← Book details Ciranin Amana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 58

Sashe 41

Ciranin Amana Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Itama Amana saboda kullum cikin sa rai take zata hadu da Alim dinta yasa take yarda da gyaran sosai,kai ba kace Amana ta taba aure a duniya ba yanda ta kara komawa kuma gashi kullum dai sai tayi kukan rashin Alim amma a hakan ba laifi ramarta kadan ce ta rashin mijin ta.
Saura kwana Uku su koma gidan Baba Sulemanu Umma ta samu Amana tace na dauki Number Hamza dake littafi jiya na ari wayar Malam na kira shi mun gaisa sosai duk sunce a gaisheki,bikin Sakina da Badriyya Saura kwana 5 biyar a fara kinga zamuje a dai dai,Badriyya tace na fada miki ta kai miki dinkunanki cikin Kano za a yo miki,wai ya cikinki na basu Labari ya zube da abinda ya faru,sunyi jaje sosai,
Murmushi Amana tayi tace Umma bari naje gidan su Nusaiba ayi min dilka da halawa,Malam Nuhu shi ya bawa Amana kudin,Amana kuwa gaba daya kwana Ukun nan a gidan gyaran jiki take yini,ko ina ta gifta kamshi take bari me dadin gaske,skin dinta tayi smooth sai sheki da kyalli takeyi,duk wannan Alim takewa tanaji wai ko zai ganta ya ganta bata lalace ba ya ganta har yanzu fa za a je da ita,yaga bata ci baya ba,kuma duk sabo da tsaro bata San ya ta Allah zata kasance ba ko Alim zai yi tunani ya daina zarginta ya maida ta wajensa kunga kenan a shirye take,dama kuma kun San Amana bata son raini akwai son har kar wanka da gyara hade da tsabta.

Umma tace kinga gobe zamu tafi ko zakiyo lallen bikin?Amana tace a'a Umma salon ya goge ma da wuri kenan ai sai naje can zanje har cikin Kano city ayi min na kece raini,
Duk sabo da Alim Amana ake wannan cakarewa.

Ta wani bangaren Amana tana Jin haushin Alim sosai yanda ya manta da ita duk zaman da sukayi,ya kasa tunani akan abinda ya gani,ya zargeta,har ya yarda zata iya cin Amanarsa,
Uhmmmmm Amana ta furta a fili tace Namiji kenan me manta alkhairi,ka shekara kana aikin me kyau rana daya ta baci ba mutunci...wai ni Alim zai yarda Ina bin maza,wai Alim ya gujeni ya manta Dani,lallai a duniya anything is possible shuru tayi tana ta tunani,
Maybe idan Alim ya ganta ma ko kallonta bazai yi ba ya manta da rayuwarta,wani Hawayene ya zubo mata masu Zafi,ganin Umma na kallonta yasa tayi sauri ta fada daki ta kwanta tana ta shesheka har bacci ya kwasheta.

Alim kam bangarensa sai duai domin yafi Amana shiga kunci yaje Har Adamawa ya gama bulayi baiga Amana ba ya dawo ya dage da addua sosai na tabbata da Alim Bai rungumi addua ba shima da tuni ya haukace ya zare.amma a haka idan ka ganshi sai ka dauka bashi da matsala haka Addua take da yawan karatun Qurani yan uwa mu dage da Addua karatun Qurani shine magani.Alim gaba daya sun rankaya sun taho Kano bikin Huzaifa aboki kuma dan uwa.

Baban su Huzaifa part guda ya warewa Amare da kawayensu haka angwaye da abokai nasu daban duk cikin gidansa sabo da Amare Sakina da Badriyya ba a cikin Kano suke ba su kuma angwaye a cikin birni suke saboda dinner kala uku da angwaye suka shirya yasa Abba yace Amare da kawayensu su taho gidansa angwaye ma haka har mijin Sakina sabo da shima sanadin zuwa zance suke haduwa da Huzaifa har zumunci ya kullu tsakaninsu tare suke shirye shiryen komai,Alim kuma shi ya shirya musu party har kala biyu,Abban mijin Sakina ma ya shirya musu daya.don haka duk shagalin biki gidan su Huzaifa za ayi shi,daurin aure ne kawai za aje gidan Amare a dauro,su kuma iyaye mata suna can zasu Kula da jamaarsu ta gari.
Alim sabo da zaman mutuncin da sukayi da Amana da kuma sonta da yakeyi yasa kaf mazan da matan gidan da yara yayi musu dunkuna na alfarma manyan mazan kala Uku uku yaran kala biyu biyu,har iyaye har Umman Amana ya bayar da nata a Dinka a ajiye mata,Amana kuwa ya Dinka mata har kala Goma da takalma da jakankuna da mayafai tsakaninsa da Badriyya sukayi sirri yace tace wai Huzaifa ne ya Dinka mata itama kar ta fada shine,Badriyya tace to bakina kanin kafata,a halin yanzu Huzaifa yasan Alim da Amana basa tare amma duk ya tambayi dalili ba wanda ya fada masa har Badriyya kawai sai ya kyaleta.
Kayan abincin biki kaf Alim ne ya saukewa su Hamza shi da kudin kayan dakin Amare,amma Sam Angwaye sukace kar a kawo Amare da cokali sunyi komai nasu.
Alim ya karbi kudin ya siyawa Hamza da Kabiru kb fili kato guda biyi a Na'ibawa Kano,sun Hamza harda kukan dadi za a koma City,
Yacewa su Haladu ma za a basu nasu suyi aure shi kuma Huzaifa yace zaiyi tallafin Gina gidajen nasu,Ishaq Saurayin Sakina yace shi kuma zai zuba musu furniture,wannan murna kawai sukeyi suna cewa duk A sanadin Amana suka hadu da wannan alkhairi,Ciranin Amana ciranin alkhairi,ta yo musu hanyar arziki gaba daya gidan,domin ta hanyar su Alim kadai Alkhairi ke fado musu,

Allah sarki Amana ana nan ana Jin dadi ta sanadinta ita kuma tana can ma ba ita ke Jin dadin ba haka ikon Allah yake.
Saura kwana biyu a fara biki misalin karfe biyar Amana da Umma suka kwado Sallama cikin gidan Baba Sulemanu,
Kaf gidan suna nan ana ta shirye shirye,nan kowa ya tashi da ihu ana rige rigen rungume Amana,Mazan kuma suka tafa tas tas da Amana suna ta kashewa ana dariya,da karfi Amana tace surprise no going back sai ihu yeeeeeee,Amana ta rike kugu tare da juyawa ta furta look at me ? Ya kuka ce heeeeeee wlh a basu wuta,Amana tace ai da girma ya fadi gwara na kwana da yunwa,nan suka hargitse da murna yara da manya Amana ta dawo gaba daya,kowa sai cewa yake I missed u Sis,yaran gida suka hada baki we missed u Anty Amana,murmushi Amana tayi tana daukansu daya bayan daya tana ajiyewa,

Nan fa aka fara labarin bayan rabuwa daga nan suka bawa Amana labarin komai na yadda suka shirya biki,suka bata labarin yadda Angwaye da iyayensu suka taimakesu sosai da kawo agaji,a karshe suka fara bata labarin kaf alkhairan da Alim ke musu,suna fada mata Amana kuma bata San sanda Ruwan Hawaye ke bulbula a idonta ba,
Yana yin wannan taimakon a danginta amma Bai taba tambayarta ba lallai badan ita yakeyi ba don taimakon Allah yakeyi,ba komai hakan ma an gode masa cewar Amana.
Lallashinta akayi sosai harda su Gwaggo,Umma kuwa tuni ta sa kayanta a dakinta ta yi sallah ta huta ta fito wajen kishiyoyinta sukayi hira sannan ta basu hakurin abinda tayi,sannan tayi musu godiyar Kula da yaranta da sukayi,
Gwaggo tace ba komai ai daki har yau nakine tunda yakice ta siya,mukan munji dadinmu arziki sai bunkasa yakeyi ta hanyar mijin Amana nan suka bawa Umma ma labarin,umman Amana ta saki baki tare da cewa ohhh....rashin rabo ya sa na tabi ina ta Shan wahala,iyyyeeeee kuce sai cin jar miya da zaki,Inna tace ah mu sai Sam barka Allah ya kai gaban Annabi,wannan yaro Allah masa Albarka,Hajiyayye kuwa daya matar ta shanye hannu tare da bugar cinya tace ai dadi ya barki baki ga yanda muka canja ba harda dunkuna naki yana wajena kala Uku Alim Bai manta dake ba harda ke,
Umma ta rike haba tace oh kinjiiii na gudu na bar ladana,to ai ta faru ta kare yanzu mun dawo kenan,gwaggo tace af wa yagaya miki barni gabas take gane min hanya yar uwa cewar Hajiyayye.

Amana kuwa Badriyya ta jawo akwati guda na kayan Alim da ya dinkawa Amana,Badriyya kuma ta cika alkawari tace Huzaifa ne yayi mata Amana tayi mamaki tayi godiya sosai.
Tace dan Allah ki fada masa idan kunyi waya to kawai Badriyya tace,

Badriyya a cikin wayoyinta biyu ta bawa Amana daya tasa sim dinta da memory wayace me kyau,sosai yanzu gidan Sulemanu suka kara nutsuwa suke zumunci,suka samu zaman lafiya ba a ware kowa.
Dama sai ba wani wasu zasu gyaru,ranar da wani ke kukan babu wani shi kuma ranar yake samun nasa kudin.
Sai yaba kyan da Amana tayi akeyi,kowa kallonta yakeyi har yan uwanta mamaki sukeyi,Amana ta kara gogewa ta Zama mace sosai,
Wannan bacin ran da ta shiga yasa ta Zama miskila,bata magana irin da,ba fada ba masifa,amma duk da haka me Hali baya fasawa watarana sai an dan gwadashi,

Alim kam rashin Amana da halin da yake ciki yasa ya tashi daga miskili, shuru shuru, mararar magana, ya dawo kasurgumin masifaffe number daya,abu kadan zaka masa ya zage yaci mutuncinta,ko maganar arzikice sai ta koma fada a wajensa,kullum cikin hade rai da bakin ciki yake,
Ko Aabid yanzu tsoronsa yakeyi da yayi abu zai ci Ubansa,Duk yan gidansu basa ma ganin fara'arsa,bare Mum da yake gani ita ce ta jawo komai.
Mum kuwa bata zo Kano biki ba sabo da bata son dangin miji,tace ranar yini zata zo a flight ta koma da yamma.
Chapter 41 · 0% Book details