← Book details Ciranin Amana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 58

Sashe 32

Ciranin Amana Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Hamza ya kalli Sakina uban waye ya taba mana ke fada min wlh ya gane kurensa yau,
Sakina kuka taci gaba dayi harda shidewa Amana a fusace ta make bakinta har sai da ya fashe tace ohhh zaki tace Babyna wlh kika sake ya tashi ban gama masa abinci ba sai na tattakaki a gidan nan.
Sakina dafe da baki sai Hawaye takeyi,
Hamza yace ki bita a hankali mana ke fada mana Mene?
Sakina tace saurayinane Mohd mukayi fada yace ya fasa aurena wai na fiye masifa ta kara fashewa da kuka kuma wlh Ina sonsa wayyo....karshena yazo...ni mutuwa zanyi.

Yaya Isa dan Allah tunda abokinkane ka bashi hakuri ko gidansu can cikin Kano city ka je ka bashi hakuri,
Ke.....ke...ke....hold there abeg wanne irin in bashi hakuri sai kace dole ki kyaleshi Allah ya baki wani ai sai ma ya raina mu yaga kamar andamu dole ya aura karshe kisha wulakanci,c cikin kuka tace dan Allah ya Isa,
Isa yace ke zan kwada miki mari wlh kinma rainani sau nawa Ina zaunar dake ina baki shawara cewar idan kin San kina son Mohd ki rikeshi sosai ki gyara wannan masifar taki kika ji ke a dole budurwa dole ya so ki ko ai gashi na kinwa kanki.

Kuka taci gaba da yi ,Amana wacce ta fito daga kitchen rike da wani bowl tace a'a ke tashi ki tafi can kofar gida wlh ko ki koma dakin uwarki kiyi ta kukanki ya dan iskanci zaki tasar min Baby yana bacci,
Shuru Sakina tayi tana kunkuni.Badriyya ce tayi sallami tabi Sakina da kallo ke ga yar iska ko kinzo sai kuka kike ma mutane kina firgita min Huzaifa kina cika masa kunne shashasha ta ja tsaki,kb dake cin indomie yace ki taya jaje saurayinta ne ya fasa aurenta Mohd abokin Isa,
Fuskar tausayi Badriyya tayi tace eyya sorry kinji Sis rashin masoyi ba dadi kamar nice ace Huzaifa ya daina kulani ai daji zan shige kawai.

Sakina tace ni dai Allah a San yanda za a dawo min dashi ehe
Harara Amana ta watso mata,Badriyya kitchen ta shiga tace Amana ki dafa da Ya Huzaifa fa,ae ai dama dashi nakeyi kira min Haladu pls na aikeshi,Amana yayanki ne fa Haladu amma zaki aikeshi,ina ruwanki to kawai ki kira min shi.

Yara yan makaranta sun taso suna ta surutu Amana da masifa ta fito kai kuyi min shuru mijina Bacci yake kwakwaran Motsi Amana ta hana yaran nan suyi har ta gama girkinta ta fesa wanka ta dan dasa kwalliya cikin doguwar rigar materal fitted gaunt tasha kyau hips komai ya fito das das ta Jere abinci a gefen bed sannan ta tashi Alim ya shiga toilet din dake cikin room din domin yin Alwala

Saude kuwa tana kauyensu bayan ta samu nasarar guduwa daga gidan Alim ko me take aikatawa oho ta ya Saude ta gudu sai mun koma wajen me gadi za muji labari
Amma dai Saude ta murmure ta dawo fes da ita tana harkokinta can kauyensu dake Gombe state.
Alim kamar gidansu yana shigewa toilet saida yayi wanka da soap din Amana,yayi Alwala da sallar Azahar,Amana kuwa period takeyi ma
Zaune yake kan katuwar sallaya abinci Jere a gabansa ga Amana tasha wanka tana aika masa da wasu sinadaran kallo masu rikitarwa.
Wasu flasks masu kyau ya bude wow....ya furta miyar danyar kubewa ce tasha kifi da tuwon danyar shinkafa,wani flask ya bude farfesun kaji sai kamshi ke tashi sai wani glass Bowl kankanace a yanke da fork spoon ciki
Ga wani zobe yasha kayan hadi a glass juck har ya fara kankara,sai ruwan roba,yanda aka kawowa Alim haka aka bawa Huzaifa ma,
Alim ya manta ma tare suke da Huzaifa ma

Amana zagewa tayi ta cire masa rigarsa ta shadda daga shi sai dogon wandonsa wai kar mistakenly miya ta bata masa riga hehehe love

Alim kamar gidan ubansa ya wani kwanta a kafadar Amana tana ta ciyar dashi saida ya koshi sosai sannan a karshe ta bashi kankana yasha,
Brush ta kawo masa sabo ya tsaftace sannan ya dinga kora zobon,
Amana kuwa abincin itama taci ta kwashe komai ta gyara room din tare da kara wanke toilet din ko Ina kamshi yakeyi,
Alim saman bed yajata suka shige sai wasanni sukeyi a ciki.
Huzaifa yaga Alim shuru yaki fitowa sai mamakin rashin kunyarsa yakeyi a gidan surukai, Badriyya tace ai mu nan gidan ba ruwan wani da wani,lallai rayuwarku tana birgeni a gidan nan kowa harkarsa yakeyi cewar Huzaifa.

