← Book details Ciranin Amana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 58

Sashe 12

Ciranin Amana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tunda suka ga haka sai suka tsani Amana suna jin haushinta tare da yi mata hassada tazo ta fisu fada wajen me me gidan gashi ita CE me renon dansa,sunga irin matan daya dauko a baya sun sami kudi da fada a part dinsa ma suke zama amma kwana kadan ake korarsu da wannan suka kwantar da hankalinsu cewar Amana ma korarta za ayi kwanan nan zasu ji abin tsiyarta,

Ko wacce da abinda take fadi kan Amana,har aka kaita wani daki lafiyayye,dan gado karami sai sip karama da madubi da toilet dinta ba sharing, kamar dakin dai yan mata,komai yaji,kayanta ta ajiye sannan tayi wanka sukayi sallah tare da Aabid, sannan tayi masa wanka tare da shafa masa mai sai kamshi sukeyi towel daure a kugunsa,suna ta hirarsu tana koya masa karatu har 9:30 Na dare sannan Alim ya dawo,ya duba ko ina baiga Aabid da Amana ba,da sauri ya kira wannan dattijuwar shugabar ma'aikata mata na gidan wato Saude,

Tana zuwa Alim yace Aabid da wannan yarinyar fa?soshe soshe Saude ta kama sannan tace Na kaita part din yan aiki suna tare da shi a can,harara Alim ya watsawa Saude yace ni nace ki kaita wani waje har yarona za akai wajen yan aiki?how dear u ko kin taba ganin me kula da Aabid a part din masu aiki maza ki kawo min su nan,

Da sauri Saude tace ayi hakuri Ahaji hakan baza ta faru ba insha'allah,jiki Na bari cike da jin haushin Amana ta fada dakin bako sallama,to uwar iya kizo inji Alhaji yana part dinsa ki dauki kayanki da Aabid can zaki zauna,munafuka saura ayi dan hali muna nan muna zuba ido kwanan nan za a koreki,kar kice zaki mike kafa matsiyaciya.

Amana ta dau Aniyar cin uban su saude sai nan da yan kwanaki,
Aabid ta nade cikin towel sosai fuskarsa kadai ake gani,goyashi tayi ta kinkimi akwatinta ta tafi part din Alim zuciyarta cike da tsoro,
Ta rasa dalilin da yasa take jin tsoron Alim,a palon kasa ta sameshi yana kallon News,sallama dauke a bakinta ta shiga,taga bakinsa ya motsa amma Sam bata ji muryarsa ba.
Aabid ta sauke cikin towel yayi fresh dashi,ba tare da Alim yayi magana ba ya mika mata uniform dinta,karba tayi tana budawa taga skert, a ranta tace yaufa akeyinta,a fili kuwa cike da tsoro tace master....master ban iya sa skert ba pls ka bani uniform me wando,
Ko kallon inda take baiyi ba kuma baice komai ba,shuru Amana tayi can tace to Master a bani kayan Aabid zan sa masa,sannan ka nuna min dakina zan je Na kwanta.
Sai da ya dauki 15mnt sannan ya mike yace biyoni ki karbi kayansa,a hankali ta bishi har bedroom dinsa ya nuna mata Sip wani part shake da kayan Aabid,akwati ta cika guda da kayan sawar Aabid har uniform din schl dinsa sanannan Alim ya gwada mata address din dakinta,godiya sannan ta sauka kasa dakin da ta fara shiga da farko me kofa biyu,daya kofar wacce zata kaita kitchen,bedroom din ya gaji da haduwa kamar Na Amarya,
Aabid ta shirya cikin kayan bacci itama tasa nata ta sukayi Addua suka kwanta tare,Aabid ya makalkaleta ya rungumeta sai kamshi sukeyi bacci me dadi ya kwashesu.

Washe gari da asubar fari Amana ta tashi Aabid sukayi sallah abinda Aabid bai taba yi ba sallar Asuba amma yau Amana ta sa yayi har azkhar ta fara koya masa,ita Amana fa yanzu bata da burin da ya wuce taga yaro me tarbiya,tana sha'awan hakan saboda gidansu kaf babu me tarbiya,shi yasa ma ta ke son koyawa yaro tarbiya duk da cewa ita bata da ita,ta sani amma tana so ta koyawa wani,shi yasa take koyawa Alim tofa kaji su Amana.
Wanka da brush tayiwa Alim sannan ta shiryashi cikin uniform din schl dinsa,ta yi wanka itama tare da tsaftace lungu da sako Na jikinta sannan ta fara shiri,uniform din Ma'aikata da Alim ya bata Riga da skert su ta ebo,tana kunkuni tasa pant da wani tight iya gwiwa,sannan tasa skert din,Amana kwai diri da sura,kamar an gwada ta skert din das a jikinta,sannan tasa rigar,gyalenta ba fari Alim ya bata ba kalar skert ne dark blue,Amana gaba daya ji take a takure take ta dabaibaye,ita da wando ta saba,
Gyalen maimakon ta yafa sai ta daura kawai a kanta ta gyaran room din tas,sannan ta fesa turarenta ta fesawa Aabid ma,7am ta riko hannun Aabid suka haura saman Alim,

Aabid da gudu ya shige bedroom Alim yana cikin bacci yaji Aabid Na tashinsa Daddy ina kwana Anty ce tace Na dinga Ce maka ina kwana,
Alim a hankali ya mike tare da shafa kan Alim yana morning son har kayi shirin schl,ae Daddy Anty tana jirana zanci abinci ta kaini schl,maza to jeka kace tazo ina nemanta,

Da gudu Aabid ya koma wajen Amana yace Anty Daddy yace kizo,gabanta ne yayi mugun faduwa kamar kwai ya fashe mata a ciki haka ta shiga dakin tana tafiya bata saba da sa skert ba,kawai garin tafiyar niggoginta skert ya hardeta ji kake rim ta fadi a kasan tiles Na dakin Alim,Alim dake kwance nade cikin bargo yana kallonta,ko sannu bai mata ba,haka ta mike tana Sosa kanta,tunda Alim yake bai taba sanin uniform din ma'aikatansa Na da kyau ba sai a jikin Amana,a ransa sai ayyana irin kyanta da kyan diri irin Na Amana amma take cutar kanta kullum abubuwan maza takeyi.

Ko gaisuwa Amana bata yi ba kawai sallama takeyi ita bata saba da gaida mutane ba,shima Alim bai damu ba yace kije kitchen ki hadawa Aabid abinci, kece kullum zaki Na dafa masa abinci,ki kaishi schl ki daukoshi ke da driver,
To kawai Amana ta furta tare da fadawa tunanin family dinta,jibi gata da son karatu, amma su iyayensu Sam ba ruwansu da ilimin yaransu,gashi suna son karatu ba dama,a fili kuwa cewa tayi master dan Allah ka sani a makarantar Aabid kaga ni a ss2 Na tsaya sai mu dinga zuwa muna dawowa tare,

Bazan saki ba cewar Alim,kafin ya rufe baki Amana tace master lada zaka samu Ina fada ma taimakon irinmu zai iya jefaka a aljanna,Fice min da gani cewar Alim, baki ta zumbura tare da ficewa tana kunkuni.Alim a ransa yace lallai yarinyar nan bata da kunya karshe,zan gyarata very soon.
Kitchen Amana ta shiga Wanda ke part din Alim,Dattijuwa Saude ta iske a ciki tana shiryawa Alim girki,ko sallama Amana batayi ba ta fara shiryawa Aabid da kanta abinci, minti kadan ta soya chips, da egg,sai tea me kauri,ta damawa Aabid oats da madara.

Saude sai kallon Amana takeyi tana dama haka take da kyau,lallai karfa yarinyar nan ta karbe gidan nan watarana, a fili Saude ta ce insha'allahu hakan ma baza ta faru ba,

Amana tana aikinta sai ji tayi Saude ta bangajeta, a zuciye Amana ta shaki wuyan Saude tare da makata jikin bango sannan ta dinga zagin Saude tare da kara makure Saude ta kwala mata ludayin miya a goshi kafin kace me goshin Saude ya kumbura ya fashe yayi wani sumtum,Amana kuwa ta gama aikinta ta jera komai a tire ta dauka ta haura saman Alim,

Ganin haka yasa Saude tace wlh baza ta kyale Amana ta mata illa ta tafi a banza ba,Saude Ce ta suri mubirgin miya tabi Amana a guje har Saman Alim,tunaninsu Alim bacci yakeyi,turus suka ja birki ganin Alim zaune cikin shiri da Alama fita zaiyi,Saude uwar makirci nan take ta fashe da kuka tace Alhaji kalli yanda wannan yarinyar tayi min duka a kitchen,ta fasa min kai akan kawai nayi mata nasihar gishirin zaman duniya,yar daba ta fara dukana harda cewa itace ajalina ta kara fashewa da kuka,Alim sarai yasan karyar Saude, Saude kuwa ganin Alim bashi da niyyar magana yasa ta kara bude baki zatayi magana,ji kake fafff Amana ta make mata baki tare da cewa ki kyale mana master dallah haka karki sa masa headache,

Bakin ciki yasa Saude shako wuyan Amana,Amana kuwa me karfin maaza Hannu tasa ta mirdewa Saude hannu, wayyooooo cewar Saude tana ta kara,Amana tace ina daga miki kafa Iya ke babbace kija girmanki kafin Na fara taka ki,wannan abin ba komai nayi miki ba wlh ki kiyayeni ko a garinmu Na kano bani da mutunci ki tambayi tarihina kiji,

Saude da kyar ta kwaci kanta ta arce da gudun tsiya,Alim Na kallonsu a ransa yace naga Alama yarinyar da ta ja da yan fashi ta fansheni ai ta kai karshe a duniyanci.
A fili kuwa tsaki yaja sannan a hankali yace idan Aabid yayi late a schl sai kin karbi punishment,da sauri ta zauna ta bawa Aabid yaci ya koshi itama taci sannan ta daukeshi ta wanke masa baki neat ita kuma ta dauko aswaki zurere Na itace ta sa abakinta sukayiwa Alim sallama driver ya daukesu a rantsatsiyar mota ta kai Aabid schl sannan suka dawo tare da driver,tana ta dirzar bakinta da itacen aswaki,Amana idan tayi brush da asuba to duk cin abinci ko sallah sai tayi aswaki haka tsarinta yake,har palon ta shigo tana aswakinta,
Alim taci karo dashi zai fita ba Wanda ya kula wani ta wuce dakinta ta kuskure bakinta ta kwanta sai bacci.

AsmaBaffa

[6/27, 9:25 PM] ‪+234 808 968 1079‬: ✳CIRANIN AMANA✳

45-50

By
AsmaBaffa

Amana duk baccin nan da takeyi a kasa ta kwanta,jiya da ta hau bed jikinta damunta yayi saura kadan ta makara a sallar asuba,shi yasa ta sauka kasa,sabo da Aabid ta kwanta a kan bed,
12:30 pm Amana ta farka,sallah kawai tayi ta fada kitchen ta shirya lafiyayyen abinci sannan tayi wanka ta shirya cikin uniform dinta,sai kamshi take zubawa saboda uniform kala biyar Alim ke bawa ma'aikatansa kuma duk shekara sai an sake musu new,a hankali Amana take tafiya saboda skert dinta bata iya tafiya da shi ba mantawa tayi ta taka kayam kayam da sauri,shi yasa a kullum sai ta fadi wajen sau biyu ko uku,
Chapter 12 · 0% Book details