Sashe 19
Ciranin Amana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kwanaki fa suna ta ja gobe Saturday gobe daurin Auren Alim,dole ya gayyaci abokansa sosai,Amana kuwa tana Palo tana jira taga wankan auren Alim,itama ta shirya cikin shadda dark brown tayi kyau kamar itace Amaryar Aabid kuwa ya tafi weekend wajen Mum Alim,
Wani gigitaccen kamshi Amana taji ya daketa,Alim ya sakko cikin hadaddiyar shigar wata tsadaddar shadda yar gaske fara kwal,yayi Kyan da bai taba yi ba a duniya,ita kanta Amana gigicewa tayi,
Da Sauri ta mike tsaye tana wani kyafta ido sannan ta fara magana,dan Allah Dan Annabi dan Darajar Allah dan girman Allah kaje dani daurin auren naka kaji,
Pls Daddy kaje dani sosai ta damu Alim sai yaje da ita,je kiyi shiri kwana yini daya zamuyi tunda ma hakane sai Na tsaya mu taho da Amaryata.cikin tawagar angwaye dake flight harda Amana,
Amana burinta idan sunje kano taje gidansu su gaisa da yan uwanta.
Gidan Amarya kuwa an cika makil ana jiran angwaye,Abba da yan uwansa duk Suna can,Mum ma ta tura Aminiyarta Haj Talatuwa da Haj sameera kanwar Abba da matar Alhj Ishaq Aisha. Duk suna gidan Amarya ana jira a daura aure.
Angwaye sun sauka a kano sun kara haduwa a manyan motoci Na alfarma tare da frnds na kano an tafi gidan Amarya daurin aure,Amana tana kusa da Alim,sai tsokanarsu akeyi cewar tayiwa Amarya wayo,Amana dai tayi shuru ita da Alim a bayan mota Khaleed ne driver,ana ta zankada tafiya,zuciyar Amana cike da kunci,shi kam Alim ya rasa dalili jin wannan auren yakeyi daban da sauran da Mum tayi masa,baya jin wani kunci,ya danganta hakan da sabo.
Amana bata kaunar ganin garin Amaryar ma sabo da haka ta kwantar da kanta a jikin kujera tare da lumshe ido,khaleed kuwa sai tsokanar ango yakeyi yaki yin shuru,sauran motocin abokan ango suna binsu a baya,
Garin Amarya aka shigo har unguwarsu da layin gidan su amarya wani dandasheshe gida da duk unguwar babu kamarsa shi aka tsaya da motoci,mutane damkam cikin masallaci da wajensa,dangin ango duk gasu nan,har su Huzaifa, Amana bude lumsassun idanuwanta tayi don kallon unguwar Amarya,ai da sauri ta kara damke idonta ganin wani tsantsararren gida me kyau,gida Na fita kunya,ga mutane sunsha wanka,kamshi Na tashi kowanne cikin shigar alfarma,
Amana sai zare ido takeyi da mamaki tana kara bude idonta sai kallon dangin Amarya takeyi cikin suturu Na gaske,da gani sun samu harka,mamaki cike da zuciyar Amana,sai murza ido Amana takeyi.
Kallo Amana take tayi tana murje ido,ga kwalla ta cika idonta har hawaye ya fara zubar mata ta rasa meke mata yawo a zuciyarta.
AsmaBaffa
[6/27, 9:25 PM] +234 808 968 1079: ✳CIRANIN AMANA✳
70-75
By
AsmaBaffa
Amana bata gama shan mamaki ba sai da taga Babanta ya fito daga gida dauke da Alawa goro da chewgum Na daurin aure domin a kauyen haka akeyi,
Hangame baki Amana tayi domin ganin su Haladu da Hamza tare da sauran yayyenta duk sunzo daga garin da suke Cirani,mamakin Amana shine ganinsu cikin shiga me Kyan gaske,gaba daya sun canja,kyansu ya fito,sunyi fresh,to me ya faru haka,amma ai suna waya dasu Baba me yasa basu bata labarin komai ba,cikin motar da take ta kalla kawai sai taga wayam ba kowa Ashe angwaye duk sun fice an barta a ciki,su Alim ta hango sai hada hada sukeyi,musamman yanda taga Alim da danginta sai wasa da dariya sukeyi,mutumin da ba ya magana shine yake ta wasa da dariya haka.