Har magriba Baba Basu dawo ba,Huzaifa har ya fito jikin mota suka hadu dasu Baba sun dawo an kwaso Baba kamar kayan wanki yana ta numfarfashi,har dakin Baba yaje suka gaisa harda yar hira sama sama sannan ya masa ya jiki,Baba yana nishi yace ina wannan dan marasa mutuncin dan uwanka mijin Amanata
Huzaifa ya sosa kai Baba yana dakin Amana yanzu ma jiransa nakeyi ya fito mu tafi kar dare yayi,
Sanda Baba ya jawo a kusa dashi ya rafkawa Huzaifa a kansa nan take wajen ya kumbura,dan ubanka fitar minshi daga gidanaa na tsaneshi,Huzaifa dafe da kansa yace Baba lafiya kara daga sandar yayi da niyyar kwala masa Badriyya ta fado dakin ta tare tace ni ka dakeni Baba akan ka daki wannan me sukayi maka?

Huzaifa ne ya janye Badriyya yana bawa Baba hakuri suka fita,
Amana ne suka fito tare da Alim kamar zasu hadiye juna,sallama yayiwa mutan gidan kaf tare da yi musu kyautar ruwan kudi,Huzaifa kuwa Badriyya ya kashe da kudi sai Haladu da Sakina.

Huzaifa yacewa Alim malam dan Allah ka shiga wajen Baba ka fito mu tafi dare nayi mana,
Murmushi Alim yayi, Amana tace karka damar min miji dariya sukayi gaba daya.
Suna shiga Baba ya dinga zagin Alim da Bala'i. Yace kuma dole ka sakar min yata gadon tsiya, Amana ce take kuka haba Baba wannan butulcine,Baba yace Butulcin Ubanki akan sun bamu yan kudi da yi mana wannan gidan.gidan banza gidan wofi nan fa Ba irin cin mutuncin da Baba baiwa Alim ba,Alim sai hakuri yake bashi tunda shi Bai San dalilin zagin da Baba ke masa ba.
A hankali yace Baba kayi hakuri amma bazan iya sakin matata ba,
Baba sai da yaja nishi sosai sabo da azaba ciwo yace da yake uwarka ce ta haifa min ita ko kai nafika iya shege na fika tantiranci,ka tambaya kaji gogaggen dan duniya ne ni nafi karfin uwarka ma.
Amana cikin kuka tace Baba wai Mene haka dan Allah,Jan hannun Alim tayi muje kawai na bika mu koma Lagos.
Baba yace kije gidan uwarwa kai na fiku tasha wlh,kaje ka kawo min takardar yata kuma saki uku tafi ka bani waje ke kuma na fada miki idan kika kuskura kika bar garin nan namu to ban yafe miki ba,

Amana tace Baba iya garin nan ko ka yarda na fita na zagashi yace ae iya garin nan zaki zauna,ko gidana zaki bari to ki zauna iya garin nan kiyi ta yawon duniyarki amma a anan garin.

Shi Baba ganinsa ya kafawa Amana tarko,Alim yace Baba na tafi Allah kara lfy ya zaro damin kudi ya ajiye masa,Baba ba kunya ya karbe tare da Jan tsaki
Amana suna fitowa waje tacewa Alim sallami Huzaifa ya tafi gida ni kuma ka jirani muje wani gida a garin nan tunda Baba Bai hanani fita a nan ba.

Haka kuwa Huzaifa ya tafi Amana ta dauko kaya a hand Bag Babba tace muje,Alim yace nifa tsoro nakeji kar Baba yayi mana wani Abin,
Dariya Amana tayi tace rana zafi inuwa kuna both Mum naka da Babana ai kawai muyi me dalili mu rufta kawai Baaaba komai ta fanjama fanjama.
Dariya Alim yayi tare da lakace mata hanci,taja Hannun Handsome Alim suka Sha kwana ta wani lungu.

AsmaBaffa

Tnx all
CIRANIN AMANA

140-145

Official

By
AsmaBaffa

QUEEN MERMU AGAIN,THS PAGE IS FOR UUUUUU

Corner su Amana sukesha kawai ba ji ba gani har Alim ya gaji yace gaskiya honey a tsaya am so tired daga cewa ba nisa nan nan sai Shan corner mukeyi da layika,
Kafeshi tayi da Ido duk ya jigata saboda Sam Bai Saba da wahala ba,gashin kansa ya hargitse harda bige kafarsa domin wajen ma ya dan yi jini kadan,
Lazy kawai kamar ba Namiji ba,yanci zamu karba wajen iyayenmu Amana ta furta tana kada masa idanuwa,murmushi Alim yayi kinga karfa wani yazo wucewa ya kallar min farin da kike min da ido am gealous,
Kuma taya zamu karbi yanci a haka wai ma ina zamu،hope dai baza mu Dade ba kinsan Aabid dina yana can Mum zata kara lalata minshi da wasu halaye kina gani yaron yanzu kullum boyeshi takeyi a room dinta ko ganinsa bamayi a gidan makaranta ma ba kullum take bari yana zuwa ba,yaron kafin na zo nan na ganshi duk ya rame,idan yace Momy ko Daddy Mum makeshi takeyi,wlh na rasa yanda zanyi da Abin ga Aabid saurin girma gareshi...
Chapter 32 · 0% Book details