ci ma kudi nima,zance kayi aka baka ni?a sadaka ka aureni tsabar gata ranar da aka daura aure ranar na bika muka tafi ba wani tarzoma,

Alim yace to naji fadi kudin gyaran jikin Amana tace salon na fadi kadan saboda da zan iya tausaya maka,kawai ka bayar da abinda kaga dama,au na tuna ribbom dina ma suna bukatar canji,
Chapter 47 · 0% Book details