Ana haka aka fara hudubar daurin aure,Amana sauke glass din window motar tayi dai dai da lokacin da taji ance an daura auren ALIM USMAN MUSA da AMANA SULEMAN HARKA kan sadaki naira million daya.
Amana poster tayi ta kame waje daya tare da hangame baki,shi kuwa Alim ya rasa me yake ji a ransa sai congrat akeyi masa da fatan alkhairi,
Baban Amana baki har kunne sai rabon alawa da goro yakeyi ana masa Allah sanya Alkhairi,Amana kuwa ta matsu mazan su watse ta shiga cikin gidansu taji wannan wanne irin abune,za a min aure ban sani ba,
Wani bangaren kuma wani nishadin dadi ta tsinci kanta ciki,tana ta tunanin duniya bata sani ba har mutane sun waste,angwaye kadai suka rage a kofar gidan su Amana,
A rude Amana ta gyara gyalenta siriri shara shara da ta yana a kanta bata daura dankwaliba sai acuci da tayi,gashi shaddar da tasha kowa ya ganta zaice Amarya ce,
Fitowa tayi daga motar kamar zata tashi sama ta wuce cikin gida ko bangaren angwaye bata kalla ba,Amana doluwa ta zama data shiga hadadden gidansu,kamar a birni,ko ina yasha tiles kofofi da windows masu kyau,cikin dakuna sun sha furniture masu kyau,
Komai Na gidan Na yan gayu,dakuna ta duba bedrooms gasu nan na maza Dana mata,Dana baki,da Na Babansu Palo da bedroom,
Dakin iyayensu ma Palo da bedroom ko wacce,kakarsu ma haka.gida ya kai gida ba jin kunya,mamakinta waye yayi gidan haka,
Yan biki mata sai kallon Amana yar gayu akeyi,ana guda,shewa,tare da tsokanar Amarya,Amana sabo da tsabar gulma dan kar ace tana so sai ta fashe da kuka tare da kallon Badariya tace ke dan uwarki ina dakin Umma,nuna mata badariya tayi ta fada ciki da kuka,
Babane ya shigo dakin shima,Amana cikin kuka tace Baba ya zaka yi min haka,ayi min aure ban sani ba,ko a waya ai ka fada min,Baba yace haba Amana ta ki yafewa Babanki kinji,uwar mijinki ce tace kar Na fada maki sabo da tana kaunarki tafi so tayi abinda zai saki nishadi,kinga gidan nan mijinki shi ya Gina min,kinga kowa Na gidan nan ya basu jari me tsoka,kannenki duk ya biya musu kudin makaranta,kudi da abinci da sutura duk shi ya aiko mana sosai har yayyenki da suke Abuja da cross river yayi musu komai,ta dalilinsa gidan nan an ci gaba,ga ilmi ana samu,
Ga shi kowa yana da aikinyi,yanzu duk iskancin da jahilcin da ake tafkawa a gidan nan Nawa ya fara raguwa, Iyayenku sun fara daina zage zage sabo da islamiyyar da kika ce su shiga,haka duk maza da mata masu shaye shaye da sata da matan ma masu mugun hali ta sanadiyyar makaranta da aikinyi da suka samu duk sun daina sai abinda ba a rasa ba,
Ki duba da kanki ki gani su Hamza duk sunyi hankali,nima yanzu alhmdllh Ina ciyar da iyalaina,to Baba kaifa ka daina daya halin naka?cewar Amana,
Jan numfashi Baba yayi yace kuci gaba da min addua Amana Na kusa dainawa,kuka Amana tasa haba Baba yanzu so kake yayanmu su gajeka,mu gaskiya kana jawo mana abin kunya,
To Amanata sai hakuri ai inji Baba,shi yasa alherin da mutanen nan sukayi mana dole Amana nayi musu abinda suka bukata,amma gaskiya uwar yaron nan mijinki da Babansa mutanen kirki ne,kinyi dace,yanda suka nuna mana kauna gamu talakawa amma suka iya hada zuriya damu ai sai dai Allah ya saka,Allah sa Albarka cewar Umman Amana dake zaune bakin gado,Amana tace nidai kawai ba a kyauta min ba,
Kudin sadakinta Baba ya mika mata dubu dari shida ta dauka haladu yaje banki ya sa mata a accnt dinta Dari hudu kuma ta rabawa iyayenta da danginta,
Gidan su Amana suna da tsafta sosai saboda shi Baba Allah yayoshi me tsamtsami,shi yasa dole kowacce ta zama me tsafta a ko ina,saboda yana ganin kazanta zai iya sakin mace.
Badariya ce ta kawowa Amana wainar fulawa da yaji me dadin gaske,ta kawo mata waina da miya ta bikinta,tuwon shinkafa miyar ganye,ummanta kuma ta kawo mata danwake me zafi,
Tun anan Amana taga canji,da Dane yaushe Badariya zata wani girmamata haka,gashi abin farin ciki Badariya ta daina zuka hayakin sigari,Umma ma da ace da ce yaushe ma zata wani saurareta idan ba kudi Amana ta bayar ba gaskiya Alim da iyayensa sun taimaka musu,ko sabo da wannan dalilin ta yiwa mijinta biyayya.
Ta fara cin danwakenta kenan Badariya ta kara shigowa Anty Amana kinga booth din motar angwaye kuwa abincine irin Na hotel da kaji,da ruwan jarka ke harda lemuka sun bude a irin abin take away suna ta ci in fada miki gaskiya yan gayu ne,amma angonki bai ci ba shi,Badariya tace kinga wannan Huzaifan ya bani da yawa Na kawowa su umma,
Anty Amana wai dan Allah nima ina da kyau?kinji wannan Huzaifan sai yace ni me kyauce,nace ai kin fimu kyau yace bai yarda ba Badriya ke ta faman surutu,Amana cike da masifa tace karki dameni dallah,
Sallamar Alim sukaji Umma dake waje tace shiga mana tana ciki ai an zama daya,tana cin danwakenta Alim ya shigo ya zauna a daya daga cikin kujerun palon.
Kwanikan gaban Amana ya shiga Budawa wainar fulawa ya gani tana ta tiriri,dama shi yana son wainar fulawa,gabansa yaja kawai ya fara ci,saida yaci ya koshi ya mike yace ki gama ki fito mu tafi ina jiranki,OK kawai tace da kyar,
Saida ya fita sannan ta sauke ajiyar zuciya tare da shakar kamshinsa,
Saida taci ta koshi sannan ta mike tace Umma zamu tafi, hhhh dariya akayi sosai amarya da ango sunzo daurin aurensu tare sun koma tare,ba a taba ganin irin wannan aure ba,Amarya kamar bata da gatan dangi,
Umma wata katuwar Leda ta mikawa Amana tare da fadin Badriya ta rubuta komai a jiki,wajen Baba Amana taje sukayi sallama,Baba yace to Amana in kayi da kyau kaga da kyau,kibi Allah kibi mijinki Idan kika tsaya wuru wuru ki gani a allonki, muna kallo za a watsaki a jahannama,gidana ba a yaji,idan miji ya sakoki to ki nemi wani gidan ba gidana ba,Amana dai aranta tace wannan ai ba nasiha bace ta kirki,kai Allah shiryi su Baba,a hakanma gwara Baba ya kamanta,Umma ba wata nasiha sai wasu kwalabe manya ta wani bani a Leda,ko mene oho,
A fili kuwa kallon Baba tayi tace ai billahillazi ya sakoni ko nayi yaji dole gidanmu zan taho, ina kakeso naje,Baba ma yace aikuwa kinyi karya in kina wasa ki gwada ki gani,Baba no...zanci Ubanki Amana karki ga ina lallabaki Na fiki iya shege,Amana tace Baba Allah baka hakuri,yawwa tashi maza kuje Allah bada zaman lafiya